Header Ads
Showing 42001 words to 45000 words out of 104570 words

Chapter 15 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1432

Ads at the middle of Article

ta koya wa su Meenah abin da tayo research haka kuma da ta shiga Company a mota ta bar su gaba ɗaya wanda tun da ta ɗebe su daga motar da suka dawo daga Company bata kuma fito dasu ba se yanzu, to in bashi bane waye yayi mata, aljanu ko wa? Kai shine ma, wallahi shine.


Da sauri ta kwashi takardun ta fita daga garden ɗin ta shigo ta main falo kafin ta sake fita da gudu gudu ta ƙarara compound ɗin tana ƙwala masa kira, sosai ta ke kiran shi not minding yadda ragowar workers suke binta da kallo, Isa me bawa flowers ruwa ne ya shaida mata ai yaje masallaci, bata ji daɗi ba dan ta so ta sake shi yayi mata confirming shine ta kuma gode masa sedai zata jira ya dawo.


Juya wa tayi zata koma ya turo ƙaramar ƙofar gate ɗin ya shigo da sallama a bakin sa, da sauri ta juya dan da ɗan karfi yayi sallamar hakan yasa itama ta ji, da gudu ta nufe shi wanda shi dan be lura da tahowar ta ba se ji yayi an faɗa kan sa da ƙarfi, ƙamshin turaren ta ne yasa ya gane ita ce ya kuwa yi saurin janye jikinsu a yana istigfar a ransa yan kuma haɗe fuska a fili.


Sakin baki tsirarun ma'aikatan dake kaikawo a compound ɗin suka yi suna bin su da kallo kasancewar da yawa sun tafi sallar juma'a, bata ko bi ta kan su ba ta ɗago tana kallon Saraki da ya haɗe rai cif sedai ita ko a kwalbar rigar ta dan bata ma san abinda tayi ya haɗe rai ba kuma dama ya saba kusan ko da yaushe haka yake haɗe rai in Yana tare da ita so shiyasa ma bata wani damu ba.


"Yaa kai kayi min assignment ko, daama wallahi na kasa yi kaga tun da safe nake zaune amma ko fahimtar question ɗin ban yi ba, Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi ya ja da ran iyayen ka, Nagode sosai, kai ban ma san ta ya zance maka Nagode ba wallahi".


Ta faɗa sounding very very happy, addu'ar da tayiwa iyayen sa a ƙarshe ya sa ya ɗan sassauta haɗe ran da yayi yana kuma tausar kan sa da ita hakan a wajen ta bakomai ba ne and he promised to transform her so be kamata ya dinga haɗe rai haka ba dole ta nasiha ce yi mata musamman irin wannan lokutan da take cikin farin ciki.


"Kalli, ƙafar ki ko takalmi babu kika fito".


"Yaa bazaka gane farin cikin da nake ji ba, I feel like in yi ta rawa har se na gaji".


"So in kikayi rawa se a san kina farin ciki kenan? Wat of kiyi alwala kiyi sallah raka'a biyu ki gode wa Allah da yakawo miki ɗauki lokacin da kika yi giving up? A tunani na hakan se fi ko?".


"Sure hakan zan yi riƙe takardun nan bari kaga in ma je inyi yanzu da sauri".


Ta faɗa tana sama sa takardun a hannun sa kafin tayi cikin gida da gudu, girgiza kai yayi ya wuce ɗakin sa bayan ya sake haɗe rai ganin yadda gana ɗaya ma'aikatan compound ɗin suka saki aikin su suka maida hankalinsu kan su.


Zama yayi kan sofa bayan ya shigo ɗakin ya cire hular kansa ya ajiye tare da pray mat ɗin kana ya wuce wajen fridge dan ciro ruwa se kuma ya ci karo da ledar kilishin jiya da cups ɗin icecream, fasa ciro ruwan yayi ya ɗauki cup ɗaya na icecream ɗin ya koma kan sofar ya shiga sha a hankali har ya ƙarar kafin ya jefa cup ɗin cikin ƙaramin waste bin dake gefen ƙofar ɗakin.


Bum yaji an faɗo Masa ɗaki without taking excuse hakan yasa ya ɗago da sauri dan ganin waye se kuma ya ci karo da fuskar ta tana sake masa kyakkyawan smile, ɗan yamutsa fuska yayi dan Allah ya sani ya fara takura


"Me kika zo yi nan".


"Ya kai fa nazo nema, kaga tun da kayi min assignment ɗin dama akwai test ɗin da Zamuyi gobe kuma kaga akwai abubuwan da ban iya ba acikin shine na ɗauko ka koya min, laah na manta ban faɗa maka ba nayi sallar na godewa Allah kamar yadda kace".


Ɗan dafe kansa yayi saboda tsabar surutunta da har ta fara samasa ciwon kai


"Ki kwashi litattafan ki gobe na koya miki".


"Yaa ai gobe ne test ɗin fa".


"To kai na ciwo yake, ya zan miki ne, a'ah".


Jikin ta ne yayi sanyi jin yace kan sa na ciwo, kwashe takardun ta da ya ajiye kan sofa a gefen sa tayi tare da juyawa zata fita


"Sorry yaa, ban sani bane Allah ya baka lafiya".


Dan tsaki yayi kafin ya dakatar da ita


"A ina zamu yi karatun dan ba dai a ɗakin nan ba".


Da sauri ta juyo cikin farin ciki se kuma ta ɗan rage fara'a


"Baka ce kanka na ciwo ba".


"Out in bakya buƙata".


"To muyi a garden ɗina ko main garden gashi can ta gefen gate".


"Meet me there a main garden ɗin by 3pm".


Da sauri ta amsa da toh kafin ta fita cikin jin daɗi....................✍️.










©️ Ouummey 📚✍️.








☑️Ote, comment and share fisabilillah.




























Ouummey 18 (8/9/2022 8:06 PM)





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________


















Page 1️⃣8️⃣
















______________________📖 Kamar yadda yace haka ta sake shi a main garden ɗin gidan by 3pm suka soma karatun, ba ƙaramin yabawa ƙoƙarin ta yayi ba a zuciyar sa ganin duk abinda ya koya mata take ta ke kwashe shi dama akace kabar abinda zuciya ke so.


Itama a nata ɓangaren haka tai ta yaba yadda yake mata bayani dalla dalla cike da ƙwarewa da sanin malamar karatu, sosai ta kasa daurewa har ta kai ga furta masa abinda yake yawo a ranta


"Yaa wai ya akayi ka iya karatun mu haka sosai, ko dai kaima law ka karanta?".


Shiru yayi mata a lokacin dan be san amsar da ze bata ba, be shirya sanar da wani asalin sa ba haka ne shirya tattauna personal life ɗin sa da outsider ba Kai koma insider ɗin ne he's not interested balle kuma ita da yanzu ne yake kan sanin wacece ita.


"Amma kuma me yasa baka nemi aiki ba tun da nasan ka gama karatun ka da alama".


Ta sake faɗa dan ta ɗau shirun sa as yes eh law ya karanta


"I was withdrawn from the school". Ya sami bakin sa da faɗa dan alamu sun nuna Yes cikakkiyar lawyer ɗin za'a yi a wajen, shikuma ba ya san duk abinda ze kawo ta zarge shi kan abinda ba haka bane.


"Eyya, so sad amma akan me?". Ta sake tambaya further Dan dai tasan baze yiwu ace akan bashi da ƙoƙari bane se dai something different da take son sani dan daga yadda yake mata bayani ta tabbatar a lokacin da yana makaranta ba za'a rasa sashi cikin gifted and talented students ba.


"Don't wanna talk about it now".


Gyaɗa kanta tayi cikin nuna fahimta kafin tace


"I understand, maybe later ko?".


Ɗaya mata gira kawai yayi dan ya fahimci in ba haka yayi mata ba ba ƙyaleshi zata yi ba alhalin taɓo maganar makaranta da karatu da tayi yasa yaji incident ɗin da ya faru ya dawo masa sabo Dan if not because of it da tuni i yanzu yana zaune in his own office handling office stuffs.


Ba su tashi daga karatun ba se da aka kira Asr prayer hakan ma dan ya tashi ne ba yadda zata yi dashi dan in ta ita ne bata ƙi sukai har magrib ba yana koya mata tana kuma ƙiriniyar tambaye tambaye abinda babu ruwan ta be kuma shafe ta ba.


Kashegari har bakin ƙofar lecture hall ɗin su ya kai ta tare da mata addu'ar fatan nasara abinda ya saka Kisnah dakatawa ta ƙura masa ido for a while kafin ta gyaɗa masa kai idon ta na kawo ƙwalla, abu ne tunda ta taso zata ce ba wanda ya taɓa damuwa da yi mata wato fatan alkhairi da nasara in zata yi assignment, test ko exam.


To wa ma take dashi bayan kawu da family ɗin sa? Se ko abokan Abbu da ta manta rabon da ta taka ƙafarsa gidan su haka suma tuni suka dena damuwa da neman ta tun bayan wani cin mutunci da kawu ya yi musu lokacin da ya kaita England karatun primary ita kaɗai shikenan duk suka zare hannayen su a kanta.


Kawu da matar sa Mommy kuwa.. hmmm.....bata masan ya zata kwatan ta su ba, ta wani ɓangaren the two are perfectly synonyms of each other, in other views Kuma su ɗin antagonist wa juna.


Suna da matuƙar close similarities ta ɓangaren tsananin son kuɗi da kwaɗayi sedai suna da bambanci wajen tsananin son ƴaƴa da Mommy ke dashi da kuma hassadar da bata ma iya ɓoye ta, munafunci da baƙin ciki kuwa wajen Mommy har na siyarwa akwai, to taya ma zata yi wani tunanin samun fatan nasara ga matar da a kullum so take taga bayan ta ko kuwa ga kawu da kullum hankalin sa na kan yadda za sami kuɗi ta kowace hanya.


Bayan su waye a cikin rayuwar ta? Ƙawayen ta, yes ƙawayen ta, taya zata fassara su? Da wa zata fara a ciki? Meenah da ba inda ta dosa a rayuwar ta ban da son holewa, ita dai tayi ta watsa ƙwayar da indai da ita to fa bata da matsala, ko kuwa da Leekha da tsabar shan giya har ya taɓa mata hanta seda akai mata aiki ko kuwa Hameedar da ƙiri ƙiri take iya fahimtar ƙyashi da hassadar ta cikin ido da Muryar ta har ma da ayyukan ta, dama dama Surayya, duk da mugun son mazan ta tana son karatu haka ta kan yi magana ta cikakkun masu hankali in taso bayan ita gaba ɗaya ragowar ukun ita ce ta sauya rayuwar su kan son karatu, a dole suke yin shi ba dan sun so ba shiyasa basa taɓa damuwa da wata matsala a karatun nasu wanda duk aka samu akasi ita ke yin tsayin daka har se ta tabbatar komai ya koma daidai kuma yana tafiya yadda ya kamata.


Ajiyar zuciya tayi kafin ta saka yarda ta ɗauke ɗigon hawayen da ya sauka daga idon ta tana ƙarasa shigewa hall ɗin, sama sama ta gaida da ƙawayen nata kafin ta maida hankali kan littafin da ta shigo dashi wanda ta fara rage karatun exams ɗin da zasu fara ne next week insha Allah, tana jin su suna hira sedai bata ma maida hankali ba balle ta fahimci akan mene suke hirar.


Cikin haka halitta ɗaya da zata iya kalla tace ta tsana a duniyar ta ya shigo cikin hall ɗin, ita bame damuwa da shiga shirin mutane bace shiyasa kafin kaji ta furta ƙi ko so abu ne da ake daɗewa sedai wannan ta furta masa kalmar ƙi da tsana so adadin da harshe baze iya ƙirgawa ba kuma ba dan komai ba se dan yadda yake nuna mata tsananin ƙiyasta ta ban mamaki da shigar da bawa ruɗani dan ko kallon banza bata taɓa gwada yi masa ba har se da shi da kansa ya siya da kuɗin sa, MALAM SAMINU kenan, shine malamin da ke ɗaukar su course ɗin CON005 haka kuma mutumin da ya ƙirƙiro wani assignment dan kawai don ganin ya kaita ƙasa sedai Allah Alhakeem baze taɓa bashi nasara ba a kanta.


Cikin haɗa murya ɗaliban duk suka shiga furta gaisuwa a gare shi, be amsa ba se da ya ƙare musu kallo har idon sa ya sauka a kanta kafin ya ɗauke kai ya amsa musu, cikin ƙankanin lokaci suka shiga aiwatar da abinda ya tarasu wato lecture, ko da ya dakata shiru yayi yana bin su da kallo kafin ya fara jefo tambayar da kusan rabin ɗaliban suka ɗaga hannu sedai gaba ɗaya ya tsalle su ya nuna Kisnah da kanta ke ƙasa, taɓo ta Leekha tayi tana mata magana a hankali da yasa ta ɗaga kan ta ta dubi Leekhar sannan ta maida kan malamin, sake maimaita mata question ɗin yayi cikin son ganin ya tozarta ta takowace hanya.


Miƙewa tayi ta fara magana amma mutumin nan yace baya ji dana haka ta fito gaban board, bata ƙi ba dan hakan a wajen ta ba sabon abu bane, takawa tayi cikin yanayin tafiyar ta yayinda kusan duk wani ido ya dawo kanta, doguwar riga ce me kamar baya sedai wannan anyi shaping ɗin ta ta yarda ya ta kamata tsam haka kuma me makon ta ɗaura ɗan kwali kan gashin ta da tayiwa bun se kawai ta naɗa shi in v style ta yadda tsakiyar ke waje kuma ba ƙaramin fito da fuskar ta ɗaurin yayi ba.


Gaban board ta tdaya kamar yadda yace kafin ta fara bayani cikin nutsuwar ta har ta kai ƙarshe sedai ko kafin ta rufe bakin ta ya sake jefo mata wata haka yai tayi mata cikin son dole se ya ruɗa ta sedai har yanzu wannan mutumin be san wace Kisnah ba, ta kuma ji daɗi sosai dan yawancin tambayar da yake yi jiya sunyi makamantan su da Ya Saraki jiya shiyasa dole ya haƙura ransa a jagule da ɓacin ran rashin nasarar da yayi.


Ko da ze fita nan ya fara karɓar assignment ɗin da ya bayar kafin yasa kai ya wuce cike da fatan samun damar ta a nan ɓangaren.


Da farin ciki sosai a fuskar ta ta fito suka wuce theatre ɗin da zasu yi test wacce take opposite da hall ɗin da suka gama lecture, cikun taimakon Ubangiji shima be bata wahala ba tayi ta gama ta bayar ta fice.


Buɗe ƙofar motar tayi ta zauna yanayin ta kaɗai ya isa bayyanar da farin cikin da take ciki a lokacin, batare da ya tambaye ta ba ta shiga sanar da Saraki duk yadda komai ya wakana daga test ɗin har yadda suka yi da M. Saminu a lecture hall, shi kansa yaji daɗin yadda ta fita kunyar jama'a dan mutane irin su Kisnah da suka yi ƙaurin suna idon kowa a kansu yake.


Cikin kwanakin da suka biyo baya sosai ta ajiye partying dasu clubbing dan fuskantar exam ɗin ta wadda daga ita se project da zasuyi shikenan sun gama degree ɗin su gaba ɗaya se zama jiran result da zasuyi shiyasa gaba ɗaya bata son jin wani abu me sunan matsala dangane da karatun nata.


A kwanakin sosai shaƙuwa ta shiga tsakanin Saraki da Kisnah saboda kusan kullum tare suke wuni suna karatu wanda shima ba ƙaramin pleasure yake driving cikin hakan ba dan kina komai hakan na tuna masa da memories ɗin karatun sa.


Ranar da zasu Fara exams ɗin sosai ya saka ta ta kusan kwana a pray mat dan ba ta sassafe bace se ƙarfe sha ɗaya tukunna shiyasa ta sami damar yin Bacci ta Sami peace of mind.


Yau ma kafin ta fita addu'o'i ya mata sosai cikin mata fatan dawwamammiyar nasara kafin ya sata karanta wasu addu'o'i kafin ta fita daga motar, itama bata wani damuwa take yin duk abinda yace dan zaman su na kwanakin yasa ta saba da yadda yake da yawan addu'a dan har sallama yanzu takanyi sa'i da lokaci kafin ta shiga waje.


A wajen sa hakan ma nasara ce shiyasa be fita takurawa da se ta canja komai a lokaci guda ba dan yasan hakan ba me yiwuwa bane kuma baya san taga kamar takura ne shiyasa yake bi da ita a hankali yadda zata yi komai cikin ra'ayin kanta ba tursasawa ba haka kuma ya fahimci in yace ce tursasa itama ɗin ba kanwar lasa bace ba tanƙwaruwa zata yi ba.


Cikin ikon Allah tayi jarabawar ta ta gama lafiya tare da taimakon Saraki da kacokan yanzu ta ɗau duk wata girmamawa ta bashi, Ya sama Ya ƙasa take kiran shi haka yanzu ya san abubuwa kaɗan kaɗan game da ita da wasu daga cikin dukiyar ta wanda da kanta sanar dashi dan samun solution kan matsalolin ɓatan kuɗi da ta nemi shawara a wajen shi.


Bayan dogon nazari ya bata solution ɗin da da taimakon Ubangiji se gashi an yi nasarar gano me wannan account ɗin da kuɗaɗen nan suka shige, wani ƙaramin ma'aikaci ne dake da post ɗin gyara files, mamaki ya kama su kamar me da tunanin taya ya kasance shi, tawace hanyar har yake samun access haka, dole akwai wani behind his shadows sedai anyi yin duniya mutumin ya faɗi wa ya sashi ya kafe kan ba kowa, dole aka miƙa shi kotu aka yanke masa hukuncin shekara biyar a prison tun da ya kasa biyan tarar da aka yanka masa ta miliyan uku, sosai Kisnah yaji tausayin sa har tana batun zata ce ta yafe sedai tuni Saraki ya dakatar da ita dan irin su dole se ana hukunta su dan ba wai ze Dena bane ko tace ta yafe ɗin.


Kayan abinci yasa ta siya ta kai gidan mutumin da a kallon farko da tayi wa gidan ta daɗa tabbatar da tabbas wani ne ya sashi dan ɗaki ɗaya ne a gidan se kitchen da toilet ɗin da aka zagaye da kwano, jijjiga kai kawai tayi kafin ta saka almajirai aka shiga da kayan abincin da suka ciki booth da su.


Godiya ba kama hannun yaro matar sa ta shiga yi ita da ƴaƴan ta mata biyar se maza biyu dan dama cikin matsalar abincin suke.


Yanzu ma zaune yake kan ɗaya daga cikin kujerun office ɗin ta na K&S shopping mall da ke gaban table ɗin ta wanda shine karo na farko da ya shiga office ɗin shima bisa dagiya da magiyar da tayi ta masa har da guntun hawayen ta, laptop ɗin da take aiki da ita

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads