Showing 33001 words to 36000 words out of 104570 words
Chapter 12 - SARAKI (The Accused Prince).txt
neman faɗuwa ta dai samu bata faɗin ba, bathroom ta faɗa a gurguje dan It's 5 mins to eight, wardrobe ta buɗe ta janyo wata straight English gown kusan similar to ta jiya sedai wannan bata kamata sosai ba kuma ta kai mata ƙasa sedai tana da tsaga sosai ta baya dan ya kai har wajen gwiwar ta, da sauri ta zura rigar bayan ta saka bra da pant ɗin ta, faɗin yadda silver gown ɗin ta mata kyau ma is a total waste of time, scarf ta janyo silver me ƙyalƙyali ta ɗaura saman kanta sedai gashin ta ya fito ta tsakiyar sa duk da ta nannaɗe shi amma seda yakai ƙasan wuyan ta.
A gurguje ta ɗebi wayoyin ta da kayan rubutun ta ta fice ko breakfast Bata iya tsayawa yi ba dan shirinta kaɗai ya cinye fiye da 40mins, bata sami kowa a falon ba ta wuce compound cikin sauri wanda takalmin ƙafarsa silver color me tsini be hana ta yi ba, tsaye tayi tana bin compound ɗin da kallo sosai ganin bata ga Saraki ba, wajen da ma'aikata ke zama in sun gama aikin su, gurin yasha grass carpet me kyau ɗauke da tables manya da kyawawan kujeru gefen su flowers ne masu kyau da ke fitar da sassanyan ƙamshi, tun da Khamees shugaban ma'aikata ya hango ta ya miƙe da sauri har ta ƙaraso, gaishe ta ya soma sedai bata kula hakan ba ta shiga tambayar sa
"Ehm wannan sabon driver ɗin be zo bane?".
"Wai Saraki? Yazo amma ya ɗan fita yana amsa call yanzun nan".
"So sunan sa Saraki kenan?".
"No baba me gadi ya kirashi da hakan dan yace abubuwan da yake kaman tafiya,magana, miskilanci da izzar shi kaman na yaran sarauta shi yasa masa Saraki amma sunan shi na gaskiya Ahmad ne".
"I see". Kawai tace ta juya daidai lokacin Saraki ya turo ƙaramar ƙofar gate ɗin ya shigo, da ɗan sauri ta ƙarasa tana masa alamun ya fito da mota.
Farar mota ya ɗauko ganin kayan jikin ta is way related to farin, da sauri ta buɗe ta shiga kana yai hanyar gate da kafin ya kai ma gate ɗin ya buɗe kansa ɗan tuni nasu gadi suka saka password ɗin ganin fita zasu yi, seda suka hau kan titi sosai kafin ta ɗan dube shi a kaikaice tace
"Good morning".
Ya ɗan yi mamakin jin ta gaida shi sedai ya dake ya amsa da "morning" batare da ya kalle ta ba hankalin sa na kan tuƙin sa, itama bata kuma cewa komai ba ta buɗe littafin kan cinyar ta ta cigaba da dubawa.
Bakowa yasan halayen Kisnah sosai ba se close friends ɗin ta dake tare da ita kusan ko yaushe wato su Meenah, ba wani abu bane gare ta gaishe da wanda ya girme ta tun bare ma in ya kama girman sa, eh tana da tsiwa da rashin kunya amma fa ga wanda ya siya da kuɗin sa ma'ana wanda ya takale ta ko ya zubar da girman shi.
"Where are we heading to?".
Batare da ta ɗago ba ta bashi amsa dan karatun ya sha kanta
"Federal University, Manyan".
Cikin ƙaton gate ɗin school ɗin ya wuce wanda tun ɓullowar motar ta security suka buɗe amma mamaki suke na yadda yau bata yi horn ba kamar yadda ta saba ga kuma yanayin driving ɗin cikin nutsuwa.
Bakin department ɗin da ta dinga kwatanta masa har suka ƙara so yayi parking tare da kashe motar, buɗe side ɗin ta tayi ta fice bayan ta kwashi litattafan ta, rufe ƙofar da ta bari a buɗe yayi yana lumshe idan sa cikin karanta suratul Kahf da be samu yayi ba yau saboda baccin da yaci ƙarfin sa.
Tun daga nesa ta hango su Meenah wannan karon su uku dan babu Surry da ke asibiti, ƙarasowa sukayi gare ta suka amshi books ɗin hannun ta suka jera tare zuwa cikin theatre ɗin, row ɗin tsakiya suka shiga kuma layi na farko suka zazzauna kafin suka fara gaisawa a tsakanin su, karɓar littafin hannun Meenah tayi ta shiga yi musu bayanin abinda tayi researching jiya wanda take tunanin za'a iya tambayar su, sosai tayi musu ƴar ƙaramar tutorial Wanda har se da lecturern ya shigo sannan ta rufe littafin ta miƙawa Leekha, karɓar Leekha tayi ta haɗa da nata da nasu Meenah ta fitar dashi can gaban theatre ɗin sannan ta dawo, miƙewa duka suka yi jin malamin na faɗin each line mutum biyu yake son gani dan gurin akwai girma sosai, fita Kisnah da Leekha suka yi suka bar Meenah da Hameedah na sake spacing tsakanin su.
Tunawa da Surayya yasa ta fasa budar saman theatre ɗin ta wuce wajen malamin dake tsaye yana jiran su gama gyarawa
"Good morning sir". Juyowa yayi ya dube ta yana amsa gaisuwar Tata
"Good morning, fatan dai lafiya".
"No sir, nazo yin report ne concerning Surayya kabeer da ba zata samu damar zuwa yin test ba saboda rashin lafiya, yanzu haka tana kwance gadon asibiti sir".
"And where's her relatives da basu zo sun yi reporting ba se ke".
"Her brother is presently in Canada for business Kuma ba ta da kowa bayan shi, matar sa kuma hate...oh Is just personal sir, but you can confirm, tana Gare well hospital, room 13, Dr Ibrahim nura ne ke handling case ɗin ta".
Gyaɗa kai yayi cikin yarda da batun nata kafin yayi wa Surayya fatan samun lafiya da tabbatar mata da zai organizing team ɗin bincike aje a dubi Surayya a kuma tabbatar da in bata da lafiya da gaske, nodding kanta tayi tare da masa godiya ta juya neman inda zata zauna.
Bin bayan ta sir Kashim yayi da ido cikin yaba kyan ta tare da mata fatan shiriya, if not sabida ayyukan ta he would have marry her fan sosai take da kyau take kuma burge shi sedai yasan ko hauka yake baze kai ta gidan su sunan wadda yake so ba duk da shiɗin ba saurayi bane dan yana da mata har da ƴaƴan su biyu.
Cikin jin daɗi take ta amsa questions ɗin cike da nutsuwa dan alhamdulillah ba abinda bata sani ba cikin wanda aka tambaya, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama ta sake bi through kafin tayi submitting ta fita, da idanu majorityn ƴan class ɗin suka bita da ido har ta fice, su fa har yau gani suke bata da wani ƙoƙari kawai tana siyan marks da jikin ta a wajen malamai though yawancin su zasu bada shedar ita bame zuwa office ɗin malamai bane se in ta zama dole.
Duk wani abu related to karatu lokacin ta take bashi cikakken shiyasa bata wasa da zuwa makaranta, ƙarya kaga ta makara dan tun fara karatun ta har zuwa yanzu da take 400l zata iya irga iya makarar da tayi haka bata yadda rashin fahimta ya shiga tsakanin ta da wani malami shiyasa kawo yanzu malami ɗaya ne suke ƴar tsaka dashi, shikuma haka kawai ya ɗau karan tsana ya ɗora mata, tun tana kau da kai da ido a kanshi dan bashi girman shi na malami har ya ƙure ta tayi masa rashin mutunci shiyasa shi kuma duk hanyar da ke disga ta ko ya kayar da ita a course ɗin ita yake nema, yanzu haka akwai assignment ɗin da aya bayar Wanda individual ne kowa da questions ɗin sa, har zuwa yau da za'a yi submitting jibi ta kasa fitar da amsar, tayi tayi har ta haƙura ta cigaba da normal routine ɗin ta sedai deep down abin na mintsinin ta a rai, bata taɓa samun wata matsala ta carry over, spill over ko resit ba se gashi yanzu ƙarfi da yaji malamin na neman kai ta ƙasa.
Cikin wannan tunanin ta ƙarasa ta shiga motar se dai bata rufe ƙofar ba, jiran su Meenah zata yi sedai bazata iya tsayuwar cikin ranar da ake yi me zafi sosai ba shiyasa ta shiga motar, hannu takai ta ƙara ƙarfin AC ɗin kana ta kwanta cikin kujerar ta ta shiga tunanin ta wace hanya ya kamata ta ɓullowa malamin.
Tayi nisa cikin tunanin har bata ma san tana hawaye ba dan ita kam kacokan fari cikin rayuwar ta ta ɗora shi ne kan karatun ta, shine number one priority a rai da zuciyar ta shiyasa yanzu da matsala ke neman Kunno Kai duk hankalin ta ya tashi, bawai bata da yadda zata yi da malamin bane dan ko yanzu taso ya bar makarantar tabbas za'a masa transfer haka kuma ko A tace tana so tana da yadda zata samu ko da baya so kuwa se ya bayar sedai tana da wani principle ɗaya, sam bata son alfarma a karatun ta, bata son hanya ko wani abu, tana so ne ta bugu ƙirji tace ta sami kwalin ta ne da ƙoƙarin ta da zufar ta, wannan shine aƙidar ta shiyasa ba ta tunkari kowa da batun ba.
A kaikaice Saraki ke kallon yadda take hawayen wanda alamu ya nuna koma meye ya sata kuka ba ƙaramin matsayi gare shi ba a ranta haka kuma ba ƙaramin so take wa abin ba, to ko dai malpractice tayi aka koro ta daga hall ɗin ɗan be ga wanda ya fito ba har yanzu bayan ita, taɓe baki yayi yana ayyana hakan ne ma dan yadda wannan take yasan ba wani abu ta iya ba balle ta tsinana dole seda satar amsar.
Ƙarasowar su Meenah ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi ta maza ta saka hannu ta share hawayen idon ta dan bata taɓa nuna karaya ba gaban su yanzu ma kuma bazata fara ba shiyasa bazata bari suga hawayen ta ba, ɗan kallon Saraki tayi ta gefen ido hopping be ganta tana kuka ba se ma taga idanun sa a kunshe suke hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya.
Fita tayi daga motar ta tsaya jikin ƙofar dake buɗe har lokacin tana facing su Hameedah dake tsaye kusa da ita, congratulations suka shiga yiwa juna na sauƙin da test ɗin ta musu kafin suka dinga thanking ɗin ta, murmushi kawai take musu batare da ta amsa ba dan tana cikin damuwa sosai, Meenah ce ta fara lura da hakan ta matsa sosai ta ruƙo hannun ta
"Kina cikin damuwa Kissy I can read it on your face, me ke damun ki pls".
Ɗan ajiyar zuciya ta sauke tana sake danne raunin ta
"Kema kin sani, me ze sani damuwa bayan CON005, wallahi har yanzu na kasa fitar da assignment ɗin nan, dama na daɗe da sanin malamin nan ya tsane ni shiyasa ya tsiro da Wannan assignment ɗin ɗan ya samu damar laƙabin carryover, ko Baki ji wai shine matsayin C.A da test gaba ɗaya ba?".
"Nikaina na kasa gane damuwar malamin nan da ke Kisnah, amma me ze Hana kiyiwa Deen magana nasan dole ze saka ya fita hanyar ki".
"Bana buƙatar connection a karatuna Leekha, I want to earn my certificate with my brain ba money ba, Dan haka ba wanda zan faɗa wa, Allah See's everything and will surely give me a way out".
"Then Goodluck Mrs brain". Hameedah ta faɗa kamar cikin wasa but cike da isgilanci da farin cikin yau dai ta ƙarewa uwar iyayin basira, murmushi kawai Kisnah tayi dan ba tun yau ba tasan Hameedah is jealous of her sedai bata damu ba dan tasan tuni ta yiwa Hameedar zarra nesa ba kusa ba.
"Hope you guys duk kun gama naku?".
"Just some little corrections". Meenah ta faɗa
"Already finished". Leekha itama ta faɗa
"Since yesterday". Inji Hameedah, gyaɗa kai Kisnah tayi kafin ta juya dan shiga mota
Wy
"Wish all of you success, will be going, see you tonight a cinema".
"See yha dear, byee". Suka haɗa baki wajen faɗa, ita kuma tai ya nasu tare da rufe murfin tana gyara zama.
'So wannan ce damuwar ta kuma the reason behind her tears, so this is how she loved her studies, he pray she get an alternative, ko ba komai she's doing good here'.
Tashin motar yayi tare da yin reverse ya fice daga makarantar haka ma Meenah da Leekha Hameedah kuma tace she get something to do..............✍️
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, comment and share fisabilillah.
Ouummey 15 (8/7/2022 9:41 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 1️⃣5️⃣
_______________________📖 "Kai ni K&S drinks".
"You show me the way". Nodding tayi ta shiga nuna masa hanya har suka ƙarasa, horn yayi security dake bakin gate suka fito dressed in blue black uniform of theirs, ko da sun ga motar tace basu fasa checking ɗin motar ba sannan aka basu hanya suka wuce first gate, ko a second and third gate ma seda aka sake duba su kafin a basu hanya suka wuce.
Ƙaton building ne da girman sa ya zarce misali da ba ma zan iya misalta shi ba, just ku auno shi a idanun ku.
Da sauri ɗaya daga cikin securityn ya ƙaraso ya buɗe mata ƙofar ta fito sannan ya maida ya rufe ta tunkari main building ɗin Company ɗin.
A hankali Saraki ya juya ya dubi litattafan ta da ke ajiye kan seat ɗin da ta tashi kafin ya sa hannu ya janyo su ya buɗe ya shiga dubawa, sannu a hankali yake bin rubutun yana karantawa kafin ya fara flipping through pages ɗin, bin paper ɗin da ta faɗo yayi da kallo kafin ya ɗauka ya warware, question ɗin assignment ɗin da take batun ta kasa ce dan gashi nan bayan sunan ta, admission number, department, course code da kuma question bata rubuta komai ba,
Sunan ta ya koma sama yana maimaitawa cikin tunani to ya akayi ya canja ya koma Kisnah, to kodai nickname ɗin ta ne Kisnah kamar yadda yaji ana kiranta?".
"Sakeenah Safwan".
Ya sake maimaita sunan kafin ya maida hankali kan question ɗin, ƙaramin cute smile ya saki ganin question ɗin ba wata me wahala bace amma har take kuka akai, kamar wanda ake controlling ya samu kan sa da ɗaukar pen ya ɗora kan plain sheet ɗin ya soma rubutu, sosai ya maida hankali kan rubutun da yake yi, seda ya cika plain sheet ɗin gaba da baya ya kuma zarar wata da ta ɓullo ta cikin textbook ɗin ta, wasa wasa seda ya cika plain sheet uku sannan ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya, bin rubutun yayi da ido yana karantawa har ya kai ƙarshe kafin ya ninke takardun ya maida mata cikin ƙaton exercise book ɗin ta kana ya cigaba da karanta textbook ɗin.
Sosai ta ɗauki lokaci supervising all the workers kafin ta fito dan tafiya gida cikin gamsuwa da aikin da suke yi, tun daga nesa da ya hango ta ya rufe littafin ya ajiye mata inda ya dauka tare da kunna motar, shigowa tayi tana karɓar file hannun ma'aikacin da ya rako ta dasu Sannan ta rufe ƙofar.
Jan motar yayi zuwa waje wanda a nan ma seda aka sake checking ɗin motar tasu kafin bar su su wuce, yanzu kam gida suka yi yayi parking a lot ɗin su ta fita, har ta fara tafiya se kuma ta tsaya har ya fito shima
"Kaje wajen Khamees me kula da ma'aikata ya nuna maka ɗakin ka".
Gyaɗa mata kai yayi taci gaba
"Help me with these files please, sun min yawa ga books again".
Karɓar files ɗin yayi a hannun ta ita kuma ta riƙe littattafan suka nufi ƙofar falo, yanzu kam ta tadda su Mommy har ma da ƙawayen ta biyu a falon gaban su cike da drinks da kayan snacks hakima Maigado a gefe riƙe da waya ta maƙala earpiece a kunnen ta, shiga tayi falon without excuse kamar yadda ta saba yayinda Saraki ya dakata bakin ƙofar yana jiran ta kai books ɗin hannun ta ta dawo ta karɓi files ɗin, jin bata ji takunsa a bayan ta ba yasa ta juyo ta dube shi yana tsaya ta masa izinin shiga
"Come in Mana, ya ka tsaya a nan".
Ɗan shiru yayi se kuma ya shiga thinking ta sanar da na ciki za'a shigo, shiru duk suka yi Mommy da ƙawayen ta suna binta da kallo har ta kai tsakiyan ɗakin tana niyyar ƙarasawa saman ta sannan ta juyo, ganin Saraki tsaye yasa ta dakata tare da dawowa kusa da ƙawayen Mommy
"Excuse me, join those two a three sitter ɗin ki bashi wajen ya zauna, ya gaji so baze iya tsayuwar har na hau sama na sauko ba".
Sosai fuskar matar ya nuna ɓaci rai sedai kafin tayi magana Mommy tayi saurin tarar ta
"Haba Kisnah, ai se ya zauna a kan rug ko ko bashi ne sabon driver ɗin ki ba?".
"Yes shine se aka yi yaya?".
"He supposed to wait outside, ba daraja bace ace muna zaune sama jere driver ma na zaune, its so disgracing, hakan ze iya sa ya dinga girman kai kalla fa ya shigo muna zaune amma ko gaida mu be yi ba".
"So sannu Nana, Nace sannu Nana Asma'u uwa ta, to yaƙi ya tsaya a wajen kinji akwai abinda zakiyi ne, kina wani maganar ba daraja bace to hell with the daraja, ke har wani daraja gare ki, to bari kiji wallahi Ya Saraki da kike magana akai ya fiki daraja nesa ba kusa ba ya kuma fiye min ke da duk abinda ya shafe ki so dubu, in bazaki iya zama inda yake ba You better pack your belongings and move back to where you return from dan nan gida nane bana gyatumin wani bane haka ba na mijin wata ba so I have the right nayi yadda naso a kuma lokacin da naso, da zaki wani ce be gaishe ku ba to ya gaida ku yace ya gaida wa, gayyar munafukai?, Mtsww, Ya Saraki have a seat please".
Ta ƙarashe looking at Saraki da har lokacin ke tsaye, without saying a single word ya zauna