Showing 75001 words to 78000 words out of 104570 words
Chapter 26 - SARAKI (The Accused Prince).txt
kasancewar da sanin sa aka bashi takardun ya aka bayan sun masa alƙawarin maƙudan kuɗaɗe.
Wani irin mazari jikin manager ya ɗauka ganin takardun a hannun Saraki yana jujjuya su tare da sake karanta su kamar wanda aka bashi aikin haddar su dan se da ya zamana ya haddace every single word dake kan papers ɗin nan, a hankali manager ya fice daga office ɗin batare da ya bari Saraki ya lura da shi ba, jiki na rawa ya zaro wayar sa ya shiga sanar da kawu halin da ake ciki bayan ya sami waje ya laɓe wanda daidai lokacin Saraki da yaga fitar sa ya biyo bayan sa da takardun a hannu ya na neman sa dan ya bashi tun kan yayi nisa.
Daidai wajen elevator yake jiyo magana ƙasa ƙasa dan haka ya ƙarasa a hankali ya ɗan laɓe dan jin waye ke waya haka cikin rawar murya alamun rashin gaskiya ga kuma ɓuyan da yayi wajen da yake tunanin ba wanda zeje dan elevator ɗin tsoho ne an dena amfani dashi so bame zuwa ta wajen se ta kama.
"Kayi haƙuri Alh ba laifi na bane, na kai takardun kamar yadda kace wallahi ban san yaya akayi aka samu wannan matsalar ba, kuma alamu sun nuna ita bata karanta ba tunda ta saka hannun wannan sabon ma'aikacin nata ne na samu yana dubawa".
Shiru yayi alamun saurare daga ɓangaren da yake kafin ya cire wayar faga kunnen sa yasa handsfree da alamun baya ji sosai kenan sedai ya rage Muryar yakai ta can ƙasa
"Lallai manager baka san da wa kake wasa ba , bari kaji in faɗa maka wallahi ko da wasa naji sunana ya fito a wannan batun se ka gwammace mutuwar ka kan rayuwar da zan sa kayi, kar kuma ka manta da nasan gidan ka, ƴaƴa huɗu ga kuma tsaleliyar mata, Har yau Sama'ila na ke kuma kasan abinda zan iya aikatawa".
Gumi manager ya shiga sharewa jin kawu ya kashe wayar sa, da sauri Saraki ya lallaɓa ya bar wajen sedai tuni manager ya ganshi dan yaji sautin takalmi kamar ana tafiya a hankali, wani tashin hankalin manager ya Kuma shiga haka kuma be yi ƙasa a gwiwa ba ya sake kiran kawu ya sanar dashi.
******
"Ya zama dole su mutu a yau dukkan su, daga ita har ɗan iskan yaron dake neman zame mana barazana, a yau zasu mutu base gobe ba dan a kan dukiyar nan zan iya yin komai akan kowa, dama na kawo waccan hanyar ne dan mu bar ta da ranta tunda kuma bata san hakan zata tafi tabi mattacen uban ta yau".
Gyaɗa kai kawu yayi cikin yarda da batun Alh Haladu kafin ya zaro wayar sa ya shiga danna kira, within minutes aka ɗauka ya kuma bada umarnin kisa ga duk wanda ke cikin motar su Kisnah bayan ya bada lambar motar ya kuma haɗa da location ɗin da suke da kuma duk Possible titin da zasu iya bi su kai gida.
*******
A rikice ta dawo K&S furnitures saboda kiran ujilar da Saraki yayi mata, a parking space ta same shi tsaye yana jiranta fuskar sa ɗauke da wani yanayi, komawa mazaunin ta tayi ya shiga driver's side tare da tashin motar ya fice, seda ya hau kan titi kafin ya ɗora mata takardun a kan cinyar ta, da kallo ta bisu kafin a hankali ta ɗauka ta shiga karantawa, cikin tashin hankali ta ɗago cikin don yi masa magana sedai ko kafin ta kai ga hakan wata babbar mota ta zo ta daki tasu, hantsila wa motar su ta shiga yi kafin cikin ikon Allah ta tsaya daidai hakan yasa wata babbar motar yowa kan su sedai tuni Saraki da ya fahimci an shirya musu ne ya figi motar cikin wani irin azababben gudu hakan ya sa itama babbar motar rufa musu baya..............................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, comment and share fidabilillah.
Ouummey 31 (8/22/2022 9:20 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 3️⃣1️⃣
________________________📖 Tsawon lokaci suna zuba azababben gudu kan shimfiɗaɗɗen titin garin har suka fara ficewa daga cikin ainahin garin suna dosar daji ka, juyawa yayi ya kalli bayan sa ta cikin mirror ɗin motar, wani irin ƙure speed yayi ganin har lokacin babbar motar na bin su a baya itama cikin nata gudun.
Cikin tashin hankali ya kallo gefen da Kisnah take zaune kamar mara rai tsabar shock da ruɗanin da take ciki
"Ki ɗaura seat belt ɗin ki da sauri, am increasing the speed now dan za su iya cimma na".
Se lokacin ta saki wani Gwauron numfashi kafin a gigice ta kalli bayan su lokacin tazarar dake tsakanin su da babbar motar Ba wata me yawa bace, hannu na rawa ta shiga ƙoƙarin saka belt ɗin wanda se da ƙyar ta iya saka shi, aikuwa take ya ƙure gaba ɗaya speed ɗin motar ya shiga tsufa azababben gudu, fit fit haka motar take wucewa kamar walƙiya hakan yasa nan da nan suka yi wa babbar motar ɗan nisa duk da alamu ya nuna shima matuƙin ta ya ƙure nasa gudun, haka suka ringa shige dajijjika kamar ba zasu ƙare ba amma ba su da alamun tsayawa, to su tsaya yin me ma.
Zaro ido yayi cikin sabon tashin hankali lokacin da ya kula da tankar mai da ta tare titin da alamu ta lalace ne a tsakiyar hanya kuma be lura ba se da ya zo daf, cikin ɗimuwa ya shiga ƙoƙarin ganin ya tsayar da motar amma inaa taƙi tsayawa saboda mugun speed ɗin da ya ƙure, hasbunallah wani'imal wakeel kawai ya shiga maimaitawa dan ya tabbatar se sun haɗu da wannan tankar haka kuma da sauri ya sa hannu ya fisgo Kisnah cikin jikin shi ya rungume cikin son kare ta ko yaya ne.
Wani irin ƙara ce ta tashi lokacin da motar su ta daki wannan tankar haka kuma tayi baya kamar wadda aka tura da mugun gudu kafin ta shiga hantsilawa tayi gefen dajin dake Wajen, seda ta jujjuya sosai kafin ta tsaya, mintuna ƙalilan Saraki ya fara ƙoƙarin ganin ya fito daga motar cikin dauriya da son ganin mutanen cikin waccan motar basu iske su a wajen ba dan yasan yin hakan tamkar ƙarshen rayuwar su ne yazo.
Da ƙyar ya iya fita daga cikin motar kafin ya samu yin dabarar da murfin ɓangaren sa ya buɗe ya zaro Kisnah da take a sume jini na bin fuskar ta, kallon ta ya tsaya yi cikin tunanin yadda de yi da ita dan tabbas baya tantama hannun sa na dama a karye yake dan yana iya jin yadda yake masa lilo haka kuma yayi masa nauyi sosai, ƙarar dosowar babbar motar wajen su yasa da sauri ya saka hannun hagun sa ya ciciɓata da ƙyar ya saɓa ta a kafaɗar sa kafin ya shiga gudu da ita ta cikin duhun ciyayi da bishiyun gonar da suka faɗa, be ko yi wani nisa ba motar su ta kama da wuta hakan yasa ya dakata gami da juyowa ya kalle ta.
Yadda take ci da wuta ya saka shi furta alhamdulillah dan yasan ba dan rahamar Allah ba da tuni suna cikin motar yayinda wutar zata tashi ta cinye dukkan wata tsoka da ƙashi na jikin su.
Jin kamar sautin Muryar mutane yasa ya juya da sauri ya cigaba da tafiya da ita cikin tsananin dauriya dan ba ƙaramin jin jiki yayi ba, wani irin jiri jiri yake ji sanadin dokuwa da kan sa yayi lokacin da motar ke tumble sedai aka ce wai shi gudun ceton rai da ban ne wanda hakan ne yasa har yake iya daurewa dan ganin sun tserewa magautan su.
*****
Can ɓangaren ƴan hirer killers ɗin da kawu ya turo kuwa suna ƙarasowa gab da wannan tanka suka tsaya tare da firfitowa dan sun hango ta tunda nesa, wajen da motar su Kisnah ke ci da wuta suka ƙarasa don tabbatar da su ne ɗin ko wasu ne sedai number motar su dake kan ci da wuta ta tabbatar musu da sune dan ga tambarin KS nan dake bayan duk wata mota tata, duk da ganin motar na ci da wuta basu fasa bincika gonakin dake gefe gefen hanyar ba dan tabbatar da sun mutu basu sami kuɓuta ba.
Ganin basu ga wani alama dake nuna sun kuɓuta ba yasa suka koma motar su suka zauna har se da gaba ɗaya motar ta ƙone ƙurmus kafin suka juya bayan sun ɗauki hotunan motar lokacin da take kan ci, number motar da kuma lokacin da ta gama ƙonewa gaba ɗaya.
*******
Gudu sosai yayi kafin ya fara tafiya a hankali kan sa na juya masa saboda tsabar jirin da yake ɗiban sa, tun yana iya tafiya har ya kasa ya nemi ƙarƙashin wata bishiya da yake ganin ta dishi dishi ya kwantar da Kisnah tare da zama kusa da ita yana maida numfashi ɗai ɗai cikin tsananin azaba da jigata.
Da hannun sa me lafiya ya dafe kan sa da yake jin kamar ana masa ihu a ciki, tun yana gani dishi dishi har ganin sa ya ɗauke gaba ɗaya ya daina gani da fahimtar komai.
*********
A hankali ta fara buɗe idanun ta tana yi tana rufewa tare da buɗe wa saboda yadda take gani uku uku har ganin ta ya daidai ta.
Cikin mamaki take bin wajen da take kwance da kallo, jar ƙasa ce sosai akayi ginin da ita dan gata nan a fili ana iya ganin ta, haba ɗaya ginin da akayi da ita be fi kamu biyar ba se kuma wasu karare ko yayi zata ce ne da aka haɗa aka tashi ɗaki dashi, a ɗan tsorace ta nemi miƙewa sedai da sauri ta dafe kanta tana faɗin
"Wash". Saboda zafin da ya ziyarci kan nata a daidai lokacin ne kuma komaɗaɗɗiya kuma yamutsattsiyar mata ta shigo ɗakin hannun ta ɗauke da wani ƙoƙo, wata irin zabura Kisnah tayi da har yasa taji kamar kanta ze faɗo saboda nauyi ga kuma zafin da ya ziyarce ta sedai bata ko kula hakan ba ganin wannan aljanar tana nufo ta.
Da sauri matar ta ƙara sa matsowa wajen Kisnah tana ajiye ƙoƙon hannun ta kan wani ɗan tudu dake gefen su, da hanzari ta saka hannun ta da ƙashi ne kawai da fata ba ko ɗigon tsoka (a ganin Kisnah ) ta ruƙo ta ganin tana neman fita daga ɗakin, wani irin ihu Kisnah ta saki jin matar ta riƙe ta haka kafin ta sami zarafin magana matar ta shiga yi mata magana cikin wata gurɓatacciyar Hausa da ba wani ganewa take ba
"Kayi haƙuli yalo, baka da lashiya magani nak kawo maka kashi".
Ai ina Kisnah bata ma tsaya ta saurare ta ba balle ta fahimci me take son cewa se ƙoƙarin ƙwace hannun ta kawai take tana zarar idon tashin hankali, cikin zuciyar ta kuwa bata bar tunani ya akayi ta zo hannun wannan aljanar ba, ganin fa bazata tsaya ba gashi maganin na neman bushewa yasa matar ta ɗan ɗaga murya ta ƙwala kiran
"Bingel".
"Na'am". Wata ƴar matashiya ta amsa tana shigowa cikin ɗakin, kallon ta mayar tayi kafin tayi mata maganin cikin wani irin yare aikuwa da sauri yarinyar ta ƙaraso ta kai nata hannuwan da bambancin su dana tsohuwa zance ko dattijuwa ce kaɗan ne, aikuwa se gashi sun danne Kisnah ta kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi, sosai mamakin yanda waɗan nan matan masu matuƙar siran ta kamar me suka iya danne ta haka har takasa motsi.
Ƙwaryar da matar ta shigo da ita ta janyo ta dangwalo wani koren abu cikin wata leda kamar mai kamar kuma ruwa me ɗan kauri ta shiga shafawa Kisnah kan goshin ta zuwa cikin kan ta kaɗan, runtse ido kawai Kisnah ta ke yi cikin tsananin zafi dan yarinyar da aka kira da Bingel ta danne mata baki da tafin hannun ta ɗaya saboda tsabar ihun da ta ke kurma musu.
Seda suka gama shafa mata maganin kafin Bingel ta cire hannun ta a bakin Kisnah, da sauri kuwa ta tofar da miyan da ta tara jikin rigar Bingel ɗin sedai ko kallon ta bata yi ba balle ta nuna ta ji haushi se ma wata ƙwarya da bata san yaushe aka shigo da ita ba da Bingel ɗin ta miƙawa matar nan suka kuma matse mata baki suka ɗura mata kafin suka sake ta, a tamanin ta duro daga kan abinda suka kwantar da ita da bata ma tantance mene ne ba ta shiga kakarin amai sedai ko ɗigo hasalima wahalar da kanta kawai tayi dole haka ta haƙura ta koma ta zauna tana hararar Bingel dan ita dattijuwar suna gama ɗura mata maganin ta fice.
Murmushi Bingel ta sake ma Kisnah da yasa tayi kamar wata zombie a idanun Kisnah duk da kuwa Bingel kyakkyawar bafulatanar daji ce sedai a idanun Kisnah ita bata ga wani kyau ba se ma tsorata ta da take yi.
A can wajen ɗakin kuwa dattijuwar na fita ta tadda wani yamutsattsen farin bafulatanin daji sedai yafi matar nan kyan gani sosai, murmushi ta sake masa da dole wanda be saba ganin su ba ya tsorata sedai a wajen su su murmushi ne hakan, da ɗan sauri dattijon ya matso kusan matar
"Nene Ina fatan kin shafa mata kuma tasha maganin".
Ya faɗa cikin cikakkiyar Hausar sa da tafi ta su matar da ya kira Nene nesa ba kusa ba, gyaɗa masa kai Nene tayi tana nuna masa ƙwaryar hannun sa
"Ƙin sha yalon can yayi sheda muka masa danna ni da Bingel, na shafa ma mun sha masa, aradu yalon kwai ƙarfin kai arɗo".
Ɗan murmushi arɗo yayi cikin fahimtar matar tasa, taurin kai shine ƙarfin kai a wajen su, kallon ta yayi yana faɗin
"Tun da ta sha ai da sauƙi, yanzu ki haɗo min wani na bawa yaron can dan shi har yanzu be farko ba kuma da alama ya fita shan wahala".
"Tau arɗo".
Ta faɗa tana shiga wata bukka nan gefen inda suke tsaye, tsawon lokaci tana ciki kafin ta fito da ƙwaryar da ta shiga a hannun ta ta miƙa wa arɗo, karɓa yayi ya juya ya shige wata bukka da ke ɗan nesa da wadda Kisnah ke ciki seda ya duƙa sannan ya iya shiga ciki, itama kamar waccan an yi mata ginin jar ƙasa kamu biyar kafin aka ƙara sa da asabari da kuma ya yume ya yumen su.
Kwance kan wani gadon kara da aka shimfiɗawa wani tsumma na hango Saraki, gaba ɗaya kamannin sa sun canja dan ƙafar sa ɗaure take da wani tsumma bayan an zagaye ta da karare haka ma hannun sa na hagu, da sallama dattijon ya shiga ɗakin yana ƙara sa gaban Saraki ya tsaya tare da bin sa da kallo na wasu daƙiƙu sannan ya ajiye ƙwaryar hannun sa ya ƙara sa wajen Saraki, hannu yasa ya ɗago ƙafar ya shiga kallon tafin ƙafar da yayi jajir dashi ga kuma alamun cuwuka sosai a jiki, hannu yasa ya lakato wani mai cikin wata ƴar jakar fata dake jikin sa ya shiga shafawa a tafin ƙafar, seda ya shafe ko ina kafin ya saki ya matsa yana taɓa ƙaurin sa da yake ɗaure da kararen, se aya taɓa sosai sannan ya gyaɗa kansa tare da yayyafa wani farin Ruwa kan gurin sannan ya tashi.
Wajen hannun ya matsa ya kama hannun ya jinjina shi cikin nasa kafin ya ajiye a hankali bayan ya ɗan jijjiga shi, a hankali ya sunkuya ya kai bakin sa ya shiga tofa abinda ban sanu ba kan hannun, koren magani irin wanda aka shafawa Kisnah ya lakata ya shafa masa shima a kansa kafin ya tashi ya fita bayan ya sake bin sa da kallo.
******
A can wajen su kawu kuwa duniya sabuwa bayan sun ga hujjojin da yaran su suka basu na shedar mutuwar su Kisnah, wani ɗan ƙwarya ƙwaryar liyafa ranar suka yi a tsakanin su shida Alh Haladu.
Seda aka kwana aka wuni da faruwar lamarin kafin ya shigar da ƙorafi kan ɓatan Kisnahn yana me nuna tsantsar damuwa da tashin hankali Wada da ƙyar ƴan sandan suka sami lallaɓashi ya bar police station ɗin bayan an barbaza jami'ai cikin garin manya dan nemo inda take.
Ranar farin ciki wajen su Mommy kamar sallah ko ma fiye duk da so tayi su wulaƙanta rayuwar ta sedai ko a hakan ma duk ɗaya dan haka ta shiga addu'ar kar Allah yasa Kisnahn ta bayyana, haka ƴan sanda suka ɗin ga shiga lungu lungu neman ta amma ko alamar ta, ba wani club, hotels ko cinema dake garin manya da jami'ai basu shiga neman ta ba amma duk ba wani labari, cikin ƙanƙanin lokaci gari ya ɗauka da batun ɓacewar Kisnah, kiran wayoyin da ake wa su Meenah da su Surayya na wai jaje yasa suka san meke faruwa a ranar kuma suka haɗu gaba ɗaya suka tafi gidan su Kisnahn sedai ba ƙaramin rashin mutunci Mommy ta shuka musu ba dan ko barin su su zauna bata yi ba ta shiga jifan su da munanan kalamai har tana neman ɗora musu alhakin ɓatan Kisnahn, al'amarin be musu daɗi ba haka dole suka tarkata ƙafafun su suka fice daga gidan sedai basu koma gida ba neman ta da suka shiga yi a wuraren da suka san suna zuwa.
A kwana na uku da ɓatan ne kawu ya shigar da batun wai yana zargin driver ɗin ta ne ya sace ta, nan fa lamari ya canja aka shiga neman Saraki ruwa a jallo sedai rashin sanin inda za'a iya samun sa ya sa dole aka taƙaita binciken bayan an saka jami'ai a ko wani titi dan bincike duk motar da tazo wucewa.
Ranar da suka kwana biyar da ɓata ne aka samu rahoton samun ƙonanniyar motar