Header Ads
Showing 201001 words to 204000 words out of 296907 words

Chapter 68 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

hakanne,kuma ma kinsan me?" Kaita girgiza tana sharar qwalla,sai ya juyo yana fuskantarta sosai

"Sanda kika gudu kano?" Saita gyada kai tana dubansa

"Abba da kansa ya kirani yace nayi wannan abun fa da bakiso din" dukka idanunta ta fidda waje kamar zasu fado tana kallonsa a tsorace,ya jijjiga mata kai

"Da gaske nake" ya sake fada yana danne dariyarsa,bai ankara ba ya takai masa duka tana sake fashewa da wani kukan a sakalce

"Allah abbana ba dan iska bane da zaice maka haka" sosai yau din take sashi dariya,ya kare dukan da daya hannun yana dariya tare da fadin

"Allah.....Allah kinji nace Allah" ta sanshi farin sani,kaifi daya ne,baya qarya,yana fadin hakan sai kunya ta kamata,ta kifa kanta a cinya tana juya yadda abban nata zaice haka,yanzu.kowa.kenan yasan abinda suke aikatawa?,tana jinsa yanata magana amma bata dago ba bare ta amsa,yana dariya qasa qasa ya tashi motar sukabar asibitin,ransa fes,zuciyarsa qal,wani farinciki daya jima rabon da yaji irinsa ya cika masa zuciya,har hakan yana bayyana kansa saman fuskarsa.

Saida sukayi nisa a tafiyar yace

"Kona ajjiyeki gidan hajiya?" Ya fadi hakanne saboda yadda yaga sam.batason zaman gidan nasu,saita girgiza kai da sauri

"Aah,nidai ka kaini gida" murmushi ya subuce masa,ya gane mai take gudu,kada hajiya ta gano tana da ciki,daga haka yabar zancan ya dauke kan motar suka nufi gida.

Sanda ya tsaida motar da kansa ya dauki hand bag dinta yana riqe da ita zuwa ciki,ta langabe kai tana kallonsa

"Ka bani,zan iya dauka" kai ya girgiza idanunsa cikin nata,yana jin wata qaunarta tana fusgarsa

"Ban yarda ba baby,dama naji a jikina,wannan rashin lafiyan akwai dalili,muje kawai,ko na daukeki?" Ya fadi shima yana langabar dakai,kunya ya bata,ta kauda kanta gefe tana gulmarsa cikin ranta,wai shi kam bayajin kunya ne ma wai?,kamar ba ciki yayi mata ba?.

Kamar yasan maganar da takeyi ya saki murmushi kadan,ya kama hannunta ya matsa kadan yana cewa

"Muje baby".

Sanda suke shiga din akan idanun hafsat dake tsaye bakin window,tunda suka fita ta kasa zama,zuciyara nata qiyasta mata gurare daban daban da zasu iya zuwa,tana goye da shukra dake ta faman rigima,ji take kaman ta yago yarinya ta ajjiyeta,qunqunin yarinyar har tsakiyar kwanyarta,idanunta suka sauka kan handbag din widad da hannayensu dake sarqafe waje guda.

Wani matsanancin qunci zuciyarta ta shiga,duk yadda taso daurewa amma ta kasa,ta saki ashar,kasheta mutanen nan sukeson yi?,bayan abinda abbas din ya aikata mata shine zasuci gaba da sabgarsu kamar ma ba'a yi mata komai cikin gidan ba?,ba zata iya dauka ba,dole kowa yasan an tabota,sai kawai ta kunce yarinyar ta aza saman kujera ta nufi qofa da wani irin mugun sauri.

Idanunsa ya lumshe kadan,yana tsaye saman kanta yana mata wani duba dake cike da shauqinta,ko yaya ta motsa sai taja hankalinsa

"Zan dan fita,amma bazan jima ba zan dawo,me kike buqata?" Ya qarashe fada yana ritsata da idanunsa masu matuqar kwarjini da jan hankali,sai tadan rufe idanunta kadan ta girgiza kai

"Babu komai"

"Really?" Ya tambayeta yana dubanta,kai ta sake gyada masa

"Okay.....zan tafi" ya sake maimaitawa,saita sake lumshe idonta,tasna me.yakeso,amma jikinta a mace yake murus,ta gyara zamanta sosai ta nutse cikin kujerar sannan tace

"A dawo lafiya"

"Au 'yar hakace yau?" Murmushi tayi kawai tana boye fuskarta,saiya saki wani murmushin,ya duqa kadan a tausashe yayi kissing goshinta sannan yace

"Take care of yourself" kai ta jinjina,sai daya juya sannan ta bishi da kallo,zuciyarta na gaya mata wai da gaske ba abun kunya sukayi ba,ta dora hannunta saman cikinta a hankali tana shafawa cike da mamaki da kuma tsoron cewa wai ciki ne a jikinta.

Dai dai sanda muryar hafsat ta ratso har cikin falon nata da wani irin amo,sai ta bude idonta a hankali tana saurarenta sanda take magana cikin rawar murya

"Wallahi bazan yafe wannan zaluncin ba,sai Allah yayi min sakayya" wani mugun tsaki widad din taja tana tabe baki gami da gyara kwanciyarta cikin kujerar,ita gaba daya mutuncin matar ya gama zubewa a idanunta,tunda take bata taba ganin yadda akema babba rashin kunya ba kamar yadda itadin taga tana yiwa abbansu mimin,ko babu komai aiya girmeta,kuma ko ummu da take tsohuwa ai tana ganin yadda take girmama alhaji,har tabar gidansu bata taba gani ta karba abu daga hannunsa daga tsaye ba,ko ya fada tace a'ah, miqewa tayi cak tana daukar jakarta ta wuce bedroom dinta,haka kawai taji batason jin wata hayaniya kusa da ita.

Hannu daya abbas ya sanya cikin zallar bacin rai ya fincikota,ya riqeta gam yana tafe riqe da ita,bai tsaya ko ina ba sai da yakai sassanta ya watsar mata da hannun cikin falon,da yatsa ya nunata

"Wannan ya zamana shine lokaci na qarshe da zaki qara gangancin cewa zaki shiga sashenta ko zaki tabata,daga lokacin da kikayi wannan kuskuren zaki fahimci baki da wayo,tunda na fahimci sauna ce ke shashasha wadda batasan girmanta ba" sosai maganarsa ta doketa kamar saukar mashi saman zuciyarta,ita din abbas yake cewa sauna shashasha?

"Kowanne suna kakeso ka kirani dashi,daidanka ne,amma bazan fasa neman haqqina ba"

"Idan kika fasa neman haqqinki kin raina Allah" kalmar da tasa ta bishi galala da kallo har ya fice,sai ta sake fashewa da kuka,dole tayi iya yinta taga ta tarwatsa farincikinsu,ba zata zauna ita kadai bacin rai ya hallakata ba.

Yana tafe zuciyarsa cike da bacin rai,mahaifin hafsat shi daya yake tunawa,mutumin kirki da kowa ya yaba halayyarsa kafin barinsa duniya,yana sonsa yana girmamashi,har yau yana tuna haquri na qarshe daya bashi a kanta kafin barinsa duniya da 'yan awanni,yaja wani dogon tsaki,xuciyarsa na ayyana masa hukunci kala daban daban da zai iya dauka a kanta.

A hankali kuma yaji yana sauka musamman daya tuna kyautar da Allah yayi masa a yau daga wajen halitta mafi soyuwa cikin rayuwarsa,sai yaji dukkan haukan hafsat din wani abune mara muhimmanci da zai iya tattarasu ya watsa kwandon shara,idan ta gaji ta sauke kamar yadda ta saba.

*******Cikin kwanakin da sukayi cikin gidan kafin tashinsu saudiyya dan qaramin yaqi aka dinga gwabzawa tsakanin abbas da hafsat din,kullum cikin kuka qorafi da masifa,dai dai sanda 'yan abun nasa suka motsa(miskilanci),yayi watsin tsiya da ita,tamkar ma ba dashi take ba.

Ta fannin widad ma sai tayi kamar batasan me ake ba,dama ita dimma ba baya bace wajen miskilancin,bare a yanzun da take mugun jin xafin mummy hafsat din haka kawai,ta tsani ta ganta tare da uncle din nata,tana dannewa ne tayi kamar bai dameta ba tunda batasan ainihin me yasa takejin hakan ba,uwa uba ko meye zatayi saidai ta jiyota daha sashensa sashenta ko.farfajiyar gidan,bata doso sassanta,wannan yasa bata dameta ba,a kullum tunaninta da zuluminta sanda kowa zaisan tana da ciki,cikin wata irin wauta dake sanya abbas din ya qunshe kansa yayita mata dariya,a fuska kuma ya tayata jimami da alhini kamar gaske.

A lokacin hafsat din ji take kamar zata mutu,yaqi kulata sannan widad din da taso rage zafi da ita ya mata shamakin da ko giyar wake tasha ba zata doshi sassanta ba,ta sanshi farin sani,yana da kawaici yana da alkunya,amma duk sanda ka sake ka turashi inda bai kamata ka turashi din ba.....to kuwa abinda zai biyo baya bashi da sauqi.

Duk haukar da hafsat din keyi hakan bai canza komai ba,don kuwa kwanakinsu biyar suka wuce kano,kai tsaye kuma sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na mallam aminu kano.

Sosai widad din tayi mamakin ganin 'yan gidansu acan suna jiransu,tayi farinciki sosai amma kuma abinda tasan tana tattare dashi ya hanata sakewa,sai qumbiya qumbiya takeyi,duk kuwa da cewa cikin abaya sakakkiya take da hijabin daya tsaya mata iya qugu saqar qasar indonesia,wanda ya sake fitar da zallar kyanta da kuma yadda ta sake cika ta kuma sake yin kyau.

Duk wani motsinta yana kan idanun abbas har sukayi sallama da 'yan gidan nasu,suka kuma bi ayarin tawagar mai girma governor din bauchi wadda kusan duka iyalinsa ne da manya manyan qusoshin gomnati da matayensu.

A darare take gaidasu saboda rashin sabo,uwa uba kusan duka sun girme mata,sa'annin yayyenta ne aurarru,saidai suna da tsananin kirkin daya gaza boyuwa,kallo daya zakayi musu kuma kasan wayayyun mata ne da suka goge da sanin rayuwa,idan akace wayewa bawai wayewa ta rashin kunya rashin da'a da rashin kamun kai ba,a'ah.......wayewa ta ma'ana da sanin darajar kai da kimar kai wadda ke gauraye da ilimin zamani.

Yadda yaga taqi walwala kafin tashinsu sai yaji duk ba dadi,tana tsaye batasan da isowarsa wajen ba

"Suma fa duk sunayi..... qila jiya da daddarema duk sai da sukayi kafin mu taho nan" abinda taji an fada kenan a kunnenta,da mugun hanzari fararen idanunta a waje ta waiwaya,duk da tasan duk duniya babu mai gaya mata hakan kanshi tsaye sai uncle din nata.....uncle abbas dinta,shi dinne,tsaye a bayanta dab da ita,hannayensa zube a aljihun wandon wata lafiyayyar suit da tunda ya sanyata ta gaza dauke idanunta daga kansa har suka iso nan,murmushi ne kwance saman fuskarsa yana jifanta da wani kallo da su kadai sukasan ma'anarsa,saita langabe kai a shagwabe tana dubansa gami da yi masa nuni da mutanen dake gabansu kadan tana masa alamar kada suji fa,kafadunsa duka biyu ya daga ya watsa hannayensa in i don't care manner,ya sake matsowa kadan yana yin qasa da muryarsa

"Wannan tsoron naki xai sa kowa ya sani" ya furta yana duba agogon hannunsa

"Feel free,u are safe dear,okay?" Saita gyada a hankali,ya aika mata da wani murmushi na musamman sannan ya juya,saita sauke ajiyar zuciya ta bishi da kallo.

Batakai ga waiwayo ba taji maganar daya daga cikin matan mai suna hajiya sha'awa

"Badai har kun fara kewar juna ba?" Kunya sosai ta kamata,saita girgiza kai da sauri,kafin ta amsa mata sauran sun iso,cikin mintuna qalilan ta shige cikinsu ta kuma fara sakewa,saboda yadda suketa qoqarin janta a jiki tare da sakata a hirar su,hirar data dinga jin kamar ta girmeta,saboda hira ce ta manyan mata,amma ta qarfi da yaji haka suke sanyata a ciki.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*A RUBUCE TAKE*
(K'addarata) Book 02


Ta hadu da mutane masu karamci,don haka bata wani jima ba ta sake sosai a cikinsu,zamu iya cewa tafiyar ta zame mata wani mabudi na alkhairi tare da sake sanin wacece ita,wanne aiki ne a gabanta?,wanne muhimmanci abbas ke dashi a rayuwarta wanda abaya duka hankalinta bai taba mata hasashen hakan ba,duk kuwa da yadda take jinsa sosai a jikinta zuciyarta da ruhinta.

Abun ya fara ne daga yadda suka maidata kamar qanwarsu,koda a aikin hajjin kowa qoqarin tallafarta tare da nuna mata abubuwa yakeyi,musamman daya zamana ita daya ce farkon zuwa wajen,cikij taimakon Allah sukayi hajjinsu lafiya suka gama,sai ya zaman lokacin komawa gida nigeria kadai ya rage musu.

A sannan taga kowacce hankalinta ya tattaru kan mijinta da sukazo tare,a lokacin suka lura da yadda ita din bata maida hankalinta sosai akan hakan kamar yadda su sukeyi,hajiya sha'awa ita ta fara fahimtar hakan,wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,tuntuni suka gane quruciyar dake dawainiya da ita,wadda wasu abubuwan take gaza yinsu,babu wadda taji kunyarta acikinsu,dukka suka hadu kamar yadda zasu yiwa qannensu uwa daya uba daya suka fara dorata akan sabon saiti.....sabon karatu da sabon darasi.

Bata taba jin kunyar wasu mutane kaf rayuwarta ba irin yadda suka sanyata jin kunya,amma ta dole sukayi mata ta sake ta kuma soma bin karatun nasu.

Abinda bata sani ba kusan kowannensu tasan halayyar hafsat ciki da bai,wannan yasa hatta gidan babu wadda tayi masa zuwa uku, lokacin da sukaga widad din a mazaunin kishiyar hafsat qaunarta da tausayin yadda zata iya zama da ita ya shigesu,wannan yasa suka samu qarfin gwiwar dora mata abubuwa masu nauyi da yawa,wadanda sukasan koda bayan rabuwarsu zai zauna a kanta ya kuma bi jikinta.

Ranar farko kuma karo na farko da taji itama tanason kasancewa da mijinta kamar kowacce mace,ta dauki waya ta kirashi,a sannan suna tare da sauran abokansu da basu taho da matansu ba,saidai dukka kewarta ya isheshi,bayason ya fiya takura mata ko matsanta mata ne kawai,duba da situation din da take ciki,amma he really needs her,kullum kwanan duniya sake shigewa rayuwarsa takeyi.

Cikin karsashi ya daga kiran,saidai muryarta kawai ya kashe masa jiki,ya jingina da kujerar yana saurarenta sanda take magana dashi cikin narke murya

"Bakayi kewata ba ko uncle?" Maganar tata tadan tabashi,har sai daya murmusa

"Har bansan yadda zan misalta miki ba babyn uncle,kawai dai baison takurawa maman baby dama babyn" har ranta taji dadin amsarshi

"Indai hakanne to kazo mu tafi,yau a wajenka zan kwana" mutuwar zaune yayi yana mamaki,widad dinshi ce ke fadar haka da bakinta?,ya rasa amsar da zaya bata har sai data sake cewa

"Hello"

"Than you baby,gani nan zuwa" abinda ya iya fadi kenan jikinsa yana dan rawa kadan,wanda ba lallai ne kai ka fahimta ba

"Ina zuwa" kawai yace musu yana barin wajen.

Kiran wayarsa ya shigo wayarta sanda ta fito daga wanka,tana tsaye jikin madubin dakin nasu tana mulke jikinta da wasu oil perfumes da hajiya fanna ta bata sanda zasu fice subar mata dakin,hajiya khairi ke tsokanar hajiya fanna

"Allah dai yasa ba kyautar turaren banza kikayi mata ba,wala'alla ki dawo ki sameta nade a gado ma tayi baccinta"

"A'ah ai ba za'ayi haka ba,na tabbatar karatunmu yana shiga,nidai ina ganin canji" qas tayi da kanta tana murmushi,dukkaninsu kunyarsu takeji,tunda sun girmeta,tana jinsu suna tsokanarta har suka fice.

Wayar ta daga tace masa gata nan fitowa,ta gama shirinta a nutse,ta dauki duk wani abu da takega ya dace da wanda taga suna dauka suma idan zasu fita din,ita kanta tana jin banbanci da canji a tattare da ita,ta kammala komai a nutse ta fito.

Ko sau daya baiji ya qosa da jiranta ba har ta iso,kasa magana yayi sanda qamshinta ya gaurayeshi,sai ajiyat zuciya mai nauyi daya sauke kawai,suna shiga dakin ya maida qofar ya rufe da wani irin zafin nama,ko ina na jikinsa yana daukan rawa.

Zaucewa ya kusa yi sanda widad din ta miqa masa kanta yadda yakeso,ta kuma hada da bashi gudunmawa,sai kansa gaba daya ya kunce,jikinsa ya dauki rawa tako ina ya fita mata a hayyancinsa.

Bawai shi ba,ko ita din a yau ta gane da banbanci,ta fahimci kuma maganganun su hajiya fanna,bayan komai ya kammala wata kunya ta kamata,yayin da shi kuma ya hanata sakat,bakinsa kuma ya kasa yin shuru,ya dinga zuba sumbatu ya kasa tsuke bakinsa,domin kuwa ta shammace shi fiye da kima,ta kuma kaishi wata duniya da tunda hajiya ta kawoshi sararin duniyar nan bai tana zuwa can din ba,ko sanda yake kidansa yayi rawarsa shi kadai yaya ya qare?,bare yanzu data bashi tallafi ta kuma miqa masa kanta kacokam.

Wannan canji na widad ya tabashi fiye da kima,ya sake kuma cusa wata irin zazzafar soyayyarta a zuciyarsa,ya sake susucewa,har abun yake bawa widad din mamaki,yadda ya dinga cire kudi yana mata siyayya abun sai ya dinga daure mata kai,wanne irin so uncle din nata yake mata haka?.

Ranar da suka fita siyayyar data sake sanya widad sallamawa abbas rayuwarta da jikinta......ta sake yaqini da yadda yake yawan fadin yana sonta,cikin shagon gold ya mallaka mata wata sarqa da farashinta yakai naira dubu dari tara da hamsin.

Kanta ya daure sosai,a wauta da quruciya irin tata tace ba zata karba ba,sai bayan taje dakinsu da ita su hajiya sha'awa suka dinga mata dariya

"Karki qara cewa ba zaki karba ba,tunda ya siya baifi qarfinsa bane,kuma tukuici ne tabbas yake baki,lallai soyayyar da yake miki tana da girma da fadi,saiki sake kula ki kuma tabbatar duk abinda yakeso kina aikatashi sau da qafa,tabbas gaba saikin mallaki abinda yafi haka muddin zaki sallamawa mijinki tare da tsare duk wani abu da yakeso,ki kuma guji wanda bayaso" ta jima a kwance tana tariyo rayuwarta ta baya,da kuma abubuwa da suka faru a yanzu,ko addu'a ce da ummu da mommynta suka yita jaddada mata ta yiwa kanta mijinta da kuma rayuwar aurenta?,ba shakka akwai tasirin addu'ar data dinga yi tuquru,sai gashi tanata ganin abubuwan da ada bata iyasu ba batama san dasu ba.

Ranar da suka qara fita siyayya gefe ta koma kawai tana kallonshi,yadda ya zage yana siyan kayan babies kamar yasan me za'a haifa,har sai data gaji da ganin yadda yake diban kaya kamar baisan ciwon kudinsa ba tayi magana

"Uncle" ta fada a narke

"Baby" ya amsa bayan yabar dukkan abinda yakeyi ya waiwayo yana duban idanunta farare masu haske sosai,wanda suka dan qara girma kadan

"Wai don Allah bakajin kunya?,ciki fa ka yiwa mace" dariyar da bai shiryawa ba ita ta kubce masa,nutsatstsiyar dariya mai wani irin siririn sauti da tasa fararen haqoransa bayyana,sakalci

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads