Header Ads
Showing 102001 words to 104570 words out of 104570 words

Chapter 35 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1436

Ads at the middle of Article

Page 4️⃣1️⃣




























_________________________📖 kan katifar su ka kwanta su biyun sedai kowa yana edge ɗaya na each side, dukkan su sun daɗe bacci be ɗauke su kowa da irin kalar tunanin da yake a ransa kafin Sarkin iya sata ya ƙwamushe su.


Yau ma seda ya tada ta da asuba sedai be fita ba se da ya tasa ta gaba tayi alwala tare da saka hijab ta zauna kan dadduma sannan ne ya fita, zama tayi jiran ayi kiran sallah na biyu ta gabatar da sallah kamar yadda yace mata sedai ta ƙi yin nafilar da yace ta yi maimakon zaman jira dan kar bacci ya ɗauke ta.


Tana idar da sallah ta cire hijab ɗin ta ninke ta maida jakar kayan ta ta koma katifa ta kwanta cikin sake sabon bacci, ko da ya dawo ya same ta kwance be yi yunƙurin tashin ta ba dan jikin sa ya bashi tayi Sallah, kan daddumar da ta bari ya zauna ya shiga yin azkhar ɗin sa ya gama ya ɗora da tasibihan da ya saba sannan ya tashi ya zare doguwar rigar jikin sa ya ajiye tare da mayar musu da ƙofar ya rufe ya wuce kan mattress ɗin ya kwanta a wajen sa tare da lulluɓa, mintuna kaɗan kuwa bacci ya ɗauke shi dan har yanzu yana ɗan jin gajiyar aikin jiya a jikin sa.


Hayaniyar yara dake tashi a tsakar gidan ya hanata bacci yadda take so dole ta haƙura ta tashi ta zauna tare da duban wall clock ɗin da ya taho dashi jiya bayan Isha da ya je siyo musu abinda zasu ci, ƙarfe tara da mintuna uku na safe amma shi ne har yara sun tashi a baccin su gashi itama sun hanata nata da iface ifacen su da duk bata saba dashi ba, ita a gida in ta kwanta bacci ba wanda ke tashin ta har se ta gaji ta tashi dan kanta, to ina ma suke da yaran da zasu dinga irin wannan hayaniyar.


Tsaki taja tana ayya na sam gidan haya be yi ba a ranta, kallon gefen da Saraki yake tayi taga shi baccin sa yake hankali kwance da alama ma be san ana wata hayaniya ba balle har ta dame shi, buta ta ɗauka ta buɗe ɗakin ta fita tana hamma a hankali, drum ɗin su ta buɗe ta ɗebi ruwa cikin butar dan zuwa toilet sedai tana zuwa bakin toilet ɗin ta ja ta tsaya ganin yadda aka yi masa kai baka ce shine wanda ta wanke jiyan nan ba, wani irin ɓaci ranta yayi da bata san sanda ta doka uban tsaki ba ta juya zuwa ɗakin su bayan ta dangwarar da butar a ƙofar shiga ɗakin.


Fitsari take ji sosai ga kuma wanka tana son yi amma a yadda toilet ɗin yake ta gwammace tayi fitsarin a jikin ta da ta shiga, takaici yasa kawai ta fashe da kuka dan fitsarin ya matse ta.


Kukan ta ne ya tashe sa daga baccin da yake yi, be miƙe ba seda ya saurara sosai yaji kukan a ɗakin su ne, zaune tsakiyar carpet ya ganta ta haɗa kai da gwiwa tana gurzar kuka kamar ƙaramar yarinya, dafe goshin sa yayi cikin tambayar kansa yanzu kuma me aka yi mata da take wanann kukan da sassafe, kallon ƙofar su yayi da haske ya ratso ta jikin labulen lu, shi dai yasan seda ya rufe ƙofar daze kwanta dan haka kenan ita ta buɗe ta fita, kenan a wajen akayi mata abinda yasa take kukan hala, ganin tunani baze kaishi ba yasa ya tambaye ta da Muryar sa irin ta wanda ya tashi da bacci


"Ada dai nasan kina da jarumtar rashin yawan kuka sedai naga alama a kwanakin nan kin koma raguwar ƙarfi da yaji, yanzu kuma me akai miki kike kuka haka kamar wata ƴar baby?".


Seda ta ja hanci kafin ta buɗe baki tayi magana cikin sautin kukan da har lokacin bata dena ba


"Ba toilet zan shiga ba, kuma duk an ɓata shi kamar ban yi wahalar wanke shi ba jiya kuma ni fitsari nake ji sosai".


"Kawai ki ce kina son yin kashi kuma sun ɓata meye na sako kin wanke shi jiya in ba salon dama kiyi min gori ba kin wanke min toilet nayi wanka, Allah ma yasa ni ban sa mutum ba".


Ta sani so yake ta bar kukan shi yasa ya tsokane ta sedai bata jin zata saki ranta in ba fitsarin nan tayi ba dan ji take marar ta ta wani ɗaure kamar zata fashe.


Fita yayi daga ɗakin ya ɗau bucket ɗin wankan su ya cika da ruwa kana ya dawo ɗaki ya ɗauki basket ɗin wanke toilet ya fita, da sauri ta tashi ta bishi daidai lokacin da ya zare jallabiyar jikin sa da ya saka lokacin da ze fito ta karɓa da sauri shi kuma ya shiga wanke toilet ɗin tana tsaye bakin ƙofar riƙe da rigar sa, seda ya wanke toilet ɗin fes kafin ya ɗauraye sannan ya karɓi rigar sa ya zura ya fito ta maida ƙofar ta rufe da sauri dan kamar ma fitsarin ya fara zubowa taji, ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta gama fitsarin tayi tsarki sannan ta buɗe ƙofar zata fito sedai taci karo da ruwa a bucket ɗin su tare da kwandon wanka bakin ƙofar, zagaye wa tayi ta wuce zuwa ƙofar ɗakin ta ɗaya labulen tana tambayar sa ruwan wankan sa ne wancan sedai amsar da ya bata yasa taji wani abu na ratsa zuciyar ta game dashi


"No naki ne, ki maza kije kiyi wankan kafin nan nawa yayi zafi se in yi in kika fito, in Kuma kika bari suka sake ɓatawa ba wanke miki zan yi ba tam".


Murmushi ta saki na farin ciki kafin ta juya ta koma toilet ɗin ta shigar da ruwan da kwandon ta rufe ƙofar ta shiga wanka tana lumshe ido saboda zafin ruwan da ke ratsa ta, duk da ta fi son wanka da ruwan sanyi amma wanan ta san zai taimaka wajen tafiyar mata da gajiyar gyara ɗakin da suka yi dan gwara shi yayi wanka tun jiyan ita kuwa se yanzu ne za tayi .


Dogon hijab ɗin da ta saka ta ɗora kan towel ɗin da ta ɗaura a jikin ta ta buɗe ƙofar ta fito hannun ta riƙe da bucket da basket ɗin su a ciki, a ƙofar su ta ajiye ta shige ɗakin da ƴar guntuwar sallama a bakin ta, miƙewa yayi ya bi ta gefen ta ya fita zuwa juye nasa ruwan yayinda ita kuma take kiciniyar cire hijab ɗin jikin ta dan ta shirya.


A nutse ta kammala shafar ta sannan ta ciri wasu riga da skirt da ta gani cikin jakar kayan da yace mata ta ta ce ta sanya, skirt ɗin baƙi ne daya sauka har kan ƙaurin ta se rigar sa ja da tayi mata cif cif a jiki, gyara gashin ta tayi ta sa masa ribbon ta zazzage jakar cikin neman abinda zata rufe gashin ta dan so take ta fita ta nema musu abin da zasu karya, se da ta birkice kayan duka kafin ta samo ƙaramin baƙin veil ɗin wata Arabian gown me sauƙin kuɗi da ya haɗa mata a kayan, mai da ragowar tayi ta rufe jakar sannan ta yafa veil ɗin da ya tsaya iya kafaɗun ta ta fita bayan ta ciri kayan tea a gurin da suka adana kayan abincin su, gas ta kunna ta ɗora ƙaramar tukunya ta zuba madaidaicin ruwa tare da jefa Lipton ɗin a ciki ta rufe ta zauna kan ƙaramar kujerar robar da ya haɗo cikin kayan robobin da ya siyo musu tana jiran shayin ya tafasa.


Tana zaune ya fito daga wanka ya nufo ɗakin, gaban ta ya tsaya yana ƙarewa shigar ta kallo kafin ya juya bayan su dan ganin ko akwai me ganin su, ba kowa se yaran da ke ta wasan su a tsakar gidan da suka yi wa kaca kaca kasancewar weekend ba boko se islamiyya ita kuma se da rana, fisgo hannun ta yayi daga zaunen da seda ta miƙe haka kuma ba ɓata lokaci ta faɗa kan ƙirjin sa dan fisgar ba ta wasa ya mata ba, cikin ɗakin ya jata suka shiga kafin ya saki hannun ta ya shiga bin ta da kallo, ran sa ya matuƙar ɓaci ganin ta zaune a tsakar gida da wannan shigar a jikin ta bayan ta san basu kaɗai bane a gidan sedai yanzu da ya gama ƙare mata kallo se ya nemi faɗan da ya shigo da ita ze mata ya rasa dan ba ƙarya kayan sun matuƙar amsar ta haka sun fito da hasken ta sosai, ba ƙaramin kyau tayi masa ba shiyasa ya manta da faɗan da ya shirya yi


"Lafiya yaa, tea fa nake dafawa Dan mu karya, am hungry sosai".


Ta tambaya ganin bece mata komai ba se kallon ta da yake yi hakan yasa ya tuno da faɗan da yayi niyya dan haka ya watsa mata harara


"Wai me yasa bakya jin magana ne, so nawa zan faɗa miki babu kyau fita da irin shigar jikin ki amma dan taurin kunne kin ƙi denawa, yanzu dan Allah dubi fa yadda kika fita bayan kin san akwai wasu mazan da basu dace su ganki a haka ba".


Kallon kanta ta sake yi tun daga ƙasa har sama kafin ta dube shi


"Yaa kalla fa kayan jiki na ba inda yake buɗe a jikina se fa hannu na kawai, and se fa da nasa veil a kaina fa, kuma iya ƙofar ɗaki na fita ba waje ba".


"Ba inda yake buɗe amma ba curve ɗin da be bayyana ba a jikin naki zaki tsaya yi min musu, meye amfanin veil ɗin naki, da baki saka ba gaba ɗaya ze fi, tunda da baki fita ba ai seki sa himma yanzu ki fitan na manta ne ba yau kika fara tallan jikin ki ba kin saba, You go ahead ki nuna halin ki anan ɗin ma kinji".


Ya ƙarashe a zafafe jin tana neman raina masa hankalin wai ba waje ta fita ba, to me ya hana ta fita wajen se taji daɗin da take so kowane low class ya kalle ta ai dama ta saba.


Ita ba me damuwa da abinda mutane suke faɗa a kanta bace shiyasa bata taɓa ɓata ranta dan an kira ta karuwa sedai bata san me yasa ba a duk lokacin da shi ya faɗa mata magana se taji rayuwar ta ya ɓaci kamar dai yau, gaba ɗaya walwalar da ta tashi da ita se ta neme ta ta rasa, bata kuma ce masa komai ba kamar yadda be kuma kallon ta ba ya juya ya zauna kan katifa yana shafa mai a jikin sa, dogon hijab ɗin da ta shiga wanka dashi ta zura jikin ta ta fita wajen gas ɗin, tea ɗin ya tafasa ba so ɗaya ba dan gashi nan yayi kala sosai, madaidaicin tea flask ɗin su ta janyo ta saka cup ta dinga ɗiba tana zubawa a ciki har ya kusa cika sannan ya ƙare ta sauke tukunyar ta ajiye a ƙasa dan dama ta kashe gas ɗin.


Ɗauraye pot ɗin tayi ta maida ɗaki sannan ta koma ta shigar da flask ɗin ciki ta ajiye tsakiyar carpet ɗin su, cups ta ɗauka ta fita ta ɗauraye suma ta kai kusa da flask ɗin sannan ta ɗauko gwangwanayen kayan madara da ya siyo jiya da dare tare da bread ta ajiye, cup ɗin da ya fi girma ta ɗauka ta tsiyaya masa tea ɗin ta saka cubes ɗin sugar huɗu ta zuba masa madara da bournvita sannan ta kai masa gaban sa da yake zaune kan carpet kusa da katifar su ya shirya cikin jeans dogo da t-shirt.


Duk abinda take yi yana kallon ta haka kuma mamaki ne ya hana shi magana na yanda ta haɗa tea daidai, tambayar kan sa ya ringa yi a ina ta koya kafin kuma ya bawa kansa amsa da ai ba wani wahala zata iya haɗawa dan alamu sun nuna ita ke haɗawa kanta.


Nata ta haɗa ta koma gefe ta shiga sipping a hankali zafin shi na ɗan ƙona ta sedai ko kaɗan ba wannan zafin ne a gaban ta ba dan zafin maganganun da ya faɗa mata ɗazu sun ninka wannan so ba iya ka, ko rabi bata yi ba taji shayin ya fita a kanta ta ajiye dan dama haka take, indai ranta a ɓace yake bata iya cin abinci shiyasa ba ta ko kalli gefen da bread ɗin yake saboda tasan ba zata iya ci ba.


Tunanin rayuwar ta ta shiga yi da yadda ta taso ba wani me kwaɓa, komai tayi kawai daidai ne a wajen kowa, bane ce mata yi, bari, gyara ko makamancin haka shiyasa take duk abinda taga yayi mata daidai a ranta, yanayin shigar ta kuwa abu ne da yabi jinin ta, tun da tayi hankali da masu irin shigar ta buɗi ido ta kuma rayu a tsakiyar su under supervision ɗin Mrs Andrew Smith Wanda itace matar shugabar makarantar da kawu ya danƙata a hannun sa, bata san meye al'adar ta ba, bata san meye daidai da ba daidai a addinin ta ba tunda bata da wani ilimi a kai shiyasa tayi adopting gaba ɗaya culture ɗin su da ma wasu da yawa daga cikin ra'ayin su da yanayin rayuwar su, sallah ce kaɗai ta banbanta sunan ta da kasancewa kafira wanda da za'a bi diddigi ita kanta sallar ba tabbas ɗin tana amsuwa dan kwata kwata ko kusa ko alama ba ta yinta yadda Annabi ya koyar, to bata da ilimin hakan shiyasa kawai dai tana yin ta ne.


Hawaye ne suka cika idanun ta dan tasan da iyayen ta basu rasu ba da bata kasance cikin irin wannan rayuwar ba balle har ya ringa samun damar yi mata gori da baƙaƙen maganganu.


Cin bread ɗin yake yana korawa da tea kamar a ɗan gaggauce dan yana so ya zagaya yaga wace irin sana'a ze kama da zata fisshe shi, har ya gama tana zaune inda take cikin rashin daɗin rai, seda ya ajiye cup ɗin hannun sa ya miƙe sannan itama ta miƙe ta ƙarasa ta ɗauke cup ɗin ta fitar waje ta dawo ta shiga gyaran ɗakin cikin sanyin jiki, katifar ta fara gyarawa ta karkaɓe bedsheet ɗin ta maida ta gyara sannan ta mai da kowane abu inda ya kamata kafin ta ɗau tsintsiya ta shiga shara, seda ta gama ta kwashe da ƙyar dan bata iya ba haka kuma bata jin ko son Kiran sunan sa balle tace ya koya mata, ruwa ta kawo tayi mopping floor ɗin iya yanda ta iya sannan ta maida carpet ɗin da ta naɗe tare da fesa room fresheners kala biyu.


Seda ta gama komai sannan ta ɗauko ƙaramin jotter da biro da ta karɓa jiya wajen saudah ta shiga rubuta masa duk abinda basu dashi na girki da ragowar amfanin yau da gobe, miƙa masa paper ɗin tayi bayan ta duba taga komai yayi, be tambayi ta me ce ba ya karɓa ya bi abubuwan da kallo kafin ya gane na meye.


Da "adawo lafiya". ta bishi da ze fita daga ɗakin duk da bece mata fita ze yi ba alamun fushi yake da ita, yana ficewa ta tura ƙofar ɗakin amma bata saka lock ba ta koma kan katifa ta shiga share hawayen da ta ke ta dannewa kar su fito a gaban sa..........................✍️.












©️ Ouummey 📚✍️.




















☑️Ote, Comment and share fisabilillah.

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads