Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 104570 words

Chapter 14 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1429

Ads at the middle of Article

dan be san side ɗin wa ze ɗauka ba.


"500k". Kisnah ta faɗa as the sum da zata biya in aka maida mata baya, da sauri wani matashi yace


"1mil".


"2 mil". Ita ma ta faɗa, shiru wancan yayi se wani ɗan magidanci da ya tashi da sauri


"2.5 mil". Ya faɗa ganin yadda wancan yayi shiru


"3 mil". Ganin kowa yayi shiru alamun ya sallama yasa dole aka maida mata baya ta kuwa miƙe ta hau cashe rawar ta ba tare da ta damu da mutanen dake wajen ba, wayar ta ta miƙawa Meenah tace tayi wa managern wajen transfer ɗin 3 million ɗin sa shikuwa se washe baki yake cikin farin ciki, irin haka na cikin dalilan da yasa suke son zuwan Kisnah wajen.


Ana gama Ra one aka fara Action Jackson, kamar dai yadda ta faɗa basu tashi ba se five mins after one, ita kanta a lokacin a gajiya take sedai tana cike da farin cikin kallon da tayi da ma na sa'insar da suka yi da mutanen.


"Amma Kisnah 3 million sabida kawai maimaita kallon waƙar 5 minutes? Haba this is way too much".


Hameedah fa ta fara kaita ƙarshe da iskancin da take mata fa, bata manta jiya yadda ta ringa kushe Ya Saraki ba har da wani kiran shi mere driver, dole ma ta taka mata birki wallahi.


Ƙanƙance golden brown eyes ɗin ta tayi cikin duban Hameedah


"Meke damuwar ki da rayuwa ta ne Meedah, batun yau ba fa kike min shisshigi da rainin hankali ba, ko dan kinga ina ƙyale ki shiyasa kika sami guts ɗin faɗa min kowace banzar magana tazo bakin ki, yanzu da na biya 3 million nawa kika cika min, nawa nai maula ina kuka Hajiya Hameedah me kuɗi taji tausayi na ta bani na cika, kin san i hate nonsense ko, to wallahi tun yanzu ki shiga hankalin ki dan ina raga miki ne being my friend if not ke in an ce kiyi dering Kisnah You won't even start, mtsww".


Da sauri Leekha da Meenah suka fara bata haƙuri yayinda baƙin ciki da ɓaci rai ya cika Hameedah, ganin ta dan Kisnah ta fisu kuɗi da kyau yasa take musu rashin mutunci yadda ta ga dama sedai ba yadda zata yi haka ta bata haƙuri itama kafin ta juya wajen motar ta tashi ga ta wuce gida.


Tsaki Kisnah ta raka bayan motar Hameedah dashi kafin ta ɗagawa su Meenah hannu alamun bye, da sauri Leekha ta tare ta


"Amma dai zaki wajen Surry gobe ko, kinga duk yau baki leƙa ta ba".


"Munyi waya da ita ɗazu kin san tana da fahimta so i brief her about that assignment, dole ba inda zani gobe saboda wuni zanyi kan shi in gani in Allah zesa in iya yi".


"Hakane, Allah ya sa ki iya ɗin".


"Ameen bye, Meenah ki gaida Momma, Leekha ki gaida Adda".


"Za su ji insha Allah, sweet dreams Queen".


Murmushi ta sake musu kafin ta ƙarasa wajen motar ta, knocking tayi ta ji shiru, ta sake yi nan ma shiru, wannan karon dagewa tayi ta ƙwanƙwasa da ƙarfi da yasa Saraki farkawa daga baccin da yake yi da ba wani daɗin sa yake ji ba dan a takure yake.


Zama yayi sosai hana gyara rigar jikin sa da ta tattare kafin yayi unlocking motar yana tada kujerar da ya kwantar, jin ƙarar buɗewa yasa ta buɗe murfin ta shiga tana faɗin "sannu". Which he answered using body language.


Rufe ƙofar tayi yayin da ya ɗau goran ruwan dake gaban motar ya fita ya wanke fuskar sa dan wartsake wa sosai, ajiye robar yayi inda ya ɗauka ya ciro kyakkyawan farin handky ɗin sa a aljihu ya goge fuskar sa kana ya rufe motar ya tashe ta tare da yin reverse ya fita daga cinemar.


Tafiya suke shiru kamar kurame se karatun Alkur'ani da har yanzu yake yi be kashe ba, time to time yake ɗan kallon ta ganin yadda ita kaɗai take sakin smiles kamar wata zararriya sedai be yi magana ba har suka kusa ƙarasawa gida,


"Please yi parking gaban wancan restaurant ɗin".
Ɗan kallon restaurant ɗin gaban su yayi kana yayi parking kamar yadda tace, fita take neman yi sedai tuni ya dannawa motar lock hakan yasa ta kasa buɗe murfin.


Juyowa tayi ta kalle shi irin na tambayar why ɗin nan, haɗe rai yayi yana kallon ta shima


"A haka kike nufin zaki shiga wannan gurin?".


Duban jikin ta tayi taga dai bata yi komai ba, fes take kamar yadda ta baro gida dan haka ta maida idanun ta kan shi


"Ai banyi datti ba ko".


"Bani kuɗin ki faɗi me zaki siya".


Ba tayi musu ba ta miƙa masa wayar ta
"Ban fito da kuɗi ba yau, ga wayata nan ka musu transfer ta nan, 7139 is the pin, kilishi nake so na 15k guda biyu kaga 30 kenan ko?, Se strawberry ice cream cup huɗu, ayi ledan wrap ɗin kilishin with two cups ko wanne".


Gyaɗa mata kai kawai yayi tare da double tapping phone ɗin dan duba in da security sedai babu dan haka yayi unlocking car ɗin ya fita.


Sake kallon kanta dan ganin ko dai dagaske akwai abinda tayi da yasa yace bazata shiga wajen ba sedai har lokacin bata ga komai ba, shrugging kafaɗarta tayi koma menene tunda dai ze siyo mata ai shikenan.


Kamar yadda tace haka ya siyo, two wrap ɗin kilishi se four cups of strawberry ice cream, buɗe bayan motar yayi ya saka kafin ya shiga mazaunin sa yana miƙa mata wayar ta, karɓar tayi tana faɗin


"Thanks Ya Saraki".


Smile ya sake mata da yasa ta zaro idanun ta tana juyowa gaba ɗaya ta zubawa fuskar sa ido


"Did you just smile Ya? Oh my God kaga kuwa yadda kayi kyau, Lord of universe ni Kisnah".


Sosai ta bashi dariya yadda tai maganar wholeheartedly, yanzu ya kuma fahimtar wani abu a tare da ita, she's Frank and open, tana yin abu da iya gaskiyar ta ne ko me za'a yi mata kuwa, kalli dai yanzu abinda tayi kamar wata yarinya ƴar 12-13 years.


"Dan Allah smile again Ya Saraki, ina son sake ganin your cute dimple pls".


"Shut up, I don't smile you're dreaming".


Kwaɓe fuska tayi
"Dreaming without sleeping, Allah nidai I see you smile".


"See, mafarki kawai kika yi, so nawa mutum be yi bacci ba yake mafarki ma, i too experience that sometimes".


"Ban taɓa ji ba amma, kenan nima yanzu nayi mafarkin kana murmushi, amma gaskiya fa kayi kyau a mafarkin".


Girgiza kai kawai yayi ya cigaba da tuƙin sa yana tunanin shekarun ta nawa da take da rashin wayo haka, kalla yadda yanzu yayi fooling ɗin ta kuma ta yarda.
'she's just a little spoiled girl'. Ya ayyana a ransa.


Cikin haka suka ƙarasa gida ta fito daga motar tareda buɗe baya ta ɗau leda ɗaya wanda ke ɗauke da kilishin da two cups na icecream ɗin ta bar ɗayar a ciki


"Ga naka nan Ya, thanks and Good night".


Ya Masa rasa me zece se kawai ya tsaya yana kallon ta, da gaskiyar mutane da ke cewa baka sanin halayyan mutum seka mu'amalan ce shi, kamar dai yarinyar nan, a kallon farko mutum ze concluding zata yi girman kai da ɗagawa, rashin mutunci da dis respect, wanda shima a haka ya kalle ta da farko, sedai yanzu sam ba haka yake gani tattare da ita ba.


Maganganun Inusa ne suka dawo masa kansa ranar da ya kawo shi gidan, gyaɗa kai yayi cikin yarda da abinda Inusan ya faɗa kafin ya sa hannu ya ciro ledar ya ɗauka ya wuce ɗakin sa.


Ajiye ledar yayi ya ciro icecream ɗin ya saka a fridge haka kilishin dan baya jin wata yunwa yanzu, komawa kan sofa yayi ya zauna tare da jawo wayar da aka bashi yai mata texting "thank you"....................✍️.








©️ Ouummey 📚✍️.










☑️Ote, comment and share fisabilillah.


































Ouummey 17 (8/8/2022 6:50 PM)





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________
















Page 1️⃣7️⃣










_______________________📖 Daga wanka ya fito ɗaure da towel a ƙugun sa se ƙarami a kansa da yake tsane gashin sa har ya tabbatar ya gogu kafin ya cire ya ajiye, kan mattress ɗin sa ya zauna tare da janyo jakar da ya zuba kayan mayukan sa ciki ya fito da wanda za shafa ya shafe jikin sa da shi kafin ya ciro mayukan gashin sa kana ya miƙe ya ɗauko madaidaicin mirror ɗin da ya siya tun yana zaune a shago ya ajiye kan sofa ta yadda ze iya ganin komai sannan ya shiga mulke gashin kan sa da su ɗaya bayan ɗaya kafin ya ɗau comb ya shiga taje shi kana yayi styling ɗin shi, sosai gashin yayi kyau ya kwanta kamar wani Balarabe.


Wardrobe ya ƙarasa ya ciro wata Black shadda da ya ɗinka tun yana kasuwa tare da Alh Musa, ba wata me tsada bace amma ba ƙaramin kyau tayi masa ba kamar ka sace shi ka gudu, links ɗin sa ya saka a hannun rigar tare da na wuya, farar hular da ya siya yake haɗa shaddar da ita ya ɗauko yasa tare da takalmin da shi kuma Alh Musa ne ya siya masa ranar da ya fara saka shaddar yace ga takalmin ya haɗa dashi se ya fi kyau.


Fatabarakallah Ahsanul khaliqeen, kyan da Saraki yayi cikin shaddar ba me faɗuwa da baki bane just imagine it yourself, turarukan da ya siyo jiya ya jawo yana feffesawa dan jin ƙamshin kowanne har ya sami wanda yayi masa ya feshe jikin sa gaba ɗaya kafin ya ajiye ya ɗau daddumar da ya ɗora kan sofa tun kafin ya shiga wanka ya feshe ta da turare itama dan yau juma'a, wayoyin sa ya kwasa ya fita tare da ɗiban canjin 2k ɗin sa na jiya ya fita bayan ya saka wayoyin sa a aljihu.


Sosai ma'aikatan gidan suka dinga yaba kyan da yayi shifa'u sedai yayi musu murmushi tare da faɗin ya gode har ya fice daga gidan pray mat ɗin sa rataye kan kafaɗar sa.


******************


"Wannan gayun se ina kuma auta".


Murmushi Laylah ta saki jin auta da ummah ta kira ta dashi wanda se tana san tsokanar ta take faɗa, juyawa tayi ta dubi umman da ke zaune kan stool ɗin mirrorn ɗakin Laylahn


"Allah umma yau tsokana kike ji kawai, bayan kin san zance gaida Mami ne".


"Oh na manta, ashe za'a je gaisuwar surukai ne, to ai ba kya tafi haka ba dama ina da saƙo wajen gimbiyar bari in baki ki tafi mata dashi".


Umma ta faɗa tana fita daga ɗakin yayinda ita kuma ta cigaba da gyara ɗaurin ɗankwalin shaddar da take yi, sosai ta ɗaura shi ya zauna kai kace kafa mata shi akai, kallon kanta take yi tun daga sama har ƙasa tare da yabawa da adon nata, turare ta ɗauka me sanyin ƙamshi ta fesa dan bata manta ba Ya Yarima ya taɓa mata faɗan saka turare me ƙarfi.


Mayafi ta ɗauka da ya hau da kayan jikin ta ta yafa tare da fita daga ɗakin nata daidai lokacin umma ta fito daga nata ɗakin hannun ta riƙe da leda me dan girma ta miƙa mata


"Gashi ki kai mata ki kuma ce ina gaishe ta sosai da sosai".


"Insha Allah umma nah, se na dawo".


"Allah ya dawo dake lafiya autar umma kuma surukar gimbiya".


Da sauri Laylah ta fice daga gidan cikin jin kunyar umman fuskar ta ɗauke da murmushin jin daɗin surukar gimbiya da umma ta kira ta dashi, driver ta saka ya kaita sashen gimbiya Haleematu dan da tazara sosai tsakanin sashen matan sarki dana waziri wanda ita ɗin ɗiya ce wajen wazirin sarki Muhammadu Hasheem II.


Da sallama ta shiga turakar gimbiya Haleematu dan tuntuni ta zama ƴar gida da bata neman iso kafin shiga, kan kilisar ta ta sake ta zaune cikin kyakkyawan adon ta dake ɓoye ainahin shekarun ta ya sa ayi mata kallon batakai haka ba alhalin tana cikin shekarun dattijan taka ne yanzu.


Da farin ciki gimbiya Haleematu ke amsa gaisuwar Laylah da ta zube gaban ta, ba ƙaramin farin ciki take yi ba a duk lokacin da tayi tozali da yarinyar dan tana ganin ta ne kamar Sarakin ta wanda ba dan wannan ƙaddarar ta sharrin maƙiya ba da tuni yanzu ana batun bikin su ne, Allah ya sani tana son yarinyar saboda irin soyayyar da take gwada wa Sarakin ta wanda ita in har zaka so Saraki to fa ka gama mata komai a duniya.


Baya ga haka ita ɗin ɗiyar aminiyar ta ce da bata da kamar ta a duk faɗin garin Giwa da kewayen ta, ga kuma babanta da ya kasance ɗan uwan me martaba kuma wazirin sa me dattako da sanin ya kamata.


Karɓar ledar hannun Laylah tayi kana ta sallama kuyangin ta suka shiga hira da Laylahn irin hirar uwa da ɗiyar ta har lokacin Sallah yayi, ko da gimbiya ta shiga yin Sallah ɗakin ta itama Laylah ɗakin kusa da na gimbiyar ta shiga ta gabatar da Tata sallar kana ta fito ta wuce personal kitchen ɗin gimbiyar dake nan falon ta.


Abinci ta dafa mata me rai da lafiya tare da lemukan gargajiya da ta san gimbiya tafi son irin su dan ƙarin lafiya da ƙarfin jiki kana ta kwaso ta jera su kan ledar cin abinci da ta shimfiɗa gefen kilisar gimbiyar.


Ko da Mami ta fito taga aikin da Laylah tayi ba ƙaramin daɗi taji ba ta dinga saka mata albarka a ranta tana fatan Allah ya dawo mata da Sarakin ta lafiya ayi bikin su dan fa tabbas ɗan nata be fa mata bayan Laylah.


Cikin so da ƙauna da kuma shaƙuwar dake tsakanin su suka ci abincin tare suna ɗan taɓa hira jefi jefi har suka gama Laylahn ta kwashe kwanikan zuwa kitchen ta kuma wanke su tare da gyara kitchen ɗin tas.


A ranar kam ma'aikatan sashen gimbiya hutu suka yi dan Laylah ce ta sake gyara sashen tare da haɗe shi da sassanyan turaren wuta me shiga rai kana ta shiga ɗakin gimbiyar ta gyara mata wardrobe kafin ta gyara ɗakin gaba ɗaya.


Waɗannan halayen na Laylah ke kuma ƙara wa gimbiya son ta Dan duk sanda tazo gidan tofa bata da zama ta dinga hidima da gimbiyar kenan har se ta koma nasu kafin ta huta wanda yanzu ma haka ne.


Ko da ta tashi tafiya kaya sosai mami ta haɗa mata har ledoji biyu tare da godiya da sa albarka har suka rabu.


Cikin farin ciki ranar Laylah tayi bacci wanda duk take gidan Mamin hakan ke faruwa dan sosai hankalin ta yake kwanciya da ƙaunar da Mamin ke mata har take ji a ranta bata da sauran matsala sets jiran dawowar Saraki dan ta san tabbas fa bashi da wata mata se ita Laylahn gimbiya.


***********


Zaune take cikin kyakkyawan garden din ta ta barbaza takardu a gefe gabanta kuwa laptop ɗin tace haka kuma hannun ta riƙe da wayar ta, wannan zaman duk na yin assignment ɗin CON005 ne sedai har fiye da mintina Talatin da zaman nata ba abinda ta fahimta haka ko kan pen bata saka a paper da sunan rubutu ba, dafe kanta tayi tana sauke ajiyar zuciya cikin tsananin damuwa dan zuwa yanzu kam bata san ya zata yi ba wallahi, tayi tayi amma ta kasa gashi ita bata san wani senior ɗin su ba a department ɗin law balle taje ko ɗora ta a hanya ayi, hasalima ko ƴan level ɗin su ba kowa ta sani ba balle ayi maganan saman su.


Cikin karaya ta miƙa hannu ɗan sake duba question ɗin a karo na ƙarshe taga ko zata fahimci me za'a yi dan Allah ya sani daga wannan karon in har bata gane ba to ta haƙura ta bar wa Allah kawai, ta tafi da carryover ɗin ta gyara next year.


Zaro takardar tayi se taga wasu takardu sun faɗo tare da ita, ɗan tsira wa takardun ido tayi ganin su ɗauke da rubutu alhalin ita tasan bata ajiye paper me rubutu ba se kuma ta kauda kanta ta ɗau wadda take buƙata a lokacin sedai ganin ta itama cike da rubutu yasa ta ɗan yi turus gaban ta na faduwa kafin kuma ta shiga warware ta da sauri har hannun ta na rawa.


Cikin sauri ta shiga bin paper da ido wadda ta tabbatar tata ce dan ga sunan ta da ragowar information ɗin ta da ta rubuta nan jikin paper, kamar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi jikin ta ya ɗau rawa kafin ta shiga karanta jerarren rubutun da akayi shi cikin ƙware wa layi bayan layi duk da kuwa takardar bame layika bace Dan plain sheet ce, tsaf ta karanci rubutun gaba da baya sedai ganin be ƙare ba yasa da sauri ta ɗauko papers ɗin da suka faɗi ɗazu ta hau neman continuation ɗin ta ɗora karatun, wasa wasa nan da nan ta gama karantawa kuma se lokacin ta fahimci me malamin ke nufi amma saboda tsabagen mugun ta yadda yayi twisting question ɗin ba za ka taɓa kawo abinda yake nufi ba kenan.


Tsananin murna ne ya kamata har da hawayen ta sosai ta ninke takardun ta maida cikin textbook ɗin ta se kuma ta shiga tunanin waye ya amsa mata question ɗin, ita dai in bata manta ba har jiya da ta shiga test bata rubuta ko A ba bayan question, kuma tun da ta fita da littafin ba wanda ta bawa haka kuma tun da ta dawo dasu ta kai ɗaki bata kuma ɗauko su ba se yanzu haka kuma ba wanda ke shigar mata ɗaki balle tace.


"Yaa Saraki". Sunan yai ringing a mind ɗin ta, ɗan shiru tayi kafin kuma ta shiga gyaɗa kanta cikin yadda da shi ɗin ne yayi mata dan tun a motar ta bar littafin da zata shiga test se jotter kaɗai ta shiga dashi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads