Header Ads
Showing 24001 words to 27000 words out of 104570 words

Chapter 9 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1426

Ads at the middle of Article

ta sake shi a bayan ta bayan ta taje shi ta masa style me kyau.


Turarurrukan ta ta feffesa kafin ta jawo black designer wedge half cover shoe ta saka ta ɗebi wayoyin ta da system ɗin ta da key ta sauka falon ƙasa, kan two sitter sofa ta zauna tana zube wayoyin ta a gefen ta sannan ta jawo Centre table ta ɗora ƙafafun ta kana ta ɗora system ɗin kan laps ɗin ta ta shiga operating hankali kwance.


Maigado dake zaune kan dining ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba dan Allah ya sani ta tsani Kisnah beyond expectation, ba ƙaramin ɓacin rai da takaici take ji ba inta dubi gidan nan ta kuma tuno wai mailakin ta ne, yanzu haka da take zaune tana dai cin abincin ne dan bazata iya zama da yunwa ba amma gaba ɗaya tunanin ta yana kan yadda zata yi Mommy ta dawo gidan ne dan su fara planning yadda zasu ɗaiɗaita rayuwar Kisnahn da gaggawa, ga shima wancan banzan yaya Awwaf ɗin ya ɗau ƙafa ya bar gari wai birthday ɗin aboki.


Tsaki tayi ta dangwarar da cup ɗin hannun ta ta wuce fuuuuu ɗakin ta, sarai Kisnah ta jita sedai ko kallon ta bata yi ba dan ba itace a gaban ta ba, kacokan hankalin ta yana kan kuɗaɗen da spy ɗin ta da ta ajiye a Companyn gine ginen ta me suna K&C (Kisnah constructions) ya turo mata an nema an rasa ba kuma batun wani bincike akai.


Kusan awa ɗaya tana latse latse a laptop ɗin kafin wayar ta da take amsa kiran ma'aikatan gidan ta hau ringing, bata ji kiran ba har se ana biyu dan gaba ɗaya hankalin ta ya tafi kan aikin da take yi, picking tayi dan ganin 0045 wato number me bawa flowers ruwa kasancewar kowane ma'aikaci yana da number base on ɓangaren da yake aiki, haka kuma an bashi phone and sim card Wanda in ya kira wannan number ce zata yi displaying, karawa tayi a kunnen ta tana sauraren bayanin da yake mata kafin ta amsa


"Su ƙaraso main falo shi da Inusan kai kuma ka koma bakin aikin ka".


Ajiye wayar tayi ta sake maida hankali kan system ɗin, tsurawa screen ɗin ido tayi ganin account details ɗin da kuɗin suka shiga bayan sun fita daga account ɗin Company, sosai ranta ya ɓaci dan wannan ne karo na kusan biyar da aka samu irin haka kuma duk ta bi diddigi wannan account ɗin dai take gani dan haka wannan karon bazata saurara ba se ta gano ainahin me shi.


Sallamar da suka yi kafin shigowa yasa ta ɗan ɗago ta kalli ƙofar kafin ta ɗauke idon ta maida screen ɗin, bata amsa sallamar ba dan hakan ba ya cikin tsarin ta, turo ƙofa Inusa yayi ya shigo yayinda Saraki ke bin sa a baya, ƙasa kan carpet Inusa ya nema ya zauna yayinda Saraki yake tsaye dan baya jin ze iya zama ƙasa wani na sama wanda ba mahaifan sa ba (Sarautar ta motsa😜😂).


Seda ta ɗan ɗauki lokaci bayan tayi saving komai sannan ta ɗago fuskar ta a sake ta dube su, da hanzari Inusa ya fara miƙa gaisuwa ta amsa fuskar ta da walwala har tana tambayar sa ya family ɗin shi da harkokin sa, amsawa yayi cikin jin daɗin yadda bata wulaƙanta su duk da sun kasance a ƙasan ta kafin ya nuna mata Saraki da bayanin shine sabon drive ɗin da aka samo mata.


Kallon ta ta maida inda Sarakin ke tsaye hannun sa cikin aljihu, idanu ta fara bin sa tun daga ƙasa kan kyakkyawar tsaftatacciyar ƙafar sa dake nan sumul kamar baya taka ta zuwa kayan jikin sa har ta kai fuskar sa sedai kallo ɗaya tayi wa fuskar tasa ta ɗauke kanta da sauri saboda wani irin kwarjini da cika ido da taga yayi mata.


Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye idanun ta na kan Inusa ta furta


"Have a seat please, za muyi magana".


Bece komai ba ya nemi one sitter sofa ya zauna yana iya ƙoƙarin sa na ganin be yi zaman da ya saba ba duk yakai zaune kan kujera wato harɗe ƙafafu kan juna, irin zaman da yayi kawai seda ya sake sata jin nauyi da ɗan shakka dan zama ne irin na cikakkun jinin sarautar da suka gawurta da isa, izza da taƙama dan ya buɗe gaba ɗaya ya cika kujerar, wannan shine karo na farko da zata ɗauki drive batare da ta ƙare masa kallon tabbatar da tsaftar sa ba kamar yadda ta saba, shiyasa tunda bazata iya duban sa direct ba take satar kallon sa ta gefen ido.


Ɗan gyaran murya tayi kafin ta juyo gare shi sedai idanun ta na kan Tvn bayan sa ne dan bata jin zata iya kallon fuskar sa dan a hakama ji take yi gaba ɗaya ya cika falon da girman sa.


"Kamar yadda nasan Inusa ya riga da yayi maka bayani, driving ɗina zaka ringa yi to every where I headed to, ban da haka babu wani aiki kuma da zaka dinga yi".


Gyaɗa kansa yayi alamar ya fahimta hakan yasa ta cigaba da magana


"Zan dinga biyanka 300k every month, zaka kuma zauna a gidan nan ne saboda ina fitar dare ko ince ko yaushe ma zan iya fita so baze yuwu se na tsaya jiran zuwan ka kafin na fita ba, akwai abincin da ake bawa ma'aikata wanda se in sun ga dama sannan za su siya in Wanda aka dafa be musu ba, fatan zaka iya aiki tare da ni".


Shiru yayi kamar baze ce komai ba saboda batun zaman gidan da ta kawo sedai kuma be san yaushe ze sami wani aikin ba in ya bar wannan, tunanin hakan yasa shi nodding kansa kafin cikin daddaɗar Muryar sa ya fara magana karon farko tun shigowar sa gidan


"In har aikin baze dinga shiga lokutan ibada ta ba I think ba matsala na karɓa".


Jinjina kanta tayi cikin tsananin mamaki a ranta, me yake faruwa ne, its as if yana bata condition ne zata ce ko sharaɗi ne oho, sedai haka kawai taji zuciyar ta ta nutsu da yanayin shi na nutsuwa so take ta yarda da sharaɗin nasa


"Is okay, in har wannan ne ba matsala, sedai fa aikin ka ze Fara daga yau ne dan yanzu haka ina buƙatar fita".


Wannan karon Inusa ne ya bata amsa
"Hakan ba matsala bane Hajiya, ai ze iya farawa yau ɗin ma".


Miƙewa tayi tana faɗin
"Toh shikenan, ku ɗan jira ni".


Step ta haye zuwa falon bayan ta ɗau system ɗin ta, zama tayi kan tsadaddun royal chairs da suka ƙawata ɗakin tana sauke numfashi, in her whole life zata iya cewa shine mutum na farko da take jin girma da nauyin sa sosai tun bayan iyayen ta da suka rasu, bata san me yasa hakan ba ko kuwa dan yadda nutsuwa ta bayyana a jikin sa da kuma Muryar sa ne ?, Ko kuwa dan tsananin kwarjinin sa ne bata sani ba.


