Showing 48001 words to 51000 words out of 104570 words
Chapter 17 - SARAKI (The Accused Prince).txt
se be sake cewa komai ba kawai ya tashi motar ya fita daga gidan sedai a lokacin fuskar sa kamar wani mala'ikan ɗaukan rai tsabar yadda ya haɗe ta, har suka je be sake kallon gefen da take ba haka itama dan taga in tayi sanyi neman sa ta dole yake yi.
Sosai partyn yayi musu daɗi ya kuma ƙayatar dasu, su Madam Kisnah ansha rawa kamar za'a cire ƙugun a yar, liƙi ne tayi kamar ba gobe haka itama an mata kamar a buɗe wani banki da kuɗin, basu tashi ba se after one Dan saura kaɗan two tayi.
Ko da ta fita da ƙyar ta gano inda ya ajiye motar ta ƙarasa, yanzu ma kamar ɗazu ba wanda yace wa ɗan uwan sa uffan har suka kai gida duk da dai ita Kisnah cike take tam da labarin da take son bashi na yadda event ɗin ya tafi sedai ganin ba fuska yasa dole ta haɗiye kayanta.
Tun daga lokacin kuma ya shiga fushi da ita, ze kaita duk inda take so batare da query ba haka kuma kome zata yi ya daina cewa komai, sosai take cikin rashin daɗin fushin nasa sedai ta rasa ta yadda zata fara bashi haƙuri dan expression ɗin sa is not helping at all, so biyu tana gwada shiga motar Ba tare da sallama ba amma ko kallon ta be yi ba balle ya harare ta yadda yake yi a baya har se ta fita tayi.
Yanzu ma jaye da babban trolley ta fito alamun dai zata yi balaguro, tasowa yayi ya buɗe booth ɗin tare da ɗaukar trolley ɗin ya saka a ciki kana ya rufe, be kalle ta ba ya ƙarasa ya buɗe side ɗin driver ya shiga tare da maida murfin ta rufe, kamar mata laka haka ta ƙarasa nata side ɗin ganin yadda yayi tafiyar da ya bar ta ko arziƙin kallo ɗaya bata samu ba daga gare shi.....................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, comment and share fisabilillah.
Ouummey 20 (8/11/2022 10:39 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 2️⃣0️⃣
______________________📖 Manyan hamshaƙan mata ne ƴan gayu cikin shigar da kana kallon su kasan sun kai sun isa sun kuma tumbatsa dan gwala-gwalai ne kawai ke ta walwali a jikin su, zaune suke a falon gimbiya Rumana gaban su cike da kayan ciye ciyen da kama gani kasan mutane ne na musamman gare ta haka masu matuƙar daraja.
A hankali wata farar mata a cikin su ta ɗago ta kalli gimbiya Rumana dake zaune cikin su ana hira tana kai kyakkyawan slice of apple bakin ta
"Amma Rumana bakya tunanin mijin nan baki yace ce bawa yaron can Jamal sarautar nan, ni kam se naga kamar hankalin sa ya fi karkata ga yaran ɗakin kishiyar ki ko da yake ba laifin sa bane a fili yake sun fi uthman nutsuwa nesa ba kusa ba".
"Haba Aunty Siyama, wannan wace irin magana ce haka, wace nutsuwa ce aka fi uthman ɗin da zan iya rantse miki baya wani shashanci, masu nutsuwar kuma ai a hakan dai a ka kori ɗaya daga cikin su kan aikata babban alfasha ko". Sarauniya Rumana ta faɗa da little ɓacin rai a harshen ta
"Alfashaar da kuka laƙaba masa ke da husna? Ko an faɗa miki ban san komai akan hakan bane, kawai na zuba muku ido ne dan nasan ba laifi kika yi ba wajen fighting Nasara wa ɗan ki, mu ajiye wannan maganar mu dawo kan wadda muke yi yanzu".
"Bana tunanin ya isa yayi hakan dai uthman shine gaba da yaron, dama wancan da aka kora ne gaba dasu gaba ɗaya shiyasa ban kwantar da hankali na ba se da na tabbatar da fitar da cikin masarauta ta sigar da shi da ita har abada dan ko cikin ta be isa shigowa ba haka Sarauta sedai yaga anayi".
"Hakan yayi kyau, sedai kin san dole uthman yayi aure ko da ba'a taɓa sarki mara mata ba".
"Takawa ma yayi magana akan hakan kuma insha Allah ina kan tunanin mafita dan yace baze bada sarauta yanzu ba har se sunyi aure yaga irin kamun ludayin kowannen su ta fuskar riƙe iyali tukuna".
"Kina da hankali kuwa Rumana, naji kina maganar su, bayan kamata yayi yace uthman kawai anya ba wata a ƙasa kuwa?".
"No ba komai Aunty Siyama, kinsan shikansa Jamal din ya girma yanzu dan he's 28 shiyasa yayi pluhralizing Amma ba wani abu ba".
"Na gane"
Juya wa sarauniya Rumana tayi ga ɗaya ƴar uwar ta su da tun da suka fara maganar bata ce ko uffan ba se danne danne da take yi a faskekiyar wayar hannun ta
"Wato har yanzu dai kina nan da halin miskilancin naki Khadijah, kina ji muna ta hira amma ko kallon mu ma ba kiyi ba, lallau Abu Sufyan yana ƙoƙarin zama dake".
Murmushi Khadijar tayi
"Hirar taku ce ba irin wadda zance komai a kai bace Aunty, abinda kuke magana akai kun san ba daidai bane haka abinda kuka aikata ke da husna, sedai ba zan iya tona muku asiri ba kasancewar ku ƴan uwa ne, amma fa bazan fasa faɗa muku ba a kullum ku ji tsoron Allah".
"To ustaxiya, mun ji kuma mun gode".
Ɗan murmushi kawai tayi ta cigaba da latse latse a wayar ta yayin da suma suka cigaba da tasu hirar.
**************
Gudu sosai motar take yi kasancewar titin ba wasu motoci da yawa se tsirarun na matafiya, shiru cikin motar ba alamun akwai me rai dan baka jin ƙarar komai se sautin nunfashin su dake fita a hankali a hankali se ko sautin karatun Alqur'ani mai girma da aka kai volume ɗin kusan can ƙarshen ƙasa.
Chatting take yi tana zaune a kujerar ta sa'i da lokaci bakin ta na sakin murmushi alamun tana enjoying chatting da koma waye take yi ɗin, ringing ɗin wayar ya saka fuskar ta ƙawatuwa da faffaɗan murmushi ganin sunan Deeq kan screen ɗin, picking tayi tare da kangawa wajen kunnen ta
"Deeeeeeeq". Ta faɗa a hankali dariya na ɗan kubce mata, daga can ɓangaren akace
"Kar ki wani kira suna na bayan kin shoshala min rashin m, Allah queen baki da kirki".
"Am sorry my Deeq, Allah na manta ne a lokacin hankali na yayi makaranta kasan dama na faɗa maka daga can muke, nasan ka fi kowa sanin halina ta wannan ɓangaren".
Ta faɗa da ragowar sautin dariya cikin muryar ta
"Sosai ma kuwa na san ki ciki da waje, from cover to cover so sedai in ba wa wasu labari".
"Yauwa my Deeq na San ka yi min uzuri ko?".
"Sosai ma kuwa Queen, kin taho ne?".
Ɗan duban titi tayi kafin ta gyaɗa kan ta
"Muna hanya tuntuni, I think be fi ragowar three hundred kilometers ba mu ƙaraso, su Surayya sun ƙaraso ne?".
"Eh na bar su sun shige ɗaki zasuyi freshen up".
"Then Sena ƙaraso ko?".
"Ok bye, I love you".
"I love you too babe". Ta faɗa tana katse kiran, a hankali ta gyara zaman ta tare da miƙa hannun ta baya ta ɗauko ƙaton headphone ɗin ta dake cikin medium handbag din ta tayi connecting da wayar ta tare da maƙala shi cikin kunnen ta ta ƙure ƙarar sa cikin waƙar koi mil Gaya ta cikin Film ɗin koi mil Gaya ɗin na jarumi Hrithik Roshan da jarumai pretty zinta sannna ta kwanta sosai cikin kujerar ta lumshe idanun ta tana bin waƙar a hankali.
Ɗan kallon ta yayi a kaikaice cikin takaicin yadda ta ƙwama uwar earpiece tana sauren waƙoƙin banza na wai arna can da ba lallai ta san me suke faɗa.
A haka ya cigaba da gudu kan shimfiɗaɗɗen titin da yasha sabuwar coal tar har suka kusa fara shiga birnin sawariya da duk wannan gudun yana amfani da Google map ne dan shi ne taɓa sanin akwai garin ma a ƙasar ba, ko da yake shi banda garin su Giwa da maƙwabtan su ba inda ya sani dan kusan ba anan yayi rabin rayuwar sa ba.
Tun daga nesa ya hango ƙarin ginin resort ɗin da kusan duk da gilasar aka yi shi, gini ne me girman gaske haka me matuƙar tsawo dan a ƙalla ze yi hawa hamsin, kyawawan furanni masu fitar da sassanyan ƙamshi zagaye dashi haka kuma dogayen bishiyun kwalliya suma sun kewaye shi hakan yasa hatta iskar wajen kusan ta musamman ce.
A bakin gate security suka tare su demanding for their approved card Wanda ake turawa duk wanda yayi booking resort ɗin wanda su ze nuna kafin a bar shi ya shige, card ɗin na ɗauke da sunan wanda yayi booking, photon sa, adadin kwanakin da ze yi lastly floor number and room number.
Dole tasa ya tashe ta tare da nuna mata securities ɗin ta window ɗin ta, da sauri ta tashi zaune sosai tare da gyara zaman ta ta janyo wayar ta ta shiga ta nuna musu card ɗin ta seda suka duba suka tabbatar kafin su tambayi na Saraki shima ta nuna musu kafin a aka basu hanya suka shige.
Parking yayi gurin da wani security ya nuna musu dan komai nasu a tsare yake shiyasa ma suke da ƙayyadaddun adadin da suke approving zaman su a wajen, ko da kuwa mutane nawa ne sukai booking in dai adadin su ya cika sedai su bawa mutum haƙuri ya tara a gaba hakan yasa babu wani hayaniya ko kace nace, so classy and peaceful.
Fitowa haka yi daga motar customer service biyu suka ƙaraso da sauri, ɗaya ya ɗau ƙaramar jakar kayan saraki ɗayan kuma ya ja trolley ɗin Kisnah, key service suka biya suka karɓi card ɗin da zasu dinga locking and unlocking ƙofofin ɗaku nan su kafin su nufi elevator, a tenth floor suka fita inda nan ne ɗakunan nasu suke, bakin ƙofar wani ɗaki suka tsaya ta saka card ta buɗe ɗakin sannan suka shiga, dakatar da ma'aikatan tayi daga ajiye jakar ta tare da faɗin su jira zasu ƙarasa mata da tata nata ɗakin, card ɗin ta miƙawa saraki tana faɗin
"Yaa ga card ɗin ƙofar ka, bari in ƙarasa in yi wanka na gaji da yawa".
Wannan karon kasa yin shiru yayi dan tun daga compound ɗin wajen ya fahimci dole se ya saka ido a kanta dan yadda yaga mutane na al'amuran su kai tsaye dan majority ma'aurata ne da suka zo yawan shaƙatawa da kuma hutawa se ko samarin da kan ɗauko ƴan matan su dan holewa wanda baya raba ɗayan biyu itama wani ta biyo.
"Ina ɗakin naki yake?".
"Room 50, kamar apartment yake ɗan yana da parlour Wanda zamu yi sharing da su Hameedah se kuma bedroom da kowa na da nashi ɗauke da toilet a ciki".
Gyaɗa kansa yayi kafin ya shige nasa ya rufo ƙofa ita kuma tayi gaba har ƙofar nasu ɗakin da duk a sake floor ne, bakin ƙofar suka ajiye mata trolley ɗin tayi musu godiya suka wuce ita kuma ta buɗe ƙofar ta shiga.
Sosai su Meenah suka nuna farin cikin ganin ta wanda da ƙyar ta samu ta zame zuwa bedroom ɗin ta tayi wanka ta saka shorts iya cinya se guntuwar shimi ta bi lafiyar gado.
A can ɗakin saraki shima wankan yayi dan ya gaji sosai kasancewar be taɓa dogon driving ba se yau shiyasa gajiya ta rufe shi.
Wanka yayi fito da bathrobe a jikin sa kafin ya zauna kan gadon ɗakin ya jawo jakar sa ya zage ya ɗau shorts da jallabiya ya saka yayi sallar zuhur da ta same su a hanya kana ya cire jallabiyar ya kwanta.
Bacci tayi me daɗi kafin ta tashi ta fita parlor ɗin taci abinci sannan suka shiga hirarrakin su irin na ƙawaye.
Ƙarfe bakwai da ƴan mintuna suka fito shirya kowacce cikin irin tata shigar suka nufi spa ɗin da ke wajen, ƙwataccen guri ne da ko a cikin resort ɗin iskar cikin sa ta banbanta da ta ko ina saboda madaidaitan bishiyun da aka kakkafa suna rausaya wa sunan fitar da tattausar iska da ta haɗe da ƙamshin fresh sea ɗin gefen wajen.
Kan kujerun da ke zagaye da table ɗin me ɗan girma suka zazzauna ana ta hira kafin daga bisani Kisnah tayi shiru da bakin ta ɗan tuni hankalin ta ya koma kan ruwan da yake ɗan motsi garai garai dashi gwanin burgewa, rabon ta da waje irin wannan shekara biyu kenan, da a lokacin tana Canada kusan duk week tana hanyar bakin beach da spa Sabida mayatar son ruwa da Allah ya jarrabe ta dashi, farkon zuwan ta nan lokacin tana level one ne da suka samu hutun first semester tazo tayi sati ɗaya ta koma lokacin tun kan ta san su Hameedah, dan har gwara Surayya da Leekha ta san su tun lokacin sedai ba wani good times suke ba ana dai hi hi ne, farkon alaƙarsu da Surayya tun wani group assignment da ya haɗa su ne daga nan kuma se suke dan gaisawa sosai har suka ɗan saba, Meenah kuwa se suna level two suka haɗu lokacin da ita Meenahn ta Sami carry over a first semester ɗin su tana kuka gaban notice board ɗin da aka kafe musu, sosai ta bawa Kisnah tausayi a lokacin dan haka ta ƙarasa ta ɗaga ta da alƙawarin insha Allah zata dinga koya mata course ɗin da ta faɗi har tayi catching up ƙarkari dai ta sa a ranta zata yi, Hameedah kuwa cousin ɗin Meenah ce da tayi joining ɗin su later farkon second semester, daga baya ne Leekha ta shiga cikin su sosai dan farko sedai ɗan gaisuwa.
Tapping ɗin ta da Surayya tayi yasa ta ɗago da sauri tana mata kallon tambaya
"Wane irin tunani kike yi haka Kisnah, anata kiran wayar ki nima ina ta miki magana amma shiru baki jini ba".
"Ringing Kuma, amma ban ji ba?".
"Ta ina zaki tafi, Allah yasa wata bata faɗa tsakiyar kogin da ba mataimaki gabas da yamma ba balle kuma kudu da arewa".
"Wane irin kogi kuma wace ta faɗa? Ban gane ba".
"Gaya min, wane me sa'ar ne haka ya sami damar sace wannan zinariya zuciyar ta kyakkyawar budurwa kamar queen Kisnah ta?, dan da alama queen ɗin mu ta faɗa cikin makauniya kurma ..........".
"Kuma gurguwar soyayya ko, dan nasan abinda zaki faɗa kenan".
Dariya suka saka duka dan sosai Kisnah tafi sakewa tayi wasa da dariya da Surayya duk cikin friends ɗin nasu kuwa, Leekha kuma, hmmm yarinyar tayi dan baza' a taɓa zama a zagi Kisnah a gabanta ba ta sani ita kanta in Kuma akayi kuskuren haka to bayan matakin da ita Leekhar zata dauka se ta kuma sanar da Kisnah ɗin, Meenah kuma tana gwada mata kulawa fiye da kowacce cikin ƙawayen nata sedai ita tasa sakin jikin ta sosai da ita duk da cewa ba wai tana ɗari ɗari da ita bane sedai ba kamar yadda ta sake da Surayya ba, Hameedah kam ba a magana dan tun da ta gane halin ta ta ci maganin zama da ita.
Ringing ɗin wayar yasa ta mida hankalin ta kan screen ɗin tayi picking tana kaiwa kunne
"Hello Queen".
Deeq ya faɗa daga can ɓangaren, da murmushi ta amsa da hi
"Kin ƙaraso ne?".
"Tun ɗazu, har na huta mun ma fito da su Meenah, muna spa".
"Okay Bari in ƙaraso".
"K". Tace tare da kashe wayar suka cigaba da hirar su da Surayya.
Tun daga nesa da ya hango ta yake ta sake mata murmushi har ya ƙaraso kusa da su, miƙewa tayi suka rungume juna kafin ta janye jikin ta ya ƙara sa kusa da su Meenah sukayi shaking hands da dukan su Sannan ya dawo wajen ta.
Kujerar kusa da ita ta right side ɗin ta ta ja masa dan ya zauna yayinda Surayya take left side sedai be zauna ɗin ba se kallon kujerar yayi ya maida kallon sa kanta Yana marairaicewa
"Please kissy muyi tseren nan da muke yi da boat a Canada, Allah i missed those moments like hell".
Ɗan shiru tayi tana kallon sa kafin ta juya ga ruwan da dama tun ɗazu take hasaso shiga cikin sa sedai tana dannewa yanzu kuwa da ya faɗa se taji hakan kawai take so, miƙewa tayi yayinda Surayya ta tambaye ta ina zata ta faɗa mata, da sauri itama fa miƙe tace zata yi, kallon kanta Kisnah tayi cikin ƙarewa shigar ta kallo, doguwar t-shirt ce irin me saukowa har gwiwar nan se ɗan bumpshort da ta saka se ko farin canvas ɗin da ta sanya a ƙafar ta, gashin ta nannaɗe cikin style ɗin bun ta ɗora p-cap, gaban Leekha ta ƙarasa ta ɗau cardigan ɗin da Leekhan ta cire ta maƙala a jikin ta dan tasan dole sanyi ze iya damun ta kafin suka nufi wajen jiragen su ukun...............✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, comment and share fisabilillah.
_The two hardest things to say in life are hello for the first time and goodbye for the last._
Ouummey 21 (8/11/2022 10:40 PM)
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
________________________________
Page 2️⃣1️⃣
________________________📖 Wajen jirgin suka ƙara sa nan Surayya ta karɓi ɗaya ta biya nata kuɗin a lokacin su kam ɗan ƙaramin receipt ɗin da yayi payment tuntuni ya nuna, guda ɗaɗɗaya kowa ya shiga shi kaɗai, seda kowa ya gama shirya wa kafin