Showing 30001 words to 33000 words out of 296907 words
Chapter 11 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
RAYUWA*
*TARE DA*
*ZAZZAFAN SALO NA SOYAYYA MAI RIKITA TUNANI DA TSUNDUMA MAI KARATU CIKIN TAFKIN SHAUQI*
*SUN SAKE SHIRYAWA TSAF,DAUKE DA WANI TARAGO MAI CIKE DA LABARAI MASU ZAZZAFAN ZAFI!!!*
*KIN SHIRYA MADAM?*
*MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*
*DAUD'AR GORA* Billynabdul
*KI KULANI* Missxoxo
*IDON NERA* Mamuhghee
*RUMBUN K'AYA* hafsat rano
*A RUBUCE TAKE* Huguma
*ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number
09033181070
*MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*
09166221261
*Yan NIJER 🇳🇪🇳🇪zaku tuntubi wannan number*
+227 90 16 59 91
*Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾
PAID BOOK
12/2/2023
Afuwan dan Allah banyi editing ba, idan kunga typing errors.
Duk irin hauka da surutan da take zubawa, Aliyu baibi takanta ba yana jinta, ya shirya Tsaf cikin jeans and t-shirt Wanda sukayi masa masifar kyau, yana baza ƙamshi, ya ɗauki tickets ɗinsu ya saka cikin aljihun jeans ɗinsa, ya nufo ƙofar fuska ba wasa, yana takunsa anatse.
Yana buɗe ƙofar suka haɗa idanu, ya sake tamƙe fuska yana kauda idanunsa daga kallonta, yana shirin tsallakata ya wuce,ta zabura ta miƙe cikin kuka tana cukuikuiye shi, tace.
"Idan an isa akaini kwatano abarni ba Nigeria ba, Allah ya tsinan bazan yardaba kawai ka sakeni yanzun nan na kama gabana...."
Ta faɗa cikin fitina da rikici mai ɗaga hankali, tana dukansa.
Dariya ya yi yana manneta da ƙofar ɗakin.
Rungumata ya yi yana rufe mata baki cikin taushin murya ƙasa-ƙasa yake faɗin.
"Astagfirullah na yafe miki My zumaty kuma bazan sake ba, haka bazan kaiki Nigeria ba, Ni dake mutu ka raba Takalmin kaza."
Ya faɗa yana sumbatar goshinta.
Kuka take tana dukansa tare da faɗin.
"Ni bana sonka Aliyu sai fa ka sakeni ko kai maye wallahi...."
Finkiceta ya yi cikin ɓacin rai yajata ya wurgata saman kujera kafin ya yinƙuro yasa kai ya fice ya murza mata key ta waje ya tafi.
Aguje ta miƙe tana faɗin.
"Ni kakeson nakasawa sabida nace bana sonka? Toh wlh kaje ka dawo ina jiranka, Ni wlh bazan zauna mijin ƙanwata ba."
Ta faɗa tana komawa ta zauna tana kuka dan taji ya rufeta ta wajen.
Aliyu fitowa Alhj Ahmed da yake kiransa cikin mota ya shiga suka tafi.
Wajen cira tickets suka tafi, aka masa canji zuwa Cotonou, Wanda jirgin sai zuwa dare zai tashi zuwa Cotonou.
Daga can Aliyu pharmacy ya biya ya siyi wani magani...🐱
★★★
*Nigeria*
Tun safe su Auwal Jawad Hassan Hussaina su Mubina Anwar Yasmin, suka zo ganin little Aliyu, fafur yaƙi yarda dasu, sbd bai sansu ba haka suka ƙari zamansu bayan sun gaisa da Aalimah suka tafi.
Jawad sai neman Aliyu yake awaya baya samunsa.
Abie ma tun jiya yake nemansa awaya baya samunsa hankalinsa duk atashe.
Aalimah kwance cikin ɗakinsu ta yi ƙarya ciwon kai, dan ta samu ta huta ita ɗaya, magani Baabah Bintu ta bata ta sha.
Aliyu yana jikinta, yana zuba mata surutu, yana dariya sai turmusarta yake,.
Aalimah taja hancinsa wanda baida maraba da JAANA ɗinta, tana zubar da hawaye, tausayin kanta take, sbd yadda takejin kishin mijinta, ta kuma san wacece Auntie Asmy bazata iya kishi da ita ba, tasha gabanta a komai.
Cikin ƙarfafa zuciyarta tace.
"Astagfirullah, yq ya Ubangiji Sarkin sammai da ƙasai ka bani ikon amsar ƙaddarata, na jure nayi tawakali na amshi ƙaddaramu auren miji ɗaya nida Auntie Asma'u, Allah ka bani juriyar ɓoye damuwata, haƙiƙa Auntie dasu Baabah sunfi ƙarfi komai awajena, sunmin halacci sun riƙe ba nuna banbanci sai ma nace sunfi sona akan sauran yaran anya idan sun gane ina kishin mijina ban butulce musu ba?'
Ta faɗa tana share hawayen fuskarta tana rungume Aliyu da yake tambayarta.
"Momy kukan me kikeyi? Kiyi shiru kinji"
Aalimah batasan me yace ba, ta yi dai murmushin yaƙe tana sumbatar kumatunsa, tace.
"I love You."
Shima ya sumbaceta yace.
"I love You Momy."
Sukayi dariya suna rungume juna.
Dai-dai lokacin Baabah Bintu da Ammie suka shigo da sallama, dan duba jikin nata.
Aalimah ta amsa tana murmushi tana gyara zamanta da cewa"Kai sai son Jiki koh Aliyu?"
Baabah Bintu tace.
"Aalimah ya kan naki?"
"Da sauƙi Baabah ina ƙoƙarin fitowa wajan Aliyu ya maƙaleni."
Ammie da Yaren Mali tace.
Aliyu taso muje kaci biscuits kabar Momy ta huta koh?"
Da yake Ammie ce bai musaba ya miƙe yana dariya ya kama hannun Ammie suka fice.
Aalimah cike da mamaki tace.
"Baabah kinga baya ƙin Ammie ko me tace masa oho ya bita."
Baabah Bintu ta zauna kusan Aalimah tana kamo hannunta tace.
"Aalimah! Ina me ƙara baki haƙuri akan abinda ya faru..."
Baki Alimah ta rufe mata da tafin hannunta, tace.
"Wlh Baabah banajin daɗin haƙurin da kuke bani, hakan ɗazu yaya Murtala ya yi ta bani haƙuri wai shine ya matsa akayi auren ganin halin da Auntie Asma'u take ciki. Toh wa ya isa yaja da hukuncin ALLAH, wlh Ni ban riƙeku ba Baabah."
Baabah Bintu ta rungumeta tana saka mata albarka.
★
Acan G.R.A
Granny ta bugewa Abie hankali harda kuka, sai an nomo mata Aliyu ta waya idan kuma wani abun ne ya samesa a faɗa mata.
Daƙyar ya samu ya lallaɓata sai fatar majina take.
★
Aliyu sai da sukayi ɗan yawo da Alhj Ahmed kafin ya dawo gida, bayan ya gama shirya mata tuggu ahanya yadda har su isa Cotonou bata wani kuzari bare ta yi masa masifar da ta saba.
Zaune take a falon ƙafa ɗaya kan ɗaya tana hura hanci, ya shigo fuskarshi babu wasa, yana riƙe da leda ƙasa² ya yi sallama.
Kallon ƙasa da sama ta masa ta kauda kanta tana amsa sallamar acikin zuciyarta.
Tsabar neman magana ya ajiye ledar akan table cikin kakkausar murya yadda zai ƙufular da ita ta yi abinda yake son yace.
"Malama karki kuskura ki shamin drinks ɗina, ban siyo da rabonki ba, tunda bakya ganina da daraja, masifa kika saka gaba, da tashn hankali."
Ya faɗa yana zungurinta akai ya nufi Bedroom Yana danne dariyarsa, sabida ganin yadda ta harzuƙa tana zazzaro masa idanunta, amman batace komai ba.
Yana shigewa ta buɗe ledar tana faɗin.
"Sai an sha ɗin kayi abinda zakayi."
Ta faɗa tana ɗaukan Apple ta fara ci ta miƙe ta nufi kitchen ta ɗauko cup ta buɗe drink ɗin ta cika cup ta shanye ta ƙara wani, sai da taji kamar cikin zai fashe tabar ɗan guntu, ta kama Apples ɗin duk ta saka musu haƙuri ta ɓatasu sauran drink ɗin ta juyeshi cikin cup ta barsa ta koma ta yi kwanciyarta, tana kallon Tv.
Aliyu duk abinda take yana kallonta ya laɓe bayan ƙofar, dariya kawai yake ƙasa-ƙasa yadda bazata jisa ba.
Sannu ahankali Asma'u ta dinga jin wata irin fitinanniyar kasala da bacci sai hammma take tana miƙa tana lumshe idanunta.
Ganin hakan ya saka Aliyu fitowa falon.
Daga nesa yace.
"Kai-kai-kai! Waye me wannan ɓarnar haka?"
Ya faɗa yana zama kusanta yana kallonta.
Idanunta alumshe cikin wata irin murya kamar ƴar maye tace.
"Nice me ka isa kayi? Ko zaka ramane?"
Aliyu ya ƙyalƙyale da dariya yana kwantowa jikinta yana riƙe ƙugunta ya ɗago kanta da hannunsa ɗayan yana kallonta ƙasa-ƙasa yace.
"Buɗe idanunki maras kunya yanzu dai dan kin isa kiyi tijarar, ɓarnarki ta ja miki ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya My Honey wife Aunt Asmy darling masoyiya ya dai? Zakiyi bacci ne?"
Ya faɗa yana lasar wuyanta zuwa marabar ƙirjinta.
So take ta tureshi ta kasa, tace.
"Baby jikina ƙaiƙayi yake min bacci nakeji, Baby ka ciremin kasala wayyo ƙaiƙayi ko ina yake min"
Ta faɗa cikin wata irin murya kamar ƴar maye, tana rungumesa tana hawaye, tana sakin nishi.
Aliyu sai yaji matsakaicin tausayinta ya kamshi, ya shiga shafa jikinta yana sosa mata cikin wani irin salo, yana manna bakinsa akan kunnenta, anutse yace.
I'm sorry my Asmy darling my wife ke ɗin ce Zuma sai da wuta, fitinarki ta yi yawa idan ba haka na miki bazaki bari mutafi lafiya ba."
Ya faɗa yana cire mata kayan jikinta baki ɗaya yana bin jikinta da wata irin susa yana kissing nata anutse.
Numfashi take saukewa cike da shagwaɓa ga mayen da take ciki ta fara miƙa tana kiransa.
"Aliyu Babyna! Ina sonka zaka bani Babies? Ina son na haifama yara dayawa, dan Allah karka sakeni kaji Baby Baban Babies Nah kaba Aalimah haƙuri kace nima bansan lokacin da na kamu da matsanaiciyar ƙaunarka ba, tamin uzuri ba laifi na bane ta kamo so ta basa kashi kaji Babynah?"
Aliyu yace.
"Yaa Ilahi! WOW! Mah Asmy masoyiya zumata, irin wannan ƙauna, Alhamdulillah ai kuwa zanyi ta banka wannan magani a juice kiyi ta sambaɗo Wannan kalaman soyayyar masu neman su zautani, muahhhh my Asmy darling masoyiyata."
Ya faɗa yana kallonta tana sauke numfashi ta yi bacci.
Lisp ɗinta ya tsotsa kaɗan ya saki yana bin jikinta da wani irin fitinannan kallo yana shafata ahankali, ya cicciɓi abarsa ya shige Bedroom, ya sakata mata rigar bacci ya rungumeta yana sakin murmushi na zallar farin ciki...
Har dare Asma'u suna shirin tafiya bata dawo hayyacinta ba sai yadda Aliyu ya yi da ita tana maƙale jikinsa tana zuba masa sambatu maye.
Shi ya shiryata Tsaf cikin shirin tafiya kafin Alhj Ahmed ya iso ɗaukan su.
Shima ya shirya ƙarfe tara da rabi suna Airport.
Aliyu yama Alhj Ahmed godiya sosai da fatan alkhairi arayuwarsa da irin yadda ya karramasu ba kowa bane awannan zamanin zai maka irin wannan mutuntawar ba dangin iya bare na Baba.
Asma'u tana jikin Aliyu a cikin jirgi, daƙyar Aliyu ya samu taci abinci da aka raba musu acikin jirgin, ta koma bacci tana masa sambatun akan kar ya maidata Nigeria zata zauna da shi.
Aliyu murmushi kawai yake...
Tsakiyar dare suka shigo garin Cotonou.
Taxi Aliyu ya ɗauka har gida.
Asma'u har yanzu bata saku ba, bacci take abunta, ajikinsa akan bed ɗinsa shima agajiye yake baccin ya ɗauke shi.
★
Washegari bayan ya yi sallar asuba ya takura Asma'u ta tashi dana yin sallah.
A lokacin, ta fara sakuwa, sai dai batada ƙarfin jiki, batayi masa rashin mutunci ba, har tayi.
Zaune take tana azkhar yunwa takeji kamar zataci babu,, cikin sanyin murya ya waigo tana kallonsa ashagwaɓe
"Ni yinwa nakeji sosai."
Aliyue zaune saman bed ya kunna wayarsa wadda ya kasheta tun shekaran jiya a Mali tunda layin ba yayi acan.
Kallonta ya yi cike da ƙaunarta anutse yace.
"Ok zo nan Mah Darling Asmy."
Kafaɗa ta maƙale tana hararensa tace.
"Bazan zo kawai ka tashi ka samomin abinda zanci, kuma azo amaidani ƙasata."
Aliyu ya yi dialing number Mama Barira cikin ikon ALLAH tana fara ringing ta ɗaga tare da Sallama.
Aliyu ya amsa yana gaisheta.
"Mama ina kwana? Ya mutan gidan? Zanzo in Sha Allah anjima nida Asma'u."
Daga can mama Barira tace.
"Kai masha ALLAH naji daɗi toh sai kunzo."
Katse kiran ya yi yana dialing number Abie.
Bugu ɗaya Abie ya ɗaga daga can yana faɗin.
"Haydar! Kana lafiya kuwa, yau kwana biyu ina nemanka ba dare ba rana, nida mahaifiyarka ga Umma ta tayar min da hankali sai rigima take harda kuka."
Aliyu ya kwantar da murya ƙasa, yace.
"Abie don Allah kayi haƙuri munje Mali ne neman Aalimah ashe sun taho Nigeria nima yau nake zauwa Asma'u batada lafiya ne bazata iya zuwaba..."
Ya faɗa yana saukowa ya fice da sauri ganin ta miƙe ta nufosa tana masifa duk da bata kuzari.
Key ya murzawa ƙofar ya nufi falo.
Abie yace.
"Subahanallahi Allah bata lafiya ya jikin nata? Alhamdulillah fa ga Aalimah da Aliyu ƙarami masha ALLAH, kayi ƙoƙari ka taho dan Allah yau ɗin tunda akwai me kula da Asma'un ko tana matsa ne?"
Aliyu yace.
"A'a da sauƙi Abie."
"Ok toh kayi ƙoƙari yau ka taho yarinyar nan taban tausayi wlh, da gani ƙarfin hali takeyi, tana son ganinka kai da ƴar uwata tunda batada lfy ka barta kai ka taho ka duba matarka da ɗanka wanda komai naka bai bari ba."
Aliyu cikin zallar farin cikin labarin mahaifinsa yace
"Ok Abie in Sha Allah yau ina tafe."
Hira sukayi sosai da mahaifinsa ya sauka downstairs, ya kaiwa Granny wayan, sukayi magana ya lallaɓata yace yau komin dare zai sauka Nigeria.
Granny cikin jin daɗi tace.
"Yawwa dan Allah kazo Allah ya.kawoka lafiya, ka gaishemin da Asma'u."
Haka suka sha fira ya mata sallama ya su kayi sallama, ya kira MAAMAH, wacce take ɗakinta bata jima da idar da sallah ba.
Ganin kiran Aliyu MAAMAH ta ɗaga tana faɗin.
"Aliyu kana lafiya kuwa?"
Aliyu yace.
"Afuwan MAAMAH nayi tafiya ne, zuwa Mali yau in sha Allah zan taho Nigeria anjima zanje nayi booking din ticket, MAAMAH yasu Mubina?"
MAAMAH tace.
"Kowa lafiya lau Aliyu Alhamdulillah tunda kana lafiya, toh me kaje yi Mali?"
Aliyu bai ɓoye mata komai ba ya faɗa.
Tace.
"Alhamdulillah! Kaga yanzu sai ka saketa tunda ta dawo hayyacinta, kuma matarka ta bayyana harda tsarabar zankaɗeɗan saurayi."
Aliyu yace.
"MAAMAH idan nazo zamuyi magana bari na sha tea cikina sai murɗawa yake..."
Ahaka ya samu sukayi sallama ya katse kiran, yana shafa kansa.
Ƙofar ya buɗe tana tsaye bakin ƙofar ta faɗa jikinsa tana sakin kuka tace.
"Aliyu ka cuceni me ka bani jikina ba ƙwari haka? Aliyu yinwa nakeji."
Ɗaukanta ya yi yana faɗin.
"I'm sorry my Zuman Haydar muje na dafa miki tea kisha please bari kukan zakije Nigeria uhmm?"
Asma'u tana kwatar da kanta ƙirjinsa ta ɗaga kanta...
Da kasan ya dafa mata tea ya soya mata ƙwai, tana gama breakfast sai bacci ya hana bacci ta hanyar cire mata kayan jikinta, ya shige bathroom da ita.
Wanka sukayi tana cikin jikinsa irin abubuwan da yake mata ya sakata wartsakewa ta biye masa tana amsar saƙon nasa...
11 am, ya lallaɓata suka tafi gidansu mama Barira, Amma sai da ya biya ya yi booking ticket ɗinsa.
Zazzaune suke Asma'u tana kallon Mama Barira ita dai bata santaba sun dai gaisa.
Aliyu yace.
"Mama Asma'u fa ta warke kina ganin tana nuna miki rashin sani."
Mama Barira tace.
"Abinda zan faɗa kenan Aliyu masha Allah naji daɗi sosai, wlh Allah ya kiyaye gaba."
Aliyu yace.
"Mama! Daman zanyi tafiyane inason ki koma can gida ku zauna kafin nazo mu wuce Nigeria."
Asma'u ta ɗago tana kallonsa tace.
"Wlh bazan zauna ba kawai malam kaini ƙasata...."
Mama tace.
"Haba! Asma'u! Babu kyau miji yana magana kina maida masa, kefa ba yarinya bace.
Aliyu kuje zanzo anjima da yaushe zaka tafin?"
Aliyu yace.
"Anjima ƙarfe biyar jirgin zai tashi."
Mama tace.
"Ok zanzo anjima bayan sallar azuhur, Asma'u! Inada fira dake dayawa idan nazo amman sai Aliyun ya tafi."
Asma'u kamar zata fashe da kuka tace.
"Tom Mama."
Aliyu yaji daɗi sosai ya kama hannayenta ta miƙe yace.
mun tafi sai kinzo."
Mama Barira tace.
"Allah ya muku Albarka..."
Ko ahanya Asma'u masifa ta kama masa tana faɗin.
"Akan me zaka min haka kuma ina ne ma zakaje ka barni?"
Murmushi ya saki yana murza tafin hannunta yace.
"Ghana zanje ganin wata mota na dawo, sai mutafi Nigeria Mah Asmy masoyiya zumata ki rage rikici kuma dan Allah ki nutsu ki saurari abinda Mama zata faɗa miki."
Baki ta zumɓuro gaba batayi magana ba.
BOWOOODEE jiya iyau duk yadda ake mata alluran bacci, bai hanaba ta sake jirɗe kayar, wanda ayanzu ya kai wajen baya ɗoruwa, cikin ƴan kwanakin da tayi asibitin har likitocin sun ce sun gaji a canza mata asibiti, bazasu iyaba, sabida kafar ta fara ruɓewa.
Koda sukazo gida ganin zata fara masa iskanci ya lallaɓata ya banka mata maganin kasala da bacci, ya samu ya yi romantic ɗinta mai wuyar faɗa har yakai ya kusanceta ta gama gigice masa tana masa kuka tare da surutai sosai Aliyu ya kashe arna yana mata kalaman soyayya tare da sambatu.
Koda suka nutsu Asma'u ta yi bacci daƙyar ya samu ya mata wanka Tsarki ya saka mata rigar bacci ya kwantar da ita, ya shiga shirya kayansa bayan ya kammala ya cire sim ɗinsa ɗaya dan barmata wayan da zai kirata, sai ya tuna akwai fa matsala gwara ya kirata awayan Mama Barira suna magana.
Kamar yadda mama Barira tace bayan sallar azuhur zata zo ƙarfe uku tazo Asma'u na bacci sun taɓa hira da Aliyu ya zayyane mata komai akan tafiyar da zaiyi can Nigeria.
Mama tace.
"Tabbas kayi tunani hakan ya yi kafin ka dawo in sha Allah komai ya daidaita tsakaninku kasan dabarar da zan shiryama?"
Aliyu yace.
"A'a mama sai kin faɗa."
Dariya ta yi tace.
"Kawo kunnenka ɗana."
Aliyu ya beƙa mata kunnensa ta masa magana.
"Idanu ya zaro yana dariya yace.
"Kai mama amman na gode fa sosai idan haka ta faru bansan irin farin cikin da zanyi ba..."
Bayan sun gama shirya komai, ya miƙe.
Ɗakin ya shiga ya ajiye mata kuɗi masu yawa ya kwanta ya rungumeta ya kissing bakinta kamar zai cinye mata baki.
Sukayi sallama da mama Barira ya bata kuɗaɗe masu yawa, yace sai sunyi waya, har wajen mota ta rakashi kafin ta dawo ciki ta zauna tana jiran tashin Asma'u...
Isma'il ya kai Aliyu airport ya dawo da motar gida.
Ƙarfe biyar da rabi Jirginsu Aliyu ya ɗaga zuwa Nigeria....
_ƘADDARAMU CE AUREN MIJI ƊAYA Mallakin Rahma Oum Farisah NE...🖊️_
Littafin kuɗi ne *09030159301*
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: huguma*
Page 16
Tunda ya fita yaso miqa mimi wajen hajiya sai ya wuce,idan ya dawo ya dauketa su wuce gida,amma tun baiyi nisa ba ogansa yayi kiransa,yayi shigowar ba zata yankinsu,don haka ya wuce da ita,sai ya ajjiyeta wajen rose abokiyar aikinsu ce,babbar macace haka,tana da matuqar kirki da son yara,sai yamma sosai sannan suka gama,ya dauketa suka yo gidan hajiyan.
A qofar gida yayi parking,ya buda murfin motar ya fita ya zagaya ya fiddo mimi,yana riqe da hannunta suna shiga cikin gidan,tana basu labarin rose da irin abubuwan data siya mata,yana saurarenta yana murmushi,yaransa sune ke debe masa mafi yawa daga damuwae hafsat.
Dai dai lokacin da widad ke daura alwala bakin famfon dake farfajiyar gidan,ta gama wanke qafafuwanta kenan tana gyara daurin dankwalinta gizo gizo ya taho,fallatsin ruwa yasa ya qara gudu,take ta rude,sai taga kamar kanta zaiyo,wannan yasa ta saki qara sannan kuma ta buga tsalle tana komawa gefe,bata dora ko ina ba sai a gabansa ba tare data lura da waye ke tsaye a wajen ba,saboda hankalinta gaba daya yana kan gizo gizon.
Baya yaja yana bata fuska gami da dubanta,baya iya ganin fuskarta,sai sassalkar sumarta data yiwa kanta rumfa,sanadin dankwalinta da ya zame yake kuma riqe a hannunta tana ci gaba da kallon gizo gizon
"Allah yasa bai tabani ba" yaji ta fadi tana ci gaba da maida daurin dankwalinta,wannan ya alamta masa ma batasan me tayi ba,sai ya kama hannun mimi suka shige cikin falo.
"Yau kice a gidan kishiyata,ko batan kai kikayi?" Hajiya ta fada cikin dariya,yayin da su nujood dake falon suka fara gaidashi,yana amsa