Header Ads
Showing 78001 words to 81000 words out of 104570 words

Chapter 27 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1443

Ads at the middle of Article

su da suka fita a cikin ta, jami'an bincike aka ɗauko suka shiga aikin su a daidai wajen da aka ga motar kafin daga baya suka sanar da cewa motar ta kama da wuta ne sanadin dukan tankar mai da ta tare hanya wanda ya dukan yasa murfin gidan man ɓalle wa abinda ya haddasa tashin wuta a motar kenan bayan ta hantsila har so biyar.


Al'amarin ya girgiza da yawa cikin jama'a dan zuwa wannan lokacin babu wani mazaunin garin manya da maƙoftaka da bai san da ɓatan the CEO na K &S companies ba, ranar kawu kam a asibiti ya kwana saboda yadda ya dinga sumewa ana yayyafi masa ruwa daga ƙarshe kuma ya dinga sambatu kamar wani zararre dole aka dangana dashi asibiti.


Duk yadda Mommy ke ƙin Kisnah seda ta ɗan yi sanyi sanadin mutuwar kafin kuma daga baya ta watsar ta shiga fantamawa cikin nera, su Maigado kuwa duniya sabuwa babanta ya zama me kuɗi.


Seda kawu yayi kwana uku a asibiti kafin aka sallamo shi lokacin ya dawo daidai sedai ba uhm balle uhm uhm sedai yayi ta kallon mutane, dole a ka rufe Companies ɗin K&S har zuwa lokacin da kawu ze dawo hayyacin sa ga kuma jimamin mutuwar mamallakiyar wajen da ma'aikatan ke ciki.


*******


Seda Saraki ya kwana shida be san wa ke kan sa ba kafin ya farfaɗo, zuwa lokacin kuwa tuni ciwukan ƙafar sa da yaji sanadin gudu cikin daji yana taka ƙayoyi sun fara warkewa, zuwa lokacin kuwa har Kisnah ta saba ganin su Bingel dan ta daina tsoron su sedai kuma bata kula su haka kuma bata iya cin abincin su sedai a bata fura da nono kullum........................✍️.


























©️ Ouummey 📚✍️.






















☑️Ote, Comment and share fisabilillah.
























Ouummey 32 (8/24/2022 10:07 PM)





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________














Page 3️⃣2️⃣






















_______________________📖 Zaune take a bakin bukkar ta kan wata tabarmar kaba tana bin Bingel da ke kwanto shanu da garken su ke can gefen bukkokin su da kallo, yadda take iya kwance su ta na shafa jikin su ba tare da tsoro ba ba kuma tare da su shanun sun wa Bingel ɗin komai ba ya matuƙar ƙayatar da ita, ba tun yau ba in taga Fulani na kora shanu abin ke burge ta da cika ta mamakin yadda suke iya controlling ɗin su, yanzu kuwa da take ganin hakan a gaban ta sosai se take jin kamar itama ta gwada sedai kuma tana tsoro.


Sanye take da kayan saƙi irin na Fulani, ƙaramar riga da bata sauka kan cikin su ba se zanin saƙi ɗaure a jikin ta shima be ko kai ƙaurin ta ba, gashin kanta ya wani barbaje kamar be taɓa ganin gyara ba, ƙafafun sanye da wani tsohon silifas da arɗo ya samo mata da ƙyar cikin garin su dan ta ƙi yadda ta saka irin takalman su.


Da sauri ta miƙe ganin Bingel na shirin ficewa da shanun bayan ta gama yi wa Nene magana cikin bahagon yaren su da ya kasance fulatanci sedai na su fulatancin ba irin na gamagarin Fulani bane, nasu na Fulani daji ya sha banban da ragowa.


"Ki tsaya ni, nima zanje".


Tsayawa Bingel tayi tana kallon Kisnah kafin ta juya ta kalli babar ta, gyaɗa mata kai Nene tayi alamun su je tare tun d tana so.


Ba yau ne ta fara fita kan ta ba ɗan kwali ko hula ba haka ba yau ta fara fita da kayan da basu rufe mata jiki ba shakka yasa ko kaɗan abin be dame ta ba ta fice a yadda take, ita matsalar ta ɗaya da kayan nauyi ga kuma zani da bata saba sawa ba da yake bata matsala wajen tafiya shiyasa ma in ta tashi take ɗaure shi can sama dan da ƙyar yake kai wa gwiwar ta, ɗaurin zanin kuwa dole ya bawa wanda yaga yadda ake yin sa dariya dan kawai cukurkuɗa kayan ta take ta cusa tayi gaba abinda, to ta ina zata fara wahalar da kanta, dole dai su ɗin zata saka tun da nata gaba ɗaya sun ɓaci da jini haka wasu guraren duk sun yayyage.


A hankali suke tafiya da Bingel yayinda shanun suke gaban su, kalle kalle take hannun ta riƙe da sandar da ta saka dole Bingel ta ɗauko mata itama wai zata taya ta kula da shanun, sosai garin ya burge ta ganin ko ina cike yake da korayen ciyayi, daga inda take ta hango kogin dake gaba da su sosai wanda da alama nan zasu tsaya da shanun, aikuwa suna kaiwa wajen taga duk shanun sun tsaya haka kuma sun fara ƴan ciye ciyen su, seda ta juya bayan ta sannan tasan ashe sun shiga daji sosai dan bata ma iya gane ta wace hanya suka kawo nan ɗin ba.


Ɗan kallon Bingel tayi kafin ta juya ta shiga bin wata hanya da taga wasu kyawawan tsuntsaye na tafiya a jere a jere a sama, sannu a sannu take bin tsuntsayen tana irga adadin su har tayi nisa bata ankara ba, seda ta gaji kafin kuma ta juyo dan komawa wajen Bingel sedai sam ta rasa ta hanyar da ta shiga wajen, hanyoyi ne da yawa gasu nan haka yasa ta daburce ta rasa ina zata bi, tsayawa tayi cikin tunanin wace hanya zata bi daga ƙarshe dai ta zaɓi bin hanyar dake right hand ɗin ta, without any second thought ta shiga tafiya tana me fatan Allah yasa hanyar daidai ta ɗauka, seda ta ɗan yi nisa kafin tafara jiyo muryoyin mutane da kuma ɗan kukan shanaye ƙasa ƙasa aikuwa cikin azama ta ƙara sauri wa tafiyar ta dan ta isko wajen dan tun da ta jiyo kukan shanu ta san ta dawo wajen Bingel.


Wasu Fulani samari ta gani kowanne riƙe da sanda a hannun sa suna tsaye suna magana da ƴar dariyar su suna nuna wani ɗan uwan su da ke duƙe ƙarƙashin wata sanuwa yana shan nonon ta, zaro ido Kisnah tayi ganin abinda yake yi kafin ta fara yamutsa fuska cikin ƙyanƙyami, wani irin amai ne ya tuƙo ta ganin yadda ruwan nonon ke biyo wa ta gefen bakin sa aikuwa nan ta duƙa ta shiga amaye ƴar guntuwar fura da nonon da yayi saura a cikin ta, kakarin aman ne yasa hankalin samarin ya dawo kanta gaba ɗaya har wanda ke ƙasan saniyar, sakin shanuwar yayi ya fito daga ƙarƙashin ta ya tsaya yana ƙarewa Kisnah ta kallo a lokaci ɗaya yana lashe ragowar nonon dake gefen bakin sa da harshen sa, da sauri ragowar samarin suka yi kan Kisnah sedai kafin su ƙarasa Bingel da ta biyo bayan ta neman ta ta riga su, ɗan duƙar da kai tayi ta gaida su kafin kuma ta zuba gwiwoyin ta a ƙasa ta gaida ɗaya saurayin dake tsaye yana kallon Kisnah.


Jinjina mata kan da yayi yasa da sauri ta koma wajen Kisnah ta bata ruwa ta wanke bakin ta ta miƙe ita kuma Bingel ta rufe aman da ƙasa kana ta ja hannun Kisnah dake tsaye tana hararar saurayin dan su tafi


"Wacece wannan?".


Tambayar da saurayin yayi mata kenan cikin Yaren su, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa ta shiga bashi amsa


"Baƙuwa ce da Arɗo ya tsinto cikin gona kwanakin baya".


"Shi arɗo ya manta da al'adar mu ne da kuma sharaɗin da wassai ya kafa mana a wannan garin da har ze karɓi baƙuncin budurwa, ko kuwa yana son jamana bala'i da masifa ne?".


Da sauri Bingel ta tare shi dan jin abinda yake faɗa


"Ai ba budurwa bace lamiɗo, matar aure ce da mijin ta aka tsince su, ya sami rauni ne sosai shiyasa baya iya fitowa".


Wani kallo saurayin da aka kira lamiɗo ya bi Kisnah dake tsaye tana kallon su cikin rashin fahimtar abinda suke cewa dan da Yaren su suke magana (kuyi hqr fa, banjin fillanci balle in yi muku😝).


"Ki cewa arɗo ya shigo fada ƙarfe biyar na yamma".


Da toh kawai Bingel ta amsa musu kafin ta ja hannun Kisnah suka wuce yayinda lamiɗo ya raka su da mayatatttun idanun sa.


Tafiya suke cikin dajin shiru ba me magana, to ita Kisnah ba gane Hausar su take ba haka kuma bata fahimtar Yaren su, har gwara su in tayu magana suna ganewa, tunani kawai Bingel ke yi na dalilin da ze sa lamiɗo yace arɗo yaje faɗa yau bayan yau ɗin ba ranar fadanci bace, to ko dai be yadda baƙuwa matar aure bace ba ko kuma meye, da wannan tunanin a ran Bingel suka ƙarasa wajen da tabar shanun ta ranar bata bari ta kai lokacin da take tashi kiwo ba ta kora shanun ta suka kama hanyar gida.


Suna zuwa gida bata kula Nenne dake mata barka da dawowa ba dan bata gane me tace ba duk inda cewa da Hausa ta faɗa se kawai ta ɗaga mata hannu tare da gyaɗa kai alamun amsawa ta wuce bukkar da aka ajiye Saraki a ciki.


Zaune ta sake shi kan gadon shi na kara da aka shimfaɗa wa wani tsumma, da sauri ta ƙara sa ta zauna gefen sa tare da kai hannu zata taɓa nashi me ciwo ya kautar da sauri yana hararar ta


"Ina kika shiga da se yanzu zaki shigo, wato a garin da baki san kowa ba ma bazaki daina yawo ba ko?".


Karyar da kai tayi cikin son Kare kanta


"Yaa ba fa yawo naje ba, I was so bored staying alone, su ba iya yarena sukai ba duk da suna ganewa amma ni ko fahimtar su bana yi sedai fa in ta zama ina bin su da kallo shiyasa yau na bi waccan yarinyar kiwo, kuma baka ga garin ba wallahi me kyau and their atmosphere is so wow banda Kuma beautiful look na garin".


Girgiza kan sa yayi kawai, ya sani dole da ma zata gaji tunda ko abokin fira bata da, haka kuma bata saba da zama waje ɗaya ba haka ma wani ƙalubalen ne shiyasa ma be yi mata wani faɗa sosai ba.


"And a haka kika fita ba".


Kallon kanta tayi kafin ta ɗan taɓe baki


"To su irin kayan su kenan, suma haka suke yawo kaga kuwa ba laifi na bane, ni bacci na zo yi dan bana iya bacci a wancan ɗakin ina jin tsoro, can't wait ka samu sauƙi mu bar dajin nan if not Allah mutuwa zan yi, bana iya cin komai se fura da nono fa yaa, kuma basa sa sugar se zuma ni kuma bana so"


Ta ƙarashe tana kaiwa kwance gefen sa, kallon ta kawai yayi bece komai ba, to me zece mata, kar tayi bacci? Bayan yasan a halin da take tana buƙatar baccin sosai dan gudun abinda ka iya faruwa da ita.


Ya ji daɗi da bata kasance mutum me saka abu a rai ba dan da wata ce ya tabbatar har yanzu ba zata saki ranta ba saboda abinda su kawu suka aikata kuma hakan ze iya sawa ta kamu da ciwon depression Wanda ita ma Kisnahn ya San tana fama dashi ko da ba yawa sedai dole ta damu, her only family turns out to be her worst enemy, abin is not easy at all.


Kamar yadda tace kuwa bacci ta shiga yi abin sa yayinda yake zaune Yana tasbihi a ransa, a rana ɗaya fa Allah ya canja musu yanayin rayuwa, yanzu dai dubi da rich, beautiful, sexy and fashionable Kisnah kwance akan gadon kara rabin jikin ta kwance kan tabarmar kaba, wa ce taɓa yadda 8 days back in aka ce masa zata yi rayuwa a irin wannan wajen, waze yarda in akace masa zata saka irin wannan kayan, waze yarda in akace masa her long black silky hair ze yi wannan busu busun ba gyara? Sure life is unpredictable and Allah is the all doer.


Rufe nasa idon yayi lokacin da tunanin rayuwar sa ta baya ta faɗo masa, ba iya Kisnah ba shikansa be taɓa kawo rayuwa a irin wannan wajen ba balle har da karaya a left hand da kuwa gocewar ƙashi a ƙafar dama banda ƙananun ciwuka duk da alhamdulillah daga gocewar ƙashin har ciwukan sun warke se karayar hannun da ake fata itama a sami dacewa.


Ƙarfe huɗu arɗo ya shigo gida kafaɗar sa saɓe da fatanya hannun sa riƙe da wani duƙunƙunen nan buhu, da sauri Nene dake aikin cura fura ta ajiye ta ƙara sa ga mijin ta ta karɓi buhun hannun sa tana masa sannu da zuwa.


Be amsa ta ba seda ya kai zaune bakin bukkar sa kafin ya amsa yana mata sannu da nata aikin, ruwa Bingel ta kawo wa mahaifin ta tare da rufaffiyar ƙwarya da ke cike da damammiyar fura da aka wadata da zuma ta ajiye masa, albarka ya sa mata kafin ya fara zubawa cikin sa furar.


Seda ya shanye tas sannan ya miƙe ya ɗau gwangwanayen da suke alwala da zagaya wa dasu ya wuce can bayan bukkokin su da suka ɗan rufa matsayin matsuguni ya rage marar sa kafin ya dawo ya shiga alwala, seda ya gama ze fita Bingel ta tare shi da saƙon lamiɗo


"Arɗo, lamiɗo yace kaje faɗa da yammaci".


Tsayawa arɗo yayi cikin fargaban dalilin da ze sa ace yaje fada bayan yau ba ranar fadanci bace, juyowa yayi ya dubi ƴar sa sosai kafin ya tambaye ta me ya faru da ake neman sa bayan yasan be aikata kowane laifi ba, take Bingel ta sanar dashi duk abinda ya faru lokacin da suka fita kiwo da Kisnah, shiru arɗo yayi yana tunanin me kiran ke nufi, shi dai yasan yarinyar matar aure ce duk da be tambaye ta ba ko mijin se dai a yanayin da ya tsince su shikam ya gane ma'aurata ne amma kuma tabbas lamiɗo da baffa arɗo kallo ɗaya suka yi wa mace suke gane budurwa ce ko matar aure, sosai dai kan sa ya ɗaure ya kasa fahimta hakan yasa ya fice da niyyar in yayi Sallah ya wuce fada dan jin dalilin kiran.


Lamiɗo ɗa ne ga Sarkin ƙauyen Banda (ƙauyen su Bingel) da ake kira baffa arɗo, baffa arɗo Dattijo ne ko ma ace tsoho dan a ƙalla yayi shekara saba'in da wasu ƴan kai, duk cikin ƴaƴan sa ba wanda ya gado shi kwabo da kwabo a kamanni kamar lamiɗo, hakan yasa ya ɗau duk wata soyayya da kulawa ya aza kan lamiɗo da ya kasance auta.


Shekaru Ashirin baya aka taɓa samun wani irin annoba da basu taɓa ganin kamar ta ba cikin ƙauyen, gaba ɗaya amfanin gona ya lalace, shanu suka murmutu, ƙoramai da koguna suka bubbushe, tashin hankali ya samu mazauni cikin rayuwar su aka shiga fafutukar neman sauƙi, cikin haka ne suka sami wani malami wai shi wassai da ya buga musu ƙasa sannan ya sanar da su dalilin wannan annoba


"Kun yi baƙuwar budurwa garin nan shekara ɗaya baya wanda itace musabbabin wannan annoba dan yarinyar mayyace haka kuma baƙaƙen rauhanan jikin ta sun nemi cutar da rauhanan da suka kafa wannan gari, sanadin wannan faɗa tsakanin su ne ya jawo wannan annoba sedai ina muku albishir da rauhanan mu sun yi nasara kan nata dan yanzu haka ta mutu, sedai akwai sharaɗi, dole duk baƙuwar da zaku yi takasance matar aure, in har kuma budurwa ta shigo dole a mallaka wa lamiɗo ita na tsawon kwana bakwai dan rauhanai sun zaɓe shi matsayin sarkin wannan gari bayan mahaifinsa ya shuɗe, haka kuma zan bashi maganin da yana ganin budurwa ze gane ta da kansa shida baffa arɗo dan gudun yaudara irin ta mutane, dan za'a iya samun wanda ze sauki budurwa kuma yace matar aure ce, hakka ba sabon halayya bace ta ɗan Adam, da ita aka halicce shi".


A lokacin ba wanda ya ja da hakan tunda dai ba wai ƴaƴan su mata akace su dinga bayar wa ba haka kuma tun daga lokacin ma babu wanda ya kuma yadda ya sauki baƙuwar budurwa se sau biyu da hakan ya faru kuma duk se da aka aiwatar da sharaɗin boka wassai aka kaiwa lamiɗo su turaka tsawon sati ɗaya kafin ya sallame su......................✍️.








Ƙaƙa ƙara ƙaƙa!!!!


Wata sabuwa in ji ɗan caca,
ga Kisnah ga lamiɗo ga Kuma Saraki,


shin me kuke tunani bayan an tabbatar wa da lamiɗo cewa Kisnah budurwa ce?


Shin kuna tunanin Saraki ze Bari a mallakawa lamiɗo Kisnah ne na tsawon kwanaki bakwai?


Shin kuna tunanin Kisnah da Saraki zasu bar ƙauyen Banda ne ko kuwa?.


Ni dai nasan...............ban san komai ba😝😂.












©️ Ouummey 📚✍️.










☑️Ote, Comment and share fisabilillah.




























Ouummey 33 (8/24/2022 10:08 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________














Page 3️⃣3️⃣












*Wannan PAGE ɗin sadaukarwa ne gare ku my best commenters*




*Itx_ammin_halimatou*
*Maman nabeehat*
*Maman Mu'awiyah*
*Mom Islam*
*Mom misra*.
*Amina tijjaney*
Zainab Habib*
*زينب*
*Ihsana*
*Real bloom*
*Da ma duk wanda ban ambata ba ina godiya da ƙauna, saraki da Kisnah sunce a faɗa muku You Are really amazing and loving*




























_________________________📖 "Mun sami labarin ka sauke budurwa a gidan ka arɗo, ko za mu iya sanin dalilin hakan?".


Da sauri arɗo ya gyara zaman sa yana share zufa da hannun rigar jikin sa da taci datti kamar ba gobe


"Allah yai maka tsawan kwana na tsinci wasu matasa biyu mace da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads