Header Ads
Showing 267001 words to 270000 words out of 296907 words

Chapter 90 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

tattare dashi,ya manta rabonsa da cin abinci cikakke,ta riga ta batashi da taste din abincinta mai dadi,damuwa da rashin samun kalar taste dinta yasa ya watsar da lamarin abinci,dole ya cire waya ya kira daya daga cikin yaransa ya gaya musu irin abincin da yakeso.

Ko da aka kawo din ba wani mai yawa yaci ba,cikinsa gaba daya a cushe yake,sai ya ture abincin ya koma ya kwanta kan doguwar kujerar falon,tunani ya masa yawa,a yanzun yake jinsa cikakken maraya gaba da baya.

Sau kusan biyar yana ganin kiran hafsat,saidai yabi wayar da kallo,harta gama ringing dinta ta katse,bayason damuwa a yanzu,don haka bashi sa buqatar daga wayarta.

Daga bangaren hafsat din sai ta dinga jin fargaba da dar dar,amma indai abinda malam ya gaya mata haka yake,me zai hana abbas din daga wayarta,tunda dai lokaci irin wannan da baya da lafiya ta tabbatar yana gida bare tace ya fita Wani aiki na musamman

"Basa qarya a zancensu,tunda ta gayamin hakanne,kawai ki shareshi" zuciyarta ta bata shawara,saita aje wayar taci gaba da sabgarta.

Washegari kafin ya fito ta gama duk abinda zatayi a kitchen din ta dawo daki ta rufe abinta,bata kuma sake fitowa ba sai bayan isha'i data tabbatar ya tafi masallaci sallah,ta zube kwanukan ta debi wasu ta koma.

Cikin kwanaki uku abinda da dawowarta abinda ya dinga faruwa kenan,wani irin zama sukeyi na shariya da fita sabgar juna,saidai widad din ta fishi daukan zafi sosai,don bata fita a dakin sai idan ya fita sallah,da yake har yanzun bai gama warwarewa ba,yana gida yana sake hutawa,ko aiki bai fara fita ba,da zarar ya fita zata fita ta dafa musu abinda zasuci ita da affan ta zuba a cooler ta koma daki,ko wanke wanke taqiyi,haka ta dinga tarawa kitchen din kwanuka itama.

Sau daya da wasa bata taba saka tsintsiyarta ta share falon ba tunda tazo cikin gidan,iya dakin da take ciki kawai take tsaftacewa,tun bai lura ba har ya lura da abinda takeyi shigen na hafsat,don kitchen din ya fara canza launi,haka qura ta fara yiwa gidan yawa,hakanan duk da baida lafiya ya zage ya gyara kitchen din da gidan,yayi tsammanin zata dauki haske ta gyara amma a banza,don ci gaba tayi da batawa tana jibge masa kayan a kitchen din,tun yana ganin zai jure har haqurinsa ya gaza,ya dinga fakonta ta fito amma ko sau daya bata bari hakan ta kasance ba,har ya gama murmurewa ya koma bakin aikinsa.

Randa zai soma fita din haka ya hadawa kansa baqin ruwan shayi a tsaitsaye,yana tsaye a falon yana kurba,gaba daya sai yakejin bashi da sukuni,idanunsa qyar bisa qofar dakin,yana jiyo hayaniyar yaron,bama rashin isashen abinci da baya samu ne damuwarsa ba,wata kewarsu da yaji ta fara shigarsa da gasken gaske,tun bayan da ya duqufa da addu'o'in da aminin mahaifinsa ya bashi bayan zuwansa dubashi,ya kasa jurewa ya ajjiye cup din ya taka zuwa dakin.

Sai da yayi knocking kusan sau biyar sannan aka tambayi waye a daqile

"Kinsan ko waye ai ko ban fada ba" ya amsa mata adan kaurare,sai tayi banza dashi kamar bataji abinda ya fada ba,har sai da ya qosa da tsaiwar ya sake bugawa,amma sai tayi biris dashi

"Open the door malama" ya fada da dan hargagi

"Dakin 'yar kwanan hotel din zaka shiga?,me zakayi da ita kai da kake da kamilar mace a bauchi?" Runtse idanunsa yayi yana jin zafin sunan data kira kanta dashi sannan ya bude a hankali yana aje numfashi

"Stop it......ki budemin qofa kiban affan"

"Affan kuma?,ai yarona ne ni kadai"

"Widad!" Ya kirata da qarfi,sai taqi amsa masa

"Ki budemin qofa nace" nan ma tayi masa shuru,har gwarancin da yaron yakeyi,da alama har yazo bakin qofar ne shima yaji.muryarsa,sai ya zame ya duqa a bakin qofar,yana jin kamar yayi zaana ya tsaga qofar ya shige,ba yaron kadai yayi missing ba,harda mamansa,yana son kallon wannan fuskar tata da ya jima bai gani ba,ya tabbatar ba zata sake ce masa komai ba,haka ya gama tsaiwarsa a wajen,ya juya a hankali ya dauki brief case dinsa ya fita a gidan.

Rana ta farko a office dinsa amma bai iya wanzar da komai ba,shi kansa yasan baiyi tabuka komai ba,tunani fal kwanyarsa,gaba daya yana jin kamar an canzashi ne,kamar ba ainihin abbas ba,yaja tsaki yafi sau dubu,ya yarfa hannuwansa har baisan adadi ba,har cikin zuciyarsa yaji bazai iya jura ba,kawai sai ya dauki wayarsa yayi qundumbala ya kira muhsin.

Kamar komai bai faru ba suka gaisa,sai abbas din ya samu kansa da bawa muhsin haquri

"Ya wuce,amma tabbas saika dage da addu'a abbas,idan ba haka ba mata basu da kirki,zasuyita saka ka kana abu kamar Wani zautacce ko qaramin yaro" ajiyar zuciya ya sauke

"Na gode" ya gaya masa

"Alfarma nake nema don Allah idan zan samu"

"Ba 'yar wannan a tsakaninmu,fadi kawai"

"Maman affan nakeson ka yiwa magana,ta hanani ganin yaron gaba daya,ta takureshi a daki, at least ta sakeshi ya dinga fitowa yana samun wadatacciyar iska" ya fada a mugun karye,karayar da shi kansa baisan ya nunata ba,sai dariya taso kubcewa muhsin,ya fahimci wani abu a cikin muryarsa wanda shi kansa baisan yana bada wannan amon ba,ba affan bane,maman affan din yake kewa gami da qishirwar gani

"Kada ka damu,zan mata magana in sha Allah" yayi masa kuwa godiya sosai sannan sukayi sallama,ya ajjiye wayar yana sauke ajiyar zuciya,sai yake jin wani sassauci cikin ransa,ya jawo system dinsa zai fara rage wasu abubuwan saboda wani dan karsashi yanzun da ya samu,sai kira ya shigo wayarsa,daya duba sai yaga number hafsat ce.

Da kallo yabi wayar yana jin wani abu yana yawo a ransa kafin daga bisani ya daga wayar,cikin salo da kisisinar jin cewa a yanzun ita daya ce a duniyarsa tace

"Barka da yamma,ya gida ya jikin?"

"Alhmdlh,ya yaran?"

"Lafiya lau suke,yaushe zaka shigo?, inaga ya kamata ka taho gida don nafijin dadin kula da kai,ga rashin lafiya sannan kuma kai daya kake zaune ai baiyi ba abun" inda ace yau ya fara sanin halaye da dabi'unta sai yace ta bashi mamaki,wato ita ba zata iya takowa ta iskeshi a inda yake ba inda ace cikin buqatar hakan yake,saidai shi ya dawo ya sameta kenan,bai shirya gaya mata komai a kansa a sannan ba,saboda zuciyarsa ta fara tsara masa wasu abubuwa a kanta,shi yasa ya hana a sanar da ita komai game da abinda yake faruwa,har kuma dawowar widad din

"Bazan iya tahowa yanzu ba,sai na warke sosai sannan"

"K'nnnnn,ai shikenan,nace pampers din nawwara,kudin makarantar yara duka sun qare fa,naji Shuru"

"Zan miki transfer ki siya" ya fada a gajarce,dama abinda takeson ji kenan

"To yayi,sai anjima" ta fadi a gaggauce kamar wadda ake jira.

Wayar yabi da kallo na wasu daqiqu,sai ya tafi contact nasa ya fara lalubar number wayar umar qaninsa.

A ladabce ya gaida yayan nasa yakuma yi masa sannu da jiki

"Kana ina?"

"Ina kasuwa,muna lissafin qarshen shekara zamu danje hutu"

"To yayi,idan kun gama ka ajjiye lissafin a wajenka,zan karba idan na nutsu na duba"

"To yaya"

"Aiki nakeson na baka,amma banason kowa ya sani,inason ya zama sirri tsakanina dakai"

"To yaaya in sha Allah"

"Ka hada kayanka ka koma gida na,karka taho har sai ranar da na umarceka,anjima idan na koma gida zan kiraka nayi maka bayanin abinda nakeso kayimin"

"To shikenan,in sha Allah" yayi masa sallama,ya ajjiye wayar,saiya sake komawa kan system din,maimakon yayi aikin dake kai,sai kawai ya fita,ya saka sunan FAAZ HOTELS ya fara wani sirrintaccen bincike a kansa.



*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 34


Tana kwancen saman gadon tana chart affan yana kwance a gefanta yayi bacci abinsa kira ya shigo wayartata,tadan saki murmushi ganin suna uncle muhsin ta zauna sosai ta daga wayar suka gaisa,cikin hikima ya sako mata zancan abbas din,yadda yaga tana kame kame ya fahimtar dashi gaskiyar zancan,sai ya fara yi mata fada cikin nasiha,nasihar data sanyata zubda qwalla,ya kuma umarceta ta buda qofarta,tabar uba da da suyi harkarsu,shi yaron ba ruwansa a fadansu,wannan tsakaninsu ne,bazai hanata hukunta abbas ba muddin zata huce,amma kada ta sako affan a ciki.

Cikin share qwalla ta bawa uncle muhsin haquri tare da bashi tabbacin ba zata qara ba,ta ajjiye wayar tana sake jin zafin abbas a ranta,a daketa a hanata kuka?,har yana da qwarin gwiwar kaita qara?,saita gyada kai tana cije lebe,ya kirawa kansa ruwa kuwa,lallai ba shakka zata hukuntashi har sai ya gwammace kida da karatu,saita sake daukan wayarta taci gaba da abinda takeyi.

Yayi aikin da yakeson yi sosai,ya kuma hada information masu yawa,wannan yaja masa lokaci,bai fita a office din ba sai da yayi sallar magariba,ko kafin yaje gida ana dab da kiran isha'i.

Komai data saba yi a gidanta na kaduna ta miqe tayi,ta tsaftace gidan saboda ita kanta jurewa take,duk da bata rayuwa a falon amma tana jin ya dameta har ranta,sabo da qazanta masifa ne,kamar yadda sabo da tsafta yakebin jini shima,tayi girkinta amma iya cikinta dana affan,ta gama ta kwashe musu,ta gyara kanta da yaronta,saboda batason abbas din ya shigar mata daki saita dawo falon tana jiran shigowarsa ta bashi affan din ta wuce dakinta abinta,aqalla ai tayi qoqari,ta kuma bi umarnin kawun nata,bata watsa masa qasa a ido ba.

Ya jima zaune cikin motar bayan ya shigo gidan,murfin motar a bude qafarsa daya a waje yana shaqar daddadan qamshin da tun daga harabar gdan kana jiyoshi, qamshin da gaba daya ya gama kashe masa jiki,bai fito ba sai da yaji ana kiran sallar isha'i sannan ya fita,ya daura alwala a famfon harabar gidan ya wuce masallaci.

Rigima yaron yaketa mata,saita sakashi a kafada ta soma zarya dashi,sanye take da doguwar rigar wata atmafa mara nauyi,an mata budadden dinki daga qasa,saman kuma yasha tattara ya zauna dai dai qirjinta.

Tana kawowa bakin qofar zata juya yana buda qofar,suka hada ido ita dashi,yayi wani irin kwarjini na musamman cikin uniform din, hular kayan na riqe a hannunsa,saita janye idanun nata ta juya zuwa ciki affan na qijrinta,yabi bayanta da kallo,ya tako a hankali zuwa cikin falon bakinsa dauke da sallama,ta duqa tana ajjiye yaron gami da amsa sallamar tasa muryarta can qasan maqoshinta,saita juya ta nufi dakinta ba tare da ta sake kallonsa ba,tana shiga ta tura qofar,ta koma saman gadon tayi kwanciyar ta gami da jan wayarta ta fara dubawa,saidai zuciyarta adan hargitse take kadan,don bugunta ma ya sauya ba kamar yadda yake a qa'ida ba,kuma ita kanta batasan dalili ba.

Tsaye yayi kawai a wajen kusan minti biyu yana duban hanyar,sai ya dauke idonsa yana sauke ajiyar zuciya,gaba daya a wannan lokacin bazaice yana jin dadin duniyarsa ba,duk yadda yaso ga qaryata hakan da gayawa kansa komai dai dai yake,amma yasan ya fada dinne kawai bawai don dai dai din yake ba.

Gurin affan ya qarasa,ya dauki yaron yayi masa wasa sosai sanann ya wuce dashi dakinsa,ya cikashi da kayan wasa ya shiga bandaki ya sake wanka, sanda ya fito harya bingire saman gadonsa yayi bacci,da alama dazun dama kukan rigimar baccin yakeyi,ya saki murmushi yayi kissing goshinsa a hankali ya gyara masa kwanciya yana jin qaunar yaron har cikin jininsa,sai ya tsaya gaban madubi ya shirya cikin qananun kaya,ya shafe jikinsa da turare sanna ya fito.

A falo ya fara zama,amma kamar wanda magnet ke jan hankalinsa zuwa ga dakinta saiya kasa samun sukuni,bayason shurunta,kasheshi yakeyi,a qalla ko fada yana da buqatar su dinga yi,duk sanda tayi masa shariya irin wannan baya iya jurewa,bashi da juriya akan abinda yakeso,sai ya taka a hankali ya saka kai zuwa cikin dakin.

Tana tsaye gaban wardrobe tana fidda wasu kaya,sau daya ta waiwayo ta kalleshi ta mayar da kanta kamar batasan da wanzuwarsa ba,ya tsaya daga bayanta yana dubanta

"Ina abinci na?" Kamar ba zata amsa masa ba,saita zuqi numfashi ta fitar ta bakinta a hankali, zuciyarta tafasa kawai takeyi amma batason tayi wani abu da zai nuna bata ganin qimar uncle muhsin,ta saki kayan hannunta ta juya ta fice ba tare data tanka masa ba,yabi bayanta sai ya sameta saman dining tana serving dinsa.

Kujera yaja ya zauna yana bin dukka motsinta da kallo,ko sau daya taqi duban inda yake,kamar ma ita daya ne cikin falon,wani irin fushi ne kwance saman fuskarta ba tare da ita kanta tasan da hakan ba,yaja ajiyar zuciya me nauyi ya sauke a hankali,dai dai sanda ta gama zuba abincin ta motsa da niyyar miqewa tabar wajen

"Dawo ki zauna" ya fada a tausashe cikin muryar bada umarni,bata musa masa ba,kamar yadda bata kalleshi ba,ta kauda kanta zuwa wani sashen daban,yaja abincin gabansa ya fara ci,saidai gaba daya girkin kamar ba nata ba,ta cika masa yaji sosai,abinda tasan yafi tsana kenan,ya lumshe ido yana jin yadda yajin ke ratsa harshensa har kwanyarsa,ya sakeyin loma ya biyu ba tare da ya bari ta gane tsananin yaji da yakeji ba,saidai idanunsa suna kanta,ya tsatstsareta dasu ya hanata sakewa gaba daya,cikin jikinta takejin laifin data masa,amma zuciyarta taqi amsar haka.

"Karomin" ya fada yana tura mata plate din,sai ta daga kanta da sauri cike da zallar mamaki ta kalli plate din ta kuma maida dubanta gareshi suka hada ido,idanun nasa da suka dan canza launi saboda tsananin zafin yaji,sai kuma ta janye idon nata ta basar,tasa hannu ta dauki plate din ta qara masa ta tura masa hadi da bashi qeya.

Spoon ya sake sakawa ya kuma cinyewa,sanda ya sake cewa ta qara masa sai data zauna sosai ta dubeshi da kyau,bakinta yadan motsa kamar zatace wani abun sai kuma ta fasa,ta sake janyo plate din ta fara zuba masa

"Wannan karon ki zuba yafi sauran yawa,muddin ta wannan hanyar zuciyarki zatayi sanyi......zan jurewa ci har sai kince na barshi haka"

"Kayita ci,bazance ka barshi ba" ta gayawa zuciyarta hakan.

Ta gefan ido ta dinga satar kallonsa ganin yana hanyar cinye uban abincin data sake loda masan,tun tana satar kallonsa harta koma kallonsa kai tsaye,ko sau daya bai kalleta ba yaci gaba da ci,ta kalli idanunsa zuwa sannan sun canza launi sosai,tasan yadda yajin abinci ke masa illa,musamman ulcer da yake da ita wadda idan ta tashi ba qaramar wahala take bashi ba,batasan lokacin data riqe hannunsa ba

"Ka barshi haka" ta fada da sauri muryarta tana rawa.

Jajayen idanunsa Ya daga ya kalleta dasu,sai ta gaza jurewa kuka ya qwace mata,ta saka dukka hannuwanta biyu ya rufe fuskarta dasu tana sakin siririn kuka.

Tsam ya miqe daga inda yake zaune ya iso gabanta ya tsaya yana dubanta zuciyarsa na wani irin tafasa,kafin yace komai tayi hanzarin bude fuskar saboda wani irin amai mai zafi daya danno mata,yana qoqarin riqeta tana qoqarin zamewa,saboda tasan muddin yaci gaba da riqeta zata wankeshi da aman.

Bata iya riqeshi ba kuwa ta fara kwararashi,bai damu da yadda ta batashi ba saboda gaba daya hankalinsa a tashe yake,dama bata da lafiya?,tun yaushe?,duka bashi da wannan amsar,ya riqe hannuwanta sosai daya hannun nasa ya dafe mata bayanta yana jera mata sannu kamar zai ari baki.

Shi ya gyara wajen,ya hada mata ruwan dumi ta gyara jikinta da ta bata shima ya gyara nasa jikin,tana kwance tana maida numfashi idanunta a kulle ya qaraso dakin,ya canza kayan jikinsa, boxer ne kawai a jikinsa,qaqqarfar kuma lafiyayyar surarsa ta fita sosai,ya dawo gaban gadon ya durqusa dab da ita ya kama lallausan hannunta ya riqe cikin nasa

"Tun yaushe ne baki da lafiya?"

"Kada ka tambayeni" ta fada muryarta tana rawa

"Why?" Ya tambayeta a mamakance,sai data zame hannunta daga nashi sannan tace

"Saboda baka damu dani bama gaba daya bare lafiyata"

Tashi yayi ya haye gadon gaba daya,ya jawota cikin jikinsa dukkaninta ya rungumeta tsam,bata da qarfin da zata qwace a jikinsa dole haka ta zauna,a hankali sai taji yadda zuciyarsa ke bugawa da Wani irin qarfi n da ya wuce qa'ida

"Tun daga wancan lokacin da abun ya faru haka kullum zuciyata take bugawa,ban taba zaton zankai wannan lokacin ban kamu da ciwon zuciya ba,komai nina aikata miki shi,amma bisa wani umarni da bansan daga inda zuciyata take karboshi ba.......kiyi haquri da dukkan abinda ya faru,ki kuma yafemin,amma nayiwa zuciyata alqawarin bazan bar wannan abun ya wuce a haka ba, kowanne irin tunani nasan zaki iyayi a kaina,dai dai ne bazan hanaki ba,amma ki bani dama......i need a chance don Allah don kuma affan bawai don ni ba" daga wannan maganar ya zame jikinsa daga gareta,ya barta da tunani.

Hijab ya dauko mata sannan ya dauko affan

"Muje kiga likita,bai kamata ki kwana hakanan ba" shi ya taimaka mata har zuwa bakin mota,sai data shiga ya kwantar da affan a baya sannan

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads