Showing 12001 words to 15000 words out of 104570 words
Chapter 5 - SARAKI (The Accused Prince).txt
ba ta da wani aiki se wannan tunanin dan ma tana ƙoƙarin ganin ta danne wani abin a ranta ko dan ragowar ƴaƴan ta su samu farin ciki sedai wani abun yana gagara dannuwa har ya fito ya bayyana kansa a zahiri.
Duk kirarin da ake yi na isowar Yarima Jamal bata ji ba ba kuma ta san anayi ba har se da jakadiyar ta ta ɗan bubbuga gefen kilisar ta kafin ta yi firgigit ta dawo duniyar mu.
"Allah ya ƙara wa gimbiyar Giwa lafiya, yarima Jamal ke neman iso".
Gyaɗa kanta kawai tayi batare da ta iya magana ba dan a lokacin da zata sami dama to tabbas kuka zata yi.
Cikin takun ƙasaita haɗi da izzar da ta zagaye jinin jikin sa yake takowa cikin falon yayinda bayi da kuyangi ke ta zubewa suna gaida shi, da fara'a yake amsa musu dan Yarima Jamal mutum ne me fara'a da barkwanci haka ko ga talakawan ƙasan sa be kasance me girman kai da ɗagawa be se ko ɗan abinda ba'a rasa ba na jinin sarauta dake yawo jikin sa.
Gaban mahaifiyar sa ya zauna yana tanƙwashe ƙafafun sa kana ya sunkuyar da kansa
"Barka da rana Mamin saraki, gimbiyar Giwa kuma sarauniyar mai martaba, fatan na same ki lafiya".
Murmushi ne ya wanzu kan fuskar sarauniya Haleematu, duk da soyayyar saraki a ranta daban ce amma tana matuƙar so da ƙaunar ragowar ƴaƴan ta suma.
Hannu takai kanshi dake sunkuye ta shafa sumar kansa da ta kasance baƙa ƙirin kuma me tsayi da kuma taushi kamar me kasancewar su jinin larabawa da kuma Fulani.
Hannu yakai ya riƙo na mahaifiyar sa kana ya ɗago yana sakin kyakkyawan murmushi, fatabarakallahu Ahsanul khaleeqeen, tabbas yarima Jamal kyakkyawa ne da ze amsa sunan kyakkyawa a ko ina, haka fara'ar fuskar sa na daɗa ƙara masa kyau da haiba.
"Ina fatan gimbiyar Giwa ta kasance cikin walwala da farin ciki, ya zamo bata da wata damuwa".
"Ina cikin farin cikin sanin ina daku a tare dani yarima sedai zuciya ta baza ta iya daina tunani da damuwa da halin da saraki na ya ke ciki ba".
"Shin ban alƙawaran tawa sarauniya sama mata farin ciki a duk inda yake ba?".
"Bana fatan yarima na yayi abinda mahaifin sa ze yi fushi da shi, kai kaɗai gare ni yanzu dan haka ba zan so rasaka a kusa dani ba in ba Haka ba zuciya ta zata buga ne dan bazan iya jurewa ba".
"Karki damu Mamin Saraki, maimartaba baze taɓa sanin na fita neman Yaya ba sedai in ke zaki faɗa masa, a yanzu haka na shigar da uzurin son barin ƙasar nan zuwa ƙasar Sarbila dan yin wani course a ɓangaren karatu na na tsawon shekara biyu, ki taya ni da addu'a Allah ya sa maimartaba ya yarda domin amincewar sa ita ce komai".
"Addu'a ta na tare daku a koda yaushe, kai da Saraki na har ma da ƙanwar ku da ke gidan aure, Allah ya tsare min ku a duk inda zaku sami kanku ya baku Sa'a da Nasara a rayuwar ku, Allah ya haskaka min rayuwar ku ya kare ku daga sharrin duk wani abin ƙi tare da ku da al'ummar Musulmi baki ɗaya".
Da Ameen yake ta amsa addu'ar mahaifiyar sa zuciyar sa cike da tsantsan tausayin ta, batun yau ba ya daɗe da sanin irin so da ƙaunar da mahaifiyar tasu ke yi musu sedai Saraki daban ne a ranta, ko da yasan hakan be damu ba domin ta na nuna musu so ne equally haka kuma dole taso Sarakin tunda shine ɗa na fari da ta fara haifa haka kuma ɗan da ke tsananin so da ƙaunar ta tare da yi mata biyayya matuƙa.
Sallama yayi mata ya fita daga kilisar ta ya wuce zuwa ɓangaren sa, alkyabbar jikin sa ya zare kana ya rage kayan jikin sa ya kwanta kan gadon sa ya shiga wassafa yadda ze fara neman ɗan uwan sa, ba wai ze dawo dashi gidan sarautar bane, a'a su san inda yake kawai suke so da kuma lafiyar shi ko hankalin su da na mahaifiyar su ya kwanta.
Ƙarar wayar sa ce ta katse masa lissafe lissafen sa, janyo wayar yayi yai picking, lumshe ido yayi lokacin da sassanyar Muryar ta ya daki kunnen sa.
"Barka kadai lovely, hope kina lafiya".
"Lafiya na ƙalau Alhamdulillah dear, ya su Mamin yaya Saraki".
"Tana lafiya lau Alhamdulillah, ya nan wajen su Mama".
"Itama suna lafiya, yau ban ji kiranka ba shine na kira inji ko lafiya".
"Lafiya lau lovely nayi busy ne kawai, dama ina so in shigo muyi magana".
"Okay to in jiraka kenan yau".
"Se gobe dai, yau zamu zauna da maimartaba".
"A fito lafiya, Allah ya ƙarawa Sarkin Giwa lafiya".
"Ameen, Ameen".
Kashe wayar yayi yana komawa kwance yana saƙe saƙe, hasashen yadda zasu ƙare da maimartaba yake bisa saƙon kiran da aka isar masa daga Sarkin, yana haka har bacci ya ɗauke shi.
_______________
Tsaye yake bakin shago yana miƙa wa Faruq ɗaya daga cikin abokan aikin sa a shagon takalman mata yana miƙa wa wasu ƴan mata suna gwada wa dan zaɓar wanda yayi musu, a sati da kwana biyar da zuwan Saraki shagon sun ƙara samun customers sosai Musamman ƴanmata wanda yawanci in suka zo haka za suyi ta ƙoƙarin jan Sarakin da hira sedai kallo basu ishe shi ba balle ya tanka musu, haka za suyi ta zuba sedai ragowar yaran shagon su amsa musu amma ba hakan ke hana su dawowa gobe ba.
Yanzu ma haka yarinyar se wani iyayi take yi amma Saraki ko kallo bata ishe shi ba dan wallahi shi ko kalar ta baze iya cewa gata ba, ita da Faruq take ta zubar ta wanda yawanci tambaya ce take masa game da Sarakin yana bata amsa iya wadda ya sani wata kuma yayi dariya har ta gama ta wuce.
"Kar ka kuma sanar da kowa komai a kaina Faruq, bana so".
Dariya Faruq yayi yana sara masa tare da faɗin Yes sir, murmushi kawai Saraki yayi da ba kowa ze San yayi ba, tuni su Faruq suka gane halin sa na rashin son magana da hayaniya shiyasa ba sa wani damuwa dan sun yi masa magana yayi murmushi ko body language.
Yau da wuri suka tashi kasancewar juma'a, wanka yayi yana komawa dan Allah yasani yana ƙoƙari da haƙuri da rashin wanka da yawa da yake yi yanzu a rana, singlet ya bari da dogon wandon jeans ɗin jikin sa ya ɗau Alqur'ani ya ɗora da bitar da yake yi dan baya son haddar sa ta Sami matsala.
Haka yake rayuwar sa kullum tsawon sati biyu kenan da zuwan sa garin manya, da safe yayi wanka ya dafa tea ya karya, ƙarfe tara ya wuce kasuwa, da rana baya cin komai dan baze iya cin abincin kasuwa ba, ƙarfe shida zuwa da rabi ya dawo gida, wanka yake fara yi se yai kwanciyar sa ya huta ko ya yi karatun sa kamar dai yau daga nan baya fita se masallaci magrib ya jira ayi isha sannan ya dawo daga nan kuma se gobe ze fito da asuba yayi Sallah.
______________
Ƙarfe sha biyu sannan suka fito daga Library, dukkan su sunyi wujiga wujiga banda Kisnah dan ita in tasa kanta zata yi abu to fa duk wuyar sa ita bata gani.
Motar Kisnah suka shiga suka fita duk da kowacce da tata ta zo, abinci suka fita ci dan basa cin komai na makarantar, EAT WELL restaurant suka je, vip suka shige akayi serving ɗin su abinda kowacce ke so suka ci suka sha kafin suka fito.
Kamar ance ta ɗaga kan ta ta sauke idanun ta kansa, zaro ido tayi tana faɗin wow tare da kwass da gudu ta nu feshi, bata yi wata wata ba ta faɗa kansa.....................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
*Vote, comment and share fisabilillah*
Ouummey 07 (8/1/2022 3:23 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 7️⃣
___________________📖 Sak saurayin da ta faɗa kan sa yayi dan it's unexpected kafin ya ɗan zare ta daga jikin sa ya ja baya kaɗan, zare Ido yayi ganin ta kafin unbelievably ya nuna ta Yana faɗin sunan ta
"Queen, Kisnah".
Da ƴar dariyar dake fuskar ta ta furta sunan sa Shima
"Deeq".
A sittin ya sake fisgota jikin sa ya ƙanƙame yana sakin dariyar farin ciki kamar yadda itama ta kasa rufe bakin ta, ƙara zare ta jikin sa yayi ya tsura mata Ido har se da ta hura Masa iska a bakin sa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya sake rungumar ta, wannan karon da kan ta tai breaking hug ɗin kana ta ja kujerar gefen sa ta zauna tana gyara zaman rigar ta da ta ɗan janye zuwa cikin ta.
Zama Shima yayi a kujerar sa ya sake kafe ta da Ido Yana kallo kamar irin Wanda ya Sami film ɗin da ya daɗe Yana jira, ɗan haɗe rai tayi tana dukan table ɗin gaban su
"Zaka Fara ko Deeq bayan kafi kowa sanin bana San wannan ƙure kallon ko".
"Uhm..hmmm...am..am sorry Kissy, kawai na kasa daina mamaki da jin daɗin ganin ki ne, we missed you so badlyyyy".
Ya ƙarashe faɗa Yana Jan ƙarshen kalmar badly ɗin, murmushin ta me cike da aji tayi kafin a ɗan shagwaɓe itama ta mayar Masa da amsa
"I missed you people so much also, it's a kinda feeling I gat at that time, I thought of nothing but home, my country, my land, my pride and my happiness, and as you can see am enjoying it here".
Gyaɗa kansa yayi cikin yarda da abinda tace "Sure I believe you're enjoying it, but what about we people, you don't have idea how we felt at the time, you leaving without even saying a goodbye is something we didn't expected".
"And am sorry for that, nasan in na faɗa muku ba zaku bar ni in tafi ba that's why I choose to just disappear without your consent".
"Allah ya shirya ki, so bani labari, how's life here in naija to you bayan nasan kin Saba da rayuwan Canada".
"The feeling of living in my home is as sweeter as honey, that's what I lack in Canada, but I missed all those partying, clubbing and dancing like hell though am trying to catch up here".
"I see, those girls?.
Ya faɗa pointing at su Meenah da suke cin abincin su hankali kwance dan sun Saba irin haka da Kisnah ɗin,
"Friends". Ta Bashi amsa a taƙaice, nodding yai Shima without saying anything dan daga yadda ta amsashi ya tuna Kisnah fa bata son yawan tambaya da bin ƙwaƙƙwafi akan personal life ɗin ta, miƙewa tayi tana duban designer and fashionable wristwatch ɗin dake tsintisyar hannun ta
"We see some other times Deeq, will be having some lectures now".
"No am not letting you off until you gave me ur digits, kaɗan daga aikin ki ki ɓace min a garin nan".
Ƴar dariya tayi a gayance da ya bayyana wushiryar ta dake ƙara Maya kyau kafin ta shiga karanta Masa number ta Yana shigarwa wayar sa, hannu ta ɗaga masa bayan ya gama sawa ta wuce wajen su Meenah da zuwa lokacin su ma sun gama ita suke jira, Surayya ce ta ɗauka mata nata abincin da akayi packaging cikin wrapping paper me kyau duk da a cikin wani ƙayataccen takeaway take dan bata Sami cin abincin ba tana ta magana da Deeq.
Makarantar suka koma dan suna da lectures biyu kafin su tashi, kamar yadda ya zame mata halayya da ɗabi'a wajen mai da hankali kan karatu yanzu ma haka tayi dan bata sake ko kallon su Hameedah ba se da suka fito daga theatre dan babu interval a jere ne lectures ɗin, wani na fita wani na shiga.
Ƙarfe shida biyar saura suka fito, kowa ka kalla fuskar sa gajiya zaka karanto kwance kanta wanda su Kisnah na ɗaya daga cikin su, na lokacin ba abinda take buƙata se wanka dan wani irin danƙo da ƙaiƙayi take jin jikin ta na mata, haka yasa hannu kawai ta ɗagawa su Hameedah da suka ƙarasa wajen motocin su kafin ta shige tata ta fige ta a ɗari ta fice a makarantar.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta ƙarasa gida dan ba ƙaramin gudu ta ɗiba ba a titin, base nace komai ba kun dai san yadda tuƙin ta yake, bata tsaya bin yadda taji parlon nasu yau shiru ba hayaniyar kowa ba ta haure saman ta, tun a nata ƙaramin parlon ta fara cire kayan ta tana watsarwa har ta ƙarasa bedroom lokacin ba abinda ya rage a jikin ta ta faɗa toilet.
Sassauƙar ajiyar zuciya ta sauke bayan ruwan sanyin ya ratsa fatar jikin ta ya shige ƙashi da jinin jikin ta, tun tana yarinya Allah ya jarabe ta da son ruwan sanyi wajen yin wanka, ba ƙaramin sanyi za'a yi ba da zaka ga Kisnah ta yi wanka da ruwan ɗumi sedai ko ta gasa jikin ta da na zafi amma fa in ta fito se ta watsawa jikin ta na sanyin nan, abin a jinin ta yake shiyasa da yawan ruwan sama da ake yi yake ƙarewa a kanta dan da taga hadari zata canja kayan ta zuwa rigar wanka ko shimi iya cinya ta fita backyard ta fara wasa a ruwan har se anyi an ɗauke a kanta kafin ta koma ta canja kaya.
Shimi ta saka me ɗan tsayi da ta tsaya iya rabin cinyar ta ragowar kuwa na waje se ƙyalli fatar ta take yi tana ɗaukar ido, tun a kallon farko zaka san ba ƙaramin laushi da santsi zata yi ba shiyasa in ta saka kayan da basu rufe mata jiki ba zakaga maza na ta ƙure mata kallo suna tanɗar baki tun bare ma ƴan bariki da suka san sittin mata.
Parlon ƙasa ta sauka ta wuce kitchen inda ta sami Rayya tana girki cikin nutsuwa, gaishe ta tayi ta amsa a sake kamar yadda ta saba dan bata kasance cikin masu wulaƙanta ƴan aiki ba.
"Ya naji gidan shiru, ina mutanen gidan?".
A ladabce Rayya ta bata amsa
"Duk basa nan, ɗazu Hajiya babba ta fita da trolley a hannu ita kuma Aunty maigado taje makaranta, yaya Awwaf kuma ........".
"Wannan surutu baki Rayya Allah ya yaye miki, kawai se kice min basa nan shikenan amsar tambaya ta, in Kuma na nemi ƙarin bayani se ki faɗa min ina suka je".
Dariya Rayya tayi
"Da ke kaɗai nake surutun nawa ai Aunty Kisnah, Allah Baki na har ciwo yake yi na rashin magana a gidan nan".
"Toh Allah ya yaye miki, nidai yau a gajiya nake bare in biye Miki , zuba min abinci in tafi dan a gajiya nake".
"Amma gaskiya Aunty Kisnah wannan yaya Awwaf ɗin ɗan Air ne".
Rayya ta faɗa tana zuba mata fried spaghetti da tayi wadda taji kayan lambu sosai, zare kyawawan oily brownish eyes ɗin ta masu kama da na mage Kisnah tayi
"Faɗa min me yayi miki ni Kisnah?".
Hankali tashe tayi maganar dan ita kan ta shaida ce Awwaf ƙwararren ɗan iska ne da bata fatan ace yayi wa Rayyan wani abu dan bazata so a ce a gidan ta aka ci mutuncin wata ba.
"Laah ba fa abin da yayi min kawai dai naji shi yana waya ne yana batsa".
Ajiyar zuciya Kisnah ta sauke
"Kome yake yi ba ruwan ki, ki kama kanki kin ji ko, bana san ko da wasa in ji wani abu ya haɗa ki dashi bayan gaisuwa, na faɗa miki".
"Insha Allah Aunty".
Karɓar abincin Kisnah tayi ta juya ta fita daga kitchen ɗin batare da ta kuma cewa Rayya komai ba,da ido Rayya ta raka bayan ta cikin kallon ƙauna, ba ita kaɗai ba duk ma'aikatan gidan haka suke san Kisnah dan bata da raina na ƙasa da ita, bata da wulƙanci balle rashin mutunci, barta dai da yawace yawacen ta, itace bata club, cinema, park, hotel da guest in, kullum tana da gurin zuwa dan bata fiye zaman gida ba se dai in tana da school wacce itace abu mafi muhimmanci a rayuwar Kisnah ɗin.
A duk yadda ake mata kallon karuwa ko ƴar iska har yau zuciyar Rayya ta kasa yarda da cewa hakan take, ita tana hango kamewa da mutuntaka a idanun Kisnah ɗin da jama'a suka kasa gani, tana ji a zuciyar ta sunan karuwa be dace da Kisnah ba duk kuwa da ayyukan ta na zahiri sun tabbatar mata da sunan a idanun jama'a sedai ita har yau zuciyar ta takawa aminta da hakan.
Plate ɗin abincin ta ajiye kan carpet ɗin da ke tsakiyar ɗakin tare da zama ta ɗau spoon ɗin, shiru tayi cikin don tunawa da wani abu da tayi kafin fara cin abinci sedai ta kasa tunawa hakan yasa ta fara cin abincin ta cike da nutsuwa, sedai tayi kusan spoon uku sannan ta tuna da takeaway ɗin da Meenah ta saka mata cikin mota, ɗan taɓe baki tayi ta cigaba da cin na gaban ta , ko rabi ba tayi ba ta ajiye spoon ɗin tana nishi jin yadda cikin ta ya cika, mamaki sosai ya kama ni dan ba wani abinci bane na zai a gani gaba ɗayan sa, kun dai san yadda ƴan gayu keyin zubin abincin su wai amma a haka rabi kawai taci.
Seda ta ɗan huta sannan ta jawo robar natural ginger drink dake ajiye gefen ta wanda ita take haɗa kayan ta ta zuba cikin fridge ɗin ɗakin ta saboda irin haka in taci abincin ta, sha tayi to her satisfaction sannan ta ajiye, laptop ɗin ta ta jawo ta shiga bincike kan harkokin karatun ta wanda tayi zurfi a cikin sa sosai ya kuma ɗauke ta lokaci me tsawo.
Se gab da magrib ta ajiye sannan ta canja kayan ta zuwa na training ta fita gudun yamma da take yi duk lokacin da take gida, riga da wando ne sport wears dark blue color masu