Showing 51001 words to 54000 words out of 296907 words
Chapter 18 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
hancinka.
Wannan ba baqon abu bane a wajensa,yayi fada yayi nasiha amma jiya iyau babu wani ci gaba,saidai yaci gaba da haquri kau da kai da nusashe ta,duk da hakan tana ganin kamar gazawarta yake gani,tunda dai tana iya nata bakin qoqarin a ganinta.
Yaran da suka garzayo suna masa oyoyo ya daure ya duqa ya rungumesu cikin jikinsa,ko daya babu wani kyakkyawan yanayi a tattare dasu suma,ita kuwa saita aje wayar hannunta tana dan sosa kai irin na marasa gaskiya,tare da qoqarin yi masa sannu da zuwa.
Amsawa yayi yana kallonta,wani hargitsatsen kaya ne a jikinta,atamfar dake jikinta ya soma gajiya da ganinta,idan zai iya tunawa da ita tazo gidan,kuma har yau ta gaza bada ita kyauta saboda tsabar baqar rowa,sau tari yakan tambayi kansa menene amfanin karatun da hafsa tayi?,tabbas da yasan haka zata ci gaba da kasancewa,baiga abinda zai sanya ya barta ci gaba da karatun ba,don wadan nan dabi'un nata babu wanda zai gani ya dauka yasan bihim a boko.
"Muje ku rakani na shirya" ya fada yana kada kan yaransa,saita bi bayansu da harara
"Agwagwa sarkin wanka" tafada,don tasan zuwa zaiyi ya hada ruwa ya musu wanka,ita duka ba wannan bane ya dameta,yadda dafa dukan shinkafar da tayi masa ta kama ta kuma yi qauri da kyau,ta yadda zata masa bayani take tunani,tasan halinsa,sarai baya wasa da cikinsa,ya baiwa abincinsa muhimmanci sosai.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 26
Koda ya shiga sassansa sai yaji dama dama,duk da cewa akwai qura data dan shishshigo masa amma kuma babu wannan dattin da annakiyar ta sassan hafsat,bai gaji sosai ba kasancewar tafiyar jirgi ta banbanta data mota,don haka ya ajjiye yaran saman kujera sunata masa hira,yahau kakkabe sashen nasa da goge goge,sai da yaga komai ya dauki haske,sannan ya hada ruwa yayi musu wanka da kyau,yana wasafa yadda zai samu lokaci yakai mimi a wanke mata gashinta.
Sai da ya gama shiryasu sannan yayi nasa wankan,ya shirya cikin kayan barci saboda tara ta gota a sannan,kamar ya kirata yace ta kawo masa abincin nan amma sai ya fasa,ya tasa yaran a gaba suka koma can.
Tana kitchen tana ta kaca kacar yadda zata hada masa koda coleslaw ne mimi ta shigo tace tazo inji daddy, saita maida.kayan hadin data debo din kawai,ta kwashi warmer da plate din ta biyo bayan yarinyar,tana dan hade ranta,wai koda hakan zai sanya yaji shakkar mata magana ko fada.
Saidai kuma ya bata mamaki,saboda yadda yakecin abincin yana yiwa yaransa hira ba tare da yace da ita komai ba,can qasan ransa yana ji ne kamar ya furzar da abincin daga bakinsa,duka dai yana daurewa ne saboda muhimmiyar maganar da zaiyi mata.
Koda ya gama cin abincin bai tashi a wajen ba,sunta hira da yaransa yana biyewa shirmensu,duk da hirar babu wani armashi,ita kuwa gogar tana zaune a gefa tana danna waya,abinda tafi kauri kenan,bata wani damu da hira da miji ba sam,lokaci lokaci takan dan sanya musu baki a hirar,a haka har nawwara dake saman cinyarsa tayi bacci,jimawa kadan mimi ma ta soma gyangyadi
"Gwara ki kaisu daki ko?" Yace da ita yana dubanta,saita aje wayarta tana dan bata rai
"Sai da nace ma mimi ta wuce daki idan ta fara jin bacci fa"
"She's too young da zata gane hakan ai" qarasowa tayi ta soma tashinta cikin hararrami,ya dakatar da ita cikin dabara ya daga yarinyar,ta kama hannunta suka wuce daki.
Ba jimawa ya miqe,ya nufi kitchen don dafa tea,saboda ba wani sakin ciki yayi yaci abincin ba.
Da kallo yabi kitchen din saboda uban wanke wanke da ya fara cin karo dashi,kana gani kasan ba iya kwanukan yau bane,saboda wasu ma sun fara bushewa wasu kuma sauran abincin ciki ya fara rubewa,kai ya girgiza takaicin na cinsa,ya matsa ya duba ma'ajiyar tukwanenta,cikin taimakon Allah ya samu wata wankakkiya,ya hada komai da komai ya tsaya ya jira ya tafasa ya juye ya dawo falon ya zauna ya fara kurba a hankali yana kallon labarai da ake haskowa a tashar alhadath,saidai sam ba ta nan hankalinsa yake ba,yana jiran jin fitowar hafsa ne,amma har ya gama babu ita ba dalilinta,wannan yasa ya miqe ya nufi dakin kansa tsaye.
Yana tura qofar suka hada ido,tana kwance tsakiyar yaran,ya qarasa shiga ciki a hankali hannayensa zube a aljihun wandonsa yana nazarin dakin a fakaice,komai babu kintsi,ko ina ba'a gyare yake ba,sai ya kauda kai ya maida gareta
"Zan wuce daki,wa zan daukar miki a cikinsu,coz na fara jin bacci,inason kuma muyi magana dake" fuska tadan yamutsa kadan
"Kawai ka kwanta a nan mana,ni bansan me yasa bakason kwana a dakina ba,saidai ni kullum ina yawon binka?" Ta fada yau dai tana dan karya murya,jingina yayi da madubin dakin yana qoqarin controlling kanta,gaba daya dakin its not well organized,komai a birkice yake ba bisa tsari ba,duk sanda zai kwana a dakin komai sai ya nemi inda aka wulla masa,wannan dalilin ya sanya zaiyi wuya kaga wani abu nasa mai muhimmanci a dakin.
Kafada ya dage
"Well,zanje na shirya"
"Yauwa,thank you"tafada tana dan jin dadi,saiya juya a hankali ya fice a dakin.
Sai da yayi shafa'i da wutirinsa,ya kuma dauka duk abinda yasan zai iya buqata sannan ya rufe sashen ya koma,ya isa dakin ya dora kayansa saman madubinta yana fadin
"didn't you sleep?" Saita motsa kadan tana cewa
"Uhmm"
"Okay,tashi,dama muyi magana dake" dan muskutawa tayi kadan,sai kuma ta miqe a hankali ta zauna tana dan murza idanu,zuciyarta na bada Allah yasa samuwa ce tazo.
Kujerar gaban madubi yaja ya zauna dab da ita,har gwiwoyinsu na gogar na juna,ya goye hannayensa a qirji yana duban fuskarta da manyan idanun nan nasa da suke saurin kassarata,tsahon wasu mintuna baice komai ba,har sai data qosa tace masa
"Wannan kallon fa?,kana azamin nauyi fa,ka tasheni bakacemin komai ba" kai ya gyada siririn murmushi yana kufce masa,saiya saki hannayen nasa ya hade yatsunsa waje guda
"Har yanzu motar da kikace min kinaso ita dince baki canza ra'ayi ba?" Wani madaukakin murmushi ya kubcewa hafsat din,abunda bata taba kawowa shi xai mata maganarsa ba,duk da dama abbas din ya iya bazata,ba daga nan ba
"Eh itace" ta fada cike da zallar zumudi
"Shikenan,nan da two to three weeks zata iso.....sannan kuma.....inaso ki duba kayan dakin da kikeson canzawa,ki turonsu ta watsapp,amma kada su d'ara 1mil,sai nasu mimi su kuma kada su wuce 50000k" wani irin mamaki da farinciki suka cikata,cikin muryar zumudi tace
"Da gask kake abban mimi?" ta fada idanunta a waje tanason ta samu tabbaci.
Kai ya jinjina mata yana sakin qaramin murmushi cikin bata tabbaci,hannunsa ta kama ya riqe da kyau tana dariyar farinciki gami da yi masa godiya.
Hannayen nasu yabi da kallo,yadda ta riqe masa.hannun dama bata aikata hakan idan ba wani abun farinciki ya sameta ba,idan bai manta ba rabon data riqe masa hannun haka tun lokacin da ya shaida mata ya biya mata hajji,sai ya zame hannun a hankali yana cewa
"Yauwa,dama nace zamuyi magana ko?"
"Ai mun gama magana,irin wannan manya manyan albishir haka?" Ta fada tana washe baki,sai ya kada kai
"Saura abu daya"
"To ina saurarenka" ta fadi ba tare data bada wani muhimmin ba
"Hafsa" ya kira sunanta,sai ta amsa tana murmushi
"Komai muqaddari ne daga Allah ko?,hakanan rayuwarmu da dukka qaddarorinmu suna hannunsa,yadda ya tsara haka bawa zaibi,hakanan fadarsa ne daga qur'ani ku auri abinda yayi muku dadi daga mata bibbiyu uku uku da hurhudu....." Statement dinsa na qarshe yasa fara'ar fuskarta taja baya,wani tunani kuma ya gilma mata,saita zuba masa idanu gabanta na wani irin faduwa,zuciyarta kamar zata fasa qirjinta ta fito
"Hafsat,Allah ya nufeni da qara aure,wanda za'a daura shi cikin sati mai zuwa"
"Meeee!!!" Ya fada da wata irin shaqaqqiyar murya,wadda tuquqin bala'i yasa ta gaza fita da kyau yadda ya kamata
"Relax,calm down please,hakan ba yana nufin matsayinki ya canza daga yadda kike a zuciyata ba....."
"Wallahi qarya ne!......qarya ne abbas......qarya ne wannan" ta fada ya qaaraaji tana nunashi kamar wata mahaukaciya sabon kamu
"Shine ka zaunar dani kana yimin wadan nan kyaututtukan?,to banaso,ka riqe kyaututtukan ka!,wallahi baka isa kuma ka qara aure ba!,ni kadai ce matarka!,ni kadai zaka zauna da ita duniya da lahira!!" Ta fadi da wani qaaraajin tana dubansa da idanunta da sukayi jazur suka kuma firfito kamar wadda aka shaqawa borkono.
"Cool down,karki bari ranki ya baci kinji......zauna muyi magana ta fahimta dake" ya fada with softness yana yunqurin kamota ganin tana shirin miqewa,fusgewa tayi tana jifansa da wani mahaukacin kallo,ta bude bakinta cikin madaukakin sauti ta fara gaya masa dukkan maganganun da suka zo bakinta,miyagun kalamai na aibatawa da kuma tunzuri,sai ya koma kawai ya zauna,ya harde hannayensa a qirji yana kallonta a nutse.
Ya sani ita aka tabo,kasancewa batun lamari na kishiya a wajen mace babban al'amari ne da ba kasafai suke iya daukan wannan mummunan labarin ba,wannan dalili ya sanya ya bata dama taketa fadin dukkan abinda taga dama ba tare da yayi yunqurin dakatar da ita ba,duk da kalamanta akwai wuce gona da iri da kuma zaqewa da yawa,amma yayi haquri ne ya jura saboda yasan wani ciwo ne da radadi daga zuciyarta,wanda shine ya dasa mata shi yanzu yanzu.
"Shine ka zauna kana kallona?, wallahi abbas baka isa ba,wallahi nace bazaiyiwu ba" sai tayo kanshi,tana rarumo kwalaben turaren dake saman madubinta ya soma qoqarin jifansa dasu.
Cikin qwarewa ya dinga sanya hannu yana cafe duk wadda ta jefo,ganin ko daya bata sameshi ba sai tayi kukan kura ta jawo bed lamp ta wurgota.
Bai samu tareta ba,amma ta dakar masa hannaye,glass din jiki kuma ya yankeshi ba tare daya lura ba,saita tsugunna inda take ajjiye takalmanta ta fara daukansu suma daya bayan daya tana masa ruwansu.
Miqewa yayi cikin zafin nama da mazantaka ya isa gareta,ya kama dukka hannayenta ya hade cikin hannunsa guda yana kallon fuskarta,ransa ya soma baci,ya dubi sashen dasu mimi ke a kwance,Allah yasa babu daya cikin abinda take wurgowa daya samesu
"Ki nutsu hafsat!,ki nutsu!"ya fada shima da murya sa mai kaifi da zurfi,saita dakata din ta kece da wani irin kuka
"Macuci azzalumi,Allah ya isa tsakanina da kai,kuma wallahi wallahi baka isa kayi wannan auren ba,idan ba haka ba sai na baka mamaki nima dakai da munafukar da zaka auro,ka fita ka barmin dakina,ka fita bana son ganinka!" Ta fada da mugun qarfi,saiya sakar mata hannaye,ya kuma taka a hankali zai fice,sautin amon muryarta ya dakatar dashi
"Kazo ka kwashesu,suma bana son ganinsu,ka debesu daga gabana!" Dawowa yayi a nutse yadan tsaya gabanta yana kallon yadda ta birkice gaba daya,jikinta banda tsuma babu abinda yakeyi,yasa hannu ya kwashe dukkan yaran ya fita dasu.
Ya jima yana mamakin baqin kishi it n na hafsat din,ashe abun ya wuce yadda take tsammani?,wanne irin hauka ne wannan?.
Bai lura da hannunsa dake zubar jini ba sai daya kwantar da yaran saman gadonsa yaga stains na jinin a jikin blue bedsheet din nasa
"Ya salam" ya fada sanda yake duba wajen,sai yaga ya yanke sosai,don haka ya koma dakin yaran dake sassanta don ya dauko first aid kit.
Tun daga falonta yana iya jiyo gunjin kukanta,irin kukan da mutum yake zama dirshan ya bude dukka muryarsa yayishi,tausayinta sosai ya saukar masa a rai,sai ya kasa wucewa ya sake komawa ta dakin,sai biyu yana murda handle din yana jinsa a riqe da alama ta kulle ne daga ciki,ya sassauta murya yana kiran sunanta
"Open the door please, don't hurt yourself fa"
"Ka tafi ka bani waje abbas,na tsaneka,banason kallon fuskarta,ka tafi nace tun ban bude na lahantaka ba!!" Duk yadda yaso ta bude din taqi,sai ma wasu miyagun kalmomin da zagi da yake antayo masa,hannunsa nata digar jini,dole ya haqura ya dauki kit din ya koma dakinsa ya gyara wajen.
Daren ranar baccinsa ragaggene,haka yayita kai kawo tsakanin dakinsa zuwa sassanta,yasan halinta da muguwar baqar zuciya,yana fargabar kada ta illata kanta ita daya kulle a dakin,saidai duk sanda yaje din zaiji motsinta,wannan ke bashi 'yar nutsuwa kadan.
*Arewabooks: Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 27
Washegari yaran da suka tashi suka gansu wajen babansu sam basu damu ba,murna suka dinga yi abinsu,shi ya dinga tiri tiri dasu,ya shiga kitchen da kansa ya hada musu breakfast mai kyau,da yake ya iya abubuwa masu sauqi hakanan cikin abinci,saboda yanayin karatun da yayi.
Sunci kuwa sosai kamar ba gobe,sai ya zauna yana kallonsu,zuciyarsa na gaya masa basa samun kamarsa,duk da store dinsa cike yake da cima kala kala,wani abun har ya rube ko ya lalace batayi amfani dashi ba bata kuma bayar ba saboda baqar rowa,yayi nasihar yayi nasihar har ya koma fadan amma a banza,mutum ne shi mai bajintar wadata iyali tun samunsa baikai haka ba,tun rank dinsa bai kai haka ba,baya son iyalinsa suga wani abu a wani gidan da babu shi cikin gidansa,to amma kusan duk wannan qoqarin nasa a yawancin lokuta a banza yake tashi.
Ruwan tea kawai ya iya sha bayan ya tabbatar sun qoshi,duk ransa a jagule in yake,saboda har sanann hafsat bata bude qofarta ba,yayi knocking yayi har ya gaji,ya ajjiye mata nata breakfast din bakin qofa amma baiga ta bude ta dauka ba.
Bayan duka sun gama ya maida kwanukan kitchen,ya zage kamar yadda ya saba yawa yawan lokutta ya soma gyaran sassan nasa,yayi masa qal yadda yakeso,ya canza bedsheet da sauransu,ya hada duk abinda ya cire da kayansu mimi da yayi musu wanka cikin laundry basket,ya aje inda mai wankinsu zai dauka,sannan shima ya shirya kansa sannan suka dawo falon hafsat din,koda wai zataji motsinsu ta bude qofar.
Saidai har suka gama zamansu ba ita babu dalilinta,a taqaice dai har zuwa azahar bata fito ba,yanason fita masallaci sallah amma kuma bazaiyiwu yabar yaran su biyu cikin gidan ba,don ita mimi din ma ba wani cikakken hankali ne da ita ba,dole ya hada kansu suka wuce sassansa,acan yayi sallar,sai la'asar daya dawo dora musu abinci yaga babu plate din daya ajema hafsat din,da alama yunwa ta korota,ta bude qofa ta dauka kenan,sai ya saki qaramin murmushi ya wuce kitchen din.
Har dare suka kwanta babu wanda yaga qyallinta,a taqaice dai washegari kusan abinda aka maimaita kenan,don haka a kwana na ukun ya shirya yaran da kayansu ya wuce gidan hajiya dasu.
Kallon farko data masa tasan hatsaniya ke tashi a gidan,ta kuma san bata rasa nasaba da batun aurensa,bata matsa da jin ba'asin kawo yaran ba,saboda tasan shi da zurfin ciki,zaiyi wahala ma ya iya zama yana fadin cikinsa,ta daiyi murna da zuwan nasu,don ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ta faru ba.
Ya jima a gidan,sai yammaci sannan ya wuce,a sannan tuni nawwara tayi bacci a jikinta,ta baiwa muneera ta kwantar da ita,sai data dawo ta zauna gefan hajiyan
"Hajiya da alama anty hafsat fa......"
"Na sani muneera" hajiyan ta katseta,saita rausayar da kai
"Shima uncle,ya haqura kawai hajiya suyi zamansu mana,irin wannan babu dadi fa don Allah" kallonta hajiya tayi,batasan ko taji abinda uwayenta ke fada ba,har mamaki suke bata yadda suketa goyon bayan hafsat akan auren nan,wanda tasan tsabar son zuciya ne,amma babu wanda baisan halinta ba da dabi'arta,idan sunce basusan yadda abbas yake samun careless daga wajenta ba wannan kam ba zata musa ba,don babu da wanda yake zancan,amma kuma sauran dabi'unta da abbas din ya dinga yaqi ta gyara fa?,ita hajiyan tasna wasu,saboda takan bashi shawari idan ta fuskanci yana cikin damuwa ne
"Ke yarinya ce,ba zaki fahimta ba,sannan keba namiji bace,nan ma ba zaki gane komai ba" amsar da hajiyan ta bata kenan,sai tace
"K'nnnn,ai shikenan" base on her experience tayi maganar,saboda taga halin da mamanta ta shiga sanda babanta yace zaiyi mata kishiya,a sannan hajiyan ce ta shiga batun(muneera 'yar dan hajiyan ce),duk da.bai fasa ba anyi,amma abubuwan da sauqi,to amma yanzun hajiyan da kanta takeson ayima anty hafsat din?.