Showing 57001 words to 60000 words out of 104570 words
Chapter 20 - SARAKI (The Accused Prince).txt
an maƙala mana".
Dariya kowa dake falon yayi ganin yadda Yarima Uthman ke ɓata fuska sedai kafin yayi magana princess ta riga shi da sauri
"Kowa ya tsaya, Abiy kawai ka sa in raba wannan gardamar kasan nafi kowa iya raba faɗa".
Da sauri Abiy ya gyaɗa kansa har lokacin da murmushin jin daɗin ganin haɗin kan iyalin sa a fuskar sa
"Sosai ma princess, na baki dama dan nasan kin fi kowa iya hukunci a nan ciki kuwa har da ni".
Cikin farin ciki princess ta ƙarasa wajen Abiy ta ɗan rungume shi kafin ta janye ta tsaya tana ƙarawa Uthman da Jamal kallo kamar me yin tsakani yayinda falon ya ɗauki shiru kowa na jiran jin me zata ce yayinda Jamal da Uthman duk kowa yayi irin nasa kalar tausayi da fuskar dan tace bashi bane.
"Ina ganin a ɗaga bikin kawai Abiy zuwa lokacin da zan gano waye ya faɗi yadda yake so tsarin bikin ya kasance se a saka sabuwar rana ko?".
A zabure duk suka hayayyaƙo suna faɗin "what" kusan a zabure, gaba ɗaya Abiy dasu Mami suka saka dariya kafin cikin dariya princess take cewa ai duk sun faɗa tun da gashi nan sun shiga tashin hankali dan za'a ƙara lokacin bikin.
"Come on my princess". Abiy ya faɗa yana buɗe mata hannu cike da ƙaunar ƴar tasa da sauri ta faɗa ya rungume ta yana tapping bayan ta kamar me lallashi, murmushi me faɗi ne wanzu saman fuskar sarauniya Rumana ranta yayi fari ƙal ganin yadda Maimartaba yake nuna son autar ta a gaban kowa baya ko jin kunya sedai farin cikin ta se ya ɗara haka da uthman yake wa wannan ƙaunar, nevertheless a haka ma taji daɗi.
A hankali ta tashi daga jikin baban ta ta koma kusa da mami ta zauna kafin ta ruƙo hannayen Mamin suka yi musayar murmushi a tsakanin su.
A hankali murmushin fuskar sarauniya Rumana yake fading har ya ɓace ɓat, in da akwai abinda taƙi jini a rayuwar ta ya biyo bayan alaƙar autar ta da gimbiya Haleematu, ta rasa wane irin sakaci tayi da har shaƙuwa irin wannan ta shiga tsakanin su haka sedai ta danganta hakan da sakewar da tayi mata kasancewar ta auta, a baya bayan nan Allah kaɗai yasan irin ƙoƙarin da take wajen ganin ta janye ƴar ta daga Haleematun sedai hakan ya faskara, zata iya cewa ƴartan tafi sabawa da kishiyar tata fiye da ita wanda hakan ba ƙaramin ciwo yake mata ba, shekaranjiya yarinyar ta dawo daga hutun dolen da ta tura ta gidan iyayen ta duk dan ta samu ta raba tsakanin su sedai tana dawowa a shekaranjiya ko sassan ta bata je ba ta wuce na Haleeman hakan kuwa ya ƙona ranta sosai sedai ita yarinyar ko a jikin ta.
Hira suka cigaba da yi cikin kwanciyar hankali da farin ciki, daga Maimartaba har Mami zuƙatan su na ɗauke da kewa da wani giɓi sedai duk sun yi ƙoƙarin danne ta ta yarda ba wanda ya gano hakan cikin ƴaƴan su.
Hira ce suke yi kan shirye shiryen bikin su Jamal da Uthman ɗin da za'a yi couple of weeks ahead, sati biyu kenan da saka date ɗin bikin which is choosen to be four weeks, yanzu haka suna batun ginin da ake kan ƙara sawa inda amaren zasu zauna ne wanda ke cikin gidan sarautar.
Seconds pass by turning into minutes and minutes to hours, hours to days and days to weeks.
Cikin hukuncin Ubangiji aka ɗaura auren Yarima Jamal Muhammad Hasheem II da amaryar sa gimbiya Fadeela Lamiɗo Turaki, Yarima Uthman Muhammad Hasheem II da amaryar sa gimbiya Sulaim Ibrahim, bidiri sosai ake sha cikin garin Giwa dama maƙwabtan ta, buki ne ake irin na ƴaƴan gata kuma ƴaƴan Sarauta, baka jin tashin komai se na kiɗan ganguna, busar sarewa da kuma algaitu.
A taƙaice dai se da akayi sati ana biki kafin aka kammala komai aka ɗauko amare daga nasu garuruwan, Sulaim ƴar abokin Maimartaba ce ta maƙotan garin su wato garin hayi, gimbiya Fadeela kuwa yar wan Mami ce Wanda shine sarkin garin su yanzu wato masarautar Fulde.
Kowace amarya se da aka fara kai ta ga gimbiya Haleematu kafin aka kai ta wa sarauniya Rumana sannan aka rakata sashen ta daga can, manya manyan sassa ne masu girma daidai gwargwado wanda tun daga ginin zaka san mazauna cikin sa matasa ne masu ji da zamani dan duk wani kayan ƙawata gida na zamani akwai shi a dukkan part ɗin biyu da suka kasance iri ɗaya har fenti se bambancin kayan ƙawar ɗaki da aka zubawa kowacce.
Sashen na kallan juna se dai da tazara me ɗan yawa a tsakani, tun washegarin kawo su suka shiga gaida surukan su inda suka haɗe a nan aka gaggaisa, sedai a kallon farkon gimbiya Fadeela ta gane gimbiya Sulaim zata yi jin kai da izza dan se wani fuffusgar kai take yi tana basarwa wanda hakan halin uwar ta ne ta ɗauke tsaf shiyasa sam basu da jituwa da mami sedai Maama wato gimbiya Rumana wanda tsabar kissa da iya ƙulla tuggu yasa jinin su ya kwanta da juna shiyasa ko da batun auren da me martaba yake wa Uthman ya sake tasowa ta zauna ta faɗakar da ɗan ta irin matar da take buƙatar ya aura wadda take ganin Sulaim takai duk yadda taso, da hilla da komai ta saka masa son Sulaim a ransa aka kuma yi Sa'a itama ta karɓe shi wanda lokacin tuni soyayyar Jamal da Fadeela tayi nisa se kawai aka nema wa kowanne auren wadda ya kawo tunda duk basu da wani aibu.
Matsayin matar wa Fadeela take girmama Sulaim sosai hakan yasa har ta so ta raina ta seda mijin ta yayi jan ido tare da gargaɗin fadeelar kafin abin ya dakata se Kuma aka koma ƴar kowa ba ruwan sa da kowa, dukkan su sha'anin gaban su suke ba me shiga harkar wani se ko ƴar gaisuwar da bata wani tsayi tsakanin su in sun haɗu wajen iyayen.
A hankali rayuwa na tafiya Sulaim ta janye daga jikin gimbiya Haleematu dan hatta gaida tan da take yi se ta daina zuwa se sa'i da lokaci in ta daɗaɗa mata bisa zuga da kitsar da uwar mijin ta tayi mata ita da mahaifiyar ta.
Ko kaɗan abin be ɓatawa Haleematu rai ba dan tun farko da ta gane halin yarinyar taji sam ta fice mata a rai se dai tana ɓoyewa dan gudun ɓullowar ɓaraka cikin alhali, bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen zaunar da ɗiyar ta Fadeela ta mata nasiha me ratsa jiki tare da ƙara tunatar da ita sanin girman na gaba da ita tare da girmama su, muhimmanci kau da kai da son zaman lafiya domin alhamdulillah ta sami Fadeela har ma fiye da yadda ta san ta dan yarinya ce me hankali da sanin ya kama ta.
Tun zuwan Fadeela gidan sarautar suka ɗin ke da Laylah dan dama se hali yazo ɗaya ake abota, tun farkon ganin ta da ita a kilisar Mami Mamin tayi mata bayanin ta da matsayin ta na surukar ta matar Sarakin ta insha Allah, da haka ta fara jan Laylah a jiki se gashi tuni sun ɗinke dan Laylah akwai saurin sabo ga kirki kamar me...............................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, comment and share fisabilillah.
Ouummey 24 (8/18/2022 9:27 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 2️⃣4️⃣
________________________📖 "Karka damu Alh Haladu, ban yi wannan tafiyar ba se dan neman mafita kamar yadda kace min shiyasa nabi duk procedure ɗin da ka sanar da ni wajen samun takardun nan, ina tabbatar maka kwanan kusa zamu mallaki dukiyar da muke ta wannan wahalar a kanta, dan dama mu muka cancance ta ba wata ƴar sa can daban ba, kai abokin sa ni kuma ɗan uwan sa ko ba haka ba?".
Kawu ya faɗa yana ɗagawa Alh Haladu gira cikin sakin murmushi me faɗi, murmushi shima Alh ya saki yana amsawa kawu
"Sosai ma kuwa Sama'ila, ban manta ba lokacin da Safwan na raye haka muka sha wahalar haɓaka dukiyar shi yana zaune taƙamar sa arziƙin sa ne kuma har ya mutu ba wani abu muka amfana dashi ba, kaga kamar ni ba abinda na samu tattare da shi se wani ɗan ƙaramin Companyn robobi, shikam wancan banzan me ruwan ustazai ko Company ɗin be tsira dashi ba se gida da gwangwanin motar da yake ciki kaga kuwa yanzu dan mun nemi haƙƙin mu ai ba laifi muka yi ba ".
"Sosai ma kuwa........" Kawu ya amsawa Haladun yana ɗorawa da
"............yanzu kaga wannan takardun sune makaman mu, muddun muka samu tayi signing akai magana ta ƙare, a da ina ta tunanin hanya mafi sauƙi da zan mallaki dukiyar na rasa amma haɗuwa ta da kai ta buɗe min kai sosai, kaga ba batun kashe ta kamar yadda da na ke hasashen yi kaga yanzu se ta rayu".
Gyaɗa kai cikin gamsuwa Alh Haladu yayi
"Haka za'a yi sedai kasan da zafi zafi akan daki ƙarfe, yanzu daka huta se ka shiga Company ka haɗa cikin takardun da ya zame mata dole ta sa hannu, sedai sefa ka kula dan kar ta gane, kai ta kowace hanya ma Karka bata damar karanta takardun, a ɗauke mata hankali da wani abu me muhimmanci gare ta ta yarda zata saka hannun batare da ta san ta saka ɗin ba".
Sosai suka cigaba da tattauanawa kan tafiyar da suke ganin zata ɓulle musu har tsawon wani lokaci kafin Alh Haladu ya bar gidan kawu zuwa nasa.
****
Rayuwa suke cikin jin daɗi a resort ɗin, kullum da wajen da zasu fita suje cikin garin Sawariya, garin da masana suka tabbatar babu wanda ya kaishi ababen tarihi da jin daɗin rayuwa a kaf ƙasar Hawarya shiyasa kowa da ya ɗan Sami chance to fa burin sa yaje garin yayi spending wasu lokuta dan jin daɗin rayuwar sa da ziyarar wajejen tarihi.
Kwanan su na shida kenan a garin kuma kullum se sun fita bisa jagorancin Asad da Deeq dan shi Asad ɗan asalin garin ne shi kuma Deeq yana yawan zuwa dan a nan ƙanwar mamar sa ke aure.
Yau da dare kam zaman haɗa kayayyakin su suka yiyyi dan gobe ne zasu bar resort ɗin saboda dama seven days suka yi booking, sun so yafi haka sedai dole suka haƙura dan Kisnah ta sanar dasu dole zata maida hankali kan batun dukiyar ta cikin ɗan hutun da suka samu kafin su ɗora batun project.
Manyan shopping bags da suka shiga one of the biggest mall na garin sukayi siyayya, da yawan su tsaraba ce suka yi wa family ɗin su ban da ita da Surayya, ita kam yawancin kayan wa Saraki ta saye su seko kayan yara da ta siya da yawa dan tana son leƙa gidan marayun d ta daɗe bata je ba saboda makaranta da abinda ya faru da Surayya, ragowar kuwa duk nata ne se wasu set ɗin Egyptian jallabiya da ta ga kwana biyu Megado na yawan amfani dasu, burge tan da suka yi yasa ta ciran mata dan har ta auno su a jikin ta, ban da ita kuwa bata ɗaukawa kowa ko tsinke ba.
Ranar basu kwanta da wuri ba saboda hotuna da suka ringa zagaye resort ɗin suna yi, a lokacin kam se da Kisnah ta kasa daurewa ta shige swimming pool ɗin da ke wajen, rabon ta da pool ta manta dan tun farkon dawowar ta da ta shiga wani ashe is not that conducive ta ɗan yi fama da rashin lafiya shine fa Abba Hameed ɗaya daga cikin abokan baban ta and the one she respect much ya hana ta swimming se gashi yau ta kasa daurewa seda tayi.
Ba ƙaramin daɗin pool ɗin taji ba dan se ayyana wa take a ranta da ta san haka yake da tuni kullum se ta shiga.
Kashegari dai suka tarkata ina su inasu suka bar garin Sawariya zuwa garin Manya cike da kewar kyakkyawar rayuwar resort ɗin se dai ga Kisnah ta ƙudure tana kammala project ɗin ta to fa se taje tayi watanni a can.
Ƙarfe ɗaya da rabi na rana suka shiga garin Manya haka kuma suna shigowa gari sukayi sallama da Kisnah dan su gaba ɗaya a motar Meenah suka yi tafiyar ita kuma daban ta zo a tata, Yana yin parking a lot ma'aikatan gidan suka dinga zuwa yi mata sannu da zuwa tana amsa musu cikin sakin fuska da fara'a, taji ba daɗi ganin bata ruƙo musu komai ba se kawai ta fiddo ragowar kuɗin handbag ɗin ta wanda suke da ɗan kauri ta miƙa wa Khamees tace ya raba a bawa Kowa.
Sabuwar godiya suka dinga yi mata har ta samu ta kufce zuwa cikin gida, bata tadda kowa a falo ba haka bata bi takan tambayar ina suke ba ta shige ɗakin ta da sauri saboda gajiyar jikin ta ba kaɗan bace.
Wanka ta sake yi kamar ba ita ce tayi har wanka biyu ba a resort ɗin kafin su taho, riga mara nauyi ta aka tabi lafiyar gado tana ƙure gudun Ac ɗin ɗakin ta da taji bata kai mata ko ina kamar dai ta samu matsala ne.
A can ɓangaren Saraki shima wanka yayi ya canja kaya sedai shi masallaci ya fara shiga ya bi jam'in zuhur ɗin da lokacin ta yayi kafin ya dawo shima ya haye mattress ɗin sa yayi ɗai ɗai ya shiga baccin gajiyar tuƙi da na zaman motar da yayi.
Kiran sallar da ake yi na la'asar ne ya tayar dashi daga baccin, nauyin da yaji jikin sa yayi masa ya sa ya sake wanka da ruwa me ɗumi kana ya fita Masallacin.
Ko da aka idar ya dawo cikin ragowar ma'aikata ya zauna yana amsa sannu da zuwan da tambayar gajiyar da suke masa kafin ya cigaba da sauraren hirar da suke a tsakanin su batare da ya tsoma musu baki ba ƙarƙari yayi murmushi in sun yi abin dariya har wajejen shida kafin ya koma masallaci ya shiga karatun Alkur'ani har aka kira magrib.
Se a lokacin Kisnah ta sami farkawa tana sauke ajiyar zuciya na daɗin da baccin yayi mata tana kuma ɗan yamutsa fuska na jin yadda ko ina na jikin ta ya mata nauyi kamar wadda tayi wani aiki na daban, wanka tayi da ruwan zafi sosai ta haɗa jikin ta kana ta ɗauka da ruwan sanyin da ya zame mata dole ta fito.
Se a lokacin ta tuno da batayi sallar Azahar ba har zuwa magrib hakan ya sa ta koma ta ɗauro alwala ta zura hijab ɗin sallar ta kan towel ɗin jikin ta ta tada Sallah, kamar yadda ta saba gabatar da sallar ta haka yau ma tayi ta ƴar faki ba yawa se lada, lol.
Gaban wardrobe ɗin ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka kafin idanunta ya sauka kan tulin tarin sutturar dake shaƙe kamar zasu yi magana, bin su tayi da ido tana tunane tunane a ranta dangane da kayan, ya zama dole tayi sauyin wardrobe and wannan karon ba zata ɓata kuɗin ta wajen siyan native dress ba da iya saka su take ba dan ba ɗaya daga cikin native dress kana daga atamfa, shadda, ko lace da ta taɓa sawa wnada in bata kuskure ba kusan shekarar su ɗaya yanzu cikin wardrobe ɗin.
Gyaɗa kai tayi tana yadda da shawarar da ta zo mata kafin ta ciri wani robber jeans ta saka tare da ƴar ƙaramar t-shirt ta gyara kan ta cikin yamutsa fuska dan se taje gyaran ka gobe insha Allah.
Gyara ɗakin tayi a gurguje dan yayi ƙura kawai gajiyar da tayi ɗazu ce bazata bar ta tsayawa gyara shi ba kafin ta kwanta, tass ta gyara ɗakin ta saka abun zuƙe datti tai cleaning ɗakin tare da mopping ɗin shi da electric mopper, haka ma falon ta zuwa mini kitchen ɗin ta da bata amfanin komai dashi se sa'i da lokaci in ta Kai mata.
Ƙasa ta sauko bayan ta gama aikin ta da ita dama ke yi duk bayan kwana biyu dan bata yarda wata me aiki ta shigar mata ɗaki tun bayan ɗauke ɗauke da ake mata a ɗakin, zama tayi kan 3 sitter dake falon ta ɗora ƙafafun ta masu ɗauke da soft bedroom slippers tana kishingiɗa.
Sunan Rayya ta fara kira da ɗan ɗaya Muryar da ya saka gaban Mommy faɗuwa dan bata san yarinyar ta dawo ba shiyasa yanzu da taji Muryar ta hankalin ta ya tashi, da sauri ta tashi daga kan royal seats ɗin dake personal falon ta ta fito har ɗan kwalin kan ta na faɗuwa saboda tsabar sauri, so take kawai taje ta ganta da idanun ta ta tabbatar ita ɗin ce ko kuwa.
"Ki kawo min something mara nauyi na ci, am so hungry, and ki haɗo min da milkshake".
"Okay Aunty". Rayya ta amsa Kisnah tana nufar kitchen daidai lokacin da Mommy ta faɗo falon da sauri, turus ta tsaya tana kallon Kisnahn, kenan dai da gaske ita ce ta dawo ɗin, wani irin ɓacin rai ne ya rufe ta dan sati ɗayan da yarinyar bata tare da su ba ƙaramin daɗi suka ji ba, hankalin su kwance suke abinda suka ga dama cikin jin daɗi da walwala da rashin tunawa ƙarƙashin wata fa suke cin arziƙi shine kawai zata wani dawo rana tsaka, to wallahi bazata saɓu ba wannan karon shawarar ƙawayen ta zata ɗauka, duk hanyar da zata kautar da Kisnah daga rayuwar su se ta bita ko dan ita da ƴaƴan ta suji daɗin rayuwa.
Kallon da ta kafe ta dashi cikin tunanin anya lafiyar ta ta faɗo haka kamar an jefo ta kuma ta zo ta tsaya waje ɗaya kamar wata sojiya se huci take