Showing 15001 words to 18000 words out of 104570 words
Chapter 6 - SARAKI (The Accused Prince).txt
ratsin fari, rigar ta kamata sosai kamar wadda akayi shaping se dogon wando shima daidai jikin ta da ya tsaya iya ƙasa gwiwar ta, robar ruwa ɗaya ta ɗauka se ƙaramar wayar ta ta zura a pocket ɗin wando, canvas me ɗan tudu fari tas ta ɗaura a ƙafafun ta wanda ya zauna a ƙafar yayi mata matuƙar kyau, kame gashin ta tayi da blue ribbon ta yi masa doughnut da yayi girma sosai a tsakiyar kanta saboda yawa da tsayin gashin, blue band ta saka a kanta kana ta jawo manya manyan headphone ta maƙala a kunnuwan ta ta kunna waƙoƙin ta na india sannan ta fita daga ɗakin tare da rufe ƙofar da key dan bata yarda da kowa na gidan ba bare har ta bar ɗakin ta a buɗe.
Yuuuuu masu aikin compound ɗin gidan suka bita da kallo cike da sha'awar yadda tayi kyau cikin kayan ta haska su, batare da kula kallon da suke bin ta dashi ba ta fita daga gidan ta ƙaramar gate ɗin ta fara gudun ta kaɗan kaɗan hankali kwance, sosai ta zagaye layikan bayan su har ta ƙarasa iya distance ɗin da take so sannan ta nufi dawowa gida, lokacin kam tuni an idar da sallar magrib dan har duhu yayi sedai abinka da unguwar masu dashi ko ina haske ne tarwai har kamar da rana dan ko allura ce ta faɗi a sauƙaƙe za'a ganta a wajen.
Cillar da robar ruwan hannun ta tayi bayan ta ƙarasa shanye ruwan lokacin har ta kusa ƙara sawa gida hakan yasa ta rage gudun da take yi zuwa joking har ta ƙarasa, a parlo ta tadda maigado zaune da system zaune kan ƙafafun ta gorar sassanyan lemu a ɓarin daman ta na fresh milk a ɓarin hagu.
Ko kallon ta Kisnah bata yi ba dan Allah Allah take taje tayi wanka saboda ginin da ta haɗa, ita fa haka take kamar kifanya, akwai ta da son ruwa sosai musamman na sanyi shiyasa a rana se tayi kusan wanka bakwai zuwa takwas, ko yanzu ma wanka tayi tare da ɗauro alwala, komai ba ta saka ba bayan towel ɗin jikin ta ta ɗora hijab ɗin sallar ta wanda shi kaɗai take da hijab ta tada sallah.
Yadda take sallar a gaggauce ze shaida wa me kallon ta bata da wadataccen ilimin addini dan komai bata karantawa a sallar ta ke yin ruku'u wanda yake kama da gaisuwar ƙwangen matasan zamani, sujjadar ta kuwa kamar yadda yara ke yi suna leƙowa ta ƙarƙashin nan, cikin mintina biyar ta gabatar da sallar Azahar, la'asar da magrib da ta tara, dama kuma kusan kullum haka take yi, isha kuwa ba kullum take samun yin ta ba, ranaku irin na yau ɗin sosai take fashin isha saboda zata fita club wanda bata dawowa se wajen ɗaya na dare ko biyu in ta kai mata.
Wasu sheɗanun kaya ta saka dan tana cikin waɗanda zasu yi rawa yau a club, ba wai tsara mata ranakun da zata yi rawar ake yi kamar yadda ake yi wa kowa ba, itace take zuwa duk ranar da taso, ranar da zata yi rawa kuwa kamar yau shigar da take yi ta daban ce, duk ranar da ta shiga fili kuwa se ta cinye kowa dan ƙwararriya ce akan hakan, wannan yasa ta tara masoya da magoya baya da yawa a club ɗin, kowa dakon ranar da zata zo yake yi, wanda yayi katari da ganin ta kuwa murna zaka ga yana yi kamar wanda akayi wa albishir.
Wasu kaya ne da marabar su da tsirara kaɗan ne, guntun wando ne iya matsematsin cinyoyin ta se baza da akayi masa da ta sauko har rabin cinyar tata, rigar kuwa zan iya cewa sunan ta brazier kawai, dan iya curve ɗin bra ne da ita seko baza itama a ƙasan ƙirjin da ya sauka har kan cibiyar ta, hannun kuwa wasu zarurruka ne da ake ɗaure su kamar dai yadda ta tsaya gaban mirror tana ɗaure su, saman ƙirjin ne aka saka net me shara shara sosai da be hana a hango albarkatun ƙirjin ta ba, net ɗin ya kai har saman ƙirjin sosai, ƙafar ta kuwa wani shegen takalmi ne me tsini kamar tsinke, tsananin mamakin yadda za'a iya taka wannan takalmin shi ya daskarar dani waje ɗaya, barima ta gwal ta ciro cikin kayan fashions ɗin ta ta saka a kunnen ta yatsun hannunta kuwa ta wadata su da gold rings uku uku a kowane hannu, sarƙar ƙafa me kyau ta ciro ta zauna kan madubi ta maƙalawa ƙafarta ta dama kana ta zaro wata kyakkyawar jigidi me wani irin sihirtaccen sound ta ɗaura a dirarren ƙugun ta, turarurruka masu matuƙar kaifin ƙamari ta ɗauka ta feffesa a ko ina na jikin ta, kallo ɗaya me kallon ta ze to mata ya kirata cikakkiyar karuwa me licence, sheɗaniya number ɗaya haka kuma wadda shiryuwar ta se Allah..................✍️.
*☑️Ote, Comment and Share fisabilillah*.
Ouummey 08 (8/2/2022 3:41 PM)
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 8️⃣
__________________📖 Box ɗin da take ajiyar keys ɗin motocin ta ta buɗe ta ɗauka ɗaya ba tare da ta tsaya duba wacce bace dan duk motocin ta latest ne, cikin ƙwarewa da iya taka takalmin ƙafar ta take taku ɗaiɗaya har ta fito daga bedroom ɗin ta, fresh kunun aya da ke fridge ɗin ta ta ɗauka gora ɗaya ta fita dashi a hannu, yanzu ma rufe ƙofar tayi bayan tayi resetting password ɗin buɗewa wanda haka take yi indai zata yi amfani dashi wajen kulle ɗakin da password.
Sskin baki maigado dake kan dining tayi cikin ƙarewa shigar Kisnah kallo, bawai shigar tata ce ta bata mamaki ba dan ta saba yin wadda ma ta fita, yadda kowane kaya ke mata kyau shine yake sa take kasa riƙe kanta kullum Kisnahn ta fito se ta bita da ido.
Yatsu biyu ta ɗagawa maigado cikin salon sheɗanci kafin ta wuce ta gaban ta tana kaɗa mata dirarren ƙugun ta da ya fito fes cikin wando jikin ta though ƴar jacket ɗin da ta ɗora kan kayan ta rufe har zuwa saman gwiwar ta, wata farar dunƙulalliyar mota ce me matuƙar kyau da ɗaukar ido ta buɗe ta saka drink ɗin ta a cikin kafin itama ta shiga ta zauna, warming up motar tayi kafin ta saki horn wa maigadi, da saurin sa ya fito daga ɗakin sa ya ƙarasa gefen gate ɗin, password ɗin gate ɗin ya daddanna gate ɗin ya fara zuge kansa shikuma ya matsa gefe, da mahaukacin gudun da ya zama tsarin ta ta fice daga gidan yayin da megadin ya koma ya sake pressing password ɗin rufe wa, kawu dake tsaye ta can saman benen sa yana kallon komai ya saki wani makirin murmushi kafin ta juya zuwa cikin parlon sa.
Wayar sa ya ɗauka dake gefen sofar da yake zaune yai daddanna wasu numbers kana ya kara a kunnen sa, shiru yayi zuwa lokacin da aka ɗaga wayar sannan ya fara magana
"Ta fito yanzu wanda am sure ba zata dawo da wuri ba se zuwa 2am dan haka ku bi bayan ta kuga inda tayi, kusan yadda zaku tare ta in ta fito lokacin dare yayi tsakiya kowa na gida, tun yanzu ku ɗau matsaya dan bana son aikin wasa, ban ce kuyi mata komai ba se barazana dan ina so ta tsorata ta bar batun dukiyar ta dake hannuna".
Amsar da aka bashi daga can ya sa ya jinjina kai cikin gamsuwa kafin ya katse wayar yana jin sa cikin farin ciki dan ba shida tashin hankalin da ya wuce yaji Kisnah na maganar karɓar dukiyar ta wadda da ita yake ci yake taƙama yake wadaƙa da bushasha shiyasa yanzu ba shi da burin da ya wuce ya mallake ta takowace hanya kuwa.
*******
*HIDEAWAY CLUB (The young Anacondas)*.
Tun kafin ta ƙaraso bakin gate ɗin club ɗin take sakin mahaukatan horn, da sauri masu gadin wajen suka wangale makeken gate ɗin, ƙaton building ne da tun kafin ka shiga zaka san babban waje ne da ya ƙawatu da kayan alatun rayuwa, ginin tsakiya ne da ya wadatu da gilasai ta ko ina ba abinda yake se ɗaukar ido da reflecting abubuwa, kyawawan fulayoyi da furanni ne shushhuke a compound ɗin club ɗin da ya zagaye ginin club ɗin dake tsakiya.
Parking tayi a parking lot ɗin wajen ta kashe motar, da gudu masu gadi da suka rufe gate suka ƙaraso wajen da take suna washe haƙora dan sun san tabbas yau kakar su ta yanke saƙa dan kyauta ne Kisnah take musu ta manya, kamar yanzu buɗe mata ƙofar tayi ta zuro ƙafafun ta kafin a hankali ta fito da gangar jikin, rusunawa sukai da sauri kowanne na gaisuwa da kirari, murmushi ta hau sake musu dan ita kam bata da wulaƙanci haka macece me fara'a da in kaga ta ɗaure fuska to fa an kai ta ƙarshe, gaishe su tayi daga tsaye sukuma suna durƙushe wanda biyu daga cikin su za su haife ta a haife dayan kuwa ya girme mata nesa ba kusa ba, check ta yi signing ta miƙa musu dan bata fito da cash ba, da sauri babban cikin su ya karɓa suna zuba godiya, bata kuma kula wanzuwar su ba ta ɗau wayar ta da goran kunun ayar ta ta rufe motar ta wuce cikin main building ɗin club ɗin.
Babban hall ne dake shaƙe da jama'a maza da mata, mostly samari da ƴan mata ne a ciki se kuwa tsirarun manyan mata da maza da tsufa yai wa gardama sukai faɗuwar baƙar tasa.
Ihu da sowa club ɗin ya ɗauka baka jin komai se kiran sunan Queen Kissy it's kuwa se murmushi take yi yalwatacce tana ɗaga hannun ta dake riƙe da key ɗin mota, ɗaya bayan ɗaya manyan yaran wajen suka ƙarasa suna rungume ta ba maza ba mata, da ƙyar suka ƙyale ta ta ƙarasa wajen su Meenah dake zaune a permanent VIP seat ɗin su, kujera Meenah ta ja mata ta zauna wanda itace permanent wajen zaman ta se Meenah a gefen daman ta, Hameedah a gefen hagun ta se Surayya da Maleeka a ragowar kujerun wajen da suka kasance biyar se wani haɗaɗɗen madaidaicin table a tsakiyar su.
Daga inda suke take kallon ƴan wajen kowa ke sabgar gaban sa gefe ɗaya kuwa ƙaton filin rawa ne da ƴan rawa kowanne na ƙoƙarin son ganin ya nuna tasa bajintar, a nan kan table ɗin su kuwa manyan kwalaben wine ne da Maleeka tayi ordering dan iya kam cikakkiyar mashayiyar giya ce, a rana se ta shanye kusan kwalba uku ko huɗu, a irin wannan ranakun kuwa da suka zo club kafin su tashi tana iya shan biyu, ita kuwa Meenah gaba ɗaya hankalin ta yana kan lemon coke da take jijjigawa dan ƙwayoyin da ta zuba su narke, ita bata shan giya amma tana shan ƙwaya, Hameedah kuwa shisha ce take zuƙa tana fesarwa cike da ƙwarewa se Surayya da ita kuma hankalin ta ke kan mazan wajen, ita bata shaye shaye ko kaɗan se dai akwai ta da son maza, gajeren tsaki Kisnah ta saki tana fincike robar coke ɗin dake hannun Meenah dan a ɗan zaman ta na mintina talatin wannan ce roba ta biyu da Meenahn zata shanye wadda ta shigo ta tarar da wata a hannun ta.
Cikin ɗan maye kaɗan da ƙwayar kan saka ta Meenah ta ɗago ta kalle ta, wata shegiyar harara Kisnahn ta wurga mata da ta saka ta komawa ta lafe cikin kujerar ta tana kumshe idanun ta dan tasan ma'anar hararar shine ta shanye iya kason ta na yau.
Miƙewa Kisnah tayi ta zare ƴar jacket ɗin jikin ta ta ajiye kan seat ɗin ta tare da wayoyin ta, gorar sassanyan kunun ayar ta ta buɗe ta ɗaɗɗaka har yai rabi kafin ta rufe ta ajiye ta fice daga VIP ɗin ta nufi wajen masu rawar.
A take duk masu rawar suka tsaya can kafin suka fara fita ya rage saura wasu uku, nan da nan aka canja kiɗan dake tashi wajen daga American songs zuwa Indian songs, wani irin kumshe idanun tayi tana jin kiɗan na ratsa ta kafin a hankali ta fara takawa ta kai tsakiyar mutum ukun, cikin wani irin salo ta fara kakkarya gaɓɓan jikin ta cikin salon waƙar tana malkwaɗe wa, banda ihu da sowa da tafi babu abinda ke tashi a wajen dan ko shakka babu tafi asalin jarumar da ta hau waƙar iyawa, haka ta dinga yin rawar waƙoƙi da dama kafin ta dakata tace a maida mata American songs ɗin, nan ma haka ta hau yi kai kace ba musulma nace balle ɗiyar hausawa kuma.
A nan ta ɓata lokaci har kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare kafin ta fita a wajen, liƙi kam ta sha shi, manyan yaran wajen sun yi ruwan kuɗi kamar a ƙasa ake samo su, daloli da saifa sunyi kuka se ko ƴan dubu dubu dan babu ƙasa da dubun, ko da ta fito kowa ba ta kalla ba duk da ɗumbin mazan dake ƙoƙarin son yi mata magana, maida jacket ɗin tayi jikin ta kana ta zauna kan kujerar ta bayan ta kwashe wayoyin ta da gorar kunun ta ta maida kan table cikin mamakin ina Surayya ta je, takaici ne ya kamata ganin yadda gaba ɗaya daga Meenah har Maleeka suka fita hayyacin su yayinda Hameedah ke ta sambatu cikin maye.
Kawar da kai tayi daga duban su ta buɗe goran kunun ayar ta ta kafa kai ta shanye dan sosai take buƙatar jiƙa maƙoshin ta, cillar da robar tayi sannan ta ja wayar ta ta hau latse latsen ta, tsawon lokaci kafin ta fara jin kan ta yana mata nauyi, jijjiga kan tayi cikin son dena jin komai ta cigaba da danna wayar ta, wani irin jiri jiri ta fara ji kafin ta fara ganin bibiyu uku uku, da sauri ta ajiye wayar tana dafa kanta da hannu ɗaya yayinda take mutstsika idon ta da ɗaya hannun.
Sedai maimakon ta dawo daidai se ma ƙaruwa da abin yake yi dan har gani take kamar gurin na tafiya, sama ta dawo ƙass, kamar dai tana yawo a cikin gajimare, tashi hankalin ta yayi dan duk iskancin ta bata shaye shaye, ba abun da ta tsana ma a rayuwar ta kamar giya, ƙwayar kuwa ko a asibiti aka bata bata sha duk tsananin da rashin lafiyar da take yi kuwa.
Kafin kace me ta rasa hankalin ta gaba ɗaya da har ta faɗa kan table ɗin gaban ta tana wasu irin surutai marasa kan gado gaba ɗaya jikin ta ya saki idanun ta sun juye.
Daga can gefen wajen zaman su wasu samari ne da kallo ɗaya zaka musu kasan manyan yara ne saboda irin shigar dake jikin su, cike table ɗin gaban su yake da kayan shaye shaye, tukunyar shisha, ƙwayoyi, kwalaben maganin tari, cocain har ma da wasu da ban ko san su ba, su huɗu ne kowanne kuma da kalar kayan mayen da yake bankawa cikin sa banda ɗaya daga cikin su da yake danna waya yanayi yana duban Kisnah a kaikaice.
Wani irin shu'umin murmushi ya saki kafin ya dubi na gefen hagun sa yana miƙewa
"Ni na wuce, yau dai tarkon da na ɗana ya kama ɗawisu".
Dariya duk suka sake na gefen damar da na faɗin
"Kai baaba yau zaka kwashi Gara yacin, ko dai nima nazo na ɗana ne in ka gama".
Wata shegiyar harara wanda aka kira da baaba ya sakar masa
"Ka jimin ɗan iska, yau ina suhan ɗin taka da har kake kiran in rage maka, to bari kaji till Dawn zan yi dan haka ma kar ku jira ni ku wuce kawai zamu haɗe gobe".
Sowa suka sa suna tafawa kafin ya musu sallama ya wuce, wajen su Kisnah ya ƙarasa lokacin tayi nisan da har bata gane waye a kanta, hannu yasa ya shafi fuskar ta yana kunshe ido saboda tsananin taushi da santsin fatar ta, wani irin lashe leɓe yayi da harshen sa cikin salon su na gogaggun ƴan guguwa kafin ya sa hannunsa biyu ya ɗauke ta kamar wata baby doll ya fice da ita daga wajen gaba ɗaya.
A tazame Surry dake wani ɗaki ita da saurayin ta suna romance ta fincike jikin ta ganin yadda yau wani namiji ya samu damar taɓa Kisnah har ma ya ɗauke ta a hannun sa, da azama ta fita daga ɗakin wadda dama basu rufe ƙofa ba, to rufewar me zasu yi bayan kowa iskancin sa yake a fili, ko kafin taje har ya saka Kisnah a mota yayi mata key, da gudu Surayya ta koma table ɗin su ta ɗau key ɗin motar ta ta fita itama, tana fitowa compound shikuma Yana fita da motar daga building ɗin, a gigice ta figi motar ta fice kafin masu gadi su gama rufe gate ɗin da ya fita.
Hannu ta kai zata yi accelerating motar se kuma ta fasa dan in yasan an biyo shi ze iya gudun da ze tsere mata dan ƙarfin hali ne kawai take yi amma jikin ta a mace yake da abinda saurayin ta ya gama yi mata.
Sannu a hankali take bin bayan motar har suka ƙarasa bakin kasuwar durumi in da ta tabbatar ko ihu tayi za'a iya jin ta saboda shagunan masu kwana dake kan titin, ƙara gudun motar tayi taje ta sha gaban shi har ƙiris ya rage bata daki gaban motar shi ba, ajiyar zuciya ya sauke jikin sa na ɓari dan da be yi saurin tsaida motar Ba da