Showing 45001 words to 48000 words out of 104570 words
Chapter 16 - SARAKI (The Accused Prince).txt
a office ne ta turo gabam sa kafin ta zagaya ta gefen sa ta shiga yi masa bayani tana daddanna keyboard ɗin.
Kwanan nan aka nemi wasu kaya aka rasa a mall ɗin kuma an rasa ta ina suka bi suka sulale daga cikin mall ɗin, kaya ne bana ƙananan kuɗi ba dan kusan rabin ribar da aka samu a wannan shekarar cikin mall ɗin suka sa suka yi order sedai kwana uku da zuwan kayan aka nemi kusan rabin su aka rasa, abinda ya jawo babbar matsala kenan aka shiga binciken ina kayan suka yi sedai har yau an kasa ganowa shiyasa tana gama exam ta maida hankalin ta kan mall ɗin ɗan yana cikin best kadarorin ta da take matuƙar so dan purposely dama ita aka buɗe wa tun iyayen ta na da rai.
Yanzu ma bayanin duk ma'aikatan dake cikin mall ɗin take masa da post ɗin kowanne da kuma albashin da yake ɗauka a duk wata, ɗaya bayan ɗaya ya fara scrolling through list ɗin har ya gama kafin ya ajiye mouse ɗin ya fuskance ga sosai.
"A yadda na bi bayanan duk ma'aikatan ban ga komai ba sedai akwai strategy da zamu bi, for now ki sa a tara su gaba ɗaya a ɗakin meeting in kuna dashi in babu kuma su taru a tsakiyar mall ɗin bayan an sallami kowane customer".
Gyaɗa kanta tayi da sauri kafin ta ƙarara wajen landline ɗin dake kan table ɗin ta ta daddanna wasu numbers ta kara a kunne, bata tsaya amsa sallamar da yake mata ba bare gaisuwar da ta biyo baya
"Ka sa a sallami kowane customer da yake cikin mall ɗin nan da mintina goma ya zama ba kowa a ciki sannan ka sanar da kowane ma'aikaci ya hallara a meeting hall in next 30 mins".
Ajiye wayar tayi ta juyo gare shi
"Na sanar dasu Ya, what next?".
"In suka taru Zamuyi addressing issue ɗin tare da yin barazana sosai kafin mu examining facial expressions ɗin su, insha Allah zamu iya gano criminals ɗin ta haka".
Faffaɗan murmushi ne ya wanzu saman fuskar ta kafin ta sara masa gani da ƙamewa tana faɗin
"Salute you sir".
Girgiza kansa kawai yayi dan yanzu ya fara sanin halin ta na surutu da barkwanci dan har ya dena damuwa, ƙarkari ya bata amsar abinda yaga ze iya Wanda baze iya ba kuma ya kalle ta kawai..........................✍️.
©️ Ouummey 📚✍️.
☑️Ote, comment and share fisabilillah.
Ouummey 19 (8/10/2022 10:16 PM )
💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠
Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey
*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*
______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________________
Page 1️⃣9️⃣
_____________________📖 Kamar yadda ta bada umarni haka akayi, 30 mins after manager ya kirata yana tabbatar mata da duk ma'aikatan na hall kamar yadda tace ayi, amsa masa tayi da gata nan zuwa ta ajiye wayar tana kallon Saraki
"Yaa suna wajen mu kaɗai ake kira".
Nodding head ɗin sa yayi yana miƙewa tare da gyara rigar yadin kuftar jikin sa da akayi wa plain ɗin ki sedai ba ƙaramin amsar shi yayi ba kamar a sace a gudu, yana cikin set goma da ya ɗin ka cikin kuɗin albashin sa na farko da ya ɗauka two weeks back, yadi kala huɗu se shadda huɗu boyle biyu.
Clutch ɗin dake haɗe da rigar jikin ta ta ɗauka kan table ɗin da ta ajiye ta farkon shigowar su ta bi bayan sa ɗan tuni ya fita. Bakin ƙofar ta tadda shi dan haka itama ta tsaya sedai kafin ta kai ga tambayar me yasa ya tsaya ya riga ta nuna hanya tare da faɗin
"You lead me".
Bata yi musu ba tayi gaba ya biyo ta a baya dan ta san be san wajen ba to mutumin da ya fara shigowa mall ɗin yau taya de san ɗakin meeting ɗin su.
Ƙaton ɗaki ne da kana shigar da zaka sheda na meeting ɗin ne saboda ƙaton table ɗin da ya zage yi ɗakin duk girman sa kuwa se kujeru dake jikin sa wanda a yanzu ma'aikatan wajen ke zaune a kai se kujera ɗaya da ba kowa dake gefen dama ga kujera guda ɗaya tal dake can gaba tana facing table ɗin wadda itace akayi purposely sabida ita.
Miƙewa gaba ɗaya ma'aikatan suka yi cikin nuna girmamawa, kujerar da manager ke kai wadda ke gefen daman ta ya miƙe da sauri ya koma cikin ma'aikatan dan akwai two vacant seats, tun kafin ma ya nemi wajen zama ta ƙarasa da sauri ta zauna kan kujerar da manager ya tashi kafin cikin muryar ban girma ta nuna masa kujerar da ita tayi supposing ta zauna.
"Please have your seat sir".
Shiru yayi cikin Binta da kallon bangane me kike nufi ba yana sake haɗe rai, haɗe hannayen ta tayi alamun Please tana sake roƙon sa da ido, harara ta yayi kafin ya maida duban sa kan ma'aikatan da wasu suka sunkuyar da kai yayinda wasu suke bin su da ido kamar television mamaki rubuce ƙuru ƙuru kan fuskar su.
Ɗan gyaran murya yayi kafin ya zauna yana fuskantar su kafin a hankali ya shiga bin su da ido cikin son ƙayyade adadin su wanda be wani sha wahala ba ya ƙirge su, su 35 ne ma'aikatan ciki dan uniform ɗin su ya banbanta da na securities da suke 10.
Cikin sassanyan Muryar sa ya soma da gaishe su gaba ɗaya
Good afternoon all".
Ɗan shiru yayi ya basu damar amsawa kafin ya cigaba
"Mun taru a nan bisa dalilin da ba na haufin kowa ya sani, wanda be sani ba ma ina farin cikin sanar dashi a yanzu cewa mun taru a nan ne kan dalilin ɓatan kaya da muka fuskanta sati da ƴan kwanaki da suka wuce, ba wai mun tara ku a nan dan binciken wanda ya ɗau kayan bane, a'a mun tara ku a nan ne dan sanar da ku mun yi nasarar gano wanda yayi hanyar ɓatan kayan wanda alhamdulillah muna kan tunanin tura case ɗin court........". Ya ɗan dakata cikin bin fuskar kowanne da kallo har idanun sa yayi nasarar sauka a inda ya dace dan yayinda ragowar kowa ke garin ciki da godewa Allah kan nasarar da aka samu me aikin yaƙe kawai yake yi haka kuma ga duk wanda yasan malamar aikin lawyer kallo ɗaya ce masa ya dasa alamar tambaya akan sa da kuma look ɗin da idon sa ke fitar wa.
"Sedai kafin mu miƙa me wannan aiki court zamu bashi dama, zamu bashi dama ta ƙarashe wato dawo da kayan salin alin ba tareda kowa ya sani ba haka batare da mun tona masa asiri ba".
Haɗe rai sosai Saraki yayi har fiye da yadda Kisnah tasan yana yi dan a wannan ɓangare sam baya wasa haka baya san wasa baya kuma san ayi masa wasan wanda irin wannan jajircewar ta samar masa da girmamawa da kuma ɗaukaka a cikin ƙankanin lokaci, a yanzu da yake zaune ba yana hango kansa ne zaune cikin mall ba ƴana hango kansa ne cikin court trying to find out a hidden truth.
Direct ya sauke duban sa gefe kujerar da mutumin yake wadda ba kowa kanta ya kuma kausasa murya sosai alamun ba wai wasa yake ba
"Ƙin amfani da damar da muka bayar ze sa mutimin ya fuskanci hukunci me tsananin tsauri wanda bana jin ya taɓa fuskanta a kaf rayuwar sa, ba zance kar me laifin ya gudu ba se dai ma nace Allah ya bashi sa'ar hakan wanda hakan shine baban kuskure na ƙarshe daze yi a rayuwar sa dan daga yanzun nan da muke zaune tare da ku anan Yana under supervision ɗin security agencies daban daban, gare ku ragowar maaikata, kusani ba wai an ɗauke ku aiki an ƙyale ku kowa yayi abinda ya ga dama bane, dukkan shige da ficen ku dama information ɗin family ɗin ku duk muna samu dan haka wanda ya tsaya yai aiki tsakani da Allah will receive two reward, one here from us a duniya and the other from Allah a nan duniya ko a lahira, wanna shine iya abinda zan iya cewa kan wannan batu, Allah ya ƙara muku lafiya da ƙarin gwiwar yin aikin ku kan gaskiya da Amana ya kuma ɗaukaka wanna waje".
Da Amin kowa da ke cikin hall ɗin ya amsa har da Kisnah dake zaune tana kallon shi cikin jin daɗi da burgewa, yadda yayi addressing issue ɗin ba wanda baze yarda cewa dagaske bane sun kama me laifin tuntuni bayan yar awa ɗaya da ta wuce lalube ne suke yi cikin duhu sedai bata san ko yanzu ya gano criminal ɗin ba kamar yadda manufar meeting ɗin take.
Cikin shan jinin jiki ma'aikatan suka fita gaba ɗaya kowa na zargin kowa sedai masu gaskiya ba su wani damu ba se masu ɗan tsatsa a zuci na rashin gaskiya suke shan jinin jikin su ya saura iya manager da Kisnah se Sarakin da ya miƙa a lokacin ya fara tafiya cikin takun sa na isa ya doshi hanyar fita
"Yaa pls ka jira ni, lissafi kawai ze yi min se mu tafi". Kisnah ta katse shi da sauri ganin yana gab da ficewa
"Ina mota". Iya abinda ya faɗa kenan ya fice batare da jiran me zata ce ba.
Cikin sauri suka yi lissafin da ya tsaida su wanda na kayan da akafi so ne cikin watan da ya wuce dan ganin ko za'a sami damar ƙara wasu tunda ana son su, takardun da zata cike kafin a shigar da file ɗin kundin fitar da kuɗi ta karɓa hannun managern da sauri tana faɗin zatai signing a gida se ta kawo masa daga baya.
Kishingiɗe kan kujerar driver yake kamar kullum yau ma ya saka wani cassette din wa'azi ne na wani babban malamin garin inda yake wa'azi kan irin tarin zunubin da ke cikin fitar da tsiraici, da sallamar da yanzu ta zame mata dole indai zata kusanci inda yake ta shiga cikin motar, gyara zaman sa yayi yana tayar da motar har lokacin yana cigaba da saurarar wa'azin, shiru duk sukayi yayinda motar ke tafiya smoothly kan shimfiɗaɗɗen titin da ba'a daɗe da zuba masa sabuwar coal tar ba, a kaikaice yake kallon ta ta ƙasan ido cike da son ganin jikin ta yayi sanyi da irin azabobin da malamin ke faɗa sedai kwata kwata ma ya lura hankalin ta baya nan yana can wani waje ne da be sani ba dan yadda ta kafe glass ɗin motar da ido bata ko ƙiftawa irin dai mutun yayi nisa a duniyar tunanin nan, be ji daɗin hakan ba dan saboda ita ya saka wa'azin ko ta rage wasu daga cikin shigar banzan da take yi, hannu ya miƙa ya canja wa'azin zuwa karatun Alkur'ani mai girma dan ya lura saurarar sa na kashe mata jiki sosai.
Juyowa yayi gaba ɗaya da san dawo da ita daga tunanin ya ɗan yi gyaran murya kafin yace
"Wa kika fahimta matsayin me laifin da yayi wannan aika aikan?".
Se da ta sauke ajiyar zuciyar firgita da ta ɗan yi kafin ta kalle shi itama
"Ban fahimci kowa ba dan dukkan su basu bada wata ƙofa ba duk da bakowa nake iya ganin sosai ba".
Gyaɗa kan sa yayi tare da yin shiru na tsawon mintina kafin ya yanka
"Ni na gane shi".
Da sauri ta karkato sosai har kamar zata bar kujerar ta zuwa tasa tana magana cike da zaƙuwa
"Wane ne yaa, wace number ce a gefen ƙirjin sa?".
Ta tambaya cike da curiosity kasancewar kowane ma'aikaci akwai identity number jikin rigar sa ta gefen ƙirjin sa ta dama haka kuma akwai sunan sa a bayan rigar haka kowanne ana bashi uniform set uku ne dan gudun matsala kamar ƙonewa, yagewa ko jiƙewa.
Kallon ta yayi for some seconds kafin ya ɗauke kai be bata amsa ba kamar yadda yaga ta zaƙu ta ji, kwaɓe fuska tayi ganin abinda ya mata kafin cikin sakkakiyar murya ta furta
"Yaa Saraki mana".
Harara ya juyo ya wurga mata ya sake maida hankalin sa kan titi, da sauri ta saki dariya kamar wata zararriya, jin taki denawa yasa ya juyo ya kalle ta hakan kula ya a dariyar ta ƙaruwa.
"Dama haka ka iya harara yaa, tabb wa yaga harira sunan wata mata".
Murmushi ne ya so ƙwace masa se dai ya danne ya ƙi ko kallon ta hakan yasa ta cigaba
"Haka ma fa ɗazu a hall ka harareni kuma guess what, wallahi ka iya sosai dan har wani kaɗawa fa gashin ifon ka ke yi".
"013". Ya faɗa da sauri cikin son ta bar zancen hararar dan se ya ji yana ɗan jin kunya, aikuwa da sauri ta tsayar da dariyar ta tana zuba masa ido
"Number criminal ɗin kenan 013".
"Amma taya akayi ka gane shi yaa, 013 sunan sa Adams kuma physically mutumin kirki ne".
"Ki bincike shi sosai though ma yadda na karanci facial expression ɗin sa he's so scared and na tabbatar ze dawo da kayan kamar yadda nace".
Girgiza kanta tayi tare da gyaɗa shi at once dan tasan tun da ya faɗa ɗin to Allah ya bashi ikon gano shi ne, batare da kuma sun sake cewa komai ba suka ƙarasa gida yayi parking ta fita, kamar yadda ta saba ta jingina jikin murfin side ɗin ta da ta rufe har ya kulle motar ya zagayo ɗan yi side ɗin ɗakunan su
"Good night yaa, have a nice sleep".
"Fi Amanillah". Ya amsa ta dan yasan tun da ta daɗi haka to ba zata kuma fita ba yau se gobe shiyasa tun yanzu ta masa bading bye, amsa matan da yayi yasa ta juya ta wuce flat ɗin su dan It's to 3 rana tayi yawa a compound ɗin.
Kwana biyu bata fita ko ina ba se ana ukun da ta shirya cikin shagalalliyar shigar da munin ta yakai wadda ya kwana biyu be ganta da irin ta ba, yau ɗin suna da babban taro ne dan yau Surry take birthday party ɗin ta wanda ya wuce satin da ya wuce da bata sami damar celebrating ba saboda ba'a sallame ta ba se shekaranjiya shiyasa suka shirya grand party na murnar birthday da kuma samun sauƙin ta dan yanzu ba kowa ne ma ze ce tayi ciwo ba se su da suka sani haka kuma samarin Surryn ba ƙaramin kashe kuɗi sukai ba wajen ƙawata shi dan yayi looking so big and classy.
Shigar da suka yi yau ɗin special ce, komai na jikin su kuɗi ne barin ma Kisnah da iya rigar da ta saka 2.3 mil tayi order ɗin ta kuma tare da ribbon ɗin ta take zuwa, takalmin da tasa kaɗai 310k ne se sun har ɗin ta me kyau da ta siya a K&S 50k Dan designer and fashionable ce sosai.
A ƙalla dai kayan da ta sanya wa jikin ta kama daga kan riga, takalmi, hat, chain, earrings, rings, watch, leg chain and glasses sun tasar wa 4mil.
A kallo ɗaya zaka yi mata kasan Yes ta haɗu, so breathtaking dan tsayawa faɗar yadda baƙar rigar me walwali ta haska ta ɓata lokaci ne, kamar wata ƴar tsanar turawa ɗin nan da ake decor da su sedai gashi Sarakin namu yaya ga Kisnah sam shigar bata yi masa ba, dan rigar a tsage take tun daga ƙasa har rabin cinyoyi haka kuma ta gefe biyun ma tsaga ce har inda ta tsakiyar ta tsaya haka ma tsakiyar bayan rigar daga ƙasa.
Daga sama kuwa ba ƙaramin kama ta rigar tayi ba kuma siraren hannu biyu gare ta se zaren da ake ɗaurewa ta baya haka kuma wuyan buɗaɗden wuya ne ta gaba da baya da yasa ake hango saman ƙirjin ta sosai ta baya kuma har tsakiyar bayan a buɗe yake.
Kallo ɗaya yayi mata tun fitowar ta ya ɗauke kai cike da takaici, takaicin yadda ƴar musulmi gaba da baya ke irin wannan shigar ba kuma a gidan ta ba a'a sedan fita wasu su gani su yaba da sunan wani abu wai party, ɗaya daga cikin manya manyan abubuwan dake ƙara yaɗa ɓarna da fasali a ban ƙasa.
Tun da ta shigo motar take washe baki tana jiran taji yace mata tayi kyau sedai taga ko kallon ta be yi ba hakan yasa ta kasa haƙuri seda ta tanka
"Yaa ba kace nayi kyau ba". Ta faɗa tana ɗan jujjuyawa daga zaunen da take cikin motar ita a dole se yaga adon nata
"Yaa baka ji bane?, Nayi kyau ko".
Ta sake faɗa jin be tanka mata ba, se a wannan karon ya ɗago ya kalle ta cikin watsa mata mugun kallon da yasa take taji jikin ta yayi sanyi
"Kyau? A cikin wannan mummunar shigar kike neman kyau".
Shiru tayi dan bata san amsar da zata bashi ba sedai ita sam bata ga aibun shigar tata ba, ita bata wani ɗau saka irin wannan kayan a komai ba dan ta ɗau hakan a matsayin tsarin rayuwar ta haka kuma kamar yadda Bature ya faɗa kowa yana da right yayi living life ɗin shi as he wish dan haka ita ba me sa ido bace akan rayuwar wasu so bata san itama a fiye sa mata idon.
"Amma Ya Saraki yau birthday ɗin Surayya ne, tayi missing exact date ɗin saboda rashin lafiyan da tayi yanzu kuma ta samu sauƙi shiyasa ka shirya wannan partyn da murna biyu, jin daɗin warkewar ta da kuma birthday ɗin kaga kuwa dole ne muyi shiga me kyau dan taya ta murna ko?".
"Shine se kun bayyana tsiraici za'a san kuna farin ciki, inda zaki kyautawa kanki da kin koma kin canja wannan rigar to something more decent and better".
Ɗauke kanta kawai tayi ganin bafa ze fahimta ba ita kuma bata shirya bin wani tsarin sa ba na daban wanda ya zaɓawa kansa dan haka kawai itama ya barta da nata.
Ganin yadda ta ɗauke kai yasan nufin ta bazata canja ɗin ba so