Nannauyan numfashi ta sauke kafin ta maida system ɗin ma'ajiyar ta ta nufi box ɗin da take ajiye keys ɗin motocin ta ta ɗauko shi gaba ɗaya, kana ta ɗauki ƴar mini purse ɗin ta baƙa ta fito bayan ta ɗebo kuɗaɗe masu yawa a cikin wani safe dake gefen wardrobe ɗin ta ta zuba.


Wannan karon da key ta rufe ɗakin kafin ta sauko ƙasa, lumshe idanun sa yayi dan ba ƙaramin hawa masa kai ƙamshin ta ya fara ba, duk da ya kasance me son ƙamshi amma be fiya son turare me ƙarfi ba.


Gaban kujerar da yake zaune ta tsaya tare da miƙa masa box ɗin, kyakkyawan hannun sa fari tas da shi dake cike da gargasa me ban sha'awa da ta kwanta luf luf ya miƙo dan karɓa, miƙa masa tayi tana sake jinjina tsaftar sa dan fararen aikafun sa dake a yanke very low bako alamun wani abu wai shi datti cikin su.


Komawa tayi ta zauna inda ta tashi ta buɗe purse ɗin ta ɗebo kuɗaɗe masu ɗan kauri da bata tsaya irgawa ba ta miƙa wa Inusa


"Ga wannan se kayi kuɗin mota, Nagode sosai Inusa, a gaida min da Ramatu dan Allah".


"Insha Allah zata ji, nasan da tasan wajen ki zan zo da se tace zata bini". (Ramatu matar sa ce, lokacin da yana aiki a gidan suna zaune ne a biya quarters ita kuma tana girki).


Ɗan dariya tayi tana faɗin
"Ai mutuniya tace sosai, nayi missing barkwan cin ta".


Da haka sukai sallama Inusa ya tashi ya fita Saraki ma ya miƙa ya bi bayan sa, a gefe guda daga cikin compound suka ɗan tsaya, Inusa ya dube shi cikin mutuntaka


"Insha Allah zaka ji daɗin aiki da ita dan sam bata da girman kai haka tana da sauƙi da daɗin mu'amala, bata da wulaƙanci sedai in akayi mata to bata haƙura se ta rama, gwargwado tana da alkhairi dan yarinya ce ta gari sedai dake rayuwa ɗan Adam baya taɓa cika cif to itama tana da nata halayyar da basu da kyaun ji balle gani, se ka kula sosai bata san yawan tambaya haka kuma bata san aringa mata shisshigi cikin al'amuran ta, in har zaka tsaya iya matsayin aikin da ta ajiye ka to na tabbatar maka se kafi kowa jin daɗin zama da ita, nasan ka baka da matsala tunda Idris ya shaida min haka sedai tunatarwa tana da daɗi, ka zama me amana dan Allah da kuma ɗauke kai ga duk abinda be shafe ka ba".


Ɗan murmusawa Saraki yayi da ba kowa ze gane yayi hakan ba jin yau wai shi ake faɗawa ya zama me amana, sedai ita rayuwa dama haka take kuma beji ko ɗiso na haushin abinda Inusan ya faɗa ba tun da ba sanin shi yayi ba balle ya san halayyar sa


"Insha Allah zan kiyaye duka, Nagode sosai".


Iya abinda ya iya furtawa kenan hakan yasa Inusa yi masa sallama ya wuce, cikin takun sa da kallo ɗaya zaka masa ka ɗauke shi as mutum me izza da taƙama ya koma hanyar falon da suka baro sedai be ƙarasa ba ta fito riƙe da purse ɗin ta waya kare a kunnen ta tana magana, da hannu tayi masa alamar ya biyo ta kafin tayi gaba, tsananin mamaki ne ya kamashi dan fa ɗazu be kalle ta balle yasan a ya take, shiyasa yanzu da ya ganta haka sanye da rigar da bata saukan mata ba ta kuma kamata sosai haka kan ta a buɗe zata fita se mamaki yake neman daskarar dashi.


Ture komai tayi gefe ya bi bayanta ganin har tayi gaba tuni, wajen parking motocin ta suka ƙarasa tayi masa pointing wata black designer car da taji wanki take ta ƙalla da ɗaukar ido ( Allah ya sani ina son baƙar mota a rayuwata😻 ).


Wajen motar ya ƙarasa ya saka key ya buɗe kafin ya matsa ya bata waje, ƙarasowa tayi cikin takun ta na ɗaukar hankali yayinda ya ke kallon ta a kaikaice ya ga inda zata shiga gaba ko baya dan fa turaren ta ya fara takura masa yana kuma son fara karantar halayen ta da ɗazu Inusa ya gama faɗa masa, bisa ga mamakin sa gaba ta zauna owner's corner ta rufe murfin dole ya ƙarasa ya shiga driver's seat ya zauna, tada motar yayi bayan ya gama karanto addu'a kamar yadda ya saba tun da can duk da be fiya tuƙa kansa ba tun dawowarsa Giwa.


Fita yayi da motar bayan an buɗe gate ɗin ya hau kan titin kafin ya fara tuƙi kamar yadda ya saba cikin nutsuwa ba garaje, ba gudu sosai yake yi ba kuma bawai salo salo yake tafiya ba, yana tsaka tsaki ne, Kisnah da tun da ta shiga motar ta maƙala ɗan gado wato earpiece ɗin ta ta maida kanta bayan kujerar ta kwanta tare da lumshe ido bakin ta na motsi kaɗan kaɗan alamun bin waƙar take yi so bata ji tambayar da yayi mata har uku ba na inda zasu, be ƙara tambaya ba ya sauka gefen titi ya faka motar ya jingina jikin makarin kujerar ya lumshe idanun sa kamar me bacci.


Jin shiru kamar ba'a tafiya yasa Hajiya Kisnah buɗe ido, sake ware manyan golden cat eyes ɗin ta tayi tana bin titin da kallo kafin ta juyo ta kalli yadda Sarakin ya baje cikin kujera, mamaki ne ya kamata to me yake nufi da tsayawa da yayi gefen titi ya wani rufe ido, badai bacci yake mata a mota ba ko, tunanin haka yasa ta zare earpiece ɗin ta ajiye kan cinyar ta ta saka hannu ta bubbuga steering ɗin, a hankali ya buɗe idanun sa ya zuba kanta wanda yasa ta janye nata da sauri daga kan fuskar sa ta koma wajen ta ta zauna sosai


"Badai bacci kake min ba ko, meye ma'anar tsayawa gefen titi da kayi bayan na faɗa maka ina sauri ne".


"Ina zamu je?".


Ya faɗa without giving attention kan tambayar da tayi masa ba, ranta fa ya soma ɓaci dan ita bata son rainin hankali ko kaɗan, in be san wajen da zasu ba shine kuma ba ze tambaya ba se kawai ya wani tsayar da ita a titi dan fa Kisnah akwai saurin fusata sedai tayi ƙoƙarin yi masa uzurin Wannan shine karon farko na aikin sa tare da ita bari ta masa uzuri,


"Ado Muhammad Manya hospital". Ta faɗa tana maida earpiece ɗin ta sedai wannan karon idanun ta na kan titin ne, cikin zaman kusan wata da yayi a garin ya ɗan sassan gurare dan haka tuni ya ɗau titin da ze kaisu can ɗin, sun kusa isa Asibitin ta bashi umarnin tsayawa gaban wani ƙaton shopping mall dan tana son yiwa Surry siyayya, bakin mall ɗin ya tsaya ta fita, ganin ba shida niyyar fitowa yasa ta ƙarasa side ɗin da yake tare da bubbuga glass ɗin windown, ɗagowa yayi ya kalle ta ɗan tinted glasses ne a motar, ganin itace yasa ya buɗe ya fito hakan yasa tayi gaba tana faɗa masa


"Follow me"..............................✍️.












Kai SARAKI kafa shiga hankalin ka, haba Ni kaina na fara gajiyawa da halinka balle kuma Aunty na Kisnah, zamu fa koreka fa tam😡😡




©️ Ouummey 📚✍️.




*☑️Ote, comment and share fidabilillah.*
































Ouummey 12 (8/4/2022 4:15 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________




















Page 1️⃣2️⃣










_______________________📖 Gudu take sosai duk da ba haka ta saba tuƙi ba dan tana san isa da wuri, a yanzu bata da burin da ya wuce ta ganta gaban Mommy dan su zata, zafin da zuciyar ta take mata a lokacin ba kaɗan bane.


Gaban wani madaidaicin gida ta tsaye tare da yin horn, da sauri me gadin ya buɗe mata mota dan a kwanan nan ya gane ta saboda Wannan shine zuwan ta gidan na uku.


Parking tayi ta fito hannun ta riƙe da ledar da tayi wa Mommyn shopping kamar yadda ta turo mata text ɗin abubuwan da take buƙata, bakin madaidaicin falon ta tsaya tare da murɗa handle ɗin ta shiga.


Muguwar harara wata kakkaurar babbar mace ta maka mata tana jan tsaki


"Yanzu kuma me kika zo yi, Ni kam na shiga uku da wannan takurar, ita uwar ki ta kasa zama gidan ubanki saboda baƙin hali ta zo nan ta tare min kema kuma kin takura min da zirga zirga kamar me neman gafara, to wallahi baze yiwu ba, ko ki ɗauke kafar ki daga gidana ko na tarkata uwar ki na kora ku gaba ɗaya".


Zuba mata jajayen idon ta Megado tayi cikin tsananin ɓacin rai da takaici yadda ƙanwar babar ta ke musu cin kashin da ta ga dama dan kawai Mommy na zaune gidan ta, baki ta buɗe zata maida mata martani sedai tuni Mommy da ta fito daga ɗakin yara inda take kwana ta rufe mata baki da hannun ta kafin ta ja hannun Megadon zuwa ɗakin da ta fito.


Harara Aunty ta bi bayansu da ita tana sakin ƙananun maganganu sedai ko kallon ta Mommy batayi ba ta shige da Megado dan in tace zata tanka yanzun nan ƙanwar tata me Huna hasiya zata nemi yi mata tijara.


Fusge bakin ta Megado tayi bayan sun zauna kan wata three sitter ƙwalli ɗaya dake ɗakin se katifun yaran Aunty Hasiyar, Ido ta zubawa Mommy ganin yadda cikin kwana uku kawai ta fara yin baƙi ga wata ƴar rama da tayi again dan mugunta kawu yayi mata ya faki idon ta ya kwashe ATM cards ɗin ta gashi ƴan kuɗin da ke hannun ta lokacin dubu da biyar ne kawai, nan gidan Aunty Hasiya kuwa ba wani jin daɗi ake ciki ba compared to gidan da ta baro, ba AC se fanka, ba ruwan roba se pure water, ba different dishes se ɗaya da matar gidan taga damar dafawa gashi tun da tazo a wannan three sitter ɗin take kwana dan Aunty tace bata da spare mattress Kuma ragowar na ƴaƴan ta ne sedai tai manage da kujerar.


Katse mata tunani Mommy tayi da dafa ta
"Yanzu Megado ba zaki sa ubanki yace na dawo ba, kina fa kallon rayuwar da nake ciki gidan wannan shegiyar yarinyar".


"Wallahi Mommy ya ƙi ko saurara ta amma abinda nake gani kawai me ze hana ki tattara mu koma, ai ba dole se ya san kin dawo ba ko?".


Zaro ido Mommy tayi
"Ashe kin manta tijarar ubanki, kaɗan daga aikin sa ma ya iya sakina kan hakan, Ni a ganina kawai zan kira ƴar iskar yarinyar can in bata haƙuri a wuce wajen, ragowar shirin mu kuwa se mu yi shi ta ƙarƙashin ƙasa ko".


"Wallahi sake raina mu zata yi Mommy, adai nemo wata shawarar ba wannan ba".


"Dole dai ita za'a yi Megado dan fa kin san in

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads