Showing 96001 words to 99000 words out of 104570 words
Chapter 33 - SARAKI (The Accused Prince).txt
haka su Kisnah suka ɗane bayan ta aka loda musu kayan tsarabar su, anan suka yi sallama da arɗo bayan ya sanar dasu sunan kauyen nasu wato Bina, haka kuma yana can cikin jihar Makwan ne, daga Kisnah har Saraki ba wanda yasan wani gari wai shi Makwan sun dai amsawa arɗo da sun gane ne kawai, da motar zata tashi kuwa Kisnah har da kukan ta na rabuwa da arɗo kafin motar ta tashi suna ɗagawa juna hannu su dashi har suka ƙule.
Tafiya ce mata daɗi dan hanyar duk kwazazzabai ne bata da kau dama kuma ba wai kwalta ce ba a wajen birji ne, se kusan yamma kafin suka sauka a wani babban ƙauye da a can cikin sa ne ƙauyen su arɗo yake wato Bina, nan ma sallah kawai suka yi suka sake neman tasha suka hau Mota zuwa cikin garin Makwan da ɗan guzurin da arɗo ya bashi da kuma wanda baffa arɗo ya ƙara musu.
Basu shiga cikin garin Makwan ba se karfe shida na yamma a yadda yaji direban motar na faɗa, ko da mota ta tsaya rasa ina zasu nufa suka yi tunda basu san ko ina ba a garin hasalima wannan ne karon su na farko na jin sunan garin da ma kasancewa a cikin sa..............................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, Comment and share fisabilillah.
Ouummey 39 (8/27/2022 9:32 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 3️⃣9️⃣
________________________📖 wani tunani yayi kawai ya tsayar musu da napep yace ya kai su nearby hotel amma ba me tsada ba, beso kashe kuɗaɗen hannun sa ba sedae ba yadda ze yi dan ba su da wajen zuwa in ba can ɗin ba.
Kamar yadda yace wa me napep ɗin haka ya kai su wani middle class hotel, room ɗaya me ɗan girma ya kama musu ya karɓi key suka wuce.
Suna shiga ta wuce toilet da sauri, ruwa ta tara ta shiga wanke jikin ta kamar me wadda ke shirin canja fata, se da tayi kusan saɓi biyar kafin ta haƙura ta fito shima dan knocking ɗin da Saraki ya dame ta da yi ne, ɗaure da towel me matsakaicin girma ta fito abinta se kanta da yasha wanki shima naɗe a ƙaramin towel, da sauri ya kau da kansa tare da bata hanya ta wuce ko a jikin ta, da sauri ya faɗa toilet ɗin ganin ta zauna kan dressing mirror gyara jikin ta, mayukan da ta gani ta dudduba ta ɗau wasu biyu ta shafa ɗaya a jikin ta ɗayan kuma a gashin ta sannan ta ɗau set ɗin comb ta tashe kanta bayan ya ɗan sha iska dan gurin basa ajiye hand dryer, seda ta gama shirya wa kuma ta tuno bata ma da kayan da zata saka dole haka ta koma ƙaton bed ɗin ta zauna jiran ya fito ya samo mata kayan da zata saka.
Shima a ta can wankan yayi har round uku dan tsabar dauɗar da ya tara a Bina jikin sa har wani ƙaiƙayi ƙaikayi yake masa, bathrobe da ya hango yasa ya ajiye towel ɗin da ya ɗauko dan ɗaurawa ya ɗau ledar sabuwar bathrobe ɗin ya farke tare da zurawa ya ɗaure sannan ya fita bayan ya goge sumar sa ya ajiye towel ɗin a nan.
Be lura da ita ba ya ƙarasa kan mirror ya fara neman man da ze shafa, ganin be ankare da ita ba yasa ta kira sunan sa a hankali
"Yaaa".
Juyowa yayi ya dube ta at the same time ya kawar da sauri ganin ta ɗaure da towel har lokacin, towel ɗin da a ganin sa be rufe komai na jikin ta ba,
"Meye haka kike zaune ba kaya?
"Ba ni da kayan da zan saka yaa, nawa kasan masu dauɗa ne I can't wore them again".
Shiru yayi dan.yasan gaskiya ta faɗa, shaf ya mance da batun kayan da zasu canja shiyasa be ko yi batun siya ba, ajiyar zuciyar rashin mafita ya saki kana ya miƙe zuwa toilet inda ya ajiye kayan da ya cire ya fito dasu yana lalubar aljihun sa dan ya ɗebo ragowar kuɗin da suka rage musu da baya tunanin sun wuce 6k.
Sak yayi jin hannun sa ya taɓo wani card me ɗan kauri kamar ID kamar kuma complimentary card know Kuma................!
Kai baya ma tunanin the last one, zaro kuɗin yayi gaba ɗaya tare da card ɗin, abin da ya gani ne ya daskarar dashi a tsaye, ganin yayi tsaye yana bin kuɗin hannun sa da kallo yasa ta kiran sunan shi har kusan so biyu amma be san tana yi ba, seda ta ɗaga murya sosai sannan yayi firgigit ya juyo ya kalle ta, hannun sa ta kalla sannan ta maida kan fuskar sa
"Yaa meye a cikin kuɗin da ka kafe su da ido har baka ji kiran da nayi maka ba kusan so uku?".
Da sauri kamar wanda ta tunatar dashi ya sake maida idon sa kan kuɗin, ganin har lokacin card ɗin na nan yasa ya kai hannu ya ɗauka jikin sa na ɗan rawar murna, taso wa tayi cikin son ganin abinda ya ɗauka da shine yasa ya kafe kuɗin da kallo cikin tunani, zaro ido tayi ganin atm card ne a hannun nasa haka kuma bata yi wata wata ba ta fisge da iya ƙarfin ta, ATM card ɗin sa ne wanda suka je bank tare ya buɗe take saka masa albashin sa a ciki, tsabar ruɗewa da farin ciki bata san sanda ta faɗa jikin sa ta ƙwaƙumeshi cikin bashi zazzafar runguma ba, wani irin shock ne me azababben ƙarfi ya ratsa jinin saraki, a daidai wannan lokacin baya tunanin in an tsaga jikin sa za'a ga jini tsabar daskarewar da yanayin yasa yayi.
Gaba ɗaya kuɗin hannun sa zubewa suka yi a ƙasa dan ba shida wani sauran ƙarfin riƙe su yayinda rawar da jikin sa ke yi ta tsanan ta kamar wanda aka jonawa wutar lantarki, to her kuwa ko a jikin ta, tana gama murnar ta ta sake shi ta tsugunna tana tsince kuɗin da ya zubar, har ta gama tsincewa yana nan daskare be ko iya ya motsa ba seda ta miƙe sannan ya iya ƙarfin halin juya mata baya da sauri dan baya son ko kaɗan taga damar sa.
Drawer dake gefe taje ta zauna tare da janyo landline ɗin wajen ta danna kiran customer care tunda ba waya a hannun ta balle tayi online shopping, ma'aikaciyar customer care ɗin ta zo ta bata kuɗin hannun ta 6k ɗin ta lissafa mata abubuwan da zata siyo musu na kayan sawa sannan ta nemi guri ta zauna bakin bed ta juya da nufin yi masa magana sedai wayam taga wajen ba kowa se ATM card ɗin da ke ƙasa, cikin rashin damuwa ta ƙara sa ta ɗau card ɗin ta koma wajen ta ta zauna.
A cikin toilet kuwa ya daɗe tsaye dafe da mirror ɗin wajen kafin ya iya dawowa hayyacin sa, he's totally out of word, be San me ze Kira recent scene ɗin ba, yanayin da ta shiga some minutes back was so unpredictable, be San da wane yanayi ya akaƙanta shi ba haka be san da sunan da ze Kira what he just experienced some minutes back ba, yanayin baƙo ne a gare shi dan ze iya rantse wa be taɓa samun contact da mace kamar yadda ya faru a tsakanin su ɗazu ba, it happened so sudden and unexpected, Kai baya jin ko yayi bayani akwai wanda ze fahimci abinda yaji a jikin sa ɗazu.
Cold shower ya sake kansa na tsawon lokaci har se da yaji ya koma daidai kafin faruwar abin, bathrobe ɗin da ya cire ya sake maida wa kafin ya gimtse fuska ya fita dan ma kar ta ga fuskar dawo masa da abinda ya wuce.
Bata lura da yanayin fuskar sa ba ta shiga lissafa masa abubuwan da ta aika a siyo musu, da kai kawai ya amsa mata tambayar da tayi masa na ko hakan da tayi yayi daidai.
Be daɗe da fitowa ba matar da ta aika ta dawo ta kuwa miƙe da saurin ta ta nufi ƙofa with minding cewa towel ne kaɗai a jikin ta, bai san me yasa ba haka kuma be san tunanin da yake ba a lokacin da ya sha gaban ta cikin sauri yana faɗin ta koma shi ze amshi saƙon cikin kau da kai, ɗan tsai tayi cikin mamakin me ze sa ya hanata karɓar aiken se kuma ta matsa baya ta koma bakin bed ta zauna yayin da shikuma ya karɓo ledar ya zo ya ajiye mata a gaban ta kana ya sunkuya ya buɗe ya ɗebi nasa ya wuce toilet Dan shiryawa.
Itama nata ta fitar ta shiga sanyawa cikin kwanciyar hankali ba tare da tunanin kar ya fito bata gama ba, doguwar rigar bacci ce me ɗan kauri da ta kai mata gwiwa se wandon ta iya cinya, gaban madubi ta ƙarasa ta ɗau ɗaya daga cikin turaren dake wajen ta shiga fesawa a jikin ta duk da ba taste ɗin ta ba ne amma ta ji daɗin ƙamshin dan rabon ta da yi tun ranar da ta bar gida suka haɗu da wannan accident ɗin.
Fitowa yayi shima sanye da nasa kayan baccin, dogon wandon bacci da rigar sa me gajeran hannu, ba ƙaramin kyau kayan suka yi masa ba da har yasa Kisnah kasa janye idanun ta a kan sa ta shiga bin shi da kallo duk inda yayi, yana sane da kallon da take bin shi sedai yaƙi kallon inda take balle yace ta daina dan baya son kallon ta tun bayan kallon farko da yayi mata bisa kuskure lokacin da ya fito daga toilet ɗin, sosai tayi masa kyau sedai yana kallon ta incident ɗin ɗazu ne ya dawo idon sa shiyasa yake gujewa kallon ta.
Knocking ɗin da aka sake yi yasa ta kalli ƙofar sedai bata yi ko yunƙurin tashi ba, wannan karon ma shi yaje ya buɗe ya karɓi abinda bata san me ne ba dan rufe yake cikin leda, godiya yayi wa wanda ya kawo ya rufe ƙofar sannan ya dawo cikin ɗakin ya janyo Centre table ɗin dake ajiye ya ɗora ledar hannun sa kafin ya zauna bakin bed ɗin ta ɗaya side ɗin.
"Ki buɗe ki ɗau abinci ki ci".
Iya abinda ya faɗa mata kenan ya tashi ya nufi wata kusurwa ta ɗakin tare da shinfiɗa daddumar da bata san inda ya samo mata ba ya tada sallah, buɗe ledar tayi ta ɗan leƙa take away biyu ta gani alamun ita ɗaya shima haka.
Nata ta ɗauka ta buɗe ta shiga ci tana lumshe ido, fried rice ce da aka wadata da veggies, da a da ne cewa zata yi taste ɗin abincin be mata ba dan a zahirin gaskiya ba wani daɗi ke gare ta ba sedai yanzu dake ta daɗe rabon ta da irin cimar se ta ji duk duniya ba abincin da yakai na gaban ta daɗi, sosai taci ta ƙoshi dan takeaway ɗin irin me biyun nan ne so abincin da yawa, tana gamawa ta far wa rabin gasasshiyar kazar dake kan abincin sannan ta kora ruwan roba, hamdala tayi ciki godiya ga Allah karo na farko a rayuwar ta, wani irin mutuwa jikin ta yayi taji ba abinda take buƙata a lokacin kamar bacci sedai sanin bata isa tayi shi batare da tayi sallah ba yasa bata ko kwatanta kwantawa ba ta jira har ya idar kafin ta ciri hijab ɗin dake cikin ledar wanda ita ta saka aka siyo shi ta hau kan pray mat ɗin ta tada Sallah.
Da wannan damar yayi amfani ya buɗe nasa pack ɗin abincin ya shiga ci a nutse, kamar yadda Kisnah taji like bata taɓa cikin n abincin da ya kai wannan daɗi ba shima haka, they spent good 3 months five days suna shan fura da nono se ko zogale da yaɗiya se kuma fruits sanda suka samu, to ba dole yanzu su having this feeling ba.
Ko kafin ya gama ci ta idar haka kuma ba wani azkhar ko tasbih ta cire hijab ɗin ta bar shi a wajen dan tsananin baccin da ke rinjayar ta, can tsakiyar bed ɗin ta haye tana sakin ajiyar zuciyar missing this kinda laushi da taushi da tayi ta shige blanket kafin ta iya ce masa good night.
Baya san abinda ze sa shi kallon ta balle har wancan ƙaddararren scene ɗin ya dinga dawo masa shiyasa be kalle ta ba balle yaga wajen da ta kwanta ya amsa mata da night kawai.
Se da ya gama cin abincin ya tattare wajen ya shiga toilet ya ɗauraye bakin sa ya fito ya nufi kwanciya sannan ya ga yadda ta raba gadon biyu ta kwanta a tsakiya, sororo ya tsaya yana kallon ta dan shi duk a tunanin sa ta ɗau blanket ne ta kwanta a ƙasa, rasa ma wane irin tunani ze yi yayi dan shima baccin yake ji gashi babu ko ƴar kujera a ɗakin balle ya kwanta, tsurar tiles ne a ƙasan se ɗan ƙaramin carpet a bakin gadon wanda ko ƙafar mutum huɗu baze ɗauka ba, haka dai yayi ƙarfin halin janye blanket ɗin da ta lulluɓa ya shimfiɗa a ƙasan ya kwanta sedai be ko yi mintuna goma ba ya miƙe jin kwanciyar ƙasan fa bazata yiwu ba saboda sanyin tiles ɗin ga blanket ɗin ba wani me kauri ba to a bikin da middle class hotel.
Sake kallon ta yayi kafin yayi ƙundunbala ya runtse idanun sa ya hau gadon yasa hannu ya tura ta one edge na gadon yana kiran Allah a ransa kamar wanda se taɓa aljana ko wata halittar daban.
Har wata ƴar ajiyar zuciya yayi ganin ya matsar da itan sannan shima ya kwanta can ɗaya edge ɗin gadon yana haɗe tafukan sa ya shiga karanta addu'ar bacci, yana gamawa ya shafe jikin sa gaba ɗaya sannan ya ɗan zura ƙafafun sa cikin blanket ɗin da ya maida mata, tsaki yayi ya miƙe ya zauna tare da karanto sabuwa addu'ar bacci sannan ya ɗan matsa kusa da ita kaɗan ya ɗaga blanket bayan ya rufe idanun sa ya tofa mata dan sam baze yi kuskuren kai hannu jikin ta wai shafa mata addu'a ba.
Mintuna kaɗan kuwa bacci yayi gaba dashi shima, kiran farko na sallar asuba ya farka dan akwai masallacin gefen hotel ɗin kasancewar gurin na musulmi, seda ya ɗaura alwala kafin ya tashe ta ta hanyar bubbuga gefen gadon sannan ya fita, yana fita ta koma ta kwanta abinta har aka idar da Sallah ya dawo ya tadda ta haka, aikuwa toilet ya shiga ya ɗebo ruwa ya watsa mata, ta kuwa tashi a firgice tana zare ido, ganin sa tsaye kanta ya sa ta tashi da sauri dan zuwa toilet dan tasan dalilin hakan.
Tana alwala tana gungunin ya takura mata har ta fito sannan tayi shiru tare da ɗaukar hijab ɗin ta da yake kan daddumar da ta ajiye shi tun jiya ta tada Sallah.
Tana idarwa ta kuma neman gado, be hana ta ba dan yasan sun kwaso gajiyar da suke buƙatar baccin sedai shi baze samu damar yi ba dan yanzu haka ya tambayi ɗaya daga cikin securities na hotel ɗin inda ze samu ɗakin haya ya kuma sanar dashi ɗaki baze gagara ba a garin dan haka se haɗa shi da ɗaya daga cikin dillalan da ya sani ko za'a dace shine da ze fita anjima kaɗan.
Ƙarfe tara ya fita daga ɗakin yayinda har lokacin take kan barci, be tashe ba se kawai ya kulle ta ta waje bayan ya ajiye mata breakfast ɗin ta, gida kusan huɗu suka je da dillalin kafin a dace da samun wanda yake so wato mara mutane da yawa, ɗaki ne ɗaya sedai da ɗan girman sa haka kuma su uku ne a gidan ba kamar ragowar da ke da mutane sama da biyar ba, seda ya tabbatar wajen yayi masa sannan suka fita suka ƙara sa wajen P.O.S ya cire kuɗin hayar shekara dubu talatin da biyar ya biya shikuma ya bashi key ɗin.
Daga nan machine ya tare ya hau bayan ya faɗa masa ya kai shi nearby kasuwar robobi, suna zuwa ya sallame shi shikuma ya shiga siyan ƴan kayan robobi da yasan zasu iya buƙata, butoci, buckets, drum, cups, Parker and dustbin, mopper da broom dan tiles ne a ƙasan ɗakin.
Seda ya siya duk abinda yake ganin zasu nema na roba a wajen kafin ya biya kuɗin ya sami me napep ya ɗaukar masa ya kai gidan sannan ya kuma komawa kasuwar Kayan abinci nan ma ya siyan musu me ɗan yawa sannan ya biya ta ƴan katifu ya siya guda ɗaya ƙatuwa dan in yace ze siya biyu to ze ci ƙarfin kuɗin bankin nasa alhalin kuma yana son ya smai ɗan jarin yin sana'a.
Yana kai wa gidan ya koma hotel ɗin ya ɗauke ta dan ya samu tayi wanka ta karya tana kwance ne kawai, suna shiga tabi gidan da kallo a lokacin ne kuma mata ɗaya da suka tarar ta fito suka gaisa sannan ta koma bayan ta faɗa musu ɗayar tayi tafiya amma gobe zata dawo.
Tare suka shiga gyaran ɗakin bayan ya share ita kuma tayi mopping duk da ba wai yayi bane dan bata wani iya ba, ba laifi ɗakin yayi kyau sedai babu labule babu kuma risho ko gas na girki haka babu kayan plates da spoon ga uwa uba kuma tukunyar da food flask, dole yace ta Masa list ɗin abin da babu ta kuwa yi bayan ta aro pen da paper wajen matar gidan ta tace sunan ta Saudah, haka ya karɓi