Header Ads
Showing 63001 words to 66000 words out of 104570 words

Chapter 22 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1437

Ads at the middle of Article

da kallo har bata ƙi ƙiftawa, sake bin trace ɗin in da take kallon yayi ya tabbatar hannun sa take kallon se ya bar ƙoƙarin sauke sleeve ɗin da yake ya ɓoye hannun a bayan sa hakan yasa ta farga ta maza ta gyara zama tana maida kanta kan system ɗin cike da kunyar da bata taɓa tunanin tana da ita ba.


Ficewa yayi ya tsaya bakin office ɗin ya gama gyara hannun rigar kafin ya wuce masallaci, ko da aka idar se da ya tsaya yayi addu'o'in sa kamar yadda ya saba kafin ya dawo har lokacin kuma tana kan aiki cikin system ga tarin tulin takardu gaban ta


"Miss lokacin sallah yayi, You leave the work kije kiyi se ki dawo ki cigaba".


Cak ta tsaya da aikin da take tana bin shi da kallo cikin tuno ita yaushe rabon ta da yin Sallah da rana irin haka, ita fa sallar ta se dare yayi take haɗe su duka tayi a lokaci ɗaya tayi ta huta dan ita bata san wannan gutsire gutsiren da ake yi, a yi ɗaya yanzu ayi wata anjima shiyasa take haɗe nata.


"Zan yi duka in na koma gida, hankali na baze kwanta ba se na gama shigar da informations ɗin nan".


Ɗan zato ido yayi yana kallon ta


"Excuse me, bangane se kinje gida ba, sallar ce se kinje gida ko aikin?".


"Haba sallar dai, aikin nan ai bazan bar office ba yau se na ƙara sa shi bari ma in ƙara maida hankali ka gani".


Mamaki ne ya kusan kar shi daga zaunen da yake, sallar take batun se taje gida Sannan zata haɗa, La hula wala quwwat, wannan wace irin rayuwa ce, anya yarinyar nan na da ilimin addini ko yaya a tare da ita kuwa? Baya tunanin hakan ko da dai hakan be kamata ya zama abin mamaki ba in yayi duba da ɗabi'un ta da kuma ayyukan ta zuwa kan shigar ta, in yayi rantsuwa baze yi kaffara ba yarinyar nan bata ma san me ye addinin ba kwata kwata, ita dai kawai tana amsa sunan musulma ne amma kuwa iyayen ta sun cuce ta cuta mara adadi.


Haɗe ran sa yayi sosai dan ma kar ta samu wani fuskar yi masa musu ko wata magana


"Ki tashi kije ki yi sallah nace kar ki bari ranki ya ɓaci".


Sakin aikin tayi ta tsaya kallon shi cikin son yin magana sedai yadda ya haɗe gabas da yamma kamar wanda ke jiran ƙiris ya rufe ta da duka yasa ta miƙe tana ture system ɗin da ƙarfi har tana kusan faɗuwa, toilet ta nufa tana maganganu ƙasa ƙasa wanda bai jin me take faɗa ta shige.


Alwala tayi sedai gyaran dake cikin alwalar ba kaɗan bane, fitowa tayi tana goge fuska da towel ƙarami tare da nufar wani ɗaki me kyau me matsakaicin girma da akayi shi dan hutawa in an gaji da aiki ta shige, da ƙyar ta sami ƙaramin veil ta naɗa shi a kanta tayi Sallar.


Baki buɗe Saraki ya bita da kallo ganin ko minti biyu cikakku ba tayi da shiga ɗakin ba amma har ta fito kuma wai tana nufin tayi Sallah


"Kam bala'i". Ya furta batare da ma yasan yayi ba, lallai this girl is unbelievable, tabɗi, lallai Yana da aiki a gaban shi amma for now Bari ya ƙyale ta kar tursasawar tayi yawa har ta fara jin haushin sa tun da suna tare da sannu ze gyara ta ne da izinin Ubangiji.


Ɗauke kan sa yayi daga kanta ya cigaba da aikin sa itama haka har se can wani lokaci kafin ta ture system ɗin tana tura baki


"Yunwa nake ji sosai yaa".


Ko kallon ta be yi ba ya cigaba da aikin sa, to ban da ma rainin hankali d ta faɗa masa me take nufin yayi mata, ko tana nufin ya fita ya siyo mata abinci ne, ashe ko zata wuni da yunwar.


Ganin yadda yayi banza da ita yasa itama ta share shi ta janyo wayar ta, order ta bayar sannan ta jingina da kujerar da take kai tana rufe idanun ta, ba ƙaramin gajiya tayi ba wallahi, ga gajiyar tafiyar jiya bata gama sakin ta ba ga ta aiki da ta kuma rafke ta se take jin kamar ba ita ba dan rabon ta da aikin wahala irin haka tun tana level two kafin daga baya taji gaba ɗaya zaman Companies ɗin ya ishe ta ba ta so ta maida ragamar kula da komai hannun kawu.


Knocking ɗin da ake a ƙofar yasa ta miƙe ta ƙara sa tareda buɗe ƙofar dan shi kam ko motsawa be yi ba balle ta sa ran yaje ya buɗe, deliveryn restaurant ɗin da tayi order ne yayi handing mata packs ɗin ya juya dan tayi musu payment online.


Gaban sa ta ajiye Masa pack ɗaya ta wuce da ɗaya wajen ta ta ajiye, fridge ta buɗe ta ciro goran ruwa biyu da lemo ta ajiye masa nasa ta ajiye nata gaban ta, ba tare da damuwar komai ba na wai yana zaune ta buɗe pack ɗin ta ta soma cin fried sphagetti with veggies da pepper soup ɗin ta hankali kwance tana yi tana sipping drink ɗin ta har ta ƙoshi kafin ta tattare komai ta ajiye a gefe ta ɗau ruwan ta sha to her satisfaction.


Duk abinda take yi yana sane sedai be maida hankali kan ta ba dan yasan dana ta saba cin abinci in public so cin abinci gaban sa baze gagare ta ba.


Messenger ɗin ta ta kira ta bashi ragowar da ta rage tace a bawa me so ta cigaba da aikin ta, wasa wasa basu bar office ɗin ba se after six, gudu sosai Saraki yayi ranar dan baya son missing magrib prayer da ake ta kira a masallatai, ko da yayi parking be fita ba se da ya sake jaddada wa Kisnah tayi sallah da ta shiga gida fiye da so uku sannan ya wuce a hanzar ce zuwa masallaci.


Ko da ta shiga wanka ta fara yi tare da canja kayan jikin ta da suka takure ta, gajeran wando ta saka da ya wuce cinyoyin ta se ƙaramar riga me kamar shimi tana yi tana tunanin yanda zata dena saka irin wannan kayan ta koma saka wasu, tuno da yace tayi Sallah yasa ta miƙe tana ɓaɓɓata fuska kamar yana gaban ta ya zurma hijabin tayi ƴar fakin ta kamar yadda ta saba.


Kan bed ta faɗa dan kam yau bacci zata yi da wuri dan ta huce gajiya ta kuma tashi da wuri gobe, da kayan jikin ta ta kwanta bayan tayi offing light tare da locking ƙofar ta, within minutes tayi bacci abin ta.


A can ɓangaren Saraki kuwa be dawo gida ba seda akayi sallar Isha, wanka yayi ya canja kaya zuwa jallabiya mara nauyi ya zauna kan sofar ɗakin ya buɗe pack ɗin abincin sa na tun office dan shikam kasa ci yayi a can, gani yake kallon sa zata dinga yi.


Seda ya cika cikin sa ya kwashe ragowar ya saka a fridge sannan ya zauna zuwa lokacin da abincin ze faɗa masa, tunanin ta ne ya faɗo masa a lokacin


"Allah yasa tayi Sallar". Ya faɗa a fili dan yasan kaɗan daga ayyukan ta taƙi yi ɗin, wanda tayi ma takura mata yayi to wanna da baya nan kuwa ai se abinda Allah yayi kawai.


Murmushi yayi tuno dramar su a office ɗin yau, ya sani she's so simple compared to girls of her age Kuma masu kyau da dukiya irin nata, ya sani da wata ce baya jin de iya tanƙwara ta cikin sauƙi haka bayan shi ɗin ba komai ne gare ta ba se mere driver Wanda yake mata aiki take biyan shi haka kuma yasan Allah ne yaso ta da shiriya shiyasa ya sa ta zama mara girman kai balle wulaƙanci though yakan ga tayi wa wasu sedai yawanci ba talakawa bane masu kuɗi ne wanda ya fahimci kodai sun shiga gonar ta ko kuwa sun wulaƙanta kan su.


Kwanciya yayi tare da karanto addu'ar bacci ya shafe jikin sa kana ya lulluɓa yana rufe idanun sa a hankali hopping bacci ya ɗauke shi kar ya kuma shiga wata duniyar tunanin da yake ta hana kan shi faɗawa a kullum.




*******


"Wai Awwaf me kake nufi da zaman da kayi a wajen ƴan iskan abokan ka bayan kasan ina jiran ka mu fara namu takun kan waccan ƴar iskar, in Kuma ka fasa ba zaka iya bane ka faɗa min in yi introducing wanda ze iya cikin tafiya ta".


Da sauri ya miƙe zaune yana hankaɗe matashiyar dake kwance kan sa, Muryar sa har tana rawa ya fara magana


"Haba Mommy wane irin bazan iya ba, kin kuwa san yadda nake burin mallakar yarinyar nan da har kike batun kawo wani, to wallahi bari kiji in kika yi hakan se na tona asirin kowa ya sani, gwara ma ki jira ni dan nan da kwana uku zamu dawo, ina dawowa kuwa ba ɗaga ƙafa zan yi ba dan nasan tun yanzu kun riga kun shirya yadda komai ze kasance".


"Are You threaten me?, Lallai har yanzu baka san wace uwar ka ba, ka wuce kwana ukun da kace ka gani in komai be faru ba, sedai kaji ana yi shashasha kawai".


Mommy ta katse wayar tana huci dan kalaman Awwaf ɗin na wai ze Tona asirin ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, zaman tayi a kan kujera tana jefar da wayar, da sauri ƙawar ta Jamila dake zaune ta cafe tana matsowa kusa da Mommyn


"Haba sadiya, meye abin fushi haka a maganar yaron nan, kin fa san su samarin nan in suka ga sun girma se haƙuri, kawai lallaɓa shi za muyi ya dawo dan plan ɗin se ya fi tafiya dashi dan nikam yanzu bana yadda da saka bare cikin aiki na kin san mutanen yanzu ba amana, kalli fa yadda yaron can Nuhu ya ci amanar Hajiya Talatu, yanzu gashi ta sanadin sa tayi biyu babu, shiyasa duk abin naka gwara shi ɗin dai, so ki kwantar da hankalin ki dan Ni nasa zamu yi Nasara, tabbas zamu lalata rayuwar Kisnah ni na faɗa miki".


Ajiyar zuciya Mommy ta sauke tare da wani zazzafan huci


"Duk yadda zan kwatanta miki yadda na tsani yarinyar nan Jamila ba lallai ki game ba, kin san dai yadda muka sha fama da rayuwa cikin talauci har Allah ya kashe iyayen ta muka dawo zama tare da ita cikin daula, ina faɗa miki yarinyar nan bata taɓa bari na na samu kwanciyar hankali ba tun ma tana yarinya har se da baban Maigado ya kai ta England karatu sannan na sami sauƙi muka sami damar rayuwa cikin jin daɗi da walwala muka huce duk wani haushin abubuwan da talauci ya sa mana a da, zan iya ce miki ban taɓa shiga cikin damuwar da na shiga ba shekaru huɗu baya zuwa yau wato dawowar yarinyar kenan, ban san wane irin banzan tunani ne ke damun baban Maigado ba amma saboda tsabar baƙin ciki yaƙi kai Maigado ƙasar waje karatu, ki ga dai yadda ita wannan ta yi kyau ta ƙaro aji ga wayewa shiyasa samari kamar ana mata wahayi dan ma ita bata saurarar su ita kuwa Maigado fa, duk da ta samu waye wa da aji amma ai ba kamar waccan ba haka kafin kiga saurayi ɗaya ya biyo Maigado da sunan aure wallahi se a fi watanni zuwa shekara, sedai an ayi rayuwa a ji daɗi sauƙi na ɗaya ita sam ba hakan a gaban ta amma da ya kike zaton tashin hankalin da zan shiga, yanzu fa ki kalla wai ta koma zuwa Companies ɗin ta zata dinga kula dasu manufar ta a hankali a hankali ta ƙwace komai nata dake hannun baban Maigado, ta yaya hankali na ze kwanta in har ban ga na Kai ta ƙasa ba fisabilillahi".


Sauke numfashi Jamila tayi tana gyara zama sosai tare da fuskantar Mommy


"Shiyasa nace miki da ki yarda Awwaf ya aure ta, a ganina ta haka ne kawai zamu sami nasara a kanta, kinga maganar Companies ko d ta ƙwace wa take dashi da zai kula mata dasu dole dai mijin t zata ɗora a kan komai so kinga sun dawo hannun mu dai haka kuma ta nan ne kaɗai zaki sami damar musguna mata ki fanshe duk tarin tashin hankali da damuwar da ta jefa ki a ciki ko ba haka ba?".


Shiru Mommy tayi dan ita kam Allah ya sani bata jin zata taɓa yarda ta bar ɗan ta auren yarinyar da ta san karuwa ce, ita da take fatan samun tsarkakkun jikoki da sirika me mutunci se ta yadda a kwaso mata kaska, to amma kuma duk batun Jamila na akan hanya, bari dai zata yi tunani taga wanne ne fi mata in ya kama auren se ta haƙura amma fa se ta tabbatar ta hana ga haihuwa dan bata buƙatar zuri'a daga gare ta.


Juyowa tayi ta kalli ƙawar ta kuma ƴar uwar ta da ta zuba mata ido dan jin me ta yanke


"Kin kawo shawara me kyau dan haka zan yi tunani Jamila, kafin dawowar Awwaf zamu tsayar da batu ɗaya".


Jinjina mata kai jamilar tayi ta reda sauke murya tayi mata raɗar da ta sa suka saki dariya tare da tafawa....................✍️.






















©️ Ouummey 📚✍️.




















☑️Ote, comment and share fisabilillah.


























Ouummey 27 (8/20/2022 8:40 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________














Page 2️⃣7️⃣






















________________________📖 yau kam tun shida ta tashi, wanka tayi ta canja kayan ta zuwa fararen sport wears ta fice training, jogging taje tayi ta dawo sannan ta wuce gym ɗin da ta saka a ka haɗa mata a wani ɗaki dake gefen personal garden ɗin ta, bata fito ba se after 8, a gurguje ta koma ɗaki tayi wanka ta zauna ta gyara jikin ta tare da shafa mayukan ta na jiki da na ka.


Tsaye tayi gaban wardrobe ɗin tana bin kayan ta da kallo cikin tunani kayan da zata saka, Muryar sa ce ta shiga maimaita kanta cikin ƙwaƙwalwar ta kamar lokacin yake faɗa


".......and the last shine you'll be dressing decently and abandoned clubbing, shikenan...........".


Ɓata fuska tayi kamar a lokacin yake gaban ta yana faɗa mata, sake kallon wardrobe ɗin tayi tana maimaita 'decent dress' a ranta sedai a idanun ta duk kayan ta a decent dan ita bata ga illar su ko aibun su ba.


Sauke idanun ta tayi kan wani Pakistan me matuƙar kyau, pusha Pink, ciro shi tayi ta warware tana bin shi da kallo, sosai ya burge ta da adon da akayi masa most especially na rashin nauyin sa, nan da nan ta zura shi a jikin ta kafin ta ƙarasa gaban mirror ta sha ga bin kan ta da kallo tun daga sama har ƙasa.


A hankali tayi sighing ganin yadda yau mata kyau sedai she's feeling uncomfortable sosai dan bata taɓa saka irin su ba, ita kam kayan ga kullum different designers English wears ne, da su ta buɗe ido kuma da su ta saba shiyasa duk lalacewar su ita bata gani.


Sake kallon kayan jikin ta tayi, rigar ta sauka har kan cinyar ta, wandon kuma ya buɗe sosai har yana fitowa ta tsayar gefe da gefen rigar yayin da ta tsuke da ƙafa se mayafin kayan dake hannun ta da bata san ya zata yi dashi ba dan bata jin zata yada shi ko a mafarki kuwa.


Turare ta fesa tare da kama gashin ta in chignon style ta ɗora masa sombrero ta fice bayan ta watsa phones ɗin ta cikin clutch kalar platform ɗin ƙafar ta wato blue.


Mommy dake zaune kan sofa tana kallon movies ta bi ta da kallo baki sake ganin kayan jikin ta, ba tare da ta kalli Mommy ba ta nufi ƙofar fita se kuma ta dakata tana dafe kan ta haɗu da faɗin


"Ouch, Allah yasa ban manta ba yau".
Da sauri ta koma falon tana ƙwalawa Rayya kira wanda yasa Rayyan fitowa daga kitchen da sauri tana amsa mata


"Please follow me akwai kayan da zaki taya ni sakko dasu, tun jiya ya kamata na fito dasu but na mance".


Saman suka koma tana gaba Rayya na bin ta a baya ta buɗe ɗakin suka shiga, kallon ɗakin kawai Rayya take tana sake ware idanu dan zata iya rantse wa tun da take bata taɓa ganin haɗaɗɗen ɗaki irin na Aunty Kisnah ba, ɗakin is just so wow masha Allah, tana can admiring ɗaki har bata ji maganar da Kisnah take mata ba se da ta taɓa ta


"Am sorry Aunty, na shagala wajen admiring ɗakin ki har ban san kina magana ba".


"Ke kam kullum ai a haka kike, Allah ya shirya ki kawai, ni ɗaukar mun wannan bag ɗin ki kai min ƙasa ki dawo yanzu Please".


Da sauri ta ɗauka tayi ƙasa duk da jakar da nauyi amma bata fi karfin ta ba, seda ta sauke bags shida kafin suka ƙare Kisnah ta rufe ɗakin suka sauka gaba ɗaya, zaune suka sami Mommy a inda take sedai yanzu gaba ɗaya hankalin ta baya kan kallon da take yana kan haɗaɗɗun bags ɗin ne, ficewa Kisnah tayi batare da tayi mata wani bayani ba kan kayan se can suka dawo falon tare da wasu ma'aikatan gidan uku.


Bags biyar ta nuna wa ma'aikatan suka ɗauka suka fitar dasu waje yayinda ta kalli Mommy


"Wannan bag ɗin ta Maigado ce, tsarabar resort ce kuma na manta ban bata ba tun jiya yanzu kuma am in hurry ba zan iya jira har ta fito ba se ki bata, am off".


Ta faɗa tana ficewa abin ta zuwa compound ɗin gidan inda aka ajiye ragowar bags ɗin kusa da blue ɗin motar da zasu fita da ita


"Yaa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads