Header Ads
Showing 60001 words to 63000 words out of 104570 words

Chapter 21 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1434

Ads at the middle of Article

yasa Mommy ta dawo hankalin ta ta shiga kame kame tana yaƙe wanda a fili kowa yake iya gane wannan fara'ar bata kai ciki ba haka kuma damuwa da ɓacin ran ta gasu nan rubuce kan dattijuwar fuskar ta.


"Sannu da zuwa, fatan kun dawo lafiya".


"Lafiya, fatan kuma mun same ku lafiya".


"As you can see". Mommyn ta faɗa tana shigewa dan ta kasa dannar kan ta shiyasa ta shige tun kafin tayi abinda zata dawo tana dana sanin ɓata shirin ta.


Da kallo kisnah tabi bayan har ta shige kafin ta ɗaga kafaɗa irin ko oho ɗin nan, abincin ta da Rayya ta kawo ta shiga ci hankali kwance tana yi tana sipping milkshake ɗin har ta gama kafin Rayyan ta kwashe kwanikan zuwa kitchen ita kuma ta cigaba da kallon da ta kunna take yi.


Seda aka kira isha kafin ta koma ɗakin ta, sallah tayi ta koma gado ta shiga chattinga a twitter tana ta murmushi dan the site and it's patronizers are so entertaining, tana gamawa da nan ta koma Instagram ta shiga posting hotunan da suka yi lokacin da zasu bar resort ɗin, within minutes sega likes da comments kamar me, tana son instagram sosai dan mutanen ciki na nuna mata ƙauna,wuyar ta tayi posting photo yanzu zaka ga likes kamar ruwan kuɗi.


Shiyasa so da yawa ita hau social sites ɗin ta takan manta da kowa dake tare da ita ne dan bata tuna komai se followers ɗin ta dake patronizing ɗin ta, tasan da ace wata business woman ce ita da cinikin da zata dinga yi ba kaɗan bane dan kamar jiran ta suke ne, kaya kuwa haka zaka ga ana tambayar pls abu kaza nata a ina ta siya da abubuwa irin haka dai.


Kashe wayar tayi ta aje bayan tayi offing datar ta ganin har ta shafe kusan awannin uku a online, wanka ta sake ta canja kaya zuwa nighties ta kwanta bayan ta kashe hasken ɗakin tare da janyo photon ta a under pillow ɗin ta ta rungume ƙam a ƙirjin ta tare da rufe jikin ta da comforter ta rufe idanun ta, tunanika sosai yake zo mata a lokacin sedai tana fighting ɗin su dan bata son abinda ze shiga barcin ta balle har yasa ta kasa samun bacci me nutsuwa......................✍️.
















©️ Ouummey 📚✍️.




















☑️Ote, comment and share fisabilillah.
























Ouummey 25 (8/19/2022 10:30 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________














Page 2️⃣5️⃣
















Not edited ❎










________________________📖 Da ɗan hanzari take shiri dan ta makara, a so samun ta ta fita tun 9 dan saka ido sosai akan companies ɗin ta sedai baccin da ya rinjaye ta yasa dole ta makara.


Dogon palazo jeans ta saka a jikin ta da t-shirt ta ɗora jacket akai, sun heart ta saka me kyau a kanta tare da Black shafe, sosai tayi kyau yau looking so responsible ba kamar sauran rana ku ba.


Wayar ta ɗaya ta ɗauka wadda take amfanin da ita ko yaushe leaving the other a ɗaki sannan ta sauko, girgiza wa Rayya da ke mata tayin breakfast Kai tayi dan bata da wannan time ɗin yanzu.


Tun a resort gaba ɗaya hankalin ta ya koma kan dukiyar ta ne, matsalolin da companies ɗin ke fuskan ta ne suka fi damun ta dan haka dole ta maida hankali dan ba zata bari wahalar Abbun ta na shekara da shekaru ya tafi a banza ba dole ta dawo hayyacin ta.


A bakin farar motar ta tarar da Saraki yana jiran ta kamar yadda ta sanar dashi ya fito da mota gata nan fitowa, da sallama ta shiga motar abinda ya sashi ɗago kai da sauri ya kalle ta cikin tsananin mamaki, kafin tafiyar su resort ta kan yi masa sallama a duk inda ta same shi dan baya ko kallon ta in bata yi sallamar ba haka kuma so da yawa ze tursasa ta fita daga motar in har bata yi ba se tayi ta shigo, amma daga lokacin da suka sami saɓani yayin birthday party ɗin Surayya ta ajiye a gefe haka shima lokacin yana fushi ba ya ce mata se tayi se gashi yanzu ta bashi mamaki.


"Good morning yaaa, ya gajiya, we're late pls muje".


Janye kan sa yayi daga kallon ta yana gyaɗa mata kai alamun amsawa kafin yayi wa motar key suka fita daga gidan cikin addu'ar sauka lafiya daga workers ɗin.


Shiru tafiyar tasu kamar ko yaushe dan da wuya kaji tashin sauti cikin motar duk sanda suke tafiya haka in ba wai na karatun Alkur'ani ba se ko wa'azin da yakan sa da yawan lokuta se kuma in maganar da ta kama tsakanin su.


"Yaa Please akwai maganar da nake so muyi in mun ƙarasa office, Dan Allah Karka ce a'a".


Ɗan shiru yayi kamar me tunani kafin ya amsa mata da "K".


Haka suka cigaba da tafiyar kurame dan yau be sa ko ɗaya ba daga karatun har wa'azin har suka ƙarasa, kamar dai kowane daga cikin companies ɗin wannan ma seda akayi screening ɗin su irrespective of wai me company ɗin ce da kan ta, wannan doka ce ta tun mahaifin ta na raye dan gudun afkuwar matsala ko tashin hankali se dai a yanzu ga Kisnah ita bata ga wani amfanin hakan ba tunda a haka ba'a fasa handama da rashin gaskiya a cikin ma'aikatan ba.


Wajen da take ajiye mota ta nuna masa ya yi parking kafin suka fito suka jera zuwa cikin babban building ɗin, gaisuwar da receptionist ɗin ke musu ta amsa tana mamakin irin kallon da biyu daga ciki suka bi Saraki dashi.


Pretending gaisawa da ma'aikata tayi hakan yasa ya ɗan yi gaba kafin ya tsaya jiran ta tun da be san kan wannan Company ɗin ba, da wannan damar ta yi amfani wajen ƙare masa kallo dan san sanin dalilin kallon da receptionist ɗin suka bishi da shi.


Baƙin dogon jeans ne a jikin sa se long sleeve shirt Fara tas ƙafar sa sanye da baƙin brogues da ya sanya, ba ƙaramin kyau yayi ba cikin shigar tun bare gashin kan sa dake ƙyalli wanda ya fito ta ƙasan beret ɗin da ya sanya wa kan sa, se yanzu ta gan dalilin da ya sanya suka wani watsa masa ido kamar zasu cinye shi da su, bata san me yasa ba se ta tsinci kan ta da jin haushin su wanda ya tursasa mata juyawa ta jefa musu wata ƴar iskar harara kafin tayi ƙwafa ta wuce inda ya tsaya suka nufi lifter.


Haushi sosai ya cika ta se cika take tana batsewa har suka shiga office ɗin, zama yayi kan kujerar dake gaban ƙaton table ɗin yana bin ta da kallo yadda take ta kumbura fuska kamar wadda aka zaga, kau da kan sa yayi yana ayyana may be ita da employees ɗin ta ne.


A hankali yake zagaye idanun sa cikin office ɗin sa yana jinjina girman gurin dan kuwa yaci ayi madaidaitan offices kusan huɗu ko uku, tsaruwar office ɗin ta burge shi dan ba'a wani cika tarkace ba amma yayi kyau sosai, ga kuma tsaftar da ya gani na wajen dan duk da bata cika shiga office ɗin ba amma a share suka tadda shi yana tashin ƙamshi.


Zama tayi ita ma kujerar dake gefen sa ta juya ta yadda zatai facing ɗin shi kafin ta soma magana cikin sanyin murya da fatan ya yarda da batun da zata kawo masa.


"Kamar yadda kaga gidan mu nasan ko ban faɗa maka komai ba kasan kawu da Mommy ba iyaye na bane, kawu ƙanin Abbu na ne da nake rayuwa tare da su currently, ba ni da wa bani da ƙani ni kaɗai ce wajen parents ɗina, kwanakin baya kasan kaɗan daga cikin matsalolin da na ringa samu daga wasu cikin companies ɗina hakan yasa na yanke shawarar yin amfani da ƙanƙanin lokacin da nake dashi kafin mu fara project dan kula da harkokin kasuwanci na sedai bazan iya ni kaɗai ba dole se da taimakon wani, Please Yaya kayi min favor ɗin karɓar aiki tare da ni, na yarda da kai nasan ba zaka cuce ni ba, ina buƙatar ka sosai cikin tafiyar kasuwanci na Yaa, alamu sun nuna akwai masu son ganin bayan dukiya ta dan haka suke min zagon ƙasa, nayi iya ƙoƙari na wajen ganin nayi tracing ɗin su sedai na kasa samun dama".


Kallon ta kawai yake tun da ta fara magana har ta ƙarasa kafin yayi ajiyar zuciya


"And what about shi kawun, ina ce shike kula da komai na companies ɗin?".


"Shine yaa, amma bana gane komai a abubuwan da yake jagora, a lissafin shekarar da ya gabata da akayi lissafin shekara me makon ace an sami riba se ma kuɗin Company da ya dulmiya, kuɗi ba ƙanana ba fa, haka ma wannan shekarar da muke ciki yanzu muna wata na huɗu ne amma kullum cikin cases ake na ɓatan kaya, kuɗi, rashin maida hankalin ma'aikata and many more problems, beside this kawu ya Fara manyan ta dole se ana taimaka masa banda haka ma kaga companies ɗin kusan biyar ne dole baze yiwu ace mutum ɗaya ke controlling abubuwan su ba in kuwa akace haka za'a yi dole a ringa samun matsaloli kamar yadda muke fuskanta yanzu".


A hankali ya ɗan gyara zaman sa cikin kujerar kafin ya kalle ta sosai


"Kin taɓa ganin an ɗauki mutum aiki ba takardu? Ko kuwa a ina za'a nemo takardun da za'a saka cikin file ɗina? Kin dai san dole a buɗe min file kamar kowane ma'aikaci ko, that aside, se wa ya dinga driving ɗin ki?".


"Is not a big deal Yaa, se na nemi new drive shikenan, maganar takardu kuma ai Company ɗin na wa ne ina da right ɗin kawo duk wanda na yarda dashi ko da kowa ne yarda ba in as much as na yarda ni shikenan".


"Okay will get to think about it". Ya faɗa yana ɗan relaxing cikin chair ɗin, marairaice fuska tayi dan Allah ya na gani so take ta san matsayar da suka cimma wa ko hankalin ta ya kwanta, yanzu kam she has no peace of mind seeing her father's hustle been wasted


"Dan Allah fa nace tun farko yaa, Abbu na yasha wahala kafin ya kafa companies ɗin nan yaa bana son wahalar sa ta tafi a banza, ka taimaka pls".


"Tun da kin matsa then fine na amince amma ina da sharaɗi".


Cikin murnar da ta cika ta ta matsin da sauri kamar zata faɗa masa tana washe baki


"Naji daɗi sosai yaa, ban damu da sharaɗin naka ba dan zan yi komai in har zaka yarda, faɗa min meye sharaɗin".


Ɗan jan fasali yayi kafin ya tsare ta da idanu


"Sharaɗin ba wani me tsauri bane, kawai ban yarda da batun ɗaukar new drive bane, I'll be driving you and also be working, and the last shine you'll be dressing decently and abandon clubbing, that's all".


Shiru Kisnah tayi yayinda duk wata murnar ta ta koma ciki, she's just thinking of how can she stopped clubbing at once, abun ya riga ya shiga jinin ta haka in ma barin ne tasan sedai ta rage bit by bit Kuma haka ya kamata yace in ma baya san clubbing ɗin se yace ta rage ba ta daina ba.


Ɗauke kan sa Saraki yayi tare da ciro phone ɗin sa ya shiga pressing kamar ma hankalin sa baya kanta yayinda yake kallon ta a kaikaice praying internally Rabb yasa ta yarda da sharaɗin sa dan haka kawai abun ya zo masa ganin yadda ta damu da dukiyar yasan wanna ne kaɗai hanyar da ze bi wajen daƙile clubbing ɗin ta though ta kwana biyu bata je ba sedai yasan saboda exams da kuma tafiyar da suka yi ne yasan tana gab da cigaba da zuwa tunda sun dawo yanzu.


Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke tare da neman seat ɗin da ta tashi ta koma ta zauna tana me cigaba da tunani, a hankali kamar wadda akayi wa dole ta furta


"Na amince".


Ɗagowa yayi ya kalle ta ya ɗan yatsuna fuska irin kamar an takura masa ɗin nan


"See ba dole bane ba fa, naga duk kin wani yi sanyi, abin nan zaɓin ki ne, you've the choice dan haka in Baki yardan ba i don't give a damn, dama zan yi saboda Abbun ki da kika sako, so in ranki be kwanata ba a bar maganar".


Da sauri ta girgiza masa kanta tana ƙoƙarin more damuwar kan fuskar ta dan kar ya fasa, she have no hope in Bashi ba so she won't let him go


"Na yarda fa yaa, ba wai ina kokonto bane in adai kawai tunanin yadda zan daina clubbing rana ɗaya bayan am used to it though da wahala amma zan yi hakan insha Allah, I'll do it for Abbu na surely".


Sauke ajiyar zuciya yayi a ɓoye tare da yin hamadala yana godewa Allah da ya bashi damar fara saita ta kan hanya cikin sauƙi, he pray one day ta zama yarinya ta gari insha Allah.


Gaban computer ta dake office ɗin ta koma ta zauna tare da typing abun da be san me take rubuta wa ba se dai hannun ta da yake jin suna motsa keyboard ɗin cike da ƙware wa, tashi tayi ta ƙara sa gaban printer da ke cikin office ɗin ta ciri wata takardu guda uku ta dawo kujerar da ta tashi wadda take opposite ɗin sa ta zauna tare da tura masa papers biyu


"You sign this papers, wannan ta farkon takardar ɗaukar ka aiki ne, ta biyun kuma takardar oath na yadda da dukkan wasu rules and regulations na company ne, ragowar takardun ka kuma zamu je court muyi affidavit ɗin ɓatan documents, ina tunanin shikenan ko".


Shiru yayi yana kallon ta kafin a hankali ya motsa bakin sa


"I thought ƙarya haramun ne a musulunci ko".


Kallon shi tayi sosai wannan karon cikin ƙosawa da halayyan nashi na yau


"Haba mana yaa, ai ni dai nayi ƙaryan ba kai ba ko, to zunubin a kaina, haba mutum kamar me wanna ko liman albarka". Ta ƙarashe ƙarshen sentence ɗin can ƙasa ƙasa kamar me ƙunƙuni


Murmushi yayi dan sarai yaji abinda ta faɗa so ya kalle ta yana ɗaga gira


"Miss kamar kina magana ko?".


Wanna karon sosai ta ɓata fuska dan Allah ta gaji da gaske


"Ni ba abinda nace fa".


"Oh i thought magana kika yi".


Girgiza masa kai kawai tayi dan ta fahimci neman magana yake ita kuma bazata biye masa ba balle har ya sami abin fakewa yace ba zai karɓi aikin nan ba dan ina hakan ta faru bata san kuma ha zata yi ba.


She really need to have a partner da zasu yi joining hands wajen ya ƙar ma ha'in tan companies ɗin ta su kuma ciyar dashi gaba se dai bayan Sarakin bata ganin akwai wani da zata iya yarda dashi a kan batun.


Turo mata takardun da yayi gaban ta tare da ƙarar ajiye pen ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, hannu yasa ta ƙara sa jan takardun gare ta kafin ta bi su da kallo kana ta ajiye ta dube shi


"A zahiri gaskiya yaa ban san wane matsayin zan baka a Companies ɗin ba dan kaga ina buƙatar ka kusan a duk Companies ɗin, me kake ganin ya kama ta a yi?".




"You decide ai ko, you're the CEO here".


Kallo kawai ta bishi dashi, ta sani yana sane yake abin da yake dan ya ƙure ta ta tanka and she won't Dan haka se ta yi murmushi


"Hakane and I'll let you know whatever my decision happens to be later".


"Patiently waiting".....................✍️.


















©️ Ouummey 📚✍️.


















☑️Ote, comment and share fisabilillah


























Ouummey 26 (8/20/2022 8:39 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________














Page 2️⃣6️⃣
























_________________________📖 Tare suka zauna a office ɗin suna ayyuka sedai ana kiran sallah ya dakata daga aikin da yake yi na bin record ɗin spendings na watan da ya wuce da ta nemi a kawo nata shine fa yake bin lissafin dan ganin ko daidai yake.


Da kallo ta bishi kafin ta kautar da kanta ta cigaba da shigar da bayanan da take cikin laptop ganin ya shiga toilet, be daɗe ba ya fito fuskar sa jiƙe da ruwa haka hannun rigar sa a nannaɗe yana ƙoƙarin saukar dashi da alama dai alwala yayi.


Ɗagowa tayi ta bishi da kallo jin fitowar sa sedai unfortunately idanuj ta ya sauka kan tsintsiyar hannun sa da yake ƙoƙarin sauke hannun rigar, wow kawai ta iya furtawa cikin ranta ganin yadda wasu kyawawan baƙin gashi suka kwakkwanta suka nannaɗe a jikin fatar hannun nasa, sosai ta kasa janye idanun ta kan hannun dan tana matuƙar son taga mutum na da gashin hannu da ƙafa, da sauri ta bi ƙafafun sa da kallo taga nan ma yana dashi ko kuwa sedai taga wandon sa a sake yake hakan yasa ta kuma maida kanta kan hannun nasa da ya gama sakin ɗaya ya koma ɗayan


Jikin shi ne ya bashi ana kallon sa dan haka ya ɗago dan yasan ita ce tun da su biyu ne a office ɗin, kanta kuwa ya sauke duban sa yaga yanda ta kafe hannun sa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads