Showing 198001 words to 201000 words out of 296907 words
Chapter 67 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
canji tattare da ita,idan akwai alamunsa to zasu bincika su dauki matakin da duk hafsat din taso.
Tana parlor tana shayar da baby yusra,su nawwara sunata sabgarsu cikin falon,sassan dai kamar ko yaushe sauqi sai wajen Allah,duk da ta dauko diyar anty ummee ta tayata zama har zuwa sanda zatayi arba'in,to amma itama yarinyar aikij ya mata yawa,abinda taga zata iya shi takeyi.
Ko kusa ko alama bataji alamun shigowarsu ba,don mota ya dauko daga airport,ba kamar yadda ya saba ba,idan flight zai biyo yana kiran umar yazo ya dauka motarsa dake nan ya daukoshi ya kawoshi gida.
Yusra ta cire daga shayarwar da takeyi,idanunta a kansa sanda yaran suketa rige rigen isa wajenshi.
Mummunan kishi ya kama zuciyarta,duk sanda zaizo mata weekend sai taga ya canza,sai taga ya qara fresh ya qara murmurewa fatarsa tayi wani lumaui,komai nasa fes kamar wanda akewa wankan inji.
Qarasowa yayi ya duqa yana shirin karbar yusra,dai dai sanda take masa sannu da zuwa,ya amsa yana dan dauke numfashinsa hadi da daukan yarinyar yana kallonta,tausayinta yana cika zuciyarsa,ba alamun qamshi jikinta bare na mahaifiyarta,yadan ja kumatunta yana mata wasa duk da ba gane komai takeyi ba,yayin da hankalin hafsat ke kansa,tanason jin tare suka zo?.
Amsarta ta fito kuwa sanda mimi ke tambayarsa ina anty widad?,yauma batazo ba?.
Murmushi ya sake,qauna ce sosai da shaquwa me yawa tsakaninsu da widad din,tamkar ma itace ga haifeta ba hafsat din ba
"Tazo,muje ku gaisa" sai ya sanyasu a gaba suka fice,suka bar hafsat da lissafin yadda zata shiga ta ganta din,don yarinyar ya canza hali,wani irin canji da tafi zaton akwai masu zugata na gasken gaske daga gefe,tasan tsaf daga halinta ba zasu hadu ba sai ranar da zata koma Kaduna.
Ya sameta harta cire kayan jikinta,ta saka wata black rmless gown A shape,tabi lafiyayyar farar fatarta ta.kwanta,ya bita da kallo tsigar jikinsa na zubawa,yana jin wani abu mara dadi na masa yawo a rai,yasan yau da gobe duka zaiyi missing dinta,saidai yasan zasu hade a kano,kuma tabbas zaya fanshe kafin su tashi.
Bakinta har kunne ta karba yusra tana mata wasa,ita da mimi da nawwara duka sun zagaye yarinyar,tana mata waqa suna mata amshi,sai ya koma gefe ya harde hannayensa yana kallonsu murmushi yana qwace masa,yana hasashen yaranta kamar haka.
Daga kai tayi suka hada ido,sai ya kashe mata ido daya yana mata murmushi,ta maida masa martani,Allah ya zuba mata son yara,baisan wanne irin son yara gareta ba,abinda ko uwarsu data haifesu bata damu da yi musu ba amma ita saita bata lokaci tana wasa dasu hadi da kula dasu.
Anan yabar mata duka yaran ya wuce sashensa, pampers din yusran da widad din taga ya cika da kashi ta cire mata cikin jin tausayin yarinyar
"Tun dazu da take kuka na cewabmommy kashi tayi sai tace ba yanzu zata cire mata ba" duban mimi widad tayi cikin mamaki,itadai ta sani,yayyenta da matan gidansu duk sanda yaro yayi bayan gida cire masa shi sukeyi,takanji sunce yana cin jikin yaro sai wajen yayi ja ya zama ciwo.
Wanka tayi mata da ruwa mai dumi sosai,ta shafeta da farar powder ta goyata ta fara gyaran sashennata,tana aikin yarannna biye da ita,yau daya nishadinsu ya canza,sashen ba aiki sosai don ba datti bane sai qura,nan da nan ta gama ta cikashi da wannan qamshin da ya zamewa gurin jiki.
Ko kafin ta gama ma yarinyar tayi barci,saita kwantar da ita tayo wankan itama ta sauya kaya ta zura hijab ta tayar da sallah.
Tana idarwa hafsat tana sallama,ta shigo idanunta akan widad din kamar zata cinyeta,bata lura ba don zuciyar a wanke take,ta gaidata ba yabo ba fallasa,ta amsa tana sake qare mata kallo.
Tabbas tayi qiba,ta kuma yi fari sosai fiye da farinta nada,amma kuma sanda ta miqe zata dauko mata yusra dake bacci bataga tudun komai a tare da ita ba,wannan shi ya saka mata shakka a ranta,ta debi yaran suka baro sashen tana lalubar number ummanta.
Bayani tayi mata na canjin data gani din daga wajenta,sannan ta dora mata da
"ta danyi watanni umma da wannan canjin,idan ciki ne ya kamata zuwa yanzu ya fito,amma banga alamar komai tare da ita ba" shuru ta danyi tana nazari,ta sauke ajiyar zuciya sannan tace
"Ba'a nan take ba hafsatu wai an dannewa bodari kai,zanyi magana dashi,kome meye yake akwai su basa rasa ganinsa".
Yana zaune daga bakin gadonsa,hannunsa dauke da tab,yana bibiyar statement na wasu masu laifi dake tsare a hannunsu,hafsat na daga gefe tana lallaba yusra tayi bacci fuskarta aa hade ranta a bace,tunda abbas din ya gaya mata kafin ta iso gadon tayi wanka take kumbure kumbure harta gama ta maida kayan jikinta ta dawo gadon,yayi haka na bawai don yana da bauqatarta ba,kawai ya fuskanci idan ba wanna titsiyen ya fara yi mata ba haka zata ci gaba da tafiya,sau daya ya kalleta bai sake dubanta ba,baisan me yasa har abada take sha'awa shigo masa bedroom da kayan data wuni dasu cikin gida ba,baisan sau nawa zai kwatanta mata bayason hakan ba,a yanzun da yake ganin sauyi daga wajen widad,sai abun ya daina bata ransa,tunda at least yana samun sassauci idan ita din taqiyi masa yadda yakeso,sai mamaki kawai da take bashi,sau tari tafi ganewa ta kwana da tufafinta,atamfa ko shaddar da tasha kwaramniyar yini guda da ita.
Dakin shuru kamar ba kowa har ya gama aikinsa,koda ba aikin yake ba haka zaman yake dama,ita bata iya hira da miji ba,shi kuma dama tun asali miskili ne,yayin da take kallon miskilancinsa a matsayin zallar wulaqanci ne kawai (bata iya tsaiwa ta karanci ya yake).
Tab din ya ajjiye a bedside drawer yana jan duvet dinsa zuwa qugunsa yana kallonta
"Kiyi qoqari gobe da sassafe ki rubuta duk abinda kuke da buqata na kamar wata biyu haka,idan Allah ya kaimu ranar alhamis zamu wuce hajji ni da widad".
Kamar wadda wuta taja ta kalleshi da sauri
"Kai da wa?" Ta sake tambayarsa ba tare data bi takan sauran bayanansa na baya ba,sunan daya fada sai taji kunnenta kamar baiji mata dai dai ba
"Widad" ya sake fada yana kallonta hankalinsa kwance idonsa yana dan lumshewa saboda baccin daya fara ji.
Cikin zafin nama ta miqe ta zauna sosai, kaman zata bige yarinyar saboda yadda ta tashin da sauri
"Kasan me kake cewa abbas?,da widad zaka tafi hajji?" Dubanta yayi
"Me na fada da yake alamta ba cikin hayyacina nake ba?" Yadda yayi maganar cikin bagararwa kamar ba wani mummunan abu ya aikata mata ba,ta tsareshi da ido,wani yayyafin zafi yana sauka daga zuciyarta yana ratsa kowanne sashe na jikinta,tafasa sosai zuciyarta ta dinga yi,ta rasa wacce kalma ce ta dace dashi,saita kuka kawai.ya balle mata,ta miqe tana sauka daga kan gadon cikin hargagi masifa da daga murya ta fara sake masa maganganu marasa dadi,ya rufe ido yana jinta har zuwa sanda tace
"Kuma duk munafukan da suke sake shirya wannan abun Allah ya tsine musu albarka idan basu fasa ba,ni dasu shege ka fasa"
Wata gigiyacciyar tsawa ya daka mata,yana dubanta da idanunsa da suka fito waje
"Shirmenki ya isheni haka,fita ki bani waje shashasha mara hankali,a gabana zaki tsaya kina furta tsinuwa munafukai da sauran shirmenki!,zaki fita ko sai na baki mamaki?" Hannu tasa tana son dauke yusra daga kan gadon,tsananin bacin rai yasa ya janye yarinyar gefe,saita koma ta tsaya tana cewa
"Mamaki kuma na nawa?,aika gama bani mamaki,wallahi tallahi inda nasan haka kake da bazan taba aurenka ba,amma kaje na barka da Allah" ta juya da gudu tana kuka da qaqqarfan sauti ta fice a dakin.
Hannunsa gaba daya qaiqayi yake,tabbas inda wani ne a waje yayi masa hakan yau sai ya gane shayi ruwa ne,bayason shaidan ya dinga tunzarashi ta sanadinta ya zama madoki,sai ya dinga ambatar Hasbunallahu wani'imal wakil.
*********Karfe goma na safiya ta gama shiryawa,tun jiya cikin zumudi ta kwana,tayi zaune a parlor tana jiransa.
Da sallama ya shigo falon,muryarsa tayi laushi sosai saboda baccin da bai samu ba isashe daren jiya,ya zama wani so cool yayi kyau cikin shigar qananun kayan da ba kasafai ya fiya sanyasu ba,yau din yayi amfani da sun glasses wanda zai hanaka gane ainihin qwayar idanunsa,sai ya qara masa wani mugu mugun kyau,har widad ta kasa dauke dubanta daga kansa.
Duk da yadda ya sakaye qwayar idanunsa amma hakan bai hanata ganin canzawar mood dinsa ba
"Oga zumudi..... let's go,banaso rana tayi mana sosai,inason na dawo gida na huta"ya fada yana duba agogon hannunsa.
Tare suka jero zuwa harabar gidan yana riqe ds hand bag dinta tana gyara rolling na mayafinta tana masa shagwabar don Allah idan anzo yin allurar ya tsaya a wajen.
Murmushi ya sake,ko yaushe tabararta na nasarar korar bacin rai ko damuwarsa,wannan ya sanya koda daga office wani abu ya bata ransa,tattara komai yake ya dawo gida,yana da yaqinin zai samu magani sa sassauci,koda batasan me yake damunsa din ba,koda batayi komai da nufin korar bacin ransa ba.
Da kansa ya bude mata seat din motar ta shiga,ya tsugunna ya tattare mata rigarta data fito sannan ya miqa mata hand bag dinta.
Hadawa tayi da hannunsa ta riqe tana kallon qwayar idanunsa
"Me?" Ya tambayeta ganin yadda ta bata fuska
"Smile mana uncle,kayi kyau yau,amma kaqi kayimin dariya.....haba mana uncle" ya qarasa fada a shagwabe.
Don dole bai shirya ba siririn murmushi ya kubce masa,ya duqa a tausashe yayi kissing goshinta sannan ya zagaya ya tayar da motar.
Suman zaune hafsat dake kallonsu ta dakin solar dinsu dake daura da wajen tayi,taji jiri kamar yana dibanta,har sai data samu waje ta zauna ta wucin gadi,kafin kuma kuma ya qwace mata,ta jima zaune a wajen tana kukan,har sai dataji shigowar sale sannan ta miqe tana barin wajen don kada ya sameta a haka raini ya shiga tsakani,saidai tana jin zuciyarta ta tsike gaba daya,zuwa yanzun komai ta fanjama fanjam,don haka wayarta kawai ta dauka ta fara neman number ummanta ba tare data damu da kukan da yusra ke tsalawa ba, wadda ta tashi daga bacci tun dazun taji ba'a Kula da ita ba.
Idanunta fal tsoro,ta waiwaya tana dubansa sanda zata shiga dakin da ake bada rigakafin tana kallonsa
"Please uncle,don Allah ka rakani"
"Muje" ya fada yana maida wayarsa aljihun wandonsa suka shiga dakin a tare.
Yadda taga suna gaisawa da likitar ya tabbatar mata akwai sabo tsakaninsu,tadan kalleshi,abbas din badai miskilanci ba,ya sansu amma ya maze mata,suka hada ido ta masa sing na zan rama,ya dage mata girarsa daya kawai.
Fitsarinta suka fara buqata,tayi ta kawo mata aka bada gwaji.
Gyara zaman glass din fuskarta likitar tayi sannan ta dago kai tana duban abbas din
"Sir,bakasan madam nada juna biyu bane?" Sosai ya kalli likitan,sai ya zare gilashin idanunsa
"Juna biyu?,Kina nufin,she's pregnant?"
"Yes sir.....alamu ma sun nuna kamar yafi wata biyu"
"Ya salam ya Allah"ya fada zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin farinciki,kamar wanda aka yiwa albishir da samun haihuwa karon farko bayan wasu shekaru daya diba yana neman haihuwar ba tare daya samu ba,ya bude idanun nasa fuskarsa na fidda wani irin murmushi yana sauke dubansa ga widad.
*H A F S A T*
Kamar zata zauce sanda taketa kiran ummanta ba tare data daga ba,muryar umman kawai takeson ji ta isar mata da saqon abubuwan da takeso a gabatar mata akan widad din,tana jin idan bata d'ai d'aita rayuwar yarinyar,ta gigita mata rayuwa ba tabbas mata ta rako duniya,indai bata dauki mataki mafi muni a kanta ba bata cika hafsatu ba,yarinyar tayi mata abubuwa masu.muni dake da yawan gaske,ba zata yaba qyaleta ba itama,ta rabata da abu mafi soyuwa a wajenta,halittar da duk duniya ba wadda take qauna sama da ita ABBAS dinta.
Sai data yi mata kira biyar a jere,ana shidan ta dauka,kafin hafsat din tace komai ta rigata
"Yauwa,nima ke naketa nema ai,ina hanyar dawowa daga gun aiki ne......,akwai gagarumar matsala hafsatu,akwai matsala" kalmomin umman nata da kuma tashin hankalin dake cikin nata kwanyar suka hadu suka kusa fasa mata kwanya,saita sulale ta zauna sosai a wajen tana jiran jin gagarumar matsalar dake tunkarosu din.
*A L H A M D U L I L L A H*
*_Masu karatu..... bakuji komai ba,baku karanta komai ba,kawai abinda zance daku shine......kuyi jumirin bibiyata,muje zuwa bayan hutun azumi,in sha Allah ina tafe da kashi na biyu na labarin A RUBUCE TAKE k'addarata,nima ba haka naso ba,amma yanayin yadda labarin ya dauko tunda farko,bazai taba qayatarwa ya bada ma'ana ba sai an cimma gacinsa,zanyi qoqari da ikon Alalh bayan sallar pages din sunfi wadan nan da muka gama tsaho in sha Alllah,fata na Allah ya bamu aron rai da lpy_*
ina muku fatan ALKHAIRI AREWABOOKS FOLLOWERS dina,wadanda baku gajiya da bibiyata, alkhairin Allah ya kaimuku a duk inda kuke,ayi ibada da bukukuwan sallah lafiya,na barku lafiya
*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*A RUBUCE TAKE*
(K'addarata)
*Book 02*
Page 01
Cikin mugun mutuwar jiki kasala da kuma fargaba ta hada kalmomin
"Wacce irin matsala kuma umma?,na shiga uku"
"Malam baiga komai akan yarinyar ba,komai ya rufe masa,bai hangi ciki ba,kamar yadda babu tabbacin babu shi".
Goshinta hafsat ta dafe,tana jin yadda zuciyarta ke tafasa,a zahiri tayi mugun tsanar yarinyar,ta zame mata qarfen qafa sosai,tanason kuma ta zama barazana ga rayuwarta,cikin tsananin fusata tace
"Umma,yayi mata koma meye,duk abinda ya dace da ita da zai d'ai d'aita rayuwarta ayishi,banason ganinta kwata kwata cikin gidan nan,yanzu haka fa abban mimi ya biya mata hajji,aikin hajji zasu tafi" ta qarashe maganar tana barkewa da kuka,don abun yayi mata ciwo ba kadan ba.
Salati umman tata ta sake kamar tana gaban hafsat din
"Kina raye kina kallo?,lallai sai munyi da gaske,sai mun tashi tsaye akan yarinyar nan"
*A B B A S*
"Ya salam" ya fada zuciyarsa na wani irin bugawa da matsanancin farinciki, kamar wanda aka yiwa albishir da samun haihuwa karon farko bayan wasu shekaru daya diba yana neman haihuwar ba tare da samu ba,ya bude idanun nasa fuskarsa na fidda wani irin murmushi yana sauke dubansa ga widad.
Ido suka hada shi da ita,ta narke fuska sosai,dab take da sakin kuka,suna hada idon kuma sai rauninta ya bayyana muraran,yasan tabbas yau akwai daru,amma koma meye a shirye yake daya shanyeshi,ciki a jikinta?,cikin da yasha yi mata wayo yana gaya mata ba tarayyarsu ce zata saka tayi ciki ba,shan ruwa a qoshi ne?,yasan lallai zai sha tuhuma.
Hannu ya miqa mata alamun ta taho har yanzu murmushi kwance bisa fuskarsa,amma sai ta kauda kai hawaye na ziraro mata,yasan za'a rina,yau saita Allahu,ya dinga danne dariyarsa sannan ya.miqe tsam ya isa gabanta,ya tsaya daga gefanta yana riqe da hannunta yana murzawa a hankali cikin nasa,idanunsa akan na dr
"Yanzu ya za'a yi?,ina fatan bazai bada matsala ba wajen tafiya"
"Bana jin gaskiya,zanyi qoqari ayi mata komai ku wuce tare,tunda bai nuna ba" ta fada ita kanta tana mamakin watannin cikin,da kuma yadda ya boye kansa da kyau,iya ganinka ba zaka hangeshi jikinta ba.
Komai da akeyi kawai tana binsa da ido ne, hankalinta gaba daya bai jikinta tunda akayi zancan ciki,tsoro da fargaba gaba daya sun hadu sun lullubeta,har suka gama komai yana riqe da hannunta,ya bude mata gaban mota ta shiga ya maida murfin ya rufe ya zagaya mazauninsa shima.
Ai yana shiga tana fashe masa da kuka,kamar wadda ke jira,ya dakata daga kunna motar ya waiwayo yana dubanta
"Ya salam ya Allah.....menene kuma?,ko wani abun na miki ciwo?"
"Wallahi idan abba yaji ka yimin ciki sai ya kashemu ni da kai" duk yadda yaso ya riqe dariyarsa amma wannan karon ya gaza,dariya ta kubce masa,har sai da yasa zara zaran yatsuntsa ya toshe bakinsa kada cibi ya zama qari,sai yaushe zata gama girma ne?,ashe har yau da sauran quruciyar nan tana nan?,ta yaya zai bullo mata,sai kawai ya juya fuskarsa zuwa kalar alhini shima yana dubanta
"Innalillahi......yanzu ya kike ganin za'a yi?" Da farko dariyarsa ta qular da ita,amma yanzun maganar da yayi saita wanke wancan
"Nima ban sani bafa....duk kaine ka jawo,saida nace banaso,kace wai idan nasha ruwa ne zaizo" ta fada yana harararsa,saiya narke fuska kalar tausayi ya langabar da kai
"To ai nima na zata