Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 104570 words

Chapter 2 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1418

Ads at the middle of Article

da bowls guda biyu se spoon uku dan shi ɗin yana da tsantseni baze iya cin abinci da abubuwan siyar wa ba, mayukan gashi ya siya suma set hakan yasa kuɗin hannun sa suka sake yin ƙasa, padlock kawai ya siya suka koma shagon.


A jimillance da Idriss yai lissafi sun kashe kusan 200k da hawa, Idriss akwai kirki, shi ya taya Saraki gyara ɗakin yana masa fira duk da shi Sarakin ba wani amsa masa yake ba se eh, a'a ko yai amfani da body language i.e jijjiga Kai ko gigizawa.


In a blinking of an eye har sun gama, sosai kuma ɗakin yayi kyau kamar bashi bane kangon ɗakin da baya ɗauke da komai sai tiles dake ƙasan ɗakin.
Daɗin ɗakin ɗaya Saraki yaji ganin cewa akwai toilet a ciki, dashi yayi amfani yai wanka bayan Idriss ya ɗebo masa ruwa cikin bucket a wani gidan wanka dake bayan su.


Se kusan ƙarfe 11pm Idriss yai masa sallama ya wuce bayan ɗumbin godiyar da ya sha wajen Saraki, basshi dai da miskilancin sa amma yasan Alkhairi, yana matuƙar daraja dukkan wanda yai masa Alkhairi komi ƙanƙantar sa haka kuma bai da girman kai wajen yin godiya in an kyautata masa.


Kwanciya yayi bayan ya canja kayan sa zuwa na bacci cikin kayan da ya siya, suratul mulk yake biyawa ƙasa ƙasa wadda bakin sa ke motsawa cikin alamun nuna karatun yake, cikin wannan yanayin bacci yai gaba dashi dan ba ƙaramin gajiya ke nuƙurƙusar sa ba duk kuwa da wankan da yayi.


******"

*MILLIONAIRE'S QUARTERS, MANYA STATE, HAWARYA*


Unguwa ce ta riƙaƙƙun masu kuɗin da suka tara ya taru, cikakkun ƴan boko da kuma manya manyan jiga jigan siyasa.


Da wani irin ihu budurwar ke magana cikin tsakiyar parlon da ya haɗa ƙofofi uku se ko stairs ɗin da zata kai mutum zuwa wani ginin dake sama.


"Na rantse da Ubangiji wannan karon Bazan yarda ba, nakai maƙura da haƙuri da wulaƙaci da rashin mutunci wannan shegiyar yarinyar, Mommy...Mommy ki fito kizo kiji dan kar ma kice ban faɗa miki ba".


Ɗaya daga cikin ƙofofin dake falon ce ta buɗe yayin da wata farar mace mai matsakaicin tsayi ta bayyana, ba laifi za'a iya sata cikin jerin mata masu kyau dan ba laifi akwai wadatar idanu se ko hancin ta da bai fiya tsayi sosai ba.
Ƙarasa fitowa tayi ta nemi ɗaya daga cikin kujerun dake falon ta zauna kafin cikin yamutsa fuska ta fara magana


"Haba Megado, me yasa kin fiya wutar ciki ne? Ko kin san ihunki ne ya tashe Ni daga bacci? Dan Allah ki dinga sassauta wa haba".


Wani kallo budurwar da aka kira maigado takewa mahaifiyar tata
"Ai dai kin san bazan zauna ina wage baki alhalin ba ayi min komai ba ko? To kiyi ewa waccan mara mutuncin yarinyar magana dan wallahi ta kaini maƙura dan haka zan fara ɗaukar mataki".


"Ke wai me yasa kin fiya wauta ne, kin san sarai yarinyar nan ba mutunci ne ya cika ta ba yanzun nan zata saka mahaifin ku yazo ya ci mutuncin mu tunda kin san tsoron ta yake ji, nace mu bi a hankali kema kin san bazan taɓa ƙyale ta ba dan haka ki kwantar da hankalinki, yanzu faɗa min me tayi miki?


"Abinci fa nasa Rayya ta dafa min saboda ina da lectures Kuma ni wanda suka dafa be min ba Shine ƴar iskar nan ta karɓe ta cinye, yanzu gashi in nace Zan jira makara zanyi".


"Ki barta dani, ba tana taƙama dukiyar ta bace muke cin arziƙi, na miki alƙawarin sena wulaƙanta rayuwar ta kuma kin tabbatar da zanyi ko?


Gyaɗa kai maigado tayi kana ta karɓi dubu biyun da mahaifiyar tata ke bata ta saka a jaka, buɗe baki tayi zatai magana sai dai ƙamshin da ya gauraye falon tareda takun takalmi ne ya katse ta.


"Ƙwas ƙwas ƙwas" haka sautin takalmin ke bayarwa wanda ya shaida na mace ne, a hankali suka ɗaga kansu zuwa staircase ɗin dake parlon duk kuwa da sun tabbatar ita ɗin ce ke saukowa.


Matashiyar budurwa ce da bazata wuce shekaru 18-19 ba, fara ce sosai domin skin ɗin ta har wani yellow yellow yake yi saboda tsabar hutu da jin daɗi, sanye take da wata guntuwar red gown da bata gama ƙarasa sauka a gwiwar ta ba, sosai rigar ta kamata ta kuma haskata, ƙafar ta na sanye da red high hill takalmi se gashin kanta da ya sha gyara ya lafe a gadon bayan ta se ko red hat da ta ɗora masa, hannunta ɗaya riƙe da car key da take karkaɗawa se ɗayan riƙe da mini red purse da ta sha adon stones se walwali da ɗaukar ido take yi.


Ƙarasawa tsakiyar falon tayi cikin takunta na cat walk, hannu ta saka ta ture hat ɗin baya hakan yasa fuskar ta bayyana kana ta ɗago ta dubi Mommy dake zaune ta sakar mata wani makirin murmushi.


Se yanzu na tabbatar da kyanta domin iya fuskar ta abar kallo ce, wasu irin idanuwa gare ta masu matuƙar maiƙo da ɗaukar hankali wato oily eyes, Haka Kuma ƙwayar idanunta ba baƙa bace golden brown ce wadda kalar take sake dulmiyar da duk me kallon ta, idanunta matsakaita ne masu ɗauke da zara zaran thick black eyelashes Wanda suke kwanciya sosai in ta rufe idanun, haka girarta cikakkiya ce dan har tana neman haɗewa sai dai ba ta ƙarasa haɗewar ba, siririn hanci gare ta mai matsakaicin tsayi se ƙaramin bakin ta mai ɗauke da kyawawan luscious pink lips Wanda kallo ɗaya za'a yi musu asan zasuyi matuƙar daɗi da laushi a baki, a taƙaice dai ita ɗin na tsananin kama da jarumar nan sridevi ta ƙasar India.


Karkaɗa mukullin hannunta tayi daidai fuskar Mommy kafin ta ce mata "Hi".


Takaici da baƙin ciki ne suka cika zuciyar Mommy da ɗiyar ta mai gado sedai ita gogar ko a jikinta, juyawa tayi ta nufi entrance ɗin falon ta fita, sai da ta buɗe ƙofar sannan ta juyo ta kalli Mommy cikin yamutsa fuska tace "oops, kinga na manta, ki faɗa wa mijinki account balance ɗina yayi low, Ina buƙatar transfer ɗin 2 millions urgently in ya fito". Tana gama faɗar haka ta fice daga falon zuwa farfajiyar gidan.


Girman farfajiyar gidan kawai ya isa sanar da ainahin girman gidan, domin kuwa kuwa manya manyan flats uku ne a cikin gidan wanda duk flat ɗaya ya yi girman gidan masu rufi asiri uku ko huɗu.


Ba tareda ta tsaya amsa gaisuwar da ma'aikatan gidan ke ma ta ba ta ɗaɗɗaga musu hannu dan sauri take yi, wata jar mota ta buɗe wadda ke cikin motoci sama da goma dake harabar gidan, motar se ƙyalli da ɗaukar ido take yi, shiga ciki tayi tai mata key kana ta fice daga gidan cikin matuƙar gudu kamar yadda ta saba.


Gudu take yi sosai yayin da ta ƙure volume ɗin motar cikin waƙar Dil to pagal hai dan ita ɗin die hard fan ɗin Indian films and music ce, yanzu haka cinema zata je kallon sabon Film ɗin jaruma Rani me suna Black, gashi ta kusa makara duk datasan bata da matsalar ticket nata a ajiye yake.


Wayar ta ce ta fara ringing hakan yasa ta rage volume ɗin waƙar tai picking tareda sa wayar a speaker ta ajiye ta.


"Hey Kisnah beauty, kina Ina ne, gamu har mun shiga cinema baki ƙaraso ba?


"On my way babe"


"Okay, se kin ƙaraso".


Kashe wayar tayi ta ƙure volume ɗin waƙar ta, tana tuƙi tana bin waƙar tareda girgiza kanta cikin zallar nishaɗi.


Gudun da take yi sam ba na hankali bane amma ba yadda mutane suka iya da ita dan har sun fara sabawa, shiyasa da yawa masu ababen hawa ke kaucewa suna bata hanya, wasu na zagi wasu na tsine mata yayin da ita bata masan sunayi ba.


Haka salan tuƙin ta yake shiyasa Bata driving da kanta se dai ta ɗau driver, to driver ɗin nata ne babansa ba lafiya dole ya ajiye aikin dan kula dashi, yanzu hakan tana kan neman wani ne shine fa kwana biyu take tuƙa kanta dan bazata iya zama gida ba dole se ta fita.


A gurguje tayi parking motar ta dan lokacin har an fara Film ɗin, hakan yasa tayi wrong parking tayi blocking wasu manyan motoci uku.


Zama tayi a gurin zamanta na musamman inda ta sami ƙawayenta huɗu duk sun iso, ba tareda ta kula kowacce ba ta zauna tareda fito da park ɗin creamy crackers ɗin ta ta fara jefawa a baki tana maida hankalin ta kan Film ɗin.................📝


Ouummey ✍️


☑️ote
Comment
Share.
























Ouummey 03 ( 7/29/2022 7:56 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________


















Page 3️⃣












__________________📖 jefa crackers ɗin take bakin ta yayinda hankalin ta gaba ɗaya ke kan moves ɗin jaruman.


Kwaɓe fuska tayi lokacin da aka haska scene ɗin da jarumi Amitabh bachan yake saka jaruma Rani Mukherjee a cikin ruwan sama, kan kace me se ga hawaye na zuba a fuskar ta, meenah da ta san haka ze faru ce ta riƙo ta jikin ta tana lallashin ta, juyowa ragowar sukayi, Hameedah, Surayya, da Maleeka sukayi suna sake comforting ɗin ta har tayi shiru, tagumi ta saka tana cigaba da kallon, ita ɗin me tausayi ce most especially ga masu nakasa da kuma talakawa, most of the times in tazo cinema se tayi kuka saboda tausayi, either na yadda wasu ke fama da talauci, yadda ake ciki zalin wasu ko rabuwar masoya kuma ba hakan ne ze Hana ta dawowa gobe ba.


"Yeeeeeeehhhhhh". Ta buga tsalle tana ihu lokacin da jarumar ta kammala degree ɗin ta tana speech ranar convocation , gaba ɗaya ta ruɗa wajen da ihun ta da tsalle wai murna take, majority na occupants ɗin ji suke kamar su shaƙe ta dan takaici yayinda minority basu ko kalle ta ba dan sun saba da ihunta tun bare in tana kallon wrestling, yanzu zaka ji tana ihun "yauwa, dake shi, ɗaga shi ka buga shi, karka bari ya yarda kai, wayyo, tashi, yauwa kauce, ehen kai masa duka........" and many more of this.


Ɗaukar ledar crackers ɗin ta tayi ta nufi hanyar fita tana waƙe waƙen ta da suka zauna a bakin ta kai kace ita ce ta raira su, bin bayanta su Hameedah suka yi yayinda meenah ta ƙara sa suka jera suna tafiya har suka fita daga cikin ainahin cinema ɗin zuwa parking lot ɗin da ta ajiye motar ta.


Maza huɗu suka tarar tsaye jikin motoci ukun da tayi blocking saboda saurin da take yi, nufar motar ta tayi zata buɗe ɗayan ya sha gaban ta yana jifanta da wani ɗan iskan kallo, ɗagowa tayi itama tana masa kallon mamaki dan bata ma lura da cewa tai blocking ɗin su ba.


"Wace iriyar kidahum ce ke da Zaki blocking ɗin mu da wata gwanganin motar ki, ko baki da idanu ne da baki ga motocin mu ba lokacin da zaki yi parking?


Sakin baki tayi tana kallon shi jin wai ita yau wani useless being ya Sami bakin zagi, bata gama dawowa daga duniyar mamakin ba ta ga wani ya zo ya tsaya gefen wancan yana hararar ta kafin ya fara magana


"Kayi mamaki ne Haroon, kalle ta fa, da ganin su kaga ƴaƴan talakawa masu shegen buri da fafa, anje an aro kaya da mota an shigo cinema dan a sami wani me ɗan maiƙo a liƙe masa, bana tantama ta ga shigar mu shine bari tayi blocking ɗin mu dan tayi driving attention ɗin mu towards her, sedai bata san tayi a banza ba, mara hankali kawai".


Wani irin tafarfasa zuciyar ta ta fara a ƙirjin ta, inda sun mata magana cikin mutuntaka ita me basu haƙuri ce dan bata da wannan girman kan, sedai yanzu da suka biyo mata ta wannan hanyar zata gwada musu ainahin wacece Kisnah.


Sam be lura da intention ɗin ta ba se ƙarar marin da ya karaɗe gurin se ko raɗaɗin da ya ratsa kwanyar sa, kafin a ankara ta saukewa ɗayan ma nasa a kuncin sa, zaro idanu Hameedah tayi yayinda Meenah tayi hanzarin riƙe ta ganin tana aniyar ƙara marin wanda aka kira da Haroon, fincikewa tayi ta ƙarasa gaban ɗayan tana nuna shi da yatsa tace "inga uban da ya tsaya maka yau a garin nan in Kai ɗan halak ne".


Juyawa tayi da nufin wucewa ragowar biyun suka sha gabanta fuska a haɗe duk da cikin ransu fargaba ce cike dan basu san wane ɗiban albarkar zata yi musu ba su kuma.


Kamar wanda ya fita daga shock haka yayi firgigit yana kallon ta cikin tsantsar takaici da baƙin ciki
"Lallai yau se na yi maganin ki, se n ga uban da ya tsaya miki a garin nan".
Ya faɗa yana zaro dalleliyar wayar sa yayi danne danne na ƴan sakanni kana ya sa a kunnen sa.


"Ina buƙatar motar ƴan sanda biyu yanzun nan ciki har da mata, ina parking lot ɗin clear screen cinema".


Gyara tsayuwa Kisnah tayi tana sakin murmushi yayinda ragowar matasan biyu suke kwarzanta wanda yayi kiran
"Gaskiya Abeed ka nuna wa yarinyar nan ko waye kai in ba Haka ba ai ƙimar mu ta zube, ace har mace ta samu guts ɗin ɗaga hannu ta mareka, gaskiya this is so disgusting".


Hura hanci kawai Abeed yake Yana aiyana abinda ze sa ayi mata a police station ɗin dan se ya sa an wulaƙan ta ta, jinginewa tayi jikin wata mota dake bayan tata ta maƙala airpeace a kunnen ta tana maming waƙar guzarish tana gyaɗa kai, su Surayya da suka san ba abinda aka isa ai mata su ma hankali kwance suka jijjingina da motocin su suna pressing phones ɗin su.


Jiniyar motar ƴan sanda ce ta cika wajen yayinda suka ƙaraso har inda Abeed ya faɗa musu, kashe motar suka yi sannan ragowar suka fiffito.


Da hannu Abeed ya nuna inda take tsaya yana haɗe fuska irin ba wasa ɗin nan
"Arrest her know". Ya faɗa cikin sigar bada umarni.


Da hanzari ƴan sanda biyu mata suka ƙara sa inda take har lokacin idanun ta a lumshe, buɗe idon ta tayi jin an riƙe mata hannu ana ƙoƙarin ɗaura mata abu, cikin zafin rai ta janye hannun tareda wanke ta da zazzafan marin da seda tayi baya kamar zata faɗi, gani take tunda tazo duniya ba'a taɓa yi mata tozarci irin na yau ba.


Da sauri ɗayar ta tare ƴar uwar ta tana wurgawa Kisnah wani mugun kallo, bata ko kalle ta ba ta janyo wayar ta daga purse a fusace ta Fara dannawa, cikin tsiwa da rashin kunya ta ke magana tana wawwatsa hannaye


"Har ni jami'an ku zasu zo suce zasu kama, waye su, eye nace waye su, waya tsaya musu, to wallahi se sun san sun taɓa ni, kuma ina buƙatar ganin ka yazun nan in ba Haka ba kasan sauran".


Kashe wayar tayi tana huci yayinda jami'an suka sha jinin jikin su, kallon kallo suka tsaya yi a tsakanin su da alama communicating suke ta hakan, tsayuwa suka gyara dan babban su yace su tsaya su gani, maybe ma duk kurari ne kawai.


"Shigowar motar ASP ne ya sa gaba ɗaya ƴan sandan zaro ido, basu kaɗai ba har su Abeed sun sha jinin jikin su da ita dan su kansu sun zata irin pretending ɗin nan ne se ga ASP a gaban su.


Tura hular kanta tayi baya shedar zata yi rashin mutunci, kallon uku saura kwata tayiwa ASP kana ta nuna matan nan biyu
"A basu suspension ɗin wata ɗaya, su kuma waɗannan a tafi da su har se na neme su, mind you wallahi aka sake a ka bada belin su without my consent se rai ya ɓaci". Ta ƙarashe tana nuna su Abeed, ba tare da ɓata lokaci ba ASP yasa ragowar ƴan sandan suka riƙo su Abeed aka danna su a mota su ma matan ƴan sandan suka shiga da kansu.


Dogon tsaki taja ta buɗe motar ta ta shiga ta tayar, batare da ta kula ko ɗaya daga cikin ƙawayen nata ba tayi wa motar key ta fice a 360, girgiza kai kawai Meenah tayi tana fatan Allah ya kai ta gida lafiya dan a yadda ranta ya ɓacin nan ta san yau gudun da zata sheƙa ba na hankali bane, sallama sukayi kowacce ta shiga motar ta ta ɗau hanyar gidan su, dama tafiyar ta suke jira dan ba wadda ta isa ta tafi ta barta sedai ita ta tafi ta barsu.


Zagi ne tashi shi har ba adadi dan da yana fitowa a jiki to fa yau da ba zata sake ganuwa ba, wani shegen parking ɗin ganganci tayi ta fice daga motar ko samun arziƙin rufewa batayi ba, daidai ƙofar da zata shiga parlor taji an bangaje ta, ɗagowar da zata yi sukai ido huɗu da Maigado, bata jira komai ba ta sauke mata nata marin a kuncin ta kafin ta ja tsaki ta wuce tana tsartar da yawu, sakarere Maigado tayi da hannu a kunci kafin ta bi ta ciki a fusace, fizgota tayi tana daidai zata fara hawa matattakala, riƙe hannun Maigado tayi wanda ta ɗaga da sunan marin ta ta murɗe shi har se da ta fara ihu kuma taƙi saki, ihun Maigado ɗin ne ya fito da Mommy dake nata parlon da baƙi, kallon kallo suka yi kafin Mommyn ta ƙaraso ta ƙwace hannun Maigado wanda ta saki ne kawai ba dan Mommyn ta ƙwata ta ƙarfi ba.


Nuna Mommy take da yatsa cikin nuna gargɗi tana faɗin
"Ki jawa ƴar ki kunne kiyi mata gargaɗi, hawainiyar ta ta kiyayi rama ta wallahi, in ba haka ba wataran se na karya ta a

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads