Header Ads
Showing 69001 words to 72000 words out of 104570 words

Chapter 24 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1442

Ads at the middle of Article

so cin abinci gaban sa baze gagare ta ba.


Messenger ɗin ta ta kira ta bashi ragowar da ta rage tace a bawa me so ta cigaba da aikin ta, wasa wasa basu bar office ɗin ba se after six, gudu sosai Saraki yayi ranar dan baya son missing magrib prayer da ake ta kira a masallatai, ko da yayi parking be fita ba se da ya sake jaddada wa Kisnah tayi sallah da ta shiga gida fiye da so uku sannan ya wuce a hanzar ce zuwa masallaci.


Ko da ta shiga wanka ta fara yi tare da canja kayan jikin ta da suka takure ta, gajeran wando ta saka da ya wuce cinyoyin ta se ƙaramar riga me kamar shimi tana yi tana tunanin yanda zata dena saka irin wannan kayan ta koma saka wasu, tuno da yace tayi Sallah yasa ta miƙe tana ɓaɓɓata fuska kamar yana gaban ta ya zurma hijabin tayi ƴar fakin ta kamar yadda ta saba.


Kan bed ta faɗa dan kam yau bacci zata yi da wuri dan ta huce gajiya ta kuma tashi da wuri gobe, da kayan jikin ta ta kwanta bayan tayi offing light tare da locking ƙofar ta, within minutes tayi bacci abin ta.


A can ɓangaren Saraki kuwa be dawo gida ba seda akayi sallar Isha, wanka yayi ya canja kaya zuwa jallabiya mara nauyi ya zauna kan sofar ɗakin ya buɗe pack ɗin abincin sa na tun office dan shikam kasa ci yayi a can, gani yake kallon sa zata dinga yi.


Seda ya cika cikin sa ya kwashe ragowar ya saka a fridge sannan ya zauna zuwa lokacin da abincin ze faɗa masa, tunanin ta ne ya faɗo masa a lokacin


"Allah yasa tayi Sallar". Ya faɗa a fili dan yasan kaɗan daga ayyukan ta taƙi yi ɗin, wanda tayi ma takura mata yayi to wanna da baya nan kuwa ai se abinda Allah yayi kawai.


Murmushi yayi tuno dramar su a office ɗin yau, ya sani she's so simple compared to girls of her age Kuma masu kyau da dukiya irin nata, ya sani da wata ce baya jin de iya tanƙwara ta cikin sauƙi haka bayan shi ɗin ba komai ne gare ta ba se mere driver Wanda yake mata aiki take biyan shi haka kuma yasan Allah ne yaso ta da shiriya shiyasa ya sa ta zama mara girman kai balle wulaƙanci though yakan ga tayi wa wasu sedai yawanci ba talakawa bane masu kuɗi ne wanda ya fahimci kodai sun shiga gonar ta ko kuwa sun wulaƙanta kan su.


Kwanciya yayi tare da karanto addu'ar bacci ya shafe jikin sa kana ya lulluɓa yana rufe idanun sa a hankali hopping bacci ya ɗauke shi kar ya kuma shiga wata duniyar tunanin da yake ta hana kan shi faɗawa a kullum.




*******


"Wai Awwaf me kake nufi da zaman da kayi a wajen ƴan iskan abokan ka bayan kasan ina jiran ka mu fara namu takun kan waccan ƴar iskar, in Kuma ka fasa ba zaka iya bane ka faɗa min in yi introducing wanda ze iya cikin tafiya ta".


Da sauri ya miƙe zaune yana hankaɗe matashiyar dake kwance kan sa, Muryar sa har tana rawa ya fara magana


"Haba Mommy wane irin bazan iya ba, kin kuwa san yadda nake burin mallakar yarinyar nan da har kike batun kawo wani, to wallahi bari kiji in kika yi hakan se na tona asirin kowa ya sani, gwara ma ki jira ni dan nan da kwana uku zamu dawo, ina dawowa kuwa ba ɗaga ƙafa zan yi ba dan nasan tun yanzu kun riga kun shirya yadda komai ze kasance".


"Are You threaten me?, Lallai har yanzu baka san wace uwar ka ba, ka wuce kwana ukun da kace ka gani in komai be faru ba, sedai kaji ana yi shashasha kawai".


Mommy ta katse wayar tana huci dan kalaman Awwaf ɗin na wai ze Tona asirin ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, zaman tayi a kan kujera tana jefar da wayar, da sauri ƙawar ta Jamila dake zaune ta cafe tana matsowa kusa da Mommyn


"Haba sadiya, meye abin fushi haka a maganar yaron nan, kin fa san su samarin nan in suka ga sun girma se haƙuri, kawai lallaɓa shi za muyi ya dawo dan plan ɗin se ya fi tafiya dashi dan nikam yanzu bana yadda da saka bare cikin aiki na kin san mutanen yanzu ba amana, kalli fa yadda yaron can Nuhu ya ci amanar Hajiya Talatu, yanzu gashi ta sanadin sa tayi biyu babu, shiyasa duk abin naka gwara shi ɗin dai, so ki kwantar da hankalin ki dan Ni nasa zamu yi Nasara, tabbas zamu lalata rayuwar Kisnah ni na faɗa miki".


Ajiyar zuciya Mommy ta sauke tare da wani zazzafan huci


"Duk yadda zan kwatanta miki yadda na tsani yarinyar nan Jamila ba lallai ki game ba, kin san dai yadda muka sha fama da rayuwa cikin talauci har Allah ya kashe iyayen ta muka dawo zama tare da ita cikin daula, ina faɗa miki yarinyar nan bata taɓa bari na na samu kwanciyar hankali ba tun ma tana yarinya har se da baban Maigado ya kai ta England karatu sannan na sami sauƙi muka sami damar rayuwa cikin jin daɗi da walwala muka huce duk wani haushin abubuwan da talauci ya sa mana a da, zan iya ce miki ban taɓa shiga cikin damuwar da na shiga ba shekaru huɗu baya zuwa yau wato dawowar yarinyar kenan, ban san wane irin banzan tunani ne ke damun baban Maigado ba amma saboda tsabar baƙin ciki yaƙi kai Maigado ƙasar waje karatu, ki ga dai yadda ita wannan ta yi kyau ta ƙaro aji ga wayewa shiyasa samari kamar ana mata wahayi dan ma ita bata saurarar su ita kuwa Maigado fa, duk da ta samu waye wa da aji amma ai ba kamar waccan ba haka kafin kiga saurayi ɗaya ya biyo Maigado da sunan aure wallahi se a fi watanni zuwa shekara, sedai an ayi rayuwa a ji daɗi sauƙi na ɗaya ita sam ba hakan a gaban ta amma da ya kike zaton tashin hankalin da zan shiga, yanzu fa ki kalla wai ta koma zuwa Companies ɗin ta zata dinga kula dasu manufar ta a hankali a hankali ta ƙwace komai nata dake hannun baban Maigado, ta yaya hankali na ze kwanta in har ban ga na Kai ta ƙasa ba fisabilillahi".


Sauke numfashi Jamila tayi tana gyara zama sosai tare da fuskantar Mommy


"Shiyasa nace miki da ki yarda Awwaf ya aure ta, a ganina ta haka ne kawai zamu sami nasara a kanta, kinga maganar Companies ko d ta ƙwace wa take dashi da zai kula mata dasu dole dai mijin t zata ɗora a kan komai so kinga sun dawo hannun mu dai haka kuma ta nan ne kaɗai zaki sami damar musguna mata ki fanshe duk tarin tashin hankali da damuwar da ta jefa ki a ciki ko ba haka ba?".


Shiru Mommy tayi dan ita kam Allah ya sani bata jin zata taɓa yarda ta bar ɗan ta auren yarinyar da ta san karuwa ce, ita da take fatan samun tsarkakkun jikoki da sirika me mutunci se ta yadda a kwaso mata kaska, to amma kuma duk batun Jamila na akan hanya, bari dai zata yi tunani taga wanne ne fi mata in ya kama auren se ta haƙura amma fa se ta tabbatar ta hana ga haihuwa dan bata buƙatar zuri'a daga gare ta.


Juyowa tayi ta kalli ƙawar ta kuma ƴar uwar ta da ta zuba mata ido dan jin me ta yanke


"Kin kawo shawara me kyau dan haka zan yi tunani Jamila, kafin dawowar Awwaf zamu tsayar da batu ɗaya".


Jinjina mata kai jamilar tayi ta reda sauke murya tayi mata raɗar da ta sa suka saki dariya tare da tafawa....................✍️.






















©️ Ouummey 📚✍️.


































Ouummey 29 (8/21/2022 10:30 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________














Page 2️⃣9️⃣




_______________________📖 Yau ma Ka&S drinks suka nufa maimakon K&S Furnitures kamar yadda su kawu suka yi hasashe dan bata jin zata iya tafiya ta bar gurin nan a yadda yake sedai a maimakon su zauna duka su biyu se ya ajiye ta shi ya tafi construction company ɗin dan cikin zuwan da suka yiyyi tare ya fahimci yadda wajen yake tafiya se a bin da ba'a rasa ba.


Cikin farin ciki kawu ya ƙaraso cike da jin daɗin ze gabatar da aikin sa hankali kwance sedai lokaci ɗaya fara'ar nan ta ɓace ɓat lokacin da yayi ido biyu da Saraki zaune kan kujerar sa cikin office ɗin Kisnah.


Be sami zarafin cewa komai ba yaga Sarakin ya miƙe dan lokacin suke da meeting da wani Company da zasu basu kwangila, cikin ɓacin rai kawu ya juya gida dan ji yayi ma sam baze iya zama cikin Company ɗin ba.


Cikin kwanciyar hankali aka gama meeting ɗin komai ya tafi daidai, sedai a maimakon Saraki ya bari a saka rabin kuɗin aikin da aka yi da su zasu biya cikin account ɗin banki se ya bayar dana Kisnah dan haka kawai yake jin something is fishy a nan ɗin ma dan haka ya ɗau wannan matakin wajen daƙile koma meke shirin afkuwa.


Tana zaune tana aikin ta can a office ta ji ƙarar shigowar alert phone ɗin ta, ajiye aikin tayi tare da jawo wayar, mamaki ne ya cika ta ganin uwar kuɗin da ya shigo cikin account ɗin ta ko da ta duba sunan se ta ga sunan Company ɗin da suke batun karɓar kwangila wajen su ne, kenan hakan na nufin an daidaita shine suka yi half payment ko me, Yes haka ne ma, to amma me ze sa a saka kuɗin cikin account ɗin ta bayan akwai na Company?.


Shiru tayi tana jujjuya lamarin cikin ranta se dai ganin ta kasa ganewa se ta ajiye shi a gefe dan ta san dole Saraki ze mata bayani.


Tuno da sunan sa ya sa ta kalli wajen zaman sa cike da kewar sa tana tuno yadda suke wuni tare tayi ta masa surutu yaƙi kula ta in ma ta dame shi ya haɗe rai shikenan ya kashe bakin maganar se ta shiga taitayin ta.


Tuni yadda ta rungume shi da yadda yayi reacting se kawai ta tuntsire da dariya tai tayin abin ta ita kaɗai kamar wadda ciwon hauka ya kama kafin tayi shiru ta cigaba da aikin ta tana sakin smiles kamar zararriya.


Hankali kwance ta cigaba da ayyukan ta tana me jin farin ciki cikin ranta.


A can ɓangaren Saraki shima aikin can ya cigaba da dubawa yana tabbatar da kasancewar komai a muhallin sa.


Kawu kuwa da baƙin ciki ya cika wa rai yana komawa gida number Alh Haladu ya kira telling him all that happened, shima sosai ran sa ya ɓaci ganin yadda yarinya ƙarama take neman wahalar dasu tun bare ma shigowar wannan ɗan iskan yaron cikin rayuwar ta kamar an ƙara mata ƙwarin gwiwa ne.


Nazari ya zauna yayi dan neman hanyar ɓullo musu tsawon lokaci kafin ya saki dariyar farin cikin samun wani solution ɗin, da sauri ya ɗau wayar sa ya shiga kiran Kawu da ringing ɗaya tayi ya ɗauka kamar dama jira yake.


"Kana ji ko Sama'ila, yanzu abinda za'a yi maza ka tafi Company ɗin furnitures, Zan turo mutane na da fake currency zasu siya set ɗin full three bedroom flat, amfanin da zuwan ka ze yi shine tabbatar da an karɓi cash ba transfer ba, na sani duk da haka ba durƙusar da gurin ze yi ba amma dai ai asara asara ce kuma ina da wanda zan tura wa kayan ya saye su daraja dan kayan gurin duk latest ne kuma ba ƴan ƙasar nan ba".


Shima Kawu washe baki yai duk da ba haka yaso ba, yaso ace wancan maƙudan kuɗaɗen kwangilar ne suka shigo account ɗin su sedai ba komai sa rage zafi.


Haka kuwa akayi, mutanen Alh Haladu suka yi shiga me kyau suka ɗau manyan motoci da kana gani kasan sun cika sun timbatsa, tarba me kyau manager ɗin wajen yayi musu aka gaggaisa kafin suka kawo batun siyan kayan da ya kawo su wanda a daidai lokacin Kawu ya ƙaraso.


Ciniki aka yi suka zaɓi kaya masu matuƙar tsada da kyau kafin akayi lissafi kuɗi ya tashi kusan miliyan 50 dan fa set ɗin 2 parlor and 3 bedrooms suka zaɓa, ana gama lissafi babban Alh cikin su yace yana zuwa ya koma mota ya ware adadin kafin ya ɗauko jakar da kuɗin ke ciki zuwa gasu Kawu, manager ya so yin magana sedai ganin yadda Kawu ya karɓe kuɗin da sauri yasa dole ya rufe bakin sa, buɗe jakar Kawu yayi gaban kowa ya fito da kuɗin aka ƙiƙƙirga aka tabbatar sun kai kafin aka shiga loda musu kayan cikin babbar motar da suka zo da ita.


Ana gamawa suka yi sallama da kowa suka ɗau hanya Kawu na ta washe baki haka shima manager yaji daɗin cinikin dan sun tabbatar musu da suna dawowa nan da two days akwai mansion ɗin su da zasu sawa furnitures Kuma a wajen su za'a siya komai.


Manager Kawu ya bawa kuɗin kan yaje yakai bank in ya tashi aiki shi ze wuce K&S couture, da haka yabar manager ya fita daga building ɗin yana dariya a ranshi ga kuma farin cikin kuɗin da zasu samu har miliyan 50, ko ba komai yasan ke tashi da twenty five millions.


**********


Ƙarfe biyar ya tashi daga aiki ya wuce wajen Kisnah tare da kiran ta ya shaida mata yana waje, ba ɓata lokaci ta fito suka wuce, sun kusa ƙara sawa take faɗa masa


"Yaya yau ina da zuwa cinema by 8pm, za'a haska Film ɗin jarumi sharukhan Chennai express".


Ɗan kallon ta yayi ta gefen ido yaga yadda take ta washe baki tsantsan farin ciki rubuce ka fuskar ta, be san ta wace hanya ze sami damar hana ta zuwa cinema ba ayanzu Amma he pray Allah ya kawo masa wata damar da ze yi hakan ko da nan gaba ne.


Gyaɗa mata kai yayi tunda bashi da wani option se hakan, gaban wani suya spot tace ya tsaya, atm ɗin ta ta miƙa masa tana lissafa masa abinda take so ya siyo ɗin, fita yayi bayan ya gama sauraren ta batare da ya karɓi atm ɗin ba, komai da ta lissafa se da ya siyo ya kawo mata sannan ya shiga motar ya cigaba da tuƙin sa, kaɗan kaɗan take kallon sa tana sakin murmushi, kusan so huɗu kenan indai zata siya abu se ya siya mata batare da ya bi takan kuɗin ta ba kuma tana jin daɗin hakan.


Suna ƙara sawa gida ta ɗauki ledar ta tare da yi masa godiya ta fice daga motar cike da farin ciki, bata ƙarasa flat ɗin ba suka haɗu da Awwaf, bata ko kalle shi ba kamar yadda ta ke masa tun da taga ya fara neman raina ta wai har ze kalle ta yace yana son ta, gaba tayi ta bar shi a wajen sedai kafin ta ƙara taku uku taji an janyo ta an rungume, fisge jikin ta tayi daga gare shi tare da ɗagowa cikin zafin rai da tsananin baƙin ciki da takaicin abinda yayi mata ta haske fuskar sada kyakkyawan marin da se da ya ɗauke masa jin sa na wasu sakanni.


Ƙara masa take ƙoƙarin yi se kuma ta fasa ta shiga nuna shi da yatsa ta fara masa masifa da cin mutuncin da duk wanda ke compound ɗin ke iya jiyo ta dan dama suna tsaye a compound ɗin ne ta hanyar shiga flat ɗin su


"Wane irin ɗan akuya ne kai da har rashin kunyar ka takai ka kai ƙazamin hannun ka jikina da wata manufa, nace waye kai da har kake da wannan guts ɗin ko an gaya maka ni ɗin sa'ar kace ko kuwa sake war da ka samu ce tasa har kake tunanin ni ɗin daidai nake da kai bari ka kawo min raini, to bari kaji wallahi wanda ya isa da kai ma be isa ba balle kuma wani banza kamar ka, an warning You for the first and last time, na rantse da Allah duk sanda ka kuma gwada irin haka se ranka ya ɓaci fiye da yadda kake zato, wannan ɗin ma Sa'a kaci na dubi matsayin mahaifiyar ka wajen ƙanin uba na if not wallahi matakin da zan ɗauka kan ka ko da kuɗi aka baka akace ka kuma trying this nonsense ba zaka kuma ba, pathetic peace of trash kawai, mtseww".


Ta ja tsaki kafin tayi gaba cikin ɓacin rai, Mommy dake tsaye tana kallon komai ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba sedai sanin ba abinda zata iya yi ko cewa yasa bata ƙarasa wajen ba ta juya ta shige falon ganin Kisnah tayo hanyar.


Ko kallon Mommyn bata yi ba ta nufi steps zata wuce ɗakin ta se kuma ta dawo ta tsaya gaban Mommyn tana jijjiga jiki tsabar bala'in da yake cinya dan ji take kamar ta koma in da ta bar banzan ta rufe shi da duka


"Haleema ki jawa ɗan ki kunne akaina, be san wace ce ni bane da alama shiyasa har yake ƙoƙarin kawo haukar iskancin sa kaina,to salin alin tun kafin in bayyanar masa a ainihin Kisnah ta ya fita a hanya ta in Kuma ba haka ba wallahi zan bi takan sa, har shi waye da ya isa ya kai ƙazamin hannun sa jikina, waye shi waye ya tsaya masa eye, ke kin San ni kin San abinda zan iya dan haka zaki iya gargaɗin sa, dan in ya kuma ban san iya abinda zan aikatawa banza ba".


Tana ƙare isar

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads