Header Ads
Showing 90001 words to 93000 words out of 104570 words

Chapter 31 - SARAKI (The Accused Prince).txt

Ads the beginning of article before Image

ummi   

03 Jun 2024

1441

Ads at the middle of Article

yi.


Seda ta jira tayi bacci kafin ta bi bayan Abbu ɗakin su inda ta same shi kwance kan gadon su har yayi wanka ya canja kaya zuwa na bacci sedai da alama yayi nisa a tunani dan be ko ji shigowar ta ba, bata ƙarasa gare shi ba seda ta yi wanka ta shirya sannan ta hau gadon har lokacin yana yadda ta same shi da farko, hannu ta miƙa ta cire masa tagumin kafin ta fara tambayar sa damuwar sa a tausashe.


Shiru yayi kamar baze faɗa mata ba kafin kuma a hankali ya janyo ta jikin sa ya nufi baki yayi magana dan basa taɓa ɓoyewa junan su komai duk kuwa da ɓacin ran da maganar zata haifar sun gwammace su fuskanci hakan su kuma tare ko ma mene ke ƙoƙarin shiga tsakanin su.


"I'm having some strange feelings Husna, Ina jin wani iri a jikina, yanayin kamar irin wani abu mara kyau na gab da faruwa, irin feeling ɗin da na ringa ji lokacin da zanyi rashin inna har ma da baffa na, bana son barin ku Asma'u but it's like something bad is about to happen sedai ban San akan wa ya ba, nidai fatana ko meye kar ya shafi princess, Husna I can't hold myself in wani abu ya taɓa min yarinya, bazan iya ɗauka ba, i pray koma meye ya tsaya a kaina dan............".


Da sauri Nana ta rufe masa baki dan tuni ya daɗe da karya mata zuciya da kalaman sa, she too is experiencing the feelings sedai yanzu da ya alaƙanta yanayin da mutuwar Inna da baffa se abin yayi tasiri a rai da zuciyar ta gaba daya har take jin kamar zata rasa su ne, kamar...kamar.... bata fata!


Kamar wanda ya dawo hayyacin sa yayi saurin gyara yanayin fuskar sa trying to hide something to her karo na farko tun fara rayuwar auren su 15years back, kumatun ta ya ja Yana sakin dariya lokacin da take faman sharar hawaye


"See this woman, are you crying for good, tabɗi amma dai anji jiki dan dama gwada ku nake na ga extent to which kike son mu ni da princess ɗina nad thank God you love us this much".


Ya ƙarashe yana mata cakulkuli, dariya take tana kai masa duka tare da magiyar ya bari amma yaƙi seda ya galabaitar da ita sannan ya kwanta gefen ta yana dariya ita kuma tana nishi, seda suka mutu kafin ya soma magana


"Ko me kika ga ya faru da bawa rubutacce ne Husna, dan haka mu kwantar da hankalin mu muyi addu'a tunda ba zamu iya sauya ƙaddara ba, now let's pray and sleep ma'un safwanu".


Ya ƙarashe in a joking tone dan yasan ta tsani ya kira ta ma'un nan, aikuwa seda ta mintsine shi kafin ta fara addu'a shima ya shiga yin tasa, tana gamawa ta shafawa kanta ta shafa masa shima yayi as she did sannan suka kwanta rungume da juna cikin blanket, shiru suka yi har ta fara gyangyaɗi kafin tai firgigit ta ce masa


"I love You".


"I love You more ma'u na". Ya faɗa kissing her forehead, and that's the end of their conversation bacci ya kwashe ta, seda ya tabbatar tayi bacci kafin ya zare jikin sa ya koma ɗakin princess, dim light ya kunna sannan ya kwanta a gefen ta yana staring at her face kamar wanda aka bawa aikin zana ta har bacci ya ɗauke shi.


Ƙarfe biyu da rabi na dare Nana ta tashi fitsari, ko da ta je ta dawo bata ga Abbu ba ɗakin Kisnah ta nufa ta kunna wuta, kamar yadda tayi zato kuwa nan ta ganshi kwance kusa da princess ɗin tasa, kamar ta tashe shi se kuma ta ƙyale shi ta koma ɗakin su ta kwanta dan gadon baze ishe su su uku ba balle ta kwanta tare da su.


Ko minti uku ba tayi ba ta fara jiyo ƙara kamar ana dukan glass ɗin upstairs ɗin su da yake daga stairs ɗin zuwa saman su akwai glass days zagaye gurin da dole se ya buɗe sannan mutum ze hawo.


Da sauri ta sauka daga gadon ta koma ɗakin Kisnah kafin ta shiga tashin Abbu cikin firgici, a razane ya buɗe idon sa dan yana cikin wani mummunan mafarki ne ta tashe shi, bata ko lura da yanayin saba ta shiga sanar da shi abin da ke kan faruwa, shima cikin tashin hankali ya saka hannu biyu ya sunkuci Kisnah suka zagaya suka fice ta ƙofar baya, Nana daga ita se rigar baccin jikin ta inda Allah ya so ta ma me kauri ce kuma haɗe take da wando suma duka haka.


Gudu ya shiga tsugawa a kan titi yayinda terrorist ɗin suka rufa musu baya dan wanda aka bari zagaye da gidan sun sanar da na ciki fitar su Abbu, haka suka dinga tsere da motar terrorist ɗin har daga ƙarshe suka kai ga harbin tayar motar, cikin ihu Abbu da yaji ƙarar da tayar tayi alamar fashe wa ya ke bawa Nana umarnin ficewa daga motar ita da Kisnah, cikin ruɗewa Nana ta sungumi Kisnah da ta farka tuni ta jefa ta window, cikin son tseratar da ƴar ta ta jefa ta gurin da bata san ina bane ita dai kawai fatan ta ta tsira.


Tun daga wannan jefawar da Nana tayi mata ta suma yayinda su kuma su Abbu motar su ta shiga karantawa tana juyawa har ta shige cikin daji kafin ta tsaya sanadin bishiyar da ta tokare ta, mintuna kaɗan kuma ta tashi da wuta gaba ɗaya (abinda kawu yaso yiwa motar su Kisnah kenan da suka gudu se kuma ba sukai ga harbin ba suka daki wannan tankar).


Duk da ƙananun shekarun ta a lokacin se da tayi kuka ba kaɗan ba domin a islamiyyar su ana faɗa musu in an mutu ba'a dawowa haka kullum Nana na faɗa mata in ta mutu ba zata sake ganin ta ba se gashi yanzu ana faɗa mata Abbu da Nanan ta sun mutu, a yadda taji labari daga baya ko gawar su ba'a samu ba wuta ta cinye komai.


Bayan bakwai ne kuma kawu ya tarkato suka dawo gidan da zama, bayan sadakar arba'in ne kuma ya shiga batun ya kamata ta koma makaranta amma ba zata cigaba da karatu a ƙasar nan ba dan wai ta samu ta manta memoryn mutuwar su Abbu...................✍️.














©️ Ouummey 📚✍️.














☑️Ote, Comment and share fisabilillah.


























Ouummey 37 (8/27/2022 12:37 PM)





💠💠💠💠💠💠💠💠
*SARAKI (the Accused prince)*
💠💠💠💠💠💠💠💠






Daga Alƙalamin Ouummey
Wattpad @Ouummey


*Marubuciyar;*
*1; HAƘORIN DARIYA*
*2; ƘASAR MU A YAU*
*3; BA NI DA LAIFI*
*4; Loading......SARAKI (the Accused prince)*








______________________________
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞


```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```


/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/


*P.W.A✍️*


_________________________________
















Page 3️⃣7️⃣
















__________________________📖 England kawu ya shirya kai ta batare da shawara da kowa ba dan tuni ya babbake kan dukiyar ta dan yace bata da wanda ya fishi a lokacin kuma ba wai ta mallaki hankalin ta bane so ze kular mata da komai zuwa ta girma, ko sati da karɓar ragamar Companies ɗin be yi ba ya sauke Alh Sulaiman daga kan duk abinda yake jagoranta ya canja manajojin da ya ga dama.


Ana ya gobe ze kaita England Alh Sulaiman ya same shi har gida kan be dace ya kai yarinya ƙarama ba wata ƙasa ita kaɗai bayan bata da kowa a can, ƙasar da komai namu ya sha banban da nasu kama daga kan al'adu, addini zuwa wayewa sedai tuni kawu yasa ƙafa yayi fatali da maganganun Alh Sulaiman suka rabu baran baran bayan kawu yayi masa cin mutunci wanda wannan ne yasa Alh Sulaiman ɗin yin fushi be kuma magana ba akan duk abinda ya shafi Kisnah dan kawu ya faɗa masa ƴa dai tasa ce dan haka baya san shisshigi da kalan dangi.


Haka kawu ya kaita makaranta yayi mata registration ɗin komai ya danƙa ta hannun shugaban makarantar da sunan ze dinga turo masa kuɗin komai na buƙatar karatu amma bazata dawo gida ba har se ta gama karatun ta zuwa matakin ƙaramar secondary.


Haka kuwa akai kawu ya dawo gida manya ya bar Kisnah garin da bata da kowa a hannun baturen da be san Allah ba, kamar yadda yace bata dawo manya ba kuwa seda ta gama primary gaba ɗaya sedai batun ilimin addini kuwa babu shi dan tun da ta bar manya ba wanda ya kuma tuna mata akwai abin bautawa da gaskiya wato Allah balle kuma akai ga su karatun Alkur'ani da hukunce hukuncen addinin Islam sedai a karan kanta ta riƙe yin Sallah dan sallah ce abu ɗaya da Nana ta fi jaddada mata fiye da komai hakan yasa duk zamanta a can bata manta da yin ta ba sedai yadda zata yi tan ne bata iya ba so take yin duk yadda taso kawai.


Dawowar ta da ƙyar kawu ya barta ta yi wata biyu a gida lokacin tana shekara goma ya kuma maida ta ƙasar Canada inda tayi karatun secondary gaba ɗaya har ta fara University kafin kuma tashi ɗaya ta gudo ta bar ƙasar shine haɗuwar su da Deeq a restaurant ɗin nan yake faɗar ta gudu ba sanar wa sedai suka neme ta suka rasa.


Dawowar ta ta nemi admission a nan manya state University department ɗin law inda kuma a nan ta haɗu da duk ƙawayen ta kamar yadda muka ji a baya .


*Wannan shine tarihin Kisnah*
(Mun dawo labari).


Shessheƙar kukan ta da yaji ya ƙara ƙarfi fiye da baya yasa ya juyo ya kai duban sa gare ta, daga zaunen da take ta ƙara takurewa kanta tsakankanin cinyoyin ta tana kukan ta da ya ɗan ƙara ƙarfi dan ta daɗe tana yin sa sedai be kai ƙarfin na yanzu ba.


Mamaki ne ya kama shi ganin yadda jikin ta yake rawa sosai kamar wadda aka watsawa ruwan sanyi a tsakiyar hunturu, gaba ɗaya se yaji jikin sa yayi sanyi, me ya same ta da take kuka haka, bata da lafiya ne ko me? Kamar wanda aka tunawa haka kalmar mara hankalin da ya kira ta ya dawo kansa, to ko shi take wa kuka? Amma in ze tuna an kira ta da kalmar da tafi wannan muni kuma be ko ga ta damu ba balle har ayi batun yin kuka? To amma in ba hakan take wa kuka ba ai ba abinda aka yi mata haka kuma iya sanin sa lafiyar ta ƙalau.


Kawar da kansa yayi daga kanta se kuma yaji baze iya ba, kiran sunan ta yayi a hankali sedai ko ɗagowa bata yi ba balle ta amsa hakan yasa ya sake kiran ta wannan karon cikin ɗan ɗaga murya, a hankali ta fara sassauta kukan har sautin ya dena fitowa gaba ɗaya sedai hawaye kafin kuma ta ɗago kanta gaba ɗaya ta sauke jajayen idon ta da kuka ya rina ya sauya musu kala.


Seda ya ɗan firgita ganin yadda kyawawan fararen sexy eyes ɗin ta suka koma kala mara daɗin kallo, kafe shi tayi da su taƙi janye wa har lokacin kuma hawayen ta basu tsaya ba se shine yayi ƙarfin halin kau da nasa kafin ya shiga mata magana cikin sanyaya Murya


"Lafiya?, me ya same ki?, Wani abun akayi miki?".


Girgiza masa kai tayi alamar a'a dan tasan ko tace tayi masa magana ba iyawa zata yi ba yadda Muryar ta ya dishe haka kuma bata saba faɗawa kowa damuwar ta ba bata kuma jin zata fara yau, a kaf rayuwar ta tana barin damuwar ta a ranta ne dan ba wanda take dashi da zarai sharing dashi, a haka ta taso har girma shiyasa hakan ya zame mata ɗabi'a yayinda take samar wa kanta mafita irin wadda taga ta dace, bata san me zata ce an yi mata ba tunda ba'a yi mata ɗin ba shiyasa kawai ta zaɓi girgaza masa kan.


"In dan mara hankalin da na kira ki ne kiyi haƙuri raina ne ya ɓaci a lokacin amma na san be dace na faɗa miki hakan ba so na janye ta ki ɗauka ban ma faɗa ba, kinji?".


Ya faɗa cikin sake sanyaya Murya, girgiza kanta ta sake yi a karo na biyu kafin ta buɗe baki tayi magana cikin dasasshiyar murya ganin yana ɗorawa kansa alhakin laifin da be aikata ba, tasan ta ji haushin sa akan kalmar haka har tayi fushi kuma ba wai ta janye ba ne sedai ita ba abinda ya sata kuka ba kenan, Allah ta tuba kalmomi nawa aka faɗa mata da suka fi wannan muni kuma bata damu ba balle ta ɗorawa kanta wahala har balle kuma dasu yin kuka.


"Duk da naji haushin kalmar amma ba shi ya saka ni kuka ba, i just feel like crying shine nayi".


Tsura mata ido yayi trying to read her facial expressions and emotions and he succeeded, ya karanto damuwa akan fuskar ta haka yayi sensing kewa a Muryar ta sedai be san damuwa da kewar akan mene bane ba gashi itama she's not trying to unveil koma meye, a yau ya kuma fahimtar wani daga cikin halin ta, tana da zurfin ciki when it comes to bayyana damuwar dake ranta sedai kuma bata da zurfin ciki kan nuna so, ƙauna ko ƙi ga duk wanda ya siffantu da ɗaya daga cikin, misali bata ji nauyin Meenah ba lokacin da ta cinye wa Hameedah mutunci haka bata ji kunyar Mommy ba Lokacin da ta ƙare wa Awwaf tanadi sedai gashi a yanzu ta kasa bayyana masa damuwar ta.


Ajiyar zuciya ya sauke cikin son calming ɗin ta dan har lokacin hawaye keep rolling down her cheeks


"Komai yayi zafi maganin sa Allah ne haka kuma bawa baya taɓa gujewa ƙaddarar sa, bawa nagari shine wanda ya amshi ƙaddarar ya shiga ƙoƙarin ganin ya cinye jarrabawar sa ta kyakkyawar hanya, in kin ji zuciyar ki bata miki daɗi se ki yawaita ambaton Allah se ki ji sauƙi ba wai ki zauna kukan da bazai miki maganin komai ba".


Yana lura da yadda ta saka hannu t hau goge hawayen daga kan fuskar ta da ta ɗa tasa tsabar kuka har ta goge su tsaff kafin ta miƙe


"Bari inje wajen Nenne".


Ta faɗa tana ficewa daga ɗakin kuma be hana ta ba dan yasan hakan ze iya taimakawa mood ɗin ta, sedai tsawon mintina da fitar tata amma ya kasa samun nutsuwa, tunani kawai yake what could be damuwar ta, ko zaman su a nan ne damuwar, ko kuwa zogalen da ta ci ne yake damun ta, but in haka ne ai be ga wani sign na rashin lafiya a tattare da ita ba .


Ranar haka ta wuni so moody, ba wani farin ciki balle walwala, sam baya ji daɗin ganin ta a haka dan ba hakan ya saba gani tattare da ita ba, ita ɗin me fara'a da walwala ce a ko yaushe ko da kuma t ɓata rai ba ya kaiwa this long dan ba saki rai ta koma daidai ba har kusan bayan kwanaki biyu, ko yaushe se dai ta zauna tayi shiru cikin tunani wanda da ita ke damun sa da surutu har se yaji ya gaji.


Cikin ikon Ubangiji ƙafar Saraki ta warke ras cikin sati biyu da suka biyo baya kuma zuwa wannan lokacin tuni Kisnah ta saki ta koma yadda take baya, surutu kam da tsokana se abinda ya ƙari, yanzu kam ta sake cikin su Nenne da Bingel dan yawanci tare suke zuwa duk in da Bingel ɗin zata dan tuni ya yarje nata fita tun lokacin da ya ganta cikin damuwar nan.


Sannu a hankali hannun sa ke samun sauƙi har yana iya yiwa kansa ƙananan abubuwa kamar ɗaukar ludayi, ɗaukar gwangwani, cin abinci da sauran abubuwa marasa nauyi da ba zasu takurawa lafiyar hannun ba.


Zuwa wata biyu da suka ƙara kuwa gaba ɗaya hannun ya warke tas dan ba abinda baya yiwa kansa kamar dai lokacin da babu abinda ya faru, duk yadda yaso ya dinga taya kawu aiki ƙi arɗo yayi yana faɗin hannun sa be gama warke wa ba, seda ya ƙara sati biyu kafin arɗon ya yarda suka dinga tafiya tare, duk da cewa be saba da aikin wahala ba amma he's trying to adopt to his new environment saboda so yake Kisnah ta kuma samun new lesson na rayuwa kafin su bar garin.


Kamar yau da ya dawo da yamma which is past five, duk da basu da agogo amma suna iya predicting lokaci ta hanyar amfani da yanayin garin, fitowar rana, yin zafin, yanayin raguwar hasken ta, fara faɗuwar ta zuwa gushewar ta gaba ɗaya.


A gajiye yake yau tiɓis dan wani yanki arɗo ya shata masa a matsayin gurin da de noma shi kaɗai iya kaci kawai arɗon ya dinga supervising ɗin shi yana gyara masa in da ya kuskure, gurin ya ɗan jima ba'a yi noma a cikin sa ba shiyasa se da yayi aikin gyara shi har na tsawon kwanan uku which today ne cikon na ukun, se kuma a fara gyaran ƙasar wato yi mata kunya kunyar da za'a zuba seeds ɗin.


Ƙarewa ɗakin kallo yake cikin son tabbatar da bata nan duk kuwa da yasan dama zata iya bin Bingel, ganin dai bata nan ɗin yasa ya shiga cire rigar jikin sa da ta kasance irin ta Fulani nan arɗo ya siya masa har set ɗin kayan uku, wanka yake san yi sedai matsalar baze iya wankan tafi ba haka kuma ba su da sabulu wanda arɗo ya siyo musu da ya shiga birni ya ƙare dan sati biyu kenan da siyo shin ga kuma waccan yarinyar da tun da ta ƙyalla ido taga sabulun ta dawo yin wanka so biyu a rana madadin ɗayan da take yi, gashi nan ta ja musu sabulun ya ƙare da wuri duk da ma ba wani sabulu me kyau bane irin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads