Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 104570 words

Chapter 4 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1423

Ads at the middle of Article

kuma adali, a iya sanin da nayi masa bashi da wata matsala, zaka ji daɗin zama dashi gwargwado, duk da ban daɗe tare da kai ba zan bada shaidar kai mutumin kirki ne, ina fatan tafiya tayi nisa tsakanin ku da me gida insha Allah zakuji daɗin juna, zaka fara aiki dasu yau, Allah ya bada Sa'a".


Motsa bakin sa yayi alamar Ameen, hannu yasa ya bubbuga kafaɗar Idris tare da yi masa murmushi alamar godiya kafin ya juya ya koma cikin shagon, juya wa Idris yayi ya hau machine ɗin sa yana girgiza kai, daga shekaranjiya zuwa yau ya gama fahimtar magana tana bawa Saraki wahala, sedai ya fahimci shi ɗin mutum ne me kirki da sanin ya kamata in an fahimce shi, tashin machine ɗin yayi ya wuce.


Zama Saraki yayi kan wani bench dake baki bakin shagon har zuwa la'asar da Alh Musa me shagon ya fito ya ganshi zaune, mamaki ne ya kamashi dan a tunanin sa ya shiga cikin ragowar yaran shagon suna hidimar su.
Sunkuyar da kai yayi ya gaishe da Alhajin ya amsa masa tareda cewa ya tashi su wuce masallaci.


Alwala yayi suka tafi masallacin, tambayoyi yake masa suna tafiya inda yake bashi amsa iya abinda ya tambaya har suka ƙarasa, sallah suka gabatar suka dawo shago, tara yaran shagon Alh Musa yayi ya gabatar musu da Saraki matsayin ɗaya daga cikin su tareda neman haɗin kansu.
Amsawa sukai yayinda suka dinga bawa Saraki hannu suna gaisawa ɗaya bayan ɗaya tareda sanar dashi sunan su, murmushi kawai yake musu har lokacin tashi yayi, Naira ɗari uku Alh Musa ya bashi as sallamar shi, karɓa yayi yana godiya cikin yanayin maganar sa can ƙasa.


Napep ya tare ya koma shagon sa, wanka yayi canja kaya ya ɗaura alwala sannan ya kulle shagon ya taka da ƙafa zuwa masallacin da ke gaba da su kaɗan.


Azkhar ya zauna ya cigaba da yi har lokacin sallah ya cika aka kira sallah ya bi jam'i, ko da aka idar be tafi ba nan ya zauna ya cigaba da karatun Alqur'ani har aka kira isha itama yayi cikin jam'i kafin ya fito.


Cikin tafiyar sa ta nutsuwa haɗi da ƙasaita ya koma ɗakin sa, indomie ya dafa saboda tafi sauri dan yunwa yake ji, wunin yau be ci komai ba tun tea ɗin da ya karya dashi.


Ko da ya gama ci tashi yayi ya fita ya rufe ɗakin ya fita strolling dan ya riga ya Saba duk dare se ya fita yayi exercise haka ma da safe, a hankali yake bin gefe gefen titi yayinda ababen hawa ke ta tsuga gudun sa akan titi, be yi nisa sosai ba ya dawo dan ba sanin garin yayi sosai ba kar yaje ya shiga inda baze fito ba.


Addu'ar bacci yayi bayan ya rage kayan jikin sa dan baya bacci da kaya ko wane iri ne, boxers kawai ya bari ya ja blanket ya rufe rabin jikin sa bayan ya ƙure gudun fanka kasancewar sa me matuƙar san sanyi.


****************


Sanye da dogon jeans ya bi fatar jikin ta ya kwanta ta sauko, rigar jikin ta buɗaɗɗiya ce da ta sauko har kan cinyar ta sedai ta ɗaure ta daga ƙasan ƙirjin ta da zaren da aka tanada, ƙafarta sanye da hill shoe kamar kullum hannunta ɗauke da wayoyinta biyu se makullin motar ta.


Abinci Maigado ke ci a dining tareda Awwaf, tana tawowa Maigado ta ja wani dogon tsaki tana hararar bayan ta wanda tana jinta amma tai mata banza, har takai ƙofar fita falon ta dawo zuwa kan dining taja kujerar gefen me gado ta zauna.


Ruwan Lipton dake cikin flask ta tsiyaya a cup ɗin gaban ta, ɗauka tayi kamar zata sha ta kai kusa da bakin ta kawai ta sake shi daidai ƙafar Maigadon, wani irin ihu Maigado ta tsala na tsananin azaba yayinda itama Kisnah ta taya ta, ihu take tun ƙarfin ta tana tsalle kai kace ita ruwan ya zubar wa.


Da gudu Mommy ta baro kujerar ta ta jawo Maigado jikin ta, har lokacin Kisnah bata bar ihu da tsalle ba daidai lokacin Kawu ya fito, ƙara ɓare baki tayi tana kallon Kawu tana yarfe hannu


"Wayyoooo Abbu na Nana ta, wayyo ƙafa ta zata cire, wayyoooo Allah Sena Rama". Haka take ta ihu tana faɗa kamar gaske.


Da sauri Kawu ya ƙaraso ya tsugunna gaban ta,


"Menene ya sameki daughter, faɗa min me ya faru?


"Ba Maigado bace, daga kawai na zo zan fita shine tace min wai karuwa nikuma nace mata ai a wajen uwar ta na koya shine fa kawai ta ɗauko hot tea ta watsa min a ƙafa, da suka ga zaka fito se kawai ta zubawa ƙafar ta kaɗan wai dan kar ka yarda dani"


Wani irin zabura Kawu yayi ya juyo wajen su Maigado da suka saki baki suna kallon Kisnah dake matsar ido tana girba ƙarya.


Wani irin zazzafan mari kawu ya sauke wa Maigado, ai tuni ta manta da ciwon ƙafarta ta shige bayan Mommy tana ihu, binta kawu yake zai dake ta tana ƙara laɓewa bayan Mommy, garin Haka Mommy ta samu rabon mari, anje Marin Maigado ta tare aikuwa ya sauka a fuskar ta.


Wata irin dariya ce ke cin Kisnah amma ta daure ta haɗiye, seda ta tabbatar ƙafar Maigado tayi tsami saboda takata da take yi haka ma shikansa kawun ya gaji sannan ta kwaɓe fuska tace


"Kawu ka ƙyale ta kaje wajen aikin ka na haƙura amma gaskiya in ta ƙara sedai ta bar min gidana ita da uwar ta dan ita take zugata, rannan naji tana cewa wai a zuba min maganin ɓera a abinci".


Zaro ido Kawu yayi cikin tashin hankali zuciyar sa na bugawa, amma wallahi Haleema ba ƙaramar mara mutuncin mata ba ce, yanzu so take a kashe yarinyar tun kafin burin sa ya cika aikuwa zata ga iskanci


"Ai dama nasan duk abinda ke faruwa ita take shirya shi, saboda tsabar baki da mutunci kike cewa a kashe ƴar ɗan uwa na da bani da kamar sa ko, to kije gidanku se na neme ki".


Zaro ido Mommy tayi
"Yanzu alaji ni zaka cewa in tafi gidan mu, saboda kawai wannan shegiyar yarinyar ta ƙulla min sharri se ka yarda, ai shikenan da ƙafar ka zaka zo nema na".


"Kaji ko Kawu dama rannan take faɗawa ƙawar ta wai ai ko ka koreta bata yin sati biyu kake biyo ta saboda baza ka iya rayuwa ba se da ita". Cewar Kisnah tana kyaɓe baki irin wai mamakin nan


Aikuwa Kawu ya shaƙa, watau har ƙawayen ta take barbaɗawa baze iya rayuwa ba ita ba, to kuwa ze bata mamaki


"Kar ki bari in dawo in same ki, in ba Haka ba wallahi se na baki mamaki kuma zaki ga abinda ze biyo baya ne".


Yana faɗar haka ya fice fuuuu cikin fushi, yana fita Kisnah ta tashi daga zaunen da take tareda karkaɓe kayan ta, p-cap ɗin kanta ta gyarawa zama, hannu ta saka a aljihun ta ta ciro cingum ta ɓare ta jefa a bakin ta.


Cikin taku ɗai ɗai ta ƙarasa gaban Mommy da ta daskare tsabar takaici da baƙin cikin korar ta da Kawu yayi, ƙas ƙas haka Kisnah ta tauna cingum ɗin bakin ta tareda yin ƙwai ta hurawa Mommy.


"To ya Kika gani Halima? Ai dama se da na faɗa miki in har baki takawa ƴarki birki ba wataran zata janyo miki abin da yafi ƙarfin ki, to kaɗan kuka gani".


Juyawa tayi ta nufi ƙofa cikin takunta na cikakkun ƴan mata masu aji da ji da kan su ta fice.


Yau ma kamar kullum cikin salon tuƙin ta ta figi motar a tsiya ce ta hau kan titi, wani irin gudu take kamar bakowa a titin se ita kaɗai, jikake fit fit ta wuce.


Zagi da tsinuwa kam ta ɗibe su kamar yadda ta saba saidai bata ma san suna yi ba dan earpiece ne a kunnen ta.


Wani irin horn take zubawa a kan titin tun kafin ta ƙaraso gate ɗin makarantar, da hanzari security biyu dake zaune suka tashi suka buɗe gate ɗin dan tuni sun gane ta, in har suka ji wannan horn ɗin to ita take tuƙa kanta kuma bata jira dan ta taɓa yin gaba da gate ɗin akai pressing charges a kanta ta biya dan ba za'a iya korar ta ba saboda kuɗin da take dashi.


Da gigitaccen gudun ta ta shige makarantar, ɗaliban da ke kan hanya kowa matsawa yake yana bata hanya dan gudun afkuwar matsala, parking tayi a parking space ɗin malamai dake gefen department ɗin su ta kashe motar sannan ta zare earpiece ɗin.


Fitowa tayi daga motar tana gyara zaman Black shade ɗin da ta maƙalawa fuskar ta, Hameedah ce ta ƙaraso wajen ta, rungumar juna sukayi sannan Kisnah ta miƙa mata mukullin motar hannun ta, sororo Hameedah tayi cikin takaicin yadda Kisnah take mai da su kamar wasu ƴan aiki ita da su Surry saboda su ta raina dan bata yiwa Meenah haka.


Haka badan ranta ya so ba se dan ba yadda ta iya ta buɗe motar ta kwaso mata litattafan ta kana ta rufe mata ƙofar sannan ta bi ta cikin hall.


Tsayawa Kisnah tayi tana bin hall ɗin da kallo ganin yadda ya cika har bata hango wajen zama, rarraba idanu ta cigaba da yi har ta hango wani space na mutum biyu sedai ba kowa a kai, cikin tafiyar ta na cat walk ta ke takawa tana ratsa jama'a har ta ƙarasa seat ɗin ta zauna, da sauri wani namiji da ke kan kujerar ya hayayyaƙo yana faɗa mata the seat is reserved.


Ko kallo be ishe ta ba se ma Instagram da ta shiga tana posting hoton da tayi yau da safe tana zaune kan gado sanye da ɗaya daga cikin kayan training ɗinta kafin ta fita jogging.


Ran saurayin ne ya ɓaci ganin ta ƙi ma kallon sa bare ta nuna ta san yana magana, kun san samarin jami'a da ɗaukar kai ga zuciya tuni yasa hannu yai watsi da litattafan da Hameedah ta ajiye mata kafin ta koma wajen zamanta.


Da wani irin kallo Kisnah ta bi litattafan da suka watse a ƙasa kafin ta kalli Hameedah da bata ƙarasa seat ɗin ta ba, wani ɗan fito tayi nan da nan Hameedah ta juyo dan hakan inkiyar su ne wa junan su, takowa Hameedah tayi ta dawo wajen Kisnah.


Miƙewa tsaye Kisnahn tayi daga seat ɗin kamar zata fita sedai kafin saurayin ya ankare yaji saukar mari mafi zafin azaba daya taɓa ji a rayuwar sa dan Kisnah akwai bala'in zafin hannu.


Cikin gigicewa saurayin ya fidda hannu da sunan ze rama sedai ko kafin hakan tuni Hameedah ta tare hannun tana watsa masa wani matsiyacin kallo kafin ta tsartar da miyau a gefe alamun dai an raina ka ɗin nan.


Sosai hall ɗin ya ɗau shiru kamar ba kowa, da yawa matan ajin so suke yau ayi musu maganin Kisnah dan majority sun tsane ta saboda yadda take da masoya kama daga malamai zuwa ɗalibai.


Cikin zafin rai saurayin ya miƙe ya fara zagin Kisnah


"Shegiya karuwa asararriya mara tarbiyya, an ji kunya dai wallahi wai nan sunan Musulma ce amma kusufa kusu far karuwanci ta haddace shi, nasan badan komai kika zauna kusa dani ba se dan kinga sabon jini bari ki je ko a sosa miki inda ke miki ƙaiƙayi sedai ki sani ƙwalelenki ƴar karuwai kawai dan da alama gado kikayi wajen gyatumi ko gyatuma".


Take hall ɗin ya ɗau sowar ihu dan an daɗe ba'a sami me guts ɗin da ya zagi Kisnah kamar haka ba, tun lokacin suna level 1, korar da aka yiwa ɗalibin bayan ƴan sanda sun hukunta shi yasa ba wanda ya sake attempting sedai a bayan idonta.


Murmushi me ƙayatar wa ta saki kafin cikin daddaɗar Muryar ta ta fara magana


"Silent everyone, Kamar dai yadda wancan jaririn ya faɗa Yes ni karuwa ce sedai na fi ƙarfin jariran da kaciyar su bata warke ba, wannan gurin se manya kamar gyatumin sa though yayi min ƙazanta da yawa, by the way a Samo projector se in haska muku yadda muke karuwanci da gyatumin sa".
Ihu gurin ya sake ɗauka har ma fiye da da kafin ta sake ɗaga hannu akai shiru


"We have 37 minutes free, I think that would be enough for you to have fun".


Kafin kace me tantiran mate ɗin su sun tafi samo projector, yayinda ragowar ke ihun zasu ga eya ne..........................✍️.


🤣😂😂 Shagali 💃, amma gaskiya Kisnah duniya ce, cikin sauƙi tayi maganin Mommy da Maigado 🤣 su Mommy za'a tafi hutu😜 team Mommy sry for u guys🤣😉.


To fa😱yau zamu sha kallo, Bari in gyara zama, kai mhiz jidderh akwai son gulma har dasu leƙe, gaskiya ku tafi department ɗin ku😂, ke meenat Ni fa na tsani sa ido meye na lekowa ta window 🙄, kai bari dai in gyara wayata in Yi wa masu karatu vedio musamman shamsiyya aradu nasan in ban ajiye mata ba seta min dundu biyu 😜😜😝.


©️ Ouummey 📚✍️




*Vote, comment and share fisabilillah*






































Ouummey 06 (8/1/2022 3:22 PM)





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________




















Page 6️⃣










___________________📖 Cikin ƙanƙanin lokaci se ga projector an kawo, socket suka kunna tareda jona shi, kujera Surayya da ƙarasowar ta kenan ta sami labari ta miƙowa Kisnah, zama tayi tareda harɗe ƙafafun ta ɗaya kan ɗaya kana ta tura p-cap ɗin ta baya, hakan yasa gaban goshin ta dake cike da baƙin sassalkan gashi kwantacce ya bayyana.


Daga zaunen da take a tsakiyar class tayi connecting wayar ta da projector ɗin, watsapp ɗin ta ta shiga da sunan mutane da komai na ciki ke bayyana kan projector, sannu a hankali har ta ƙarasa kan wani suna da tayi saving da *TRASH* ta shiga cikin messages ɗin sa.


Can farkon chat ɗin ta koma sannan ta fara scrolling a hankali yadda kowa ze iya karantawa bayan ta ƙara wa text ɗin girma, kan kace me hall ɗin ya kacame da ihun irin kalaman batsan da baban yaron me suna Ishaq yake turowa, tsaff suka gama karance text ɗin kafin ta juya zuwa inda Ishaq ke tsaye, miƙewa tayi hakan yasa kowa yayi shiru


"Kana da tantama akan ba mahaifin ka bane a nuna maka shaida?".


Ta tambaya cikin sigar rainin wayon nan, sunkuyar da kai Ishaq yayi yana zubar da hawayen kunya da nadamar abinda yayi gashi yana zaman zaman sa cikin mutuntaka ya zubar wa da kansa mutunci.


Ƙasaitaccen murmushi Kisnah ta sake kafin ta juya ga ƴan class


"Oops yaron ya bani tausayi, kun san mu karuwai akwai imani i can't display his father's nude, se dai ya kamata kafin ka san yadda zaka zagi wani ka san su waye iyaye da relatives ɗin ka, har ila yau You all have to know and believe *KISNAH IS THE REAL QUEEN, AM BORN TO RULE* ".


Tana faɗar hakan ta juya wajen zaman da tun farko ya janyo case ɗin, hayaniya ce ta cigaba da tashi a hall ɗin, da yawa sun sha jinin jikin su da Kisnah ɗin dan yau kam sun ƙara tabbatar da ba ƙaramar hatsabibiya bace, ranar dai Ishaq se guduwa yayi dan be dawo seat ɗin da yake faɗa akai ba.


Shigowar lecturern su ya saka ta zare earpiece ɗin da ta maƙala tun bayan zaman da tayi wanda Meenah dake gefen ta ce ta taɓo ta, duk iskancin Kisnah tana da matuƙar san karatu, babban burin ta a wannan duniyar ta zama *LAWYER* dan har rehearsal ɗin yadda sunan ta ze koma *BARRISTER KISNAH* take yi shiyasa bata wasa da karatu haka bata taɓa missing school in har ba Rashin lafiya ba.


Sosai ta maida hankalin ta kan malamin da ke ta bayani tana jotting wasu tana understanding wasu, wata irin ƙwaƙwalwa Allah ya bata me saurin fahimta da ɗaukar abu, wuyar ta ta saka kanta tofa duk wahalar karatu a wajen Kisnah se ya koma bakomai ba shi yasa dole su Surayya ke haƙurin zama da ita dan suna amfana sosai ta ɓangaren karatu haka kuma ba dan ita ba da yawanci karatun ma ba yi zasuyi ba dan baya gaban su.


Ko da malamin ya fita tattare littattafan tayi waje ɗaya Meenah dake gefen ta ta ɗauka haɗe da nata, fita sukayi a hall ɗin dan basu da wata lecture ɗin se after 2 hours, library ta wuce suka bi bayan ta, haushi sosai ya kama Surry da Hameedah dan su in akwai abinda suka tsana be wuce wannan shiga Library ɗin ba se dai kuma ba yadda zasu yi dan indai zata shiga dolen su su bita.


Haushin Kisnah Hameedah ke ji ganin yadda ta zama boss ɗin su, komai se abinda tace zasu yi, in partying ɗin ne, in clubbing ɗin ne, karatun ne ko zaman gida du se abinda tace.


Haka ba yadda suka iya suka shiga, circulation suka samu suka zauna kowacce ta ciro book ɗin da zata karanta suka mai da hankali kai.


_____________


*MASARAUTA*


A can masarautar DAULATUL NOOR kuwa al'amura na tafiya yadda ya kamata a ɓangaren sha'anin sarauta, sedai a ɓangaren Haleematus~Sadiya kawai dai tana rayuwa ne blankly, Sam babu ɗigon farin ciki a rayuwar ta se ɗumbin baƙin ciki da damuwa da take ɓoyewa a ranta saboda wasu rayuka da ba zata so dakushe rayuwar su ba.


Kamar yau da take zaune cikin hamshaƙin falon ta da yaji kayan alatun sarauta, duk inda ake neman haɗuwa da tsari na ƙyale ƙyalen gidan sarauta to fa tabbas akwai shi a wannan falo.


Kishingiɗe take akan kilisar ta idanun ta lumshe tayi nisan kiwo cikin duniyar tunani da ta zame mata abokiyar rayuwa tun bayan barin hasken ranta kuma gudan jinin ta YARIMA SARAKI ƙasar, a kullum

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads