Showing 99001 words to 102000 words out of 104570 words
Chapter 34 - SARAKI (The Accused Prince).txt
list ɗin ya kuma fita siyowa ita kuma ta zauna tana bin ɗakin da kallo cikin jin haushin rashin toilet a ciki, gidan madaidaici ne da ke da soro biyu babba da ƙarami se tsakar gida me ɗan faɗi, kitchen a gefen dama se toilet a kusa da ƙofar shigowa se kuma nasu ɗakunan da ke jere sedai da ɗan tazara kaɗan tsakanin ƙofofin su kasancewar ɗakunan da girman su, daga jikin ɗakin Kisnah akwai ɗan ƙaramin corridor da tun da ta ganshi tasa a ranta nan zasu ajiye kayan ruwan su.
Be dawo ba se yamma suka kuma shiga gaganiyar saka curtains ɗin masu matsakaicin tsada se dai suna da kyan su ba laifi.
Yana gamawa yace ta sa masa ruwan ɗumi a ƙaramin gas ɗin su me kai uku da ya siyo fitar sa ta ƙarshe yayi wanka, bata ƙi ba ta fita ta cika ɗaya daga cikin sababbin pots ɗin d aya siyo da ruwa ta matsa dan kunna gas sedai yaƙi kamawa, da ta gaji se kawai ta koma ɗakin ta faɗa masa yaƙi kamawa, seda ya fito ya gwada mata yadda ake kunnawa sannan ta gane akwai banbanci da nasu na gida...................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, Comment and share fisabilillah.
Ouummey 40 (7/28/2022 3:05 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 4️⃣0️⃣
_______________________📖 Ruwan na tafasa ta shiga ƙoƙarin juye shi cikin bucket sedai ta kasa kuma bata san kiran shi dan taga yadda ya gaji sosai, tana ta kokawa da tukunya har ruwan ya zubo mata a ƙafa bata lura ba se zafin da taji ya ratsa kwanyar ta, ai ba tasan sanda ta saki tukunyar da ta ɗauka ba tana sakin ihu at the same time, a gigice ta fito daga ɗaki jin ihun ta haka ma maƙociyar ta saudah, inda take durƙushe riƙe da ƙafar ya ƙarasa da sauri tare da kaiwa tsugunne yana ƙoƙarin riƙo ƙafar tata dan ko be tambaya ba tukunyar da ta faɗi can gefe da kuma ruwan da suke malale a ƙasa ya shaida masa abinda ya faru, fatan sa Allah yasa ba ta ƙone sosai ba.
Se da ƙyar ta cire hannun ta daga kan ƙafar da tayi jaa sosai na azaba, hawaye kawai take yi dan ko sautin kukan babu dan bata taɓa cin karo da irin wannan azabar ba a kaf rayuwar ta se yau, gefe saudah ta tsaya tana mata sannun da bata iya ta amsa ba se Saraki ne ya amsa mata kafin ya tayar da Kisnah tsaye ya saka a gefen jikin sa suka shige ɗakin su.
Duk da suna cikin tashin hankalin ƙonewar da tayi amma hakan be hana wani baƙon yanayin kasancewar Kisnah cikin jikin sa ziyartar sa ba sedai be maida hankali ga hakan ba buƙatarsa kawai ya zaunar da ita ya duba mata ƙafar, Allah ya taƙai ta dan fatar bata tashi ba sedai ƙafar da ta yi jajur, duk da gajiyar jikin sa haka ya kuma miƙewa ya fita yaje ya siyo mata ointment da zata shafawa wajen da kuma pain killers da zata sha dan kashe zugin.
Kallon sa take yi tana jin wani shauƙi da farin ciki ganin sa duƙe gaban ta yana shafa mata ointment ɗin a ƙafar ta cikin kulawa da takatsantsan, tausayin sa ne ya kama ta ganin duk yau be zauna yana ta zirga zirgar ganin komai nasu ya kammala, wankan da ze yi yaji daɗi ma be samu ba ga abin da ya faru, duk se taji tana jin haushin kanta, yanzu da tana shiga kitchen sosai ai da ta iya juye ruwan zafi da kuma bata ƙara sashi ya wahala ba.
Yana gama shafa mata ya ajiye man ya ɗau pain killers ɗin ya miƙa mata biyu, dafe gaban kansa yayi tuno ba ma su da ruwan da zata sha maganin, suna da ruwa a drum ɗin su da ya kira me ruwa ya zuba musu sedai yasan baze yiwu ta sha magani da shi ba, to amma ai a Bina ruwan da suke sha wannan sedai a kira shi ruwan roba a kan sa, tuno hakan yasa ya miƙe ya ɗau cup ɗaya cikin kayan su ya fita ya wanke sannan ya zubo mata ruwan a cikin sa ya dawo, bata yi musu ba ta karɓa duk da tsanar da take wa magani amma haka ta rufe ido ta shanye dan bata san ƙara masa wani gajiyar na ƙin shan maganin ta kan wadda take tattare dashi.
Ajiye cup ɗin yayi a gefe ya fita wajen da incident ɗin ya faru ya tarar har saudah ta gyara wajen ta ajiye musu tukunyar a gefe haka ta goge wajen, godiya yayi mata a ransa sannan ya kuma zuba wani ruwan ya ɗora da kansa, ruwan na tafasa ya juye ya sirka ya kai toilet ɗin, tsayawa yayi yana kallon toilet ɗin cikin ɗan ƙyanƙyami dan a rayuwar sa yaƙi jinin toilet mara inganci, a ganin shi gwara toilet ɗin su na Bina dan shi ƙasa ce haka kuma da kansa yake gyara shi kullum so biyu a rana kuma hankalin sa a kwance yake sanin su biyu kawai ke amfani dashi akasin wannan.
Sam ji yayi baze iya shiga ba se kawai ya ɗau bucket ɗin ya maida ƙofar ɗakin su ya shige tare da zama kan katifar su nesa da inda take zaune.
Bata kawo komai ba ganin ya zauna a tunanin ta someone is using the bathroom shine yake jira sedai ganin har ya fara bacci yasa ta bubbuga katifar tana kiran sunan sa
"Baccin ai ze fi daɗi in kayi wankan, nasan ma zuwa yanzu na cikin toilet ɗin ya fito".
"Na fasa". Cikin mamaki ta dube shi cikin son dalilin fasawar
"Amma saboda me, kalla fa ka gaji da yawa You need to take a warm bath se ka fi jin daɗin jikin ka, ko kuma dan incident ɗin da ya faru ɗazu ne, kayi haƙuri Please Allah ban iya bane amma naga yanda kayi and next time zan yi daidai, an sorry please".
"The toilet is not clean". Ya bata amsa yana lumshe idanun sa, bata ce masa komai ba se miƙewa da tayi ta ƙarasa inda ya ajiye musu detergents da su toilet wash da ya siyo musu ta ɗau robar wasu ɗin, disinfectant da kuma toilet freshener ta fita, be san ta fita dan baccin da ya fara ya ci ƙarfin sa.
Duk yadda take jin zafin taka ƙafar haka ta daure dan bazata iya kallon shi ya zauna da tarin gajiyar da yake ciki ba bayan all he's going through is because of her, Kai abubuwan hannun ta tayi ta ajiye gefen toilet ɗin kaɗan sannan ta koma corridor ɗin da drums ɗin su ke ajiye ta ɗau empty bucket ta zuba ruwa sosai ta fara ƙoƙarin ɗauka sedai nauyin da ta ji yasa ta ajiye tana yarfe hannun ta, kwaɓe fuska tayi dan all these are new to her, bata Saba da irin wannan rayuwar ba sedai bata jin zata fasa wanke toilet ɗin, da ƙyar ta iya kai bucket ɗin bakin door na toilet tana sauke numfashi tare da kallon palms ɗin ta da suka ɗan yi ja, numfashi ta sauke cikin faɗa wa kanta zata iya ta juya zuwa ɗakin su ta ɗauko daya daga cikin brooms ɗin da ya siyo ta ɗauko me ƙwari ta jujjuya a hannun ta (tsintsiyar kwakwa), banɗakin ta koma ta tura ƙofar, yamutsa fuska tayi itama dan itama ta ga rashin clear ɗin da ya faɗa, tunani take ta ina zata fara wanke wa se kuma tunanin kar ta ɗebi germs a kayan ta yasa ta ajiye broom ɗin ta tsugunna ta tattare ƙasa wandon fakistan ɗin jikin ta har zuwa kusa da gwiwar ta sannan ta ɗaure rigar a ƙugun ta se kuma ta tsaya kallon broom ɗin kamar zata fashe da kuka dan siri sirin saman ta san baze iya wanke toilet ɗin nan ya fita ba.
Saudah dake tsaye ta window ɗin ta tana kallon ta ce ta fito kamar zata yi wani abu, motsin ta yasa Kisnah kallon wajen suka haɗa ido se ta ɗan sake mata ƙaramin murmushi, maida mata saudah tayi tana ƙarasowa kusan ta
"Lafiya kike tsaye bakin banɗaki haka".
"Ehm ina son wanke toilet ɗin ne but nasan wannan broom ɗin won't clean anything, ya zan mata pls".
Ƴar dariya saudah tayi kafin ta shiga ɗakin ta ta fito da wata wuƙa kana ta karɓi tsintsiyar hannun Kisnah ta shiga datse ta a ranta tana mamakin yadda zata ce zata wanke toilet ɗin da bata ko daɗe da gama wanke shi ba, tana rage ta tana tambayar Kisnah yayi amma se tace a'a a sake datsewa har seda aka kai tsintsiyar kusan rabi kafin tace yayi mata ta karɓa tare da yiwa saudah godiya ta wuce toilet ɗin ita kuma saudan ta shiga gyara wajen .
Ajiye komai tayi a gefe na tunanin bata saba ba bata kuma taɓa yi ba ta zuba toilet wash a floor ɗin tare da detergent tare da disinfectant ta zuba ruwa ta shiga wanke shi da iya ƙarfin ta, kusan saɓi uku tayi wa floor ɗin kafin ta ga yayi mata daidai a idanun ta ta saka ruwa ta ɗauraye sannan ta sake feffesa disinfectant da kuma toilet freshener, take kuwa scent ɗin toilet ɗin ya canja ba kamar ɗazu da yake fitar da wari kaɗan kaɗan ba.
Bucket da broom ɗin ta maida corridor ɗin su sannan ta koma ta kwashi ragowar disinfectant, toilet wash da toilet freshener dan detergent kam se da ta ƙarar dashi tas, ajiye kayan tayi inda ta ɗebe su cikin wani ƙaramin basket sannan ta matsa wajen da yake kwance, hannu ta kai da niyyar tashin sa se kuma ta maida ta zuba wa fuskar sa ido cikin yi masa kallon ƙurilla a karo na farko tun da suke tare.
Kallon sa take tana admiring duk wani abu na fuskar sa da idon ta ya kai kan sa har ta sauke duban ta kan ɗan siririn baƙin gashin da ke saman bakin sa da be haɗe da madaidaicin gashin dake haɓar sa ba, jajayen laɓɓan sa ta ƙurawa ido kafin kuma ta kawar da kai da sauri tana ɗan matsawa baya jin hannun ta ya fara mata ƙaiƙayin son shafa gaba ɗaya fuskar sa tun bare ma gashin haɓar sa, ɗan gyaran murya tayi cikin kunyar kanta da ya kamata sannan ta shiga bubbuga pillown da kan sa ke kai tana kiran sunan sa.
A hankali ya buɗe idanun sa dake cike da bacci ya zuba a kanta yana kallon ta, kallon da ya haifar da wani electrification a cikin jikin ta gaba ɗaya sedai ta kasa kawar da kanta duk da abinda take ji dan kyan da idanun sa suka masa a lokacin baze bar ta ta janye ɗin ba, rufe idon da yayi yasa tayi firgigit cikin tuna abinda ya kawo ta dan haka ta sake kiran sunan sa, wannan karon bata kalli fuskar sa bata shiga masa magana Muryar ta a sanyaye dan tun kallon farko da yayi mata komai na jikin ta ya saki.
"Ka daure ka tashi kaje kayi wanka, na kai maka ruwan toilet".
Maida idanun yayi ya rufe dan baya jin ze iya tashi a lokacin saboda daɗin da baccin yayi masa
"Lokacin Sallah fa yayi ma, gashi can naji kamar ana kira a masallaci".
Ta faɗa da sauri dan tasan abinda zata ce kenan ya tashi ba musu, aikuwa dai tar ya buɗe idon sa yana kallon ɗakin su da yake da ɗan duhu kafin ya miƙe ya zauna na wasu sakanni Sannan ya tashi ya ɗau buta ya fita, ruwa ya zuba na alwala sedai yana buƙatar amfani da banɗaki dan fitsari yake ji, takaici ne ya kama shi na tuno yanayin banɗakin na ɗazu, be san me yasa masu gidajen hayar garin nan basa yin toilet a ɗaki dan duk gidan da suka je kafin nan suma toilet a waje yake kuma guda ɗaya, be yi shiru ba lokacin ya tambayi dillalin ko ze iya samun ɗaki me haɗe da toilet sedai amsa ya bashi da su basa toilet a ɗaki sedai in gidan kai ne.
Ɗaki ya koma ya fara fitar da kayan wankin toilet dan gwara ya wanke ta shiga a tsaftace duk kuwa da gajiyar da yake tare da ita har lokacin, bata ce masa komai ba ya fita daga ɗakin hannun sa ɗauke da robobin sedai yana dosar wajen ya hango floor ɗin very clean and neat ga Kuma ƙamshi da yake yi, tsaye yayi yana bin toilet ɗin da kallo kafin ya juya zuwa ɗaki da sauri.
Ajiye robobin yayi cikin baskets ɗin su ya shiga bin Kisnah dake zaune da kallo, a ƙafar wandon ta da hannun rigar ta ya tsayar da kallon sa ganin yadda suka jiƙe, basket ɗin kayan wankin toilet ya ɗauka ya shiga bubbuɗe su yana dubawa, alamun an yi amfani dasu da ya gani yasa ya tabbatar itace ta wanke.
"Wa ya saki fita wanke toilet bayan kin San da ciwo a ƙafar ki kuma ba iya wanke irin wannan kikai ba, what in kika faɗi fa".
Yaso ya bata dariya sedai kuma ta ji daɗin kulawar sa
"Taya bazan je wankewa ba bayan ka kwanta a gajiye baka yi wanka ba saboda rashin kyan toilet ɗin, nikam ba zan iya barin ka kwanta haka ba".
Sosai kalaman ta suka yi tasiri a ran shi haka kuma yaji daɗin concern ɗin da ta yi showing Masa sedai be nuna ba ya bar abin a ransa
"Rashin yin wanka na is none of your business, ƙafar ki ya kama ta ki maida hankali ta warke ba yin abinda ba'a saki ba".
"Ciwo na is none of your business, wankan ka ya kamata ka maida hankali kayi ba damuwa akan ciwon da ke jiki na ba". Ta bashi amsa cikin jin haushin rashin appreciating effort ɗin ta.
Murmushi ne yayi escaping a lips ɗin sa jin ta maida masa da amsa daidai abinda ta faɗa masa, be kuma cewa komai ba ya fita daga ɗakin ya wuce toilet ɗin bayan ya ɗau mini basket ɗin wankan su dake ɗauke da sponge, soao, shower gel, da turaren wanka.
Ba kaɗan ba yaji daɗin wankan duk da ruwan ya Salamce ba kamar lokacin da ya sirka shi ba da zafi sosai, ko da ya gama se yaji kamar ya sauke wasu nannauyan kaya a jikin sa, fitowa yayi hannun sa riƙe da bucket ɗin ruwan basket ɗin wankan a cikin sa jikin sa sanye da baƙar jallabiyar da ya shiga da ita a hannun sa.
Gaba ɗaya se yaji shi so uneased feeling kamar kowa na kallon shi dan be saba hakan ba, be ji sauƙin abin ba se da ya shiga ɗakin su sannan ya sauke ajiyar zuciyar relief.
Tashi tayi ta fita daga ɗakin ganin ya ciro kaya ze saka amma ya ƙi sawari ya tsaya kallon ta riƙe da kayan a hannunsa, lokaci ta bashi sosai sannan ta koma ɗakin dan tasan ya isa ace ya gama shiryawa, jallabiya ya ɗora kan three quarter ɗin da ke jikin sa ya ratse ta ya nufi fita
"Ina kuma zaka je yaa".
Ta tambaya da sauri, ɗan tsayawa yayi tare da kallon ta
"Ita kuma sallar wa ze yi min?, ko bake kika faɗa min an kira ba?".
"To wasa nake ai, na faɗa ne dan ka tashi kayi wanka, shugaban an iya baƙar magana".
Ta ƙarashe can ƙasa kamar me gunguni.
Bece mata komai b aya koma cikin ɗakin ya zare jallabiyar jikin sa ya ajiye kan jakar kayan sa kana ya nemi waje yayi zaune kan carpet ɗin dake tsakiyar ɗakin ya rage daga shi se three quarter da t-shirt mara nauyi da ta kama shi a jikin sa.
Tana ganin ya koma ɗakin ta fita ta shiga neman abinda zata ɗora musu girkin dare, jallof sphagetti take son yi sedai basu da kayan miya da vegetables ɗin da zata haɗa dasu, komawa ɗakin tayi ta dube shi yana zaune
"Zan ɗora girki yaa amma babu kayan miya da sauran abin buƙata".
Shiru yayi yana tunanin wane girki ta iya da har zata ce masa ba kayan haɗi, shifa ko da ya siyo kayan abinci ba wai nufin sa ta dinga girki ba dan yasan ba abinda ta iya, ya siyo ne dan ya dinga dafawa da kansa, yayi musu breakfast, lauch da dinner, in Kuma ya fara fita sana'a se ya dinga musu breakfast da dinner launch Kuma se ta dinga siya.
"Ki bar girkin se gobe yau zan siyo abinda za'a ci gobe kuma se ki min listing duk abinda babu se a siyo".
Ya faɗa yana kaiwa jingina, bata ƙi ba ta koma ta zauna bayan ta mayar da abubuwan da ta fito dasu da wanda zata yi aikin girkin dasu.
Haka suka cigaba da zama shiru kowa da tunanin da yake a ransa har aka kira magrib ya fita, kamar yadda yace haka ya shigo da ledar da yayi musu takeaway da zasu ci da dare bayan yayi sallar isha a masallaci................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, Comment and share fisabilillah.
Ouummey 41 (8/28/2022 8:55 PM)
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________