Showing 87001 words to 90000 words out of 104570 words
Chapter 30 - SARAKI (The Accused Prince).txt
iyayen sa ba baya.
Sama'ila a nasa ɓangaren shima kyakkyawa ne duk da shi mahaifiyar sa ya gado, tun a yarintar su Safwan mutum ne meson neman na kansa yayinda Sama'ila ya kasance me son jiki wanda hakan ne yasa basa shiri sam da mahaifin sa malam Yaƙoub dan in Safwan ya damƙi aikin gona abin se sam barka yayinda Sama'ila ze yi kwance a ɗaki ko ya tafi wajen matasa tsaran sa wasa.
A haka rayuwa tayi ta tafiya har Allah ya ɗauki ran Inna ladi lokacin haihuwa dan ta sami wani cikin daga baya, cikin alhini aka yi mata sutura aka kaita makwancin ta rayuwa ta cigaba da tafiya har lokacin da suka zama samari.
Lokacin ne kuma Safwan ya hana baban su Malam Yaƙoub zuwa gona shi ya cigaba da yin noman suna samun abin da zasu ci har ma su siyar da wasu su sami kuɗin ɓatar wa.
Kwatsam wata rana Malam Yaƙoub ya tafi gona wai duba aikin Safwan, dake aka cein ajali yayi kira dole a amsa, a gonar wani baƙin miciji ya sari malam Yaƙoub da yayi sanadin ran sa dan kafin a man gan shi har rai yayi halin sa.
Wannan mutuwa ta malam Yaƙoub ya saka Inna A'i da ƴaƴan sa su Sama'ila cikin tashin hankali, sedai dole haka ba yadda suka iya su ka saka haƙuri da dangana cikin ran su suka cigaba da rayuwa, sedai kuma lafiya tayi wa Inna A'i ƙaranci dan haka take yau lafiya gobe babu, tsananin son abin duniya da buri da ya nuna kan sa cikin halayyar da rayuwar ɗan ta Sama'ila ya sa kullum cikin yi masa nasiha take da bashi misali da ɗan uwan sa sedai dake yayi nisa sam baya jin kira sedai ya amsa mata da toh kurum amma ba abin da ya fasa, shine yau satar akuya, satar kaza gobe damfara kai abu dai iri iri.
Ana haka ne kuma itama aka wayi gari babu Inna A'i, bayan rasuwar ta ne aka yi rabon gado inda Safwan ya haɗe kan kuɗaɗen sa ya shiga duniya cirani bayan ya bar amanar gonar sa da ya shuka auduga hannun wani abokin baffan sa Malam yaƙoub.
Ƙasar Hawarya garin Manya nan ne malam yaƙoub ya yada zango inda ya shiga fafutuka da ɗan abinda yake hannun sa, shoe shiner, yalo, kayan miya duk malam Safwan ya sai da har yazo ya sami aikin gadi a wani babban Companyn sayar da auduga.
Rayuwa ta cigaba da tafiyar masa a haka yana aikin sa yana kuma leƙa gida in ya sami fama, amfanin gonar sa kuwa a can yake saidai wa ya biya ma'aikata da suka kula da ita ya kuma san wa Malam Umaru abokin baban sa wani abu har zuwa lokacin da yaji wasu mutane na batun ai masu Company suna neman audugar da zasu siya amma kwana biyu wahala take yi dan wadda aka samu baya da wata yawa, jiki na rawa Safwan ya yake bawa ma'aikacin da ya kawo masa labarin batun tasa audugar da yake nomawa, mutumin be yi ƙasa a gwiwa ba ya sanar da ɗaya daga cikin manyan ma'aikatan batun Malam Safwan, aikuwa cikin kwana uku suka haɗa committee aka je da malam Safwan aka gano gonar, sosai suka yi farin ciki da ganin noman sa dan duk cikin wadda aka samu ɗin ba wadda ta kai ta Malam Safwan kyau da yawa, take suka siye ta a tsaye suka bashi kuɗin.
Wannan kuɗaɗe su sukayi sanadin barin Safwan harkar gadi ya tarkata kuɗin sa ya koma gida ya shiga noman auduga haiƙan bayan ya ƙara siyen manyan gonaki har biyu ya adana ragowar kuɗin sa cikin banki.
Noman auduga fa ya karɓi Safwan dan har rige rigen siya ake tsakanin manyan kamfanoni dan yana bayar da ita da sauƙi ga kuma kyau da take da, sannu sannu gonakin Safwan suka yi yawa dan ya shiga sahun masu yawan gonaki a garin su yayinda Sama'ila ya na can yabi abokai yawon holewa da kuɗin gadon sa.
Kuɗi da sun fara zauna wa Safwan hakan yasa ya bar noma sedai yana da amintattun yaran da ya ɗora suke kula masa da komai shikuma ya tarkato ya dawo garin manya da tulin kuɗin sa ya shiga gina nasa kamfanin na sarrafa auduga, sannu a hankali gini ke tafiya yayinda kasuwar auduga ke daɗa bunƙasa, cikin ikon Allah kuwa se ga Company ya kammala, an ɗau dogon lokaci yana aikin zubawa Companyn injinan aiki da duk abubuwan buƙata kafin komai ya haɗu da taimakon abokin da yake ganawa n yafi ɗan uwa a wajen sa wato Sulaiman wanda shine mutumin da yayi masa hanyar arziƙin tun farko dan shine mutumin da ya sanar da masu Company nan batun audugar Safwan ɗin tun farkon lokacin da suke nema.
A farkon buɗe Companyn an sa masa suna SC textiles ne wato Safwan Congo fan yace duk da yake zaune a garin manya dake ƙasar Hawarya to fa ƙasar sa ta haihuwa dai har ila yau Congo ce, cikin ikon Allah Company ya dinga haɓaka, komai suka fitar se an siya kamar me cikin ƙanƙanin lokaci Safwan ya sake buɗe SC couture da ake zuba ɗin kuna kamar ba gobe ya ɗora abokinsa Malam Sulaiman matsayin me kula da komai.
A kuma shekarar ne Allah ya nufe shi da sauke farali yaje yayi aikin hajji ya bar shi as shekara me zuwa ya biyawa Malam Sulaiman shikuma ya zauna ya kula da harkokin su, haka kuwa akayi malam Sulaiman ya tafi aikin hajji ya dawo a matsayin Alh Sulaiman dan tuni Safwan ya koma Alh Safwan.
Shekarar da ta zagayo Alh Safwan ya buɗe Companyn SC drinks and table water, a lokacin kam gurare kaɗan kaɗan ne a garin manya da ba'a san shi ba saboda akwai shi da taimako ga tausayi hakan yasa kullum yana hanyar gidan marayu da nakasassu kai tallafi.
A zuwan da yayi wata rana ne ya haɗu da Nana Asma'u, budurwar da ta canja masa duniyar sa gaba ɗaya, daga workaholic da Alh Sulaiman yake kiran sa zuwa real Safwan, yaji sha'awar ajiye iyali shima yayi settling down sedai zuwan sa garin Congo dan sanar da baffannin sa ya tarar Sama'ila yayi aure, ya auri wata bazawara me ɗa ɗaya suna cikin matsin da ƙangin rayuwa ɗan Sama'ila dai bashi da sana'ar yi, be baro garin ba se da ya wadata ƙanin sa da duk abinda suke buƙata shi da iyalin sa ya kuma jari.
Tare da iyayen sa suka dawo garin aka nema masa auren Asma'ul husna wajen Sarkin garin da shine babban kowa na garin balle kuma ƴaƴan gidan marayu.
Ba'a ɓata lokaci ba aka yi bikin su bayan wata ɗaya dan haka ƙa'idar su take basa sa lokacin aure da tsawo, soyayya ce sosai tsakanin Safwan da Asma'u dan ba wanda ke tare dasu da besan wannan ba.
Basu taɓa haihuwa ba har suka shekara biyar, zuwa lokacin duk hanaklin su a tashe yake sedai shi Safwan yana ƙoƙarin dannewa dan lallashin matar sa, asibitocin da suka je ba zasu ƙirgu ba sedai ko ina faɗa musu ake lafiyar dukkan su ƙalau lokaci ne kawai be yi ba, a shekarar ne kuma matar Sama'ila ta haifi ƴa mace bayan namijin da ta haifa ya rasu, ranar suna Sama'ila ya sanya wa yarinya sunan wata tsohuwar budurwar sa da yake tsananin so wato bilkisu, anyi ɗauki ba daɗi kafin matar sa Haleema ta haƙura da batun sunan ta shiga kiran yarinya da Maigado dan bata tunanin zata iya ambaton ta da sunan bilkisu.
Se da Safwan da Asma'u suka cika shekara tara da aure kafin Allah ya azurtata da juna biyu, kwatanta yadda suka ɗauki cikin a ransu ɓata baki ne, sun yi kuka sun yi dariya sun yi murna sun yi sadaka sunyi kyauta at long last suka dira a ƙasa me tsarki dan nuna godiyar su wa ubangiji, ko da Safwan ya tashi dawowa can ya bar Asma'u bayan ya ajiye mata masu kula da ita har huɗu dan yace a ƙasa me tsarki zata haihu dan ɗan ko ƴar su Sami tubarakin ƙasar.
Wata sha ɗaya sannan Asma'u ta haifi santaleliyar ƴar ta mace me matuƙar kamanni da duka iyayen ta biyun, dogon gashi da suffar jikin ta sak Asma'u ce yayinda tsayin ta da kamannin fuskar ya kasance na Safwan, murnar da wannan ahali suka yi a lokacin bame misaltuwa bace, nan suka shiga kula da ƴar su da taci sunan kakar ta wato Sakeena da suke kira da Kisnah cikin so da ƙauna bayan sun tarkato sun dawo garin Manya.
Haihuwar Kisnah ya zowa Alh Safwan da matsanancin buɗi dan a shekarar ya samu nasarar buɗe manyan Companies ɗin sa har uku da tashi ɗaya ya sanya musu sunan ƴar sa wato K&S FURNITURES, K&,S CONSTRUCTION, K&S FLOUR AND FOOD STUFFS, haka kuma ya bi duk ragowar Companies ɗin ya canja musu suna zuwa K&S.
Duk wani mazaunin garin manya ya sani ya kuma shaida irin soyayyar da Alh Safwan je wa gudar ƴar sa Kisnah dan tun da tayi wayo da ita yake zuwa ko ina in ka cire wajen aiki, a kuma lokacin ne ya haɗu da Alh Haladu wanda ya ɗauka ya bawa matsayin manager dan takardun sa sun kai, soyayyar da Alh Haladu ke nunawa Kisnah ce ta saka Alh Safwan sake masa har suka dawo abokai ya danƙa masa kula da K&S drinks and table water da K&S flour and food stuffs saboda aminci yayinda har lokacin suna tare da Alh Sulaiman.
Wata rana da ta kasance baƙar rana wa ahalin, ranar da ta kafa baƙin tarihi a zuƙatan su da ma rayuwar su gaba ɗaya..........................✍️.
Me ya faru a wannan ranar, wane tarihi ne baƙin tarihin......amsar ku na wajena😍.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, Comment and share fisabilillah.
Ouummey 36 (8/26/2022 9:51 PM)
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 3️⃣6️⃣
_________________________📖 ƙarfe tara na daren ranar they were sitting a falo having fun with her parents as always, she was just 5 a lokacin, ranar Abbu kamar yadda take kiran mahaifin nata be fita aiki ba yadda ya saba ko da Nana as she called her mom ta tambayi Abbu dalilin ƙin fitar he answered her with
"Am going no where today sweetheart, will be spending the day with you and my cute, beautiful and charming princess".
Ko da take yarinya lokacin ba ƙaramin daɗi ta ji ba da abinda Abbu yace, she really loves her Abbu as you loved her haka ma Nanan ta, kasancewar only daughter ɗin su yasa suke pampering ɗin fiye da zato sedai hakan be sa sun kasa tsawata mata ba, in har tayi ba daidai ba suna nuna mata sedai in a cool way da zata ji a ranta Yes she's wrong, bata yi daidai ba.
Ranar they wore the same dress with there Nana, blue black Arabian gown that fits their complexion dan dukkan su farare ne sedai Kisnah tafi Nana dan ita Nana hasken ta me duhu ne ba irin na Kisnah ba da ta gado Abbu.
Sun yi yawo gurare da ba zata iya tuna adadin su ba, sun ci from all they want, sun siyo duk abinda suka so daga me amfani har zuwa mara amfani, a ranar duk abinda tace yi mata kawai ake ko da wanda basu saba yi mata ko barin ta tayi ba a baya.
Tjey spent the day together kamar yadda Abbu yayi alƙawari dan se after 7, ko da suka dawo wanka kawai sukai tare da Sallah sannan suka kuma biye mata suka cigaba da shiririta da kayan wasan ta har almost 9 Wanda ƙa'ida lokacin baccin ta nine ɗin ne, sedai ranar bata san me yasa Abbu keep saying Nana ta bar ta ba while Nana tayi insisting she should sleep saboda tana da school kasancewar gobe Monday.
Abbu follows them to her room da suka shiga Nana zata yi mata shirin bacci, its not odd Abbu follow them Dan sometimes shi yake canja mata kayan ka but se jikin Nana yayi sanyi ganin ya karɓi ragamar shirya princess ɗin tasu as they called her majority of times, gefe Nana ta koma ta na kallon su kawai while he dress her happily suna dariya, she's having some kinda bad feelings and it's just recently, se take ganin kamar something is about to happen, kamar akwai wani obstacle da ze zo ya shiga tsakanin wannan father-daughter love ɗin, sedai ta danne wishing all that's about to happen ya canja zuwa khair.
Ko da Abbu ya gama shirya ta be tafi ba se ma ya sami gefen bed ɗin ta ya zauna, bayan yayi mata addu'a se kuma ya shiga sake tsokanar ta suka shiga wasa da pillows ɗin bed ɗin maimakon ya sata tayi bacci, tears rolled down Nana's cheeks haka kawai, she keep staring at them tana jin wani abu a jikin ta, something me kama da kewa, kewa irin me cin ran nan, sincerely she's missing them while gasu a gaban ta, da ƙyar ta iya daurewa ta share hawayen ta tana sakin broad smile da ya kai har tsakiyar zuciyar ta ganin gaba ɗaya hankalin su baya kanta, they were busy playing and seeing them like this is all she have and want at the same time.
So da yawa in ta kalli relation ɗin ƴar tasu da mahaifin ta mamaki kan kamata, tare take wuni da ita a gida in ba school amma a fili yake ƴar tasu ta fi shaƙuwa da mahaifin ta sama da ita sedai kuma mamakin baya zuwa ko ina yake ɓacewa dan tasan akwai manyan dalilan da zesa hakan faruwa.
To Abbu Kisnah has always been his first priority and she's still har yanzu, kafin ta shiga school ko ina zashi da ita yake zuwa hatta da office, seda tayi da ƙyar sannan yake tafiya office ya barta, lokacin tashi nayi kuwa haka ne ajiye komai duk muhimmancin sa ya taho gare su kuma tun a compound ze Fara ƙwala Kiran princess yayind ita kuwa duk baccin da take kira ɗaya yake yi ta farka ta fice da sauri neman mahaifin nata, and one more thing baya taɓa shigowa gida be ruƙo mata wani abu ba, a rubuce yake kullum akwai abinda ze siyo ya kawo mata and that helped in bringing the level of shaƙuwar su so high.
Weekend kuwa is never a leisure time wa Abbu tunda aka Kisnah ta fara wayo, he spent every of his weekends trying to pleases her and make her happy ta hanyar kaita gidajen wasa, adventure palaces, shoppings da ma gurare da dama.
Yasha haɗa musu tafiya to outside Hawarya ƙasashe masu irin kayan tarihi na yara ɗin nan duk dan jin daɗin ƴar sa wannan ma ya taimaka sosai wajen samar da shaƙuwa da fahimta tsakanin ta da mahaifinta.
For Nana kuwa daga baya ƙin bin su gurare ta dinga yi dan gajiyar da ita suke yi su kuwa ko a jikin su shiyasa tace ta dena binsu se wajen da itama take son gani, ko da yarinyar ta fara zuwa school majorityn lokuta Abbu ke dressing ɗin ta dan ko Nana ta zo haka ne persuading ɗin ta akan ta tafi ta yi girki ze taya ta shirya princess Shirin da sometimes har se ta gama girki su basu gama shi ba sun ɓige da wasa se ta shigo su kwakkwaɓe fuska suna bata haƙuri.
Zaman sa me kuɗi be sa yace ya ɗau driver was ƴar sa ƙarama da bata san komai ba, da kansa yake kai ta ya ɗauko ta in Kuma aiki yayi masa yawa ya kira Nana taje ta ɗauko ta, wannan gatan yasa Kisnah zama very happy and active, a lokacin mutane da yawa na mata kallon ƴar turawa ne saboda ƙibar da tayi tana yarinya ga kuma kyau da fari kamar ka sace ta.
Gyaran muryar da Nana tayi yasa ya kallo gefen ta daidai yana ɗaga pillow ze buga wa Kisnah da ta ke ɓuya, hararar wasa ta masoya Nana ta jefa masa hakan yasa ya sake pillown hannun sa da sauri ya riƙe kunnuwan sa dan se lokacin ya tuna ashe barci suka kawo Kisnah tayi,
"Am sorry my life". Abbu ya faɗa while holding his two ears
"Nana Abbu is sorry please". Kinsha ta faɗa itama tana riƙe da kunnuwan ta kamar yadda Abbun ta yayi, girgiza kanta kawai Nana tayi dan ta saba da irin wannan halin nasu, ba dama ɗaya yayi laifi se su haɗe mata kai su dinga bata haƙuri har se taji she have no option but to forgive them.
"Oya bid her goodnight and move to our room".
Nana ta faɗa in serious tone dan in ba haka tayi wa Abbu ba he won't mind spending the night with princess gobe kuma ya makara aiki haka itama princess din ta makara school.
Be yi abinda ta ce ba se ya fice daga ɗakin, bin shi tayi da kallo tana sakin smile dan tasan yayi fushi kenan tun da ta kore shi daga wajen princess, ƙara sawa gadon yarinyar tayi ta zauna bakin gadon ta shiga tofa mata addu'a kamar yadda suka saba duk kuwa da cewa Abbu yayi mata amma ƙa'ida ne itama se tayi mata, tana gama ta saka yarinyar ta haɗe palms ɗin ta kafin ta saka ta ta karanta Suratul nas, Suratul falaq and Suratul Ahad da kanta tare da ayitul kursiyyu sanan ta umarce ta ta kwanta ta ja mata blanket kan cikin ta tare da mata offing light ta kunna mata qur'anic recitation a mp3 ɗin ta da aka siyo purposely sabida hakan da kuma ƙara koyan karatun da take