Header Ads
Showing 84001 words to 87000 words out of 104570 words

Chapter 29 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1445

Ads at the middle of Article

maimaita mata daidai lokacin kuma da Saraki ya sake yin wata gyaran muryar kafin ta gane me take nufi.


Miƙewa tayi da sauri ta ƙarasa bukkar tare da shigewa dan tun ɗazu take cikin jimiamin rashin farkawar tasa kasancewar tun da suka zo ƙauyen ya farfaɗo bata taɓa ganin yayi nauyin bacci irin wannan ba.


Bata lura da kallon da yake mata ba ta ƙarasa gaban gadon karar da yake kwance ta kai zaune


"Yaa lafiya kuwa yau irin wannan bacci haka, Allah har kasa hankali na ya tashi".


Ko kallon ta be yi ba ya sake yin gyaran murya shi a dole yana neman arɗo


"Yaa arɗo fa baya nan, yau tun sassafe ya fita gona, ya shigo baka tashi ba so se ya tafi".


Se a lokacin ya kalle ta, arɗo baya nan to wa ze taimaka masa yau gashi yana son zagayawa dan fitsari yake ji saboda magungunan da baffa arɗo ya bashi ya sha a can da kuma wanda ya taho dasu yasha kafin ya kwanta.


"Bari in kawo maka ruwa kayi alwala se kayi sallah".


Ta faɗa tana miƙewa zata fita, da sauri ya tsayar da ita dan ji yake kamar marar sa zata yi bombing


"Zan yi fitsari tukunna". Tsayawa tayi tare da juyowa ta kalle shi, ze yi fitsari tabɗin, to ita yaya zata yi mishi ga baffa baya nan.


"Bari in faɗa wa Nenne in ji ko za'a sami wani da zai taimaka maka to".


Wani banzan kallo ya watsa mata jin wani wai se ya tsaya an samo wanda ze taimaka masa, kawai tace so take ya saki fitsarin a nan mana


"Malama in zaki zo ki taimaka min na je bayi ki zo in Kuma ba so kike na sake shi a jiki na ba, salon gulma kawai".


Dariya ce ta ciyo ta ba kaɗan ba ganin yadda yake magana yana ɓaɓɓata fuska at the same time yana mutsu mustu da alamu dai da gaske fitsarin ya matse shin.
Gaban gadon ta matsa tare da miƙa masa hannun ta, se ya gama hararar hannun kafin ya kama da nashi ya fara ƙoƙarin miƙewa ita kuma ta saka ɗayan hannun ta tallafe nasa me ciwon, da ƙyar ya samu ya iya miƙewa dan ba wani ƙwari gare ta ba har kusan faɗo masa tayi.


A hankali yake taka ƙafar sa me ciwon yana bada ƙarfin sa ga mara ciwon ita kuma ta saƙalo hannun ta a ƙugun sa yasa hannun sa me lafiya ya zagaye wuyan ta har suka ƙara sa wani ɗan ƙaramin sabon makewayin da aka yi musu shi jiya wanda duk aikin baffa arɗo ne, ba kamar nasu arɗo ba nasu ginin jar ƙasa ne gaba ɗaya se asabarin da aka rufe saman dashi haka kuma a gefen bukkar su aka yi shi da ke da ɗan nisa da tasu Nenne.


Se da ta shigar dashi banɗakin kafin ta fita bayan ya zauna kan wani ƙaton dutse dake ciki sannan ta koma ta zubo masa ruwa a gwangwani ta tura masa ta koma gefe tana jiran sa.


Ɗan gyaran muryar da yayi ya shaida mata ya gama dan haka ta shiga ta kama shi suka fito se wani hahhaɗe rai yake kamar wanda aka doka ko aka zage shi, se da ya zauna sosai kan gadon sa kafin ta kalle shi cikin tsokana


"Yaa ya Zamuyi ina kashi ya matse ka kuma baffa baya nan?".


Ta faɗa tana saka yatsa a baki irin wai tana tunanin kamar dai yadda yara suke yi, kunya ce ta kama Saraki ganin yadda yarinya ƙarama take neman raina shi, dariya tayi ganin yadda ya sake matse fuska kafin kuma ta haɗiye kayar ta saboda mugun kallon da ya jefa mata


"Am sorry Yaa, Kai ne kake ta wani haɗe rai bayan fitsari kawai kayi kuma ai nima ina yi ba, to meye abin ma damuwar bari in kawo maka ruwan alwalar".


Tana faɗa ta fice da sauri fuskar ta ɗauke da murmushi dan Allah ya sani ya bata dariya ba kaɗan ba.


Inda yake zaune ta kawo ƙatuwar ƙwaryar da yake alwala a ciki tare da wani gwangwanin cike da ruwa, a hankali ya matsa bakin gadon ya tara hannun sa ta shiga zuba masa ruwan yana alwala, yana gamawa ta ɗauka ta fice dashi ta zubar kana ta dawo ɗakin, ganin yana Sallah ta juya ta fita wajen Nenne.


Ko zama bata yi ba Nenne ta tura mata madaidaiciyar ƙwarya rufe da faifai tare da mata alamun ta kaiwa Saraki, ɗauka tayi ta koma bukkar su inda ta tarar ya idar yana zaune yana azkhar, ajiye masa tayi tare da neman guri ta zauna nan kusa da shi, tana zaune ya ƙarasa azkhar ɗin tare da yin addu'a sannan ya dube ta


"Meye kuma?".


Da ido ta nuna masa ƙwaryar da ta ajiye a gefen sa


"Nenne tace in kawo maka".


"Bakin kawo ba, to me kuma kika tsaya jira".


Kwaɓe fuska tayi tana fatan Allah yasa ya yarda dan ita fa bata ƙoshi ba, su Fulani haka suke da ƙauron hannu, ƴar fura da nonon ma da za'a bata ba za'a bata a wadace ba kamar ta wani roƙa.


"Rage min zaka yi Please Yaa, Allah Ni kam ban ƙoshi ba".


Bece mata komai ba ya miƙa hannun sa na hagu da yake da lafiya ya ɗau ƙwaryar tare da buɗe wa ya ɗau ludayin ciki ya ɗebo ze Kai Baki se kuma.ya dakata yana kallon ƙwaryar da hannun sa, a jiye ludayin yayi ya zubawa furar ido kafin ya ɗago ya kalli Kisnah dake zaune tana bin shi da kallo, shi kam Allah ya jarrabe shi a kwanakin nan, hannun dama a karye ko da wanne ze ci abinci yau oho, dama arɗo ke zama ya bashi gashi kuma yau baya nan.


"Lafiya yaa, ko hannun ne yake ciwo?, Ka fama ƙafar ka ne?".


Ta jero masa tambayoyin ganin yadda ya tsaya yana kallon ƙwaryar hannun sa kamar me neman wani abu a ciki, be amsa ta ba se ƙwaryar da ya miƙa mata ta sa hannu ta karɓa kafin ta juyo Muryar sa very low


"Feed me". Ɗan zaro ido tayi tana buɗe baki, ganin abinda yayi yasa shima ya zaro mata nasa kyawawan idanun


"Hannun dama na akwai ciwo I can't eat or drink with left hand, is haram in Islam, so Mrs is not as you think".
Ya ƙarashe yana tsuke baki kamar ƙaramin yaro abin kuwa ba ƙaramin burge Kisnah yayi ba, hannu ta sa ta dafe bakin preventing herself bursting into laughter.


Gyaɗa kai tayi tare da ɗaukar ludayin ta ɗebo furar tare da nufar bakin sa saying
"Haaa, oya buɗe bakin".


Seda ya harare ta kafin ya buɗe bakin sa ta saka masa ya shiga sha, ɗebo wa tayi ta kai bakin ta itama ta sha tana lumshe ido dan se taji kamar tasa ta fi daɗi kan wadda aka bata, sanin neman magana take yasa be ko kalle ta balle yayi mata maganar sha masa da take yi.


Haka suka cigaba da sha su biyu, in ta bashi ta bawa kanta har suka shanye kafin ta sa harshe ta lashe lips ɗin ta, da sauri Saraki ya kawar da kai ganin abinda take yi ya nemo wani ɗan tsumma a gefe ya goge bakin sa kafin ya jingina jikin jan bangon su.


Fita tayi da ƙwayar ta ajiye kana ta dawo da maganin sa da Nenne ta bata ta kawo masa, be yi musu ba ya karɓa yasha ya koma ya jingina yadda yake kafin ta kawo maganin ya rufe idanun sa ya shiga tunani, shikam ya gaji da zaman nan da yake yi waje ɗaya, gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa saboda zaman ga kuma son barin garin da yake yi saboda yanayin cimar su da kuma wajen zaman su, yasani ciwon jikin sa baya rasa nasaba da kwanciya kan gadon karar da yake yi kullum ga kuma wuni zaune waje ɗaya, taya jikin sa baze yi ciwo ba.


Abincin su, hmmm wani daban shima kenan, be ga laifin Kisnah ba da tace ba zata iya cin komai na cimar su ba se fura da nono wanda dama shi ne main food ɗin su, se ku ganyayyaki, zogale, rama, kai abubuwa dai da bai taɓa sanin akwai su ba balle ya san sunan su, bawai ya raina musu bane ba, ya sani suna iya ƙoƙarin su wajen kula dasu, ko ɗauko su da arɗo yayi wani abu ne dan a yadda yanzu duniya ta lalace ba kowa ne ze iya kasadar ɗaukar su ba batare da yasan ko su waye su ba, mugaye ne ko mutanen kirki, kawai dai basu saba da wanann yanayin rayuwar ba adopting ɗin shi cikin sauƙi abu ne me wuya a gare su, addu'ar sa ɗaya Allah ya bashi lafiya da gaggawa su bar garin dan ko a wajen shi ba'a samu matsala ba ya tabbatar a wajen ta se an samu.


Nauyin da yaji a ɓarin hangun sa yasa ya buɗe ido yana kai duban sa wajen, itace kwance a jikin sa kan ta a gefen kafaɗar sa ragowar jikin ta kan gadon shi tana bacci, sosai yake mamakin saurin baccin da take yi yanzu sedai daga baya ya dena, to in bata yi bacci ba me zata yi, ita ba waya ba balle ta danna, ita ba abokin fira ba gashi tun jiya ya gargaɗe ta da kar ta kuma fita, dole kuwa ta yi bacci ai.


Zame ta yayi ya kwantar ya cigaba da tunanin sa har be san lokacin da shima baccin ya ɗauke shi ba.


Muryar Nenne dake ta magana a bakin ƙafa ya farkar dashi dan bashi da nauyin bacci, motsawa yayi yana gyara zaman sa tare da yamutsa fuska jin hannun ya sake saboda nauyin da ya bashi da yana bacci, gyaran murya yayi saboda har lokacin Nenne bata dena magana ba, ajiye kwanon hannun ta tayi tana faɗin


"Nashe ga nan abinshin ku bakin danga".


Da toh ya amsa mata dan ya gane me take son cewa, ga abincin su nan a bakin ƙafa, hannu yasa ya shiga bubbuga kafaɗar Kisnah dake kwance dan taje ta ɗauko kwanon da Nennen ta ajiye, buɗe idanun ta da suka sauya kala saboda bacci tayi a kansa tana bin sa da su dan son jin dalilin tashin ta


"Ki tashi ki ɗauko kwano ga shi can bakin ƙofa and ki duba min kamar lokacin Sallah yayi".


Zaune ta miƙe tana yin miƙar da ta sa Saraki kau da kan sa da sauri ganin fitsarar da take yi gaban sa ba ko kunya, se da tayi son ranta kafin ta miƙe tana tafiya a sanyaye ta ɗauko kwanon ta dawo ta ajiye sannan ta fita, gwangwani ta ɗauka ta ɗauraye bakin ta sannan ta shiga bukkar Nenne dan ta gama cure furar ta shiga ɗaki.


"Lokacin sallah yayi Nenne?".


Gyaɗa mata kai Nenne tayi tana mata murmushi itama ta maida mata tare da fita zuwa tasu bukkar ko ɗaki zata ce dan dai tasu ginin ƙasa ne gaba dayan ta se asabari a sama da aka rufe saman dashi.


Gaban shi ta zauna tana ɗan jingina jikin kafaɗar sa dan jikin ta ba wani ƙwari saboda baccin da tayi, ture ta yayi daga jikin sa hakan yasa ta shiga ƙunƙuni ƙasa ƙasa, haɗa idon da suka yi yasa ta kwaɓe fuska


"Ai dai ba abinda nace".


"Buɗe kwanon nan".


Matsawa tayi gaban akushin da ke ajiye ta buɗe shi, yamutsa fuska tayi ganin abinda ke ciki kafin ta maida ta rufe, kallon shi tayi tana faɗa masa me ke ciki ganin yadda ya bita da kallo................................✍️.


















©️ Ouummey 📚✍️.


















☑️Ote, Comment and share fisabilillah.














Ouummey 35 (8/25/2022 9:57 PM)





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________












Page 3️⃣5️⃣


























_________________________📖 kallon kwanon yayi ya kuma kallon ta yana tunani me ye something atrocious ɗin da tace,


"In gani".


Matsar da kwanon tayi gaban sa yasa hannu ya buɗe, zubawa zogalen da yasha haɗi yaji ƙuli ƙuli yayi kyau ido yayi, so this is something atrocious a wajen ta kenan, ɗago wa yayi ya dube ta se kallon sa take tana ɓata fuska, miƙa mata kwanon yai ta karɓa tana neman rufewa ya tare ta


"Bani naci". Zaro ido tayi waje jin abinda yace, shin be ga meke cikin kwanon bane da zece ta bashi, ko kuwa dan yana jin yunwa ze ci, in kuwa hakane yanzu zata je ta maida wa Nenne su dai kawai a basu furar su sha.


"Yunwa kake ji ko yaa, bari na maida mata abin nan nace a bamu fura kaji, dama nasan kaima bazaka iya cin wannan trash ɗin ba".


Dakatar da ita yayi daga fitar da zata yi


"Wannan ɗin nake son ci, in ke a wajen ki trash ne to ni a wajena yafi ye min all that luxurious dishes, ko kin manta da background ɗina ne, being with you doesn't make me as you, you're rich and am not, you're from a high class family and am from from a middle class family, so you go and get the fura, as for me this is what I want but don't forget we have no any relation with these people, they're only helping and yet they are trying their best with all they have, if you won't appreciate it I think you shouldn't curse it".


Cak ta tsaya a inda take tana sauraren sa, sosai jikin ta yayi sanyi da kalaman sa, 2 mins back ba taga aibu a cikin maida zogalen ba amma yanzu kam da ya faɗa mata wannan words ɗin se taji sam bata kyauta ba, ta sani wannan shine cimar su and shine abinda suka basu, in ta koma tace a canja is like ta Raina musu, bata gode ba kuma ta raina wa ƙoƙarin su.


A hankali ta dawo ta zauna in da ta tashi ta saka hannun ta ta ɗebo zuwa bakin sa, buɗe wa yayi ta saka masa ya shiga taunawa knowing ba zata ci ba sedai ga mamakin sa she feed herself also kuma duk yadda taso ganin wani baƙon reaction akan abinda bata saba ci ba be gani ba dan bata nuna masa komai ba ta shiga taunawa har ta haɗiye though deeo down tana dannewa ne amma ji take kamar tayi amai.


Haka suka cinye zogalen tass kafin ta ɗebo masa ruwa yasha ya kuma yi alwala, kallon ta yayi lokacin da ta koma ta zauna, fasa tada sallar yayi ya dube ta


"Ke ba zaki yi sallar bane?".


"Zanyi da magrib".


Ba abin mamaki bane a wajen sa jin hakan daga gare ta sedai abin haushi ne dan be manta not more than 10 days back da suke tare a Company yana ƙoƙarin saka ta yin Sallah a kan lokaci duk in lokaci yayi amma shine har zata ce masa wai zata yi da magrib, a yanda ya ke ji kaman ya rufe ta da duka wallahi se dai Allah ya taimake ta hannun sa be da lafiya


"You get up go and pray ko se ranki ya ɓaci, mara hankali kawai".


Tun tsawan da ya daka mata tayi wuff ta fice daga ɗakin sedai jin last word ɗin da ya faɗa ya mata ciwo, itace mara hankali, mara hankali fa ya kirata, is he in his right sense kuwa ko ko dan bata nuna masa kalar ta bane, ko kuwa gaskiyar Hameedah ne ta sake masa da yawa, aikuwa in haka ne ze san da ita yake wallahi.


Cikin ɓacin rai tayi alwalar ta koma bukkar su ta yafa wani baƙin saƙi da Nenne ta bata wai mayafi tayi sallar, tana idarwa ta matsa can gefe ta zauna ya shiga tunani, tunanin iyayen ta dama rayuwar ta gaba ɗaya!




*SAKEENA SAFWAN*




Sunan mahaifin ta Alh Safwan Yaƙoub, asalin su mutanen ƙasar Congo ne dake maƙwabtaka da tasu, cirani ya kawo shi ƙasar Hawarya inda ya bar ƙanin sa ɗaya tal da yake dashi a can gida Congo, mahaifin su Safwan wato Yaƙoub manomi ne me ƙaramin ƙarfi wanda yake da mata biyu, A'i da suke kira Inna se kuma Inna lami da ainahin sunan ta Sakeena ne.


Inna A'i ita ce mata ta farko wajen Malam Yaƙoub da aka yi masa auren ladan noma da ita, shekara huɗu da auren amma bata taɓa ko ɓarin wata ba balle a yi batun haihuwa hakan yasa iyayen Malam Yaƙoub sake nemo masa auren Sakeena wato ladi.


Shekarar farko ta auren bata ƙare ba se da ciki jikin ladi, wata goma cif cif ta haifi ɗan ta namiji, sati na zagayowa kuwa aka raɗa masa suna Safwan, Safwan na isa yaye Inna A'i ta karɓe shi daga hannun ladi ta cigaba da rainon sa cikin tsananin soyayya.


Shekarar Safwan uku Allah ya azurta Inna A'i da samun nata rabon wanda ba ƙaramin murna ladi da malam Yaƙoub suka yi ba, aka raini ciki cikin tsananin kulawa har zuwa haihuwar sa itama ta haifi nata namiji yaci suna Sama'ila da sati ya zagayo.


Haihuwar Sama'ila yasa malam Yaƙoub maida wa ladi Safwan ganin babu ɗa ko ɗaya a wajen ta ita, a wannan shekarar kuma Inna ladi ta yi ɓaci har so huɗu d hakan ya tasar wa da malam Yaƙoub hankali aka shiga neman magani.


Ciki na biyar ɗin da aka samu kuwa ya zauna da taimakon Ubangiji sedai ko da aika haife shi be zo da rai ba, bayan wannan se da ta sake yin biyu suma suna mutuwa kafin haihuwar ta tsaya gaba ɗaya.


Safwan da Sama'ila sun tashi tare duk da kana ganin Safwan zaka san shine gaba da Sama'ila dan gaba ɗaya ya gado malam Yaƙoub wajen ƙirar jiki irin ta cikakkun jaruman maza yayinda a kamannin fuska kuwa ya haɗe kamannin iyayen biyu hakan ya sa ya tashi da tsananin kyau dan duk

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads