Showing 282001 words to 285000 words out of 296907 words
Chapter 95 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
Sakato tayi da wayar a hannu,ranta yana mugun baci,batakai yabar duk abinda yakeyi ba kenan saboda ita yazo ya daukesu?,cikin wannan bacin ran ta kira fahad ta gaya masa inda suke din,wanda saboda dan nisan dake tsakanin airport din da station din sai daya dan dauki lokaci,sauran wadanda basuga amfanin abinda tayi din ba sukace tunda ba abun hawa na haya available na zasu tsaya wani jira ba sai kawai suka dauki taxi drop suka wuce suka barta ita da su baaba hassana 'yan kanzaginta,sai da suka jima da wucewa sannan fahad ya iso,tayita masa bala'i amma yayi biris da ita bai kulata ba tunda ya riga yasan hali.
Sai da aka gama hada masa dinkin sannan ya dawo ya dauki su widad,tuntuni an gama suna zaman jiransa ne ma
"Ba komai,tunda dai ya gama alhmdlh" abinda tace dashi kenan sanda yake bata labarin abinda ya tsaidashi,shi kansa baiji dadi ba,don shima yana da baqi daga wasu garuruwan da sukazo masa saboda yana sanya ran zaiyi walima a goben kamar yadda ya saba kowacce haihuwa,haihuwar affan ce kawai bai samu yayi ba.
Tunda suka isa gidan tana farfajiyar gidan a zaune ta kasa shiga ciki,kowa saidai yazo ya wuceta,tun a sannan hidimar da akeyi da yadda taga gidan ya fara tara jama'a ya tsaya mata a rai,kowa yana ciki yana huce gajiya harda su mimi,amma baqin kishi ya hanata sakat.
Sanda motar abbas din ta shigo harabar gidan idanunta akai,baqin glass ne,bata lura da waye da waye a wajen a ciki ba sai da suka bude,su marwa suka fara fitowa sabe da yaran dake cikin wani lallausan blue din abun daukan yaran suka nufi cikin gidan,ta qurawa motar ido tanason ganin wadda zata fito,sai bayan kusan minti uku sannan widad din ta fito tana murmushi,da alama wata maganar sukayi da abbas din data bata dariya.
"Kan abu ta kazar uba" hafsat ta fada cikin ranta,zuciya tayi mugun dibarta,batasan sanda ta isa gaban motar ba side din da abbas din ke zaune cikin wani mugun fushi
"Ai dama odan bakayi haka ba ba kaine abbas ba,idan bakayi haka kai din ba namiji bane,dan kunama.....tabarmar qashi RIGAR K'AYA" ta da cikin madaukakin sautin da yaja hankalin mutanen cikin gida da sauran na farfajiyar wajen,ganin yadda hankula ke dawowa kansu bai saka ta fasa magana ba
"Ni dana taho daga wata uwa duniya ka zubeni a station ka kasa zuwa daukata,amma ka dauki 'yar gwal da danyen jego a gaban mota kana yawo da ita,kabi ka tattare a gindinta ita da danginta,kana musu wahala kana musu bauta......wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni da.......".
Tsawar daya daka mata ta yanke sauran maganar,yayi wata irin fitowa daga cikin motar,Allah ya kissimawa widad ba za'a kwasheta da kyau ba,cikin gaggawa ta shiga tsakani ta dora hannayenta kan qirjinsa tanason yaja baya,ta tabbatar gamuwarsu da hafsat din ba zata taba kyau ba,batason kuma zuciyar nan data taso masa ta sanya ya biye mata ga mutane a wajen.
'yan uwan abbas dake kusa ne suketa yima hafsat fada suna janyeta,ana tsaka da haka kiran dan auta a dakinsu baban abbas din ya shigo yana shaida masa sun bata kwatancen masaukinsu,sai ya kashe wayar yana huci ya juya ya koma cikin motar ya figeta ya fice daga gidan.
Iska me zafi widad ta furzar,tabi hafsat da kallo wadda aka janyeta can bayan gidan
"Barin hali sai mutuwa"ta fada tana mamakin halin halin tantagaryar hauka irin na hafsat din.
Ranar gaba daya a birkice hafsat din ta yini,donma 'yan kanzaginta suna dannarta,da qyar takai ga shigowa falon,saidai gaba daya a hargitse take.
A yanzun widad din tafi qarfin raini,kuma tafi qarfin ta keta idanunta ta gaya mata maganar banza,uwa uba kuma tana tsakiyar danginta da hafsat din bataga alamun daukan raini ko wargi daga wajensu ba,haka ta yini har dare a falon tana qunsar takaici,saidai idan abun ya qume mata da yawa ta fita ta matse hawaye ta dawo.
Har tayi shirin kwanciya abbas din ya shigo,har yanzu fuskarsa babu walwala,ta kalleshi cikin langabar da kai a shagwabe tace
"Angon qarni babu fara'a, gaskiya ba kanta,abunma ko kyau baiyi maka ba" dole ta sakashi dariya,sannan ta gyara zamanta
"Kaci gaba da haquri uncle don Allah"
"Wanne haqurin?,haqurina ai ya gama qarewa......akwai abinda kuke buqata?,zan tafi masauki wajen baqi na" kai ta girgiza,don babu ce kawai basu da ita,ya tsugunna yayi kissing yaransa duka,harsu mimi da tasa aka debo mata suka kwanta gaba daya su bakwai kenan harda ita,da yake gadon babba ne ba wanda ya matsi wani.
Har ya fita tana juya abun a ranta, zuciyarta duka ba dadi,batason bacin ran nan nasa,fatanta ko yaushe mummyn mimi ta gyara halinta ko zai samu nutsuwa.
Dakin da su gwaggwo mero suka sauka ya leqa don ya musu sallama,baima san hafsat din tana cikinsu ba sai daya shiga,ya gama yi musu sallama ya miqe ya fice,sai hafsat din tayi zumbur ta dauki jakarta ta biyo bayansa.
A tsakiyar falon ta cimmasa,tana riqe da qugunta,zuciya kuma na ingizata tace
"Muje masaukin tare,acan nima zan kwana" wani banzan kallo ya watsa mata,yaja mata tsaki yayi gaba,saita sha gabansa cikin kuka
"Wallahi na gaji da wanna wulaqancin da kakemin,kamar nima ba matarka bace,yau saidai duk abinda zaka yimin ka yimin,na gaji da wannan rashin adalcin" sosai zuciya ya ciyoshi,ya finciki jakar hannunta yayi wurgi da ita sai gata a bakin qofa
"Na fiki gajiya,na gaji dake gaba dayanki,kije na sakeki saki daya,badai shikenan ba?" Wutace ta kawo mata ta kuma dauke mata a take,saita aza hannu aka ta kurma wata uwar kururuwa data zama tamkar shele ga dukkan wani me rai da yake gidan,shelar tata kuwa ta iske kowa,take falon ya fara karbar jama'a dake cikin gidan banda na harabar gidan da kunnuwansu baije wajen ba,a lokacin abbas ya jima da ficewa daga gidan yana jin kamar an zare masa qaya.
Faduwa tayi tahau tirje tirje a wajen, gwaggwo hassana ce ta riqeta tana kiran sunan Allah kafin sauran su tayata riqe hafsat,tanata abu kamar wadda ke shirin hawa bori ko kuma tayar da iskoki
"Ku cikani,ai kuna gani,a gabanku ya sakeni,saki uku kenan yayimin,saki uku kenan fa".
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 41
Saita sake fashewa da kuka,tana jin kamar ranta zai fita,kamar alqiyamarta aka tsayar mata ita kadai.
"Ikon rabbi sai kallo,wannan wanne irin musiba ce?,saki haka bagtatan?,wannan abu nu hassana yafi qarfina" gwaggwo hassana ta fada tana kama hafsat daketa zamewa tana tumuwa a qasa
"Kiyi haquri tunda aikin gama ya riga ya gama" amma inaaaaa.....sai hafsat din ta hau zage zage,ta dinga debo ashar tana qundumawa widad
"Sai naga bayanki,yadda kika hanani zaman lafiya saida kika cisgeni daga gidana wallahi tallahi kema ba zaki sake jin dadin abbas ba.....na rantse kinci bashi bazan qyaleki ba" gwaggwo mero ce ranta yayi mugun baci,ta sanya widad ta koma dakinta abinta ta dubi hafsat
"Sakin nan dai ba ita tayi miki shi ba,hasalima batasan me ya hadaku ba,kuma zaman gidan aure dama kowa ya iya allonsa ya wanke ne,halinka kuma shike sai daka,indai bazakiyi haquri kija bakinki ki karbi qaddaraki ba har zuwa wayewar gari,to don Allah bamason hayaniya da tashin hankali ki wuce kitafi,mu taron farinciki ne ya hadamu" gwaggwo mero ta fada wadda ta jima dama tana juya maganganun da sukayi da 'yar uwarta hajiya na qarshe kan yadda take gasa abbas.
Banda tsoron fita da takeyi da daddaren ba shakka saita yayyabawa gwaggwo mero maganganu,don tana ganin a yanzun ta zama munafuka ne, goyon bayan widad takeyi.
Ranar wani irin dare mai mugun tsaho da baqinciki hafsat ta gani,ta dinga kuka kamar idanunta zai fado,idan ta tuna wai a yau ta rabu da abbas uban yaranta rabuwa ta har abada?,sai taji kamar mafarki takeyi,lallai namiji qanin ajali ne,namiji tabarmar qashi,namiji bashi da tabbas yau ita ta gani zahiran!!! (To masu karatu kunji fa,nidai nace uhmmmm).
Ita kanta widad batayi cikakken bacci ba,idan ta kalli su mimi sai tausayinsu ya kamata,ta dinga kiran wayarsa yaqi dagawa,sai daga qarshe ya daga a dake yace da ita
"Meye kike ta kirana?,idan zaki samu guri ki kwanta saboda baqinki na gobe gwara ki kwanta" kit ya kashe wayar,yasan magana zata masa akan abinda bakin alqalaminsa ya riga ya bushe,a daren yau sakayau ya dinga jin kansa,zuciyarsa tayi wani irin fes kamar an fito masa da ita an wanke,hankalinsa kwance yayi baccinsa,irin baccin ma da shi ya jima baiyi ba.
Washegari kowa da harkokinsa na bikin suna ya tashi,sai hafsat da jama'arta dake qule a daki,wanda kowa ke mamakin abinda ya hanata tafiya tun sassafe,yadda ta dinga yi a daren jiyan basu zaci hantsi zai daga basu tafi ba.
Widad na kitchen tana hada ruwan zafi suna magana ita dasu marwa dasu muneera gwaggwo hassana ta shigo,suka hada ido da widad din ta jefa mata Wani munafukin kallo,widad din ta basar ta gaidata a matsayin matar kawun abbas din,ta amsa mata kadaran kadaham,sai tahau neman abinci,sai data gama diban komai sannan tace
"Mudai wannan bikin sunan ba damu za'ayi ba,dole muje mu raka diyarmu da aka kora......yarinya kin samu duniya,ku dama sadakar yalla wuyarta ku shiga gida,saikun fidda kowa,da biye biyen malamai duk sai kunbi kun ishi kowa".
Ran widad ya baci da kalaman gwaggwo hassana,itadai tasan ba wani abu daya taba hadasu ballantana tace,akan hafsat din?,ita meye nata a ciki?,ita tayi sakin?.
"Gwaggwo ni bansan meye sadakar yalla ba kwata kwata,saboda tsatsona ni balarabiya ce,kuma duk wanda ya kalleni ya kalli ahalina ya sani,malamai kuwa isa ce,kuma na gode da kika shaidamin aikina yayi,zanje na qarawa malamina kudi yaci gaba da aiki kada ya daga qafa"
Kuka gwaggwo hassana ta saki tana jan salati wai widad tayi mata rashin kunya,duka kitchen din sai akahau kallon kallo,kowa yaqi tanka mata,don duk sunsan itace bata da gaskiya,haka ta fita tana fatar majina tana kaiwa gwaggwo mero qararta,a cewarta yanzu ita daya takejin maganarta.
Suna tsaka da maganar abbas ya shigo gidan cikin wata danyar gezna fara qal,sai maiqo takeyi,ta fidda zatinsa da kwarjininsa gami da kyansa da wani irin kamala.
Gwaggo hassanar tana ganinsa sai tayi shuru,ta wuce dakinsu sumi sumi,ya tsugunna yana gaida gwaggwo mero tare da tambayarta me ya faru
"Fitina ce kawai sukeson ja kafin hafsatu ta fita a gidan nan"
"Bata tafi ba?,zaman me takeyi?" Ya fada fuskarsa a hade,sai ya miqe ya nufi dakin, gwaggwo mero ce ta dakatar dashi
"Ka barsu muga iya gudun ruwansu,neman wanda zai tayasu dama sukeyi" .
Dole ya haqura da shiga dakin,amma ya kasa ya tsare yaqi barin gidan,daga qarshe ya zauna daga bakin gate yana amsa waya.
Abinda baiyi zato bane ya sameshi,wato qarin matsayin da yaketa addu'ar tabbatuwarsa idan da alkhairi,hadi da tafiya course na watanni shida america.
Dai dai sanda hafsatu ke fitowa da jakarta fuska qozai qozai ita gwaggwo mero,don gwaggwo fanteka tace ita fa babu inda zata sai an gama suna taci abinda tazo ci,idan sun koma dai tazo gida ta sameta ta sake jajanta mata,bayan sun fita taja tsaki tana gunguni
"Yarinyar da ba mutuncin kowa take gani ba, zamanta da yaron nan har yai alkhairin da ita qanwar cikinta ya samemu ta sanadinta,ita da ya shekara kusan takwas da ita har ta gama zamanta bamu sameshi ba,yo na meye zan damu kaina?,saina gamacin qwai kaji da nama,ina gani an tirke sa za'a kayar kawai sai na yiwa kaina na tafi rakiyar sakakkiya?,da yake nice maqunshin gishiri"(😂😂,niko nace gaskiyar ki hajiua fanteka,shi mutum mai yawan alkhairi dama maqiyinsa ma wataran masoyinsa yake komawa,Allah kada ka jarrabemu da hannun 'yan dambe).
"Alhamdulillah, Alhamdulillah,Allah ya tayaka riqo,kai nayi farinciki,inama ace yar uwata tana raye taga wannan rana da taketa roqa maka ita" gwaggwo mero ta fada zuciyarta a karye,abinda kuma ya shiga kunnen hafsat kenan wanda ya sakata tsananin rudewa,ko ba'a fada ba tasan wani promotion dinne ya samu,dai dai sanda take fita a rayuwarsa?,wannan wacce irin hasara ce ta tafka.
Ko gwaggwo mero dake ban baki tare da musu fatan sauka lafiya basu kalla ba,suna fita wajen gidan ta damqi hannun gwaggwo mero
"Na shiga uku mero,ya samu promotion,kuma wallahi babban matsayi ne ya samu wannan karon" ta fada qwalla na zubo mata
"Eh to dai hakanan zakiyi haquri,duk wani abun rashin haqurinki ne sila,yqnzu gashi kin bar mata gidan kin bar mata mijin,kin bar mata yaran" maganar gwaggwo hassana saita zama kamar kamar wani fami ta yiwa hafsat din,taji kamar itama tana layin maqiyanta ne,amma dole haka ta danne don tana buqatar dan rakiya,bazaiyiwu ta tafi ziqau ba abun sai yayi mata yawa.
Abinka da ba 'yan halak ba,isarsu keda wuya laifin yaso ya koma kamar na gwaggwo hassana ne ma,ummanta tana salati tana komai amma tana fadin su gwaggwon basu kyauta mata ba,ta yaya suna wajen zasu bari ya qarasa tsinke ragowar igiyar da tayi saura?.
Abun duniya ya taru ya ishi gwaggwo hassana,ta kama baki kawai tana kallon qarfin halin umman hafsatun,wato shi dai abun arziqi bai karbi kare ba wato,hakanan matsiyaci ko a tandun mai aka sakashi haka za'a fiddashi qamas,haka ta karkade zaninta ta tashi ta wuce gida cikin takaici,abun arziqin da tasoyi ya koma na tsiya,can kuma ga daula da gagarumin bikin sunan da za'a yi ta yiwa kanta rasa rasa,sai ta yiwa gwaggwo fanteka barka da batayi biyu babu ba.
******Kwananta biyu cikin matsanancin hali na kuka da damuwa,har daga qarshe umman nata ta gaji da ji ta zaunar da ita
"Nifa wannan koke koken naki ya fara isata,wai shin abbas shine autan maza koko ya aka fara?,kinga fa babu ta inda Allah ya rageki in gaya miki,kin samu a jikinsa kin tara abinda kika tara,ki gama iddarki ki gyagije ki fara zawarci me lasisi,wallahi da gudu zaki samu manema,ai sai wani ya yar wani yake dauka,abu daya zaki.masa ki rama,kema da zarar kin gama iddarki ki rattaba aurenki kawai,shine qarshen baqincikin da zaki cusa masa,yara kuma ya baki abinki,ta nan ma kadai zamu sake samun wasu kudin shigar".
Da wannan shawarar suka dinga shige da fice saida aka saka baki aka bata su mimi,kallonsu kawai yakeyi,yasan manufarsu,don haka dukkan abinda ya tashi bayarwa na amfanin yaran qeqe da qeqe yayi musu,na watanni uku cas ba qari babu dadi,haka umman da hafsat din sukayita zaginsa sunayi dashi a gaban yaran,mimi da nawwara saidai su bata rai,babu damar yin magana,don tun randa nawwara tayi magana da yake ta danfi mimi tsiwa uwar ta gwabje mata baki basu sake cewa komai ba,saidai suyita bata fuska,takaici da baqinciki ya ishi hafsa,don ko widad aka zaga a gabansu sai fuskarsu ta canza
"Shegu an goga musu baqin hali" haka hafsat din ke fada.
Watanni uku aka bawa abbas din kafin tafiyar da zaiyi america, office zasu gama masa dukkan shirye shiryen tafiyar,sun bashi damar tafiya da mata daya da yara uku zasu dauki nauyinsu,idan yana buqatar qarawa kuma wannan saidai yayi a aljihunsa.
Hankali kwance cikin wata irin nutsuwa yake dukka shirinsa,yanason tafiya da widad amma baisan ya zata kasance ba,saidai yana mata shirin ba tare data sani ba incase koda zai buqaci hakan,don bayajin zai iya nesa da ita na wadan nan watannin.
Gefe guda kuwa widad din ta gaya ma kanta aikine sosai ya sameta,idan a baya su biyu ne yanzun ita daya ce dashi,uwa uba kuma riqe namijin da a baya yake da mata biyu yanzu ke daya ce dole saikin zage damtse kin ninka shirinki,duk da hafsat din akwai ya babu ce,amma dai duk tsiya macace itama.
Ta tsaya ta gyara kanta da kyau,ciki da waje ta fara canzawa tana komawa yarinyarta danya shakaf,ta sake shiga classes kala kala da groups groups 'yan gaske na manyan matan da suka fita gogewa a komai, groups na hajiyoyi masu mutunci da tarbiyya da ake mugun qaruwa,ta shiga ne ta sanadiyyar su anty fanna da a yanzu suka zame mata madubi kuma makaranta,gefe guda kuma ga su anty madeena da anty deena da sauran yayyenta da kowannensu yanzu zaman lafiya sukeyi sosai,dama can widad din akwai sauqin kai da bin na gaba da ita koda tazarar shekarunku babu yawa,to har kawo aure bai canzata ba,saima sake riqe yayyenta da kyau datayi.
Ga mummynta itama da bata jin kunyar yi mata bayanin komai,widad din kawai