Header Ads
Showing 129001 words to 132000 words out of 296907 words

Chapter 44 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

dazu muka shigo daki ni dakai fa,nidai kunya nakeji" ta qarasa maganar tana turo baki,bai shirya ba bai kuma zata ba dariya ta kubce masa,yasa hannunsa saman bakinsa ya dara kadan sannan ya janye

"Ok, come closer" ya fada yana daga mata hannu,bata musa ba tasake matsowa,ya sukuya a hankali ya bata wani irin hot and deep kisses saman goshi da kuncinta,sannan yaja baya yana cewa

"Na bawa Allah amanarku,ki kula da kanki" ta gyada kai a hankali,sannan ta motsa bakinta

"A dawo lafiya,Allah ya kiyaye yasa ku dawo lafiya" lumshe idanu yayi har ya fice,ji yayi a duniya kamar ba'a taba masa addu'a ba, siririyar muryarta ta dinga masa amsa kuwwa a kunne,har suka isa airport yana wassafa wasu abubuwa da yawa a kanta.

Kafin jirginsu yakai ga tashi yayi kiran hafsat,ko ba komai yana son ya sauke nauyin dake kansa,yanason kuma yayi magana da yaranshi,sai daya kira sau uku,ana hudu yaci sa'a aka daga,saidai muryar yaran ce,ya biye musu sukayi surutu sosai har sai da yaji ya siqe

"Ku bawa mommynku" ya fadawa mimi,shuru na sakanni ya ratsa,sannan yaji mimi tace

"Tace bacci takeyi" idonsa ya rufe sannan ya budesu lokaci guda, irin yadda yakanyi wajen hadiya fushi idan ransa ya baci,baya so tana saka yaransa a ire iren wadan nan abubuwan nasu,yanzu ko ba komai ta koyawa yarinyar qarya

"Alright....idan ta tashi kuce nace ta kula daku,daddynku zaiyi kewarku"

"A dawo lafiya daddy,ka siyo mana jirgi" murmushi ya kufce masa,yana fatan wataran dukkansu ya kaisu umara ko aikin hajjin suma

"In sha Allah mimi na,i love you"

"I love you too daddy" ta amsa masa,dai dai lokacin hafsat da haushi ya cikata tayi fam ta warce wayar,ta jefi yarinyar da harara

"Uwar kinibibin tsiya,i love you too daddy" tayi maganar tana kwata muryar yarinyar

"Koni ban fada ba sai ke,saikibishi ai uwar son uba" taja tsaki tana jefa wayar gefe,harta koma zata kwanta sai kuma taji ta fasa,ta miqe ta fada bandaki ta watsa kwaskwarima,ta fito ta fara shirin fita,su mimi kuwa kaya kawai ta fidda musu tace su debo wasu ta saka musu,gida zasu,idan sun qarasa can a samu wani yayi musu wankan, yaro ba hankali,da murnarta ta shiga dakinsu ta debo musu kayan,uwar ba tare data tsaya wani dubawa ba ta karba ta saka musu,ta hado kansu ta sanyasu a motarta suka fice daga gidan,gidan kamar mazaunin bola,saidai hankalinta a kwance yake,tasan me sanya damuwar saita gyara din baya qasar ma gaba daya,duk sanda ta samu chance ta gyara din,hankalinta yayi gidan,tana son su hadu da anty ummee taji sabbin shawarwari,tana jin kamar tafiyar ta ta fara baudewa.

A daren ranar daya sauka ya sake kiran hafsat din don ya gaya mata sun sauka lafiya,amma harta qaraci ringing dinta bata daga ba,har a lokacin ma tana gida bata koma ba,mamarta ta sake cewa da ita

"Shareshi,wani abunma duk laifinki ne,ace mijinka baya shakkarka me akayi kenan" .

Yasan dai ba yadda za'a yi ya mata irin wanna kiran tace bata gani ba,kuma koda a daxun baccin take da gaske ai yaci ace tayi kiransa bayan ta farka,ransa yakai qololuwar baci,yaji kuma a ransa bazai sake kiranta ba indai shine,sai ya maida akalar kiran nasa ga widad.

Dukkaninsu wata irin sakewa sukayi shida ita,sunyi hira mai tsaho,duk abinda tayi a yau din sai data zayyane masa shi kuma yana kwance saman gadon hotel din da suka sauka yana biye mata,a nan take bashi labarin taga tallan wajen wani koyar da girki a kaduna tanaso

"Iyeee .... dole wai so take ta fini iya girki...... alright,zansa Samuel ya yiwa rose magana" da murnarta sosai ta shiga masa godiya,har yaga godiyar kamar tayi yawa,ita kuwa a wajenta normal ne,kamar yadda aka horeta kenan a gida.

Kwana daya da zancan kuwa saiga rose tazo har gida samuel ya kawota,haduwar farko jininsu ya hadu da rose din,saboda tana da matuqar kirki da kuma ban dariya,wannan ya sanya saurin sabo a tsakaninsu duk da rashin saurin sabon da widad ke dashi,shiryawa sukayi ita da muneera da aka bar mata suka wuce wajen sukayi register da komai da komai sannan suka dawo gida,tun daga ranar rose ce ke zuwa ta kaita ta kuma dawo da ita gida,cikin lokaci qalilan sukayi sabo,itama tana son widad saboda kirkinta,don idan sun dawo din sai ta tsare rose ta zauna taci abinci,harma suyi hira da ita,sau tari ma idan ta gwada abinda ta koya saita ajema rose din,komai tabgwada din kuwa sai yayi kyau exactly kamar yadda ta koyo,abun yayita bawa rose mamaki da sha'awa,wata irin gifted ce weedad din.

Ganin yadda widad din keda sha'awa girke girke,sai rose din ta ware wasu ranaku take koya mata irin girkin nasu qabilar,idan sukayi wasu daga ciki takance

"Oga yanaso wannan" tsaf widad ta dauke wadanda tace yafiso din,ta dinga practicing nasu da kyau,har suka zauna mata,ita a karan kanta dadi takeji,tana jin dadin yadda a yanzun ta fara iya kalolin girke girke da dama, yadda ta maida hankali a kitchen yanzun bata maida haka kan karatunta ba,gefe guda ta matsawa anty deena, kullum saita qara mata bayani akan abincin ainihin qasarsu,duk da wannan dama tana ganin ummu tana yinsu sosai,saidai bata taba cewa zatayi da kanta ba.

Cikin wata daya ta koya abubuwa da yawa ta fannin girki,ansha barna,don kullum da abinda za'a girka,saidai ta samu experience sosai.

Tun saura kwana uku su dawo take ta practicing abinda zata dafa musu shida hajiya,sunyi hira da anty deena da anty madeena sosai,sun kuma bata shawarwari cikin hikima,ana ya jibi zasu dawo muneera ta taimaka mata suka gyare gidan tas,sukayi goge goge sosai,washegari kuma rose tace mata

"Madam ko za'a kaiki saloon?" Fadin da rose din tayi sai ya zama kamar tuni a wajenta,tace ta kaita.

Waje ne mai kyau da zaka yiwa kallo daya kasan sun iya aikinsu,cikin yarensu sukayi magana da rose bayan sun gama gaisawa,mutum biyu aka gamawa sannan aka kama kanta.

Sosai matar tayi mamakin yanayin kan widad din,da kanta matar mai suna ada tace bata buqatar relaxer.

Wani irin gyaran kai akayi mata,wanda ita kanta widad din sai data tsaya ta kalla kanta da kyau a madubi bayan sun koma gida,muneera tace

"Wallahi matar nan ta iya gyara matar uncle,inama idan bikina ya taso nan zanzo tayimin"

"Kizo wallahi,saina rakaki" ta fada tana sake kallon kanta dadi yana cikata.

Isowar yammaci sukayi a washegari,kafin isowar tasu komai ya kammala kamar wata babbar mace,cikin atamfa ta shirya dinkin riga da skert,saidai ta gaza daura dankwalin sai yafashi tayi saman kanta,tana maqale jikin window din falonta har zuwa sanda motar data daukosu ta sako kai harabar gidan.

Bin motar tayi da kallo,tana zuciyarta na bugawa da sauri da sauri,farincikin da batasan dalilinsa ba takeji yana ratsa zuciyarta,taci gaba da kallon motar har ta shige parking lot

"Sun iso,bakiji shigowar motarsu ba?,kizo muje mu taraso" muneera dake sanya hijab dinta ta fada tana kallon widad, waiwayo tayi tana duban muneera,sai takejin kamar qafafunta ba zasu iya kaita wajen ba,ta girgiza kai

"Kije yanzu ai zasu shigo" kai ta kada tana dariya

"Oh,wai kunyar hajiya kenan kikeyi,to nidai nayi nan" ta fadi tana yin gaba da sauri,ta bude qofaf ta fice.

Sanda ya shigo ta dauka zata iya dakewa,sai tsintar kanta tayi a gabansa,shima yayi tsammanin zai iya jurewa amma sai ya kasa, hannuwansa gaba daya ya bude mata,batayi wata wata ba ta fada ciki,ya maida ya rufeta gam a cki yana sauke wata wawiyar ajiyar zuciya,yayin da ita kuma ta fashe da kuka sosai cike da wani tune na shagwaba,sai ya gaza jurewa tsaiwar,ya sulale ya zauna a wajen,hakan ya bata damar zama sosai a jikinsa.

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Page 66



Sun dauki mintuna a haka sannan ta daga kanta suka hada idanu,shima ita yake kallo,haka kawai taji wata kunya ta kamata,saboda kallon da yake matan ya mata nauyi sosai a gangar jikinta da zuciya,hakanan bata saba ganin kalar kallon ba a tattare dashi,saita cusa kanta a qirjinsa tana shaqar wani bala'e'en qamshi da fatarsa ke fiddawa

"Eheenn.....baby na ta fara sanin kunya ne?" Tambayar data sakata ji kamar zata nutse,sai kuma ta janye jikinta da sauri tana fadi cikin fidda idanu waje

"Hajiya!" Dukkansu bin falon sukayi da kallo,ba hajiya babu burbushinta,sai suka kalli juna a tare,kafin yayi komai ta rigashi miqewa tana narke ido

"Hajiya fa uncle" amsar da shima bai santa ba,yasan dai yana gaba tana biye dashi,komawa tayi ko ciki ta shige.

Tare sukayi hanyar dakinta,suna zuwa widad din ta lafe daga bakin qofa,shi ya tura ya leqa,saiya samu hajiyan zaune cikin dakin daga qasan carfet ta miqe qafafunta

"Oh,hajiya kina ciki kenan" ya fada cikin jin kunya da nauyi yana shafa kansa,mazewa tayi kamar ba abinda ya faru

"Wallahi,kasan ko yaya tafiya take ba'a rasa jiki da gajiya,kaima ya kamata ka shiga ciki ka huta hakanan,sai Allah ya kaimu anjima"

"To hajiya a huta lafiya" ya fadi cikin jin nauyi,sai data murmusa sannan ta amsa mishi,ya maida qofar ya rufe sannan ya juyo suka hada ido da widad din.

Qwalla ce ta cika mata idon tana dubansa a shagwabe

"Ban mata sannu da zuwa ba"

"Tace ta yafe,naje na huta,anjima saina rakoki ko?" Kafada ta maqale alamun bata yarda ba,sai ya qara taku ya matsa ya buda qofar kadan

"Shiga to ku gaisa" nan ma ta sake maqale wuya,sakin qofar yayi ya koma da baya ya rungume hannayensa yana kallonta

"To ya kikeso ayi?" Hawayen dake maqale ne ya sauko mata

"Ba kaine ba......kaine ka jawomin Allah" dariya ta taso masa,ya murmusa yana kallonta

"Ni me nayi tsakani fa da Allah" kuka ta sake masa,da sauri ya kalli qofar dakin sannan ya dawo da dubanshi kanta,ya tako da hanzari ya iso gabanta

"Sorry..... sorry,kiyi shuru mana please,kafa hajiya taji,nayi alqawari zan rakoki,zan kuma gayawa hajiyan laifin nawa ne shikenan?" Kai ta gyada masa,sai ya saka hannu a aljihunsa ya fidda handkerchief ya soma dauke mata hawayen,idanunsa na manne da manyan fararen idanun nan nata dake yawan daukar hankalinsa,ya jima baiga abu mai daukan hankali kamarsu ba,daga bisani ya sauke dubansa kan mitsitsin labbanta jajaye da taketa motsasu kamar zatace wani abu,tsigar jikinsa ta zuba,ya dauke idonsa daga nan yana cije labbansa,ya gama yaja baya jikinsa na wani irin mutuwa,ko a ina ta samu irin wannan fitinannen turaren?.

Kasa jurewa tayi ta jashi zuwa dining tana buda masa abubuwan data dafa,a mamakance yake kallonta,baiyi shakka ba saidai mamaki,yasan halinta a dan zamansu bata qarya,at last ya rasa me zaice mata

"Bari na huta,ki zaba duk abinda kikeso idan na bude jakata a matsayin gift na wannan abincin" murmushi tayi

"Ni hajiya nayiwa fa"

"Ya salam" ya fada a qasan ransa yana lumshe idanu, yarinyar ta gama dashi,yasan ta fada ne har ranta da kuma quruciya,batasan hajiyarsa itace weak point dinsa ba

"Yes.....i know, that's why nace ki zaba duk abinda kk so,hajiyata duniya ta ce,itace komai nawa" kai ta gyada masa tana murmushi

Wanka kawai ya sakeyi,ya shirya cikin toilet don kada ma tace zata masa bore,lallabawa yakeyi,yana da buqatar ta a kusa dashi sosai,ko bata kawar masa da qishirwarsa ba dumin jikinta zai masa amfani ko yaya.

Gadonsa ya haye yana lumshe idanu,qamshin da bedsheet din ke fitarwa har cikin jininsa,idanun nasa a lumshe yace

"I hope ba muneera kika bari ta shigo dakin uncle ba" kai ta gyada tana murmushi

"Anty widad ce" sosai ta bashi dariya,har sai daya bude idanuwansa a kanta yana kallonta,tana da wani irin salo da yake sauke masa komai na daga gajiya da bacin rai,yayi mamakin yadda ta iya duka wadan nan aikace aikacen,komai na gidan ya zama akan saiti

"Anty?,su anty manya" ya furta cikin salon tsokana idanuwansa suna lumshewa sakamakon dankwalin dake yafe a kanta ya silale ya fadi,sassalkan gashinta da aka masa wani irin nadi jiya a saloon ya bayyana kansa.

Da fuskar shagwaba ta kalleshi,abinda ya qarawa cute baby face dinta kyau matuqa

"Ni din ko?,ni ba anty bace?"

"Wait....kinaso a dinga kiranki anty?" Kai ta gyada

"Good,zan koya miki wani abu,indai kika tsaya kika iya kike yimin,ba anty ba.....har mommy za'a ce miki" ya qarasa fada yana lumshe idanunsa,cikin zumudi take kallonsa

"Yes,na yarda uncle"

"Good.....bari na huta sosai tukunna.... Amma,zo muga wannan gyaran kan naki" ya fada yana yfitota da hannu muryarsa na qara yin laushi,bata kawo komai a ranta ba ta rarrafa zuwa gabansa,ta kuma miqa masa kan tana jin dadin yabawar da yayi

"Anty rose ce ta kaini fa,tacemin ka taba cewa zaka kawo madam ayi mata irinsa dama"

"Yeah" ya fada da qyar kamar mara lafiya,ya tuna lokacin,hafsa yaso kaiwa,tace bata da wannan lokacin, infact ma tace zaman banza ne da bata lokaci,saboda koda anyin zai yamutse shine da zarar sun dawo,ya kuma sakata zuba ruwa akan,shikenan ya tashi a aiki,gwara ya bata kudin taje ayi mata kitso ko wani gyaran mai sauqi.

Ajiyar zuciya ya sauke,ya saka hannayensa gaba daya ya birkitota jikinsa,a dan tsorace tayi yunqurin tashi,muryarsa a kakkarye yace

"Don't.....do me a favor please,bacci nakeji ki tayani,ko kin fita ma na tabbata ba kowa,just one hour kawai" wani irin abu taji yana mata yawo cikin jikinta a sanda yake maganar wanda ya zare mata duk wata laka ta jikinta,sai kawai ta maida kanta saman dantsensa dake cike da muscles ta kwantar,a hankali ya nutsa yatsun hannunsa cikin sumarta, numfashin ya fusga da kyau kamar zai qwace ya samu ya nemoshi,sai ya cure jikinsa waje guda,yayin da widad din tayi lamo tana jin faduwar gaba da fargaba.

Tafiyar tsutsa yaci gaba da yi mata saman kanta yana yamutsa gashin da kyau,qamshi da santsinsa yana bashi wani salon nishadi,bai farga ba sai ji yayi tana sauke numfashi a hankali,daya duba yaga bacci ne ya dauketa,ya saki murmushi a hankali yana gyara mata kwanciya cikin jikinsa,ya tabbatar itama akwai gajiya a tattare da ita,don iya ayyukan daya gani tayi ba qaramin qoqarin gasken gaske tayi ba,baima taba kawowa kansa zata iya ba,ko makarantar da rose din ke kaita ya barshi ne kawai suna fita saboda rage zaman kadaici bawai don a koyo komai ba,ashe abun ya wuce yadda ya daukeshi.

Basu hadu da hajiyan ba sai washegari,saboda ya riqeta a dakinsa,tunda hajiyan ta shiga dakin itama bata fito ba, muneera ce ta debo musu komai takai daki,shima ya dauki sauran yakai musu dakin,daga qarshe sai daya kira hajiyan a wayarsa,tace ta bari sai goben sannan ta haqura,saidai fa gaba daya jinta take cikin wani sabon yanayi,ko yaya ta motsa idanunsa yana kanta,duk bayan wasu mintuna sai ya jangwalo abinda zai bada connection a tsakaninsu,tanata zamewa amma kamar sake diga danqo take a tsakaninsu,shi kansa baisan me yake faruwa ba.

Tare sukayi breakfast a falon, muneera da widad nata gyaran wajen hajiya ta dubeshi

"To nifa yau sai gida" da mamaki ya kalleta

"Ah...haba hajiya,ki bari ki qara koda kwanaki uku ne mana,sai mu wuce tare ko?" Kai ta girgiza

"A'ah abbas,ai tunda komai ya kammala zaman me kuma za'a yi?,gwara na koma gida na nima nafi hutawa sosai" kafewa tayi tace bauchi zata tafi,da qyar ya sha kanta ta bari sai gobe,idan yaso sai su wuce gaba daya,da wannan maganar da sukayi ya wuce daki yace zaiyi wanka ya fita headquarter ya bada report na dawowarsa,zai kuma sake daukan excuse na three to four days.

Ya fidda dukka kayan jikinsa yana daure da towel wayarsa ta dauki ringing,ya dawo da baya yana duba me kiran hannunsa a qugunsa,hafsat ce,yayi mamakin ganin kiran nata,tun randa yayi alqawarin bazai sake kira ba bai kuma din ba,hakanan itama koda wasa bata kirashi ba,komawa yayi ya jingina da mirror din dakin ya daga kiran tare da yin sallama,sannan yayi shuru yana jiran jin dame tazo.

Kamar ba zata tanka ba bayan ta amsa sallamar sai kuma tace

"Au ashe kun dawo"

"Eh" ya amsa mata a taqaice,abin ya sake bata ranta

"Yanzu kayi tafiyar wata guda,ka dawo qasar amma ka kasa gayamin ka dawo abban mimi,adalci kenan hakan?" Maimakon ransa ya baci baisan murmushi ya kubcewa fuskarsa ba,rainin wayonta ya fara yawa,idan tayi wani abun kamar zautacciya

"Ai baki da buqatar jin komai daga gareni,so kinga baki da matsala dani"

"Haka ma zaka ce?,duk abubuwan daka yimin kai baka gani?,kullum nice mai laifi a wajenka,kayi tafiyarka daga wajen wata,ka tashi dawowa ka sake sauka a wajenta ba tare da nasan ma ka dawo ba sannan ace ana kyauta min" saita fashe masa da kuka kawai,shuru yayi yana saurarenta,tasan weak point dinsa ne,amma bazai yarda ta raina masa hankali ba,don haka ya aje wayar saman mudubi kawai ya rabu da ita,duk da yana saurarenta.

Jin tanata faman sharan majina baice mata komai ba ya kuma tunzura mata zuciya,kukanta banza shirunta banza kenan?.

"Laifi nane da nayi kiranka" ta fada tana shirin kashe wayar

"Wait.....am on my way tomorrow" baiji ta amsa ba,tadai yanke kiran,duk da haka ya tura mata gajeran saqo saboda ya fita hakkinta yana sake jaddada mata,ya aje wayar saman mudubin yana fidda iska daga bakinsa,hafsat.....hafsat.....ya yarda jarrabarsa kenan a rayuwa,ya taka zai shige bandakin sai yaji an turo qofar,yadan tsaya daga bayan labule kadan saboda yasan me shigowar,kuma tabbas

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads