Header Ads
Showing 54001 words to 57000 words out of 104570 words

Chapter 19 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1435

Ads at the middle of Article

ta lissafa masa fina finan da ta kalla shima haka


"Kin kalli mother India?".


"No, Amma naji ana yayi kyau so after na bar nan zan neme shi in kalla".


"Yayi kyau over wallahi, ai ina dashi, go and freshen up Nima kafin nan nayi wanka na huta se kizo mu kalla".


"Okay, yanzu kuwa dan har na fara zumuɗi, yauwa room nawa ma?".


"Wai har kin manta?, Jiya fa na gama faɗa miki".


"Kai dai tuna min ina sauri in wanka".


"Room 52 girl".


"Ok, see yha soon Mr Man".


Ta faɗa tana shigewa ɗakin nasu shima ya wuce nasa, a falon ta tadda su Surayya duka suna zaune da alama har sun yi wanka dan sun cire sport wears ɗin, bedroom ɗin ta ta nufa zata shige Meenah ta dakatar da ita da sentence ɗin ta


"Wai Kisnah a ina kika samo mutumin nan da yau gaba ɗaya ya ɗauke hankalin ki daga kan mu da ma Deeq, dan gwara ma Deeq ya je unguwa ze dawo amma daga jiya da muka zo wajen nan zuwa yau a falo kaɗai muke samun zama dake daga mun fita shikenan se kuma mun ganki".


"He's a friend, don't mind".


Haka ta faɗa kafin ta wucewar ta ciki, da ido suka rakata har ta ƙarasa shigewa kafin Surayya tayi saurin canja topic ɗin Leekha na karɓa mata dan kar ma akawo wani batu kan Kisnahn.


Wanka tayi kamar yadda tace masa ta canja kayan ta zuwa guntun wando iya gwiwa da ƴar ƙaramar rigar sa da bata ƙara sa sauka kan cikin ta sosai ba ta kitse jelar kanta tare da kame ƙarshen da ɗan ƙaramin band yadda ba zata since ba dan sosai kan ke da santsi.


Gaba ɗaya nan ta baro wayoyin ta dan bata san tana kallo ana damun ta da kira shiyasa ma ba zata tafi da ko ɗaya ba, adai falon ta kuma tadda su har yanzu suna zaune se dariya suke yi alamun hirar tana kai musu yadda suke so gaban su cike da kayan ciye ciyen da drinks kala kala.


"Se na dawo".


"Ina kuma zaki yanzu?". Wannan karon Leekha ta tambaya, ɗan kallon Leekhan tayi cike da jin haushin yadda suke wani titsiye ta kamar wata ƙaramar yarinya sedai sanin ba halin Leekhan bane hakan se ta mata uzuri yau ɗaya dai


"Ɗakin Asad, akwai Film ɗin da zamu kalla tare a system ɗin shi".


"Why not shi yazo ku kalla a nan?". Hameedah tayi interrupting sedai ko kallon ta Kisnah bata yi ba ta dubi Surayya


"Mind joining us?".


"No, am feeling somehow sleepy, kya bani labari".


Gyaɗa kanta tayi tana ɗagawa Meenah yatsu biyu


"Se na dawo babe".


"Hope you enjoy the movie". Meenah ta amsa mata sannan ta fice, tana fita Surayya ta miƙe ta musu good night ta shige bedroom ɗin ta haka ma Leekha ya saura Hameedah da Meenah, juyowa Hameedah tayi tana kallon Meenah da wani expression on her face yayinda Meenahn ta kau da kai kamar bata gani ba ta mata sallama ta wuce, dole ba dan ta so ba itama ta wuce nata bedroom ɗin dan ba yadda zata yi bayan ta kashe ƙwan ɗakin.


Knocking biyu Kisnah tayi Asad ya buɗe mata ƙofar ɗauke da murmushi a saman fuskar sa yana sanye da three quarter da farar t-shirt da ta kama jikin sa sosai, itama smile ta Masa tare da shiga ɗakin ya maida ƙofar ya rufe.


Kan doguwar sofar dake ɗakin ta zauna tana ɗan miƙe legs ɗin ta, be zauna ba ya wuce wajen fridge ɗin ɗakin ya zubo musu dambun naman dake cikin wani rufaffen madaidaicin container ya Kuma ɗauko drinks ya kawo ya ajiye kan Centre table ɗin da ke falon ya koma ya ɗauko glass cups masu kyau guda biyu ya ajiye sannan ya koma ya ɗauko system ɗin sa dake kan bed kana ya dawo ya janyo table ɗin gaban sofar a hankali kafin ya zauna kusa da Kisnah yana danne danne cikin system ɗin kafin ya ɗago ya dube ta


"Ready?".


Yesssss". Ta faɗa prolonging the 'S' sound.


"Here we go". Ya faɗa yana starting film ɗin sannan ya ɗora kan table ɗin suka shiga kalla.


Tun kafin ayi wani nisa sosai Kisnah ta fara kuka dan sosai Film ɗin yake da abun tausayi, lallashi ne Asad ya sha shi dan kamar wata ƙaramar yarinya haka ta koma, wasa wasa ba Film ɗin ya ƙare ba se after 2 dan it's a 3 hour film, ko da aka gama bata tafi ba wani Indian comedy na Rani Mukherjee me suna Aiya ya saka mata dan lightening mood ɗin ta, cikin ƙanƙanin lokaci kuwa se gashi tana sheƙa dariya kamar ba ita ce ta sha kuka ba, a hankali a hankali bacci yake fisgar ta dan yau ta gaji sosai har ma dai yayi nasarar sace ta gaba ɗaya, gyara mata kwanciya Asad yayi ya cigaba da kallon sa har se da Film ɗin ya ƙare wanda lokacin it's to five am sannan ya fara tashin ta a hankali.


A hankali ta fara buɗe idanun ta ta sauke kan sa, murmushi me sanyi ya yi mata kafin cikin cool and low tune ya Fara mata magana


"Hey sleeping beauty, it's subhi, kije kiyi sallah a ɗakin ki, okay?".


Out of sleep ta gyaɗa masa kai kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa sedai dake ba sakin ta baccin yayi ba se ta kasa har se da ya riƙe ta helping her to stand ya kaita har bakin ƙofa sannan ta zare jikin ta tana lumshe masa ido alamun zata iya tafiya, waving ɗin ta yayi ta fita kafin ya maida ƙofar ya tafi toilet dan yin alwala.


Tafiya take a hankali har tana ɗan layi na bacci har ta wuce ɗakin su bata sani ba , daidai lokacin Saraki ya fito dan tafiya masallaci kamar yadda ya saba dan a can yake karatun Alkur'ani tare da nafilolin sa kafin exact lokacin sallah yayi, sosai yayi mamakin ganin ta a wannan lokaci and to his utmost surprise kamar ma layi take alaman bata cikin hayyacin ta sosai.


Kamar ya wuce ta sedai ya kalli ƙofar ɗakin su da ta wuce a baya sosai dan shi yana room 45 ne su suna 50 amms har ta wuce ɗakin nasu tama gota nashi, da sauri ya ƙara sa inda take tare da ruƙo ta dan dakatar da ita, a hankali ta juyo dan fa baccin ne sosai a kanta, ganin shi yasa ta ɗan ware sleepy eyes ɗin ta da suka canja kala zuwa golden brown saboda bacci


"Yaaaaaaa". Ta ja sunan sosai abinda ya sa Saraki kuma shaida ba'a hankalin ta take ba


"Yaaaaaaa ɗakiiii zaaani".


Cikin takaici ya juya ta zuwa hanyar da ta baro hakan yasa ta buɗe idon sosai ta gan a bakin room 43 ma take


"Kaga ban ma san na wuce ɗakin bama, am toooo sleeeepyyy".


Bece mata komai ba har lokacin sedai cikin ransa cewa yake taya zata san ta wuce tunda bata cikin hankalin ta?


Har bakin ƙofar ɗakin nasu ya rakata kuma be tafi ba seda yaga ta shiga cikin parlon kafin ya juya ya koma hanyar da ya baro heading to the elevator.


A falo ranar Kisnah ta kwana dan baya iya kai kanta ɗaki ba saboda nauyin baccin dake kanta, se after seven ta tashi ta koma bedroom ɗin ta ɗora baccin ta daga inda ta tsaya.


Ƙarfe goma ta farka ta shiga wanka sannan ta shirya bayan ta fito, yau kam ba laifi Canadian gown ta saka da yakai mata ƙasa dan har yana jan ƙasa ta baya ta sake gashin ta bayan ta taje shi tare da shafe shi da mayukan kai masu ƙamshi ta feshe shi da turaren gashi ta ɗora masa sun hat me kyau sosai kalar brown Wanda gown ɗin jikin ta milk and brown ce haka takalman ƙafar ta milk heels ne.


Ƙarar wayar ta yasa ta ƙara sa inda ta watsar dasu jiya da dare ta ɗaya wadda take ƙarar ta kai kunnen ta ganin sunan Surry


"Mun fita kina bacci Queen, in Zaki biyo mu muna highway mountain".


"Okay, I'll see in zan zo ɗin".


"Okay". Surry tace tare da kashe wayar.


Zama ta ɗan yi tana tunanin ta bisu ne ko kuwa tayi zaman ta?


"Garden". Kamar daga sama haka sunan ya faɗo cikin ranta, da sauri kuwa ta miƙe dan a rayuwar ta tana matuƙar son guri me korayen ciyayi da bishiyoyi shiyasa tun tana yarinya Abbi yayi mata ƙaton garden a gidan su.


A hankali a hankali take takawa kan corridor ɗin ɗakunan dan sosai marbles ɗin ke da santsin da in batayi taka tsantsan ba ze iya tiƙa ta da ƙasa saboda tsinin takalmin ta, gyaran muryar da taji a bayan ta yasa ta ɗan waiga hakan yasa suka yi four eyes da Saraki da ya fito dan zagaya wa saboda jiya gaba ɗaya a ɗaki ya wuni shiyasa yanzu yake buƙatar fresh air


"Good morning yaaa".


Gyaɗa mata kai yayi alamar amsawa dan yanzu kam ya sauko daga fushin da yake yi dan ganin abinda ya faru jiya yasan da beyi fushi ba da ko yaya ba zai bata space ɗin kwana wani waje ba dan zata kasance ƙarƙashin idon sa ne.


"To where?".


"Garden, won't mind joining me please, am lone".


"Okay". Ya ce mata dan haka suka jera suka cigaba da tafiya, daɗi sosai Kisnah ta ji ganin ya dena fushi da ita haka itama se ta ajiye alwashin ta a gefe.


A tare suka shiga elevator ɗin ɗan yana da faɗi sosai, a third floor suka sauka dan akwai garden me kyau a floor ɗin kafin ta masa jagora zuwa garden ɗin da tun 2 years back ta haddace hanyar shiga cikin sa though an samu sauye sauye a resort ɗin.................✍️.








©️ Ouummey 📚✍️.










☑️Ote, comment and share fisabilillah.










































Ouummey 23 (8/17/2022 8:10 PM )





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________








Assalamualaikum warahmatullah ɗauka cin masoya littafin *SARAKI* daga kowane group most especially*SARAKI FANS CLUB* ina godiya sosai da addu'o'in ku ga ƴar uwa ta , Allah ya saka da alkhairi ya bar ƙauna, Allah kuma ya jiƙan dukkan musulman da suka riga mu gidan gaskiya, marasa lafiya Allah ya basu lafiya, mu da muke da ita Allah ya kara mana ya bamu ikon gode, masa Ameen summa Ameen.


Once again, nagode Allah ya bar zumunci da ƙauna 🥰.












Page 2️⃣3️⃣
















_______________________📖 sunkuyar da kanta tayi ƙasa ganin irin kallon da yake watsa mata na rashin yarda kafin ta sake ɗagowa sedai wannan karon idon ta ya ɗan sauya launi


"I swear to God ban Sha komai ba, so nawa zan faɗa maka bana shaye shaye ne yaaa"?".


Ta ƙarashe maganar ranta na suya, a rayuwar ta taƙi jinin shaye shaye shiyasa kullum cikin yiwa su Hameedah faɗa take yi, ita magani ko na rashin lafiya in har ba kwantar da ita tayi ba bata taɓa shan sa, duk kuwa irin ciwon kan da zata yi ko ciki sedai ayi mata allura dan magani is her perfect enemy.


Ɗan furzar da iska yayi daga bakin sa kafin a hankali yayi magana batare da ya kalle ta ba


"What about haɗa hanyar da kika ringa yi jiya da na ganki, me ya kawo shi?".


"Bacci ne a kai na sosai saboda na gaji sosai jiyan kuma ban samu hutu ba shiyasa bacci yaci ƙarfi na but am in my sence".


"Then daga ina kika fito a lokacin dan nasan ba yadda za'a yi ki fito daga ɗakin ku at that time in har kina hankalin ki kamar yadda kika ce, to me ma zaki fita nema?".


"Ba daga ɗakin mu na fito ba, Asad ya taso ni daga ɗakin sa da nayi bacci yana faɗa min lokacin subh prayer yayi". Ta faɗa da ɗan nuna gajiyawa cikin Muryar ta dan wallahi ban dashi ɗin bata ga wanda ya isa ya tasa ta gaba haka yana mata irin wannan tambayoyin bata ci masa mutunci ba.


Sedai ta rasa me yasa she's very and very tolerant when it comes to Saraki abinda bata ɗauka wajen kowa se shi yayi mata bata damu ba, kalli dai yadda yayi fushi har ta je bashi haƙuri yana wani yaga ta abinda ta tabbatar da wani ne da se taci masa a lokacin kuma bata jin zata sake kallon shi da mutunci se gashi shi yayi duk kuwa da ta ji haushin abinda yayi mata amma da ya saki fushin se taji ba zata iya share shin da tace ba.


"Naje kallon Film ne ɗakin sa and I over slept there shine ya tada ni na fito har muka haɗu".


Ta faɗa da ɗan sauri ganin be amsa bayanin da ta yi masa ba se ma zuba mata ido kawai da yayi yana kallo wanda se da ta gwammace da bulala yasa ya dake ta da hukuncin da yake mata da idanun sa.


"Na fahimta and dama I thought so, sedai Sam be dace ba a bisa tsarin musulunci mace baliga ta shiga ɗakin namijin da ba muharramin ta ba har ta kai irin lokacin da kika kai saboda gudun sheɗan and Kuma mutane ma zasu iya miki wata kallon na daban dan ba wanda yasan dalilin zuwan ku ɗakin kamar yadda ni kika min bayani yanzu, so pls kar ki sake hakan, okay?".


A hankali ta gyaɗa masa kanta tana auna zantukan sa cikin ranta, ita bata ga abin wani rashin dacewa ba tunda ba wani abu suka yi ba a ɗakin, kallo fa kawai tayi se kuma bacci ya kwashe ta and he woke her up, to meye a cikin hakan?, Babu komai!
And mutane, who cares about them da abin da zasu ce? Sun daɗw ba su ce ba she didn't give a damn, Amma tun da yace hakan insha Allah zata yi ƙoƙarin dainawa dan dai ta riga ta saba.


Zama suka cigaba da yi bakin pool dake ciki garden ɗin ƙafafun ta cikin ruwan shi kuma yana kallon ruwan ƙafarsa a tanƙwashe, fira suke yi jefi jefi wadda a hankali yake sako mata nasiha cikin hirar wadda alamu suka nuna suna tasiri a ranta.


Basu bar wajen ba se da aka kira zuhur, masallacin dake resort ɗin ya wuce bayan yace taje tayi sallah a ɗakin su, sallar tayi ta zauna jiran shi kamar yadda yace mata, 30 minutes after se ga Knocking ɗin shi, wayar ta ta ɗauka ta riƙe a hannu kafin ta nufi ƙofar ta buɗe, ɗan ja baya yayi ya bata hanya ta fito sannan suka sake fita daga resort ɗin zuwa parking lot, motar ta dake nan a rufe masu kula da wajen suka yaye musu, tass take ba ko alamar datti dan da alama kullum ake buɗe ta a goge a kuma mayar a rufe.


A hankali motar ke tafiya kan titin dake wajen yayinda motar tayi shiru ba abinda ke tashi se karatun Alkur'ani se ko sautin Muryar sa dake bin karatun can ƙasa, daga kan kujerar da take zaune take ɗan kallon shi a kaikaice cikin yanayin burgewa dan yadda bakin sake motsawa yana bin karatun cike da ƙware wa ba ƙaramin burge ta yayi ba.


Da haka ya ƙarasa da ita highway mountain wajen su Meenah, yana ajiye ta ya juya dan se six zasu bar wajen and now it's only to 2, ya kawo ta ne dama dan kar ya wuce ɗakin sa ta tafi wajen Asad yake kowa ne oho, sedai yasan ba yaron da ya gansu a bakin spa bane dan ba haka yaji ta kira wancan ba though be riƙe sunan ba.




****************




Ranar juma'a ce, ranar da ta kasance farin cikin dukkan wani musulmi dake faɗin duniya, kamar yadda yake al'ada a ƙasar Hausa sanye kusan kowane magidanci, tsoffi da yara suke da sabon kayan su, ba wai se lallai sabo fil da ba'a taɓa sawa ba a'a har da waɗanda ya kasance irin ƙasan akwatin nan wato masu kyau da ba'a saka su sosai ba irin dai na sallah ko wani sha'ani.


Falo ne me matuƙar girma da aka ƙawata da kayan ƙawa da alatun sarauta, matuƙar girman falon ya isa a yi bedroom biyu a cikin sa kai har ma da toilet in da za'a zauna a tsara.


Falon Maimartaba Sarki Muhammad Hasheem II kenan da yake zama tare da iyalin sa gaba ɗaya a dukkan ranaku irin na yau wato juma'a da kuma asabar dan samar da shaƙuwa da ƙauna tsakanin sa da ƴaƴansa da ma matan sa gaba ɗaya.


Zaune yake kan ɗaya daga cikin manyan leather seats da suka ƙawata falon ya hakimce ciki irin zaman da ya kasance sabon sa sedai yau ba rawani ko wani abu da yayi wa ƴaƴan sa shamaki da kyakkyawar fuskar tasa, hasalima sanye yake cikin baƙar jallabiyar da ta saukar masa har kan dunduniya kansa a buɗe ba ko hula yayin da yatsan tsakiyar hannun sa na dama ke sanye da counter yana lazimi jefi jefi kuma yana sauraren hirar ƴaƴan nasa, gefen daman sa ya kalla a nutse inda gimbiya Haleematu ke zaune ya sakar mata tattausan murmushi


"Gimbiyar Giwa kin kuwa ji abin da ƴaƴan ki ke taunawa a kai?".


A ɗan nutse ta gyara zaman ta tana sake masa nata murmushin


"Naji su sarki na, ai dama na daɗe ina faɗa maka ƴaƴan nan naka kunyar su da sauƙi tun bare ma wannan baban namu".


Ta ƙarashe tana ɗan hararar Jamal dake cikin ƴan uwan sa biyu da suka rage a gidan, yarima uthman da princess wadda asalin sunan ta kausar ne.


"Ayya Mami ayya, Allah ni Ina da kunya, Allah yasa Abiy yaji ya Uthman ne yake magana bani ba ko Maama?".


Da sauri sarauniya Rumana ta gyaɗa kanta cikin goya wa Jamal baya tana ƴar dariya


"Sosai ma kuwa babana, duk laifin na wancan yaron ne amma dake uwar sa bata son laifin sa ai kaga mu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads