Showing 225001 words to 228000 words out of 296907 words
Chapter 76 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
ka samu kebewa da matarka?,me yasa baka gayamin ba?,ai da ban dawo yanzu ba bare naga cin amanar da kuke aikatamin"
"Cin amana kuma?" Widad ta fada cike da zallar mamaki, saboda nauyi da kalmar tayi mata,me yasa hafsat din take abu kamar kwancan hauka?, uncle abbas din kwartonta ne ko kuwa?,ita bataga dukka abinda yake faruwa a gidan ba,oh.....hala ma dadi abun ya mata kenan?,shi yasa a jiya fanna keta mata fada kan matakin da ta dauka,tace sam baiyi ba,zata sake nesanta kanta da mijinta ne hadi da kawo kusanci tsakaninsa da hafsat din,ta gani,ta gani kam
"Ke ba dake nake ba,kiyimin shuru tun ban cimmaki na lallasaki ba" wani murmushi widad din ta sake,hankali kwance ta girgiza kai
"Wuce nan......wuce nan wallahi,me jiya ma tayi ballantana yau?"
"Ya isa....ya isa" abbas ya tsaidasu yana daga hannunsa,hafsat dake kallon widad kamar wata sakarya cike da madaukakin mamaki yadda yarinyar ke kallonta kanta tsaye,ba alamun tsoro ko shayi a tattare da ita,ta dauke dubanta daga kan widad ta mayar kan abbas
"Kaga abinda ka jawomin ko a wajen diyar cikina?.....shikenan b......burinka......yac.....cika" tana kaiwa qarshe kuka ya kubce mata,sai tayi dakinta da gudu gudu ba tare data dauke jakarta a wajen ba.
Kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai mimi da nawwara suka shigo da gudunsu hannuwansu dauke da leda babba
"Daddy.....kaga abinda abban kaduna ya bamu,yanata sallama bakaji ba,yace zai dawo anjima" idanunsa dauke dauke da damuwa da bacin rai ya bude yana kallon yaran,abban kaduna amini ne ga mahaifinsa,kuma shine a yanzu ya bashi part daya cikin gidan suke zaune,saboda yana kallonsa tamkar dan cikinsa.
"Me aka samo mana" widad ta fada cikin qoqarin kawo raha da kawar da bacin ran data fuskanci ya taba zuciyarsa,ta karba ledar ta bude tana biyewa yaran tare da sako abbas din a ciki.
Cikin mintuna qalilan tayi nasarar kore masa bacin ransa,shima ya zauna cikinsu ana rabon kayan wasan yara fal leda da chocolates masu yawa daya kawo musu,sai da aka kusa kiran sallah sannan ya nufi daki yace zai daura alwala,su shirya idan ya dawo zasu fita yayi musu takeaway.
Murna yaran suka hauyi,nawwara tace baei ta gayama mommy sai mimi ta jawota
"Kina gaya mata zata hanamu zuwa,don Allah kada ki gaya mata kawai kiyi Shuru"
Tsaf ta shirya cikin gold laffaya data sake fiddata a jinin larabawa sosai,sanda ta fito parlor din narkewa abbas yayi a wajen yana binta da wani kallo mai nauyi,ko nawa ne.....kuma komai yawan kudi bayajin qyashin kashewa ya siya mata wasu kaya daya gani suka burgeshi ko kuma kayan gyara,saboda ya sani,komai ta saka yana dacewa da ita fiye da yadda ya gansu.
Yatsunta ta murza saman fuskarsa tana murmushi
"Yallabai" murmushin shima ya saki yana gyara tsaiwarsa
"Wudd(so,qauna,soyayya mai zafi)" kai ta langabe gefe,tana jin dadin sunan sosai
"Ka yima mommyn mimi magana sai mu wuce gaba daya,kada a dauko mata abinda batajin cinsa"
"Saidai ke ki kirata" ya amsa mata yana shafa gefan sumar fuskarsa zuwa habarsa,gaba daya ta gana tsumashi,bai taba ganin mutumin da ciki ya boye sosai a jikinsa,ya kuma yi masa mugu mugun kyau ba kamarta.
Kafada ta daga,ta kuma taka a hankali ta nufi dakin.
A nutse tare da sallama ta tura qofar ta shiga,da sauri hafsat ta daga kanta tana mamakin jin muryar yarinyar cikin dakin,sai data shiga sosai yadda zata ganta da kyau sannan tace
"Maman mimi..... uncle yace ki shirya ki samemu a mota,zamu dan fita shan iska" widad tayi maganar cikin wani salo me aji da gayu.
Ashar hafsat din ta saki sannan ta miqe tsaye kamar kububuwa
"Ga hanya nan ki ficemin daga daki tun baki raina kanki ba,ke har kin isa na shiga rigar alfarmarki don zan fita da mijina,idan kunje kada ku dawo" fuska tadan yamutsa cikin nuna yanayin alhini
"Ayyah....me yayi zafi?,Allah ya baki haquri" widad ta fada qaramin murmushi yana qwace mata,wanda hakan ya sake tunzura hafsat, saita tako kamar zata yo kanta,widad din ta juya ta fice abinta.
Ta samu duk sun fice daga parlor din babu kowa,don haka ta tsaya taci dariyar da taketa dannewa
"Inda ta kamaki da kinci qaniyarki" ta gayawa kanta da kanta tana ganin tsaurin ido da qoqarin da itama tayi dariya na sake qwace mata.
Ta jima tsaye tana duban bakin qofar bayan fitar widad din,ta hango soma wanzuwar raini qarara a tsakaninta da yarinyar,banda haka a baya yaushe ma ta isa ta isko falonta indai ba ita tayi kiranta ba sanda ta maisheta ma'aikaciyarta?,balle har ta samu sararin da zata shigo har daki ta gaya mata magana mai kama da jirwaye,saita koma ta zauna tana huci,ta sake tashi tana laluben su mimi,daga bisani ta fahimci dasu akayi tafiyar,domin kuwa ga kayansu nan tun na safe zube a falon,kenan har canjin kaya tayi musu,ta lailayo ashar ita daya ta dura
"Zasu ci ubansu ne,gobe ko dakinta akace su kalla ba zasu sake ba" saita koma daki kwanyarta cike fal da tunani, itakam dai banda uwa uwace,da tace anya ummanta tana mata abinda ya dace da dukka iyayen kudaden da take turawa da sunan za'a yi mata aiki irin wanda takeso?.
Widad da kanta ta zaba musu wani eatery suka sauka a can,kowa yayi order din abinda ransu yakeso,yau kam mimi kamar tayi me saboda dadi,don sam a gidansu bata saba ganin wannan rayuwar ba,shi kansa abbas din ba qaramin dadi yakeji ba duk sanda ya debo familyn nasa sukayi fita irin wannan,suna cin abincin suna raha a tsakaninsu,bayan sun kammala yayi musu takeaway suka tafi dashi,ya tsaya wani supermarket ya hado musu da sauran kayan qwalam.
Tayi zarya daga dakinta zuwa falon bayan fitarsu sau babu adadi,jiran dawowarsu kawai takeyi,suna sallama tana fitowa daga dakin,sanye da wata riga ruwan madara mai dan qaramin hannu daga can saman kafada,a saman rigar ta daura fallen zani.
A yadda taga abbas da widad din sun shigo a tare suna dariya ya sake hassalata,tana isa tsakar falon tasa hannu ta janyo mimi ta zuba mata mari
"Gidan ubanwa kika tafi?, daga yau idan akace ki sake binta ba zakiyi marmari ba,saikin gayan uban wa ya baki umarnin fita....." Tayi maganar tana sake cakumo yarinyar kamar ta samu babba,ta kuma ware yatsunta zata sake zuba mata masu,abbas ya dakatar da ita a tsawace
"Kina dukanta ba zaki sauke hannunki ba zan rama mata,kuma da izinin ubanta mahaifi ta fita" ya amsa mata cikin tsananin fushi shima.
Idanunta dake cakude da bacin rai ta daga ta kalleshi
"Me ka shawo a waje?,'yata zan hukunta kakemin shamaki?,to wallahi ba wanda a isa ya hanani hukuntata,tunda ba wanda ya haifa min ita" tayi maganar tana sauke kallonta akan widad da takejin inda za'a bata bindiga yanzu,a kuma bata damar kashe mutum guda daya tak a duniya ita zata harbe,bata sauke dubanta ba abbas ya zare yarinyar daga hannunta yana cewa
"Idan kina haukarki kiyi ke daya,karki sake kice zaki huce kishin haukarki akan yarinyata,don abun bazaiyi miki kyau ba" sai ya miqata ga widad dake tsaye tana kallon zallar hauka daga wajen mummy hafsat din.
Ganin ya miqata ga widad saita zabura
"Karki sake ki tabamin 'ya don baki da iko da ita,idan kinji haushi kema ki haifi taki" waiwaya abbas yayi yayi mata alamar su wuce daki abinsu,kwnataccen murmushi ta sake masa a shagwabe
"Take it easy sir.....banason ka qare da ciwon kai please" kai ya gyada yana lumshe ido
"I Will handle it in sha Allah" saita kama hannun mimi suka wuce dakinta,suna tafiya tana shafa mata wajen tare da lallashinta,akwai qauna sosai tsakaninta da yarinyar,tana son widad din sosai,wannan yasa itama widad din duk cikin 'yan uwanta tafi sonta,uwa uba ma kama da takeyi da uncle abbas dinta.
Shihewarsu daki da mimi ya sake hargitsa hafsat din,ta fashe masa da kuka tana masa hauka sosai,widad dake daki batasan ainihin abinda ke faruwa ba,don bata tantance abinda hafsat din ke fada,amma tashin muryarta da hayaniyarta ta tabbatar har harabar gidan ta isa.
Batasna ya suka qarke ba,wajen goma da rabi ya shigo dakin,sosai kansa yake sarawa,qasan zuciyarsa yana ambaton sunan Allah,mutum ne da baya qaunar hayaniya ko kadan,ga hafsat kuma wannan din ba komai bane,ya duqa yasa hannu ya dauki mimin
"Ka barta uncle ta kwana a nan" kai ya girgiza kadan
"No.....i need space,i want to be with you..... only you" jin abinda yace sai bata qara magana ba,bashi ba,ita kanta tasan tayi tsananin kewarsa,tana kuma buqatarsa,ba zata bari kuma haukar hafsat ya bata musu wannan daren ba kamar yadda hajiya sha'awa tasha gaya mata
"Akwai hanyoyi da yawa da kishiya zata iya sace miki kwana,bawai saita hanyar dauke miki miji ya kwana a dakinta ba".
Ko inda take zaune tana gursheqen kuka bai kalla ba ya kwantar da mimi daketa baccinta saman gadon,ya gyara mata kwanciyar gami da tofeta da addu'a,ya tsaya sosai bisa qafafunsa yana duban qofa
"Ko qwarzane na gani da safe a jikinta,wallahi wallahi ki kuka da kanki" daga haka ya fara nufar qofa
"Ai da saika barta wajen uwar daka sake mata" Ta amsa masa tana sakin wani kukan baqinciki daga zuciya zuwa maqoshinta.
Kamar yadda ta saba bata barshi ya kwana da wani bacin rai ko tunanin hafsat ba gaba daya,ta dauke dukka wani tunani da hankalinsa zuwa wata duniya ta daban,ta sakar masa ragamarta gaba daya,ya fanshe dukka wata gajiya bacin rai da kuma bashin daya dauka a kanta,shi kansa yasan ya bata aiki da yawa,bashi da wani sauran aiki sai lallabarta da tattalata da ya shiga yi tamkar wani sabon qwai.
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 13
*W A S H E G A R I*
K'arfe shida da mintuna na saafiya ya baro masallaci,bayan ya gama 'yan addu'o'insa.
Daga bayansa yaji tafiya,kafin ya waiwaya an ambaci sunansa,tuni ya gane muryar sai ya rage tafiyar da yakeyi yaja baya kadan hadi da waiwayawa.
Karasowa mutumin yayi fuskarshi qunshe da murmushi ya miqawa abbas din hannu,maimakon ya bashi hannun shima sai ya rusuna yana gaidashi cike da matuqar girmamawa.
Kin amsa masa yayi har sai da sukayi musabahan,duk da har yanzu abbas bai miqe tsahonsa ba saboda bashi girma
"Ban sani ba ko yara sun gaya maka saqona" yayi murmushi
"Eh abba.....sunce kazo zamu gaisa"
"Eh.....to ma sha Allah,na sake dawowa amma ban samu ganinka ba dai,mu qarasa gidan,inason magana da kai" tare suka jera da mutumin,suna tafe suna dan taba hirarrakin da suka shafesu,har suka isa cikin gidan.
Bayan gaisawa da ma'aikatan gidan,kai tsaye suka wuce setting room dinsa.
Sunansa abban ya kira yana duban fuskarsa
"Nazo jiya sau biyu kamar yadda na gaya maka,saidai duk zuwan da nayi din na iske rikici ne da hayaniya tana fitowa daga gidan har harabar gidan nan,ya akayi kabar gidanka yake neman zama haka?,me yake faruwa?" Gyara zamansa abbas yayi yana sunkuyar da kansa,abban kamar mahaifi yake a wajensa,babu abinda zai boye masa,don haka ya gaya masa komai.
Shuru yayi na wasu mintuna sannan ya sauke ajiyar zuciya
"Ba yadda za'a yi ka ajjiye mata biyu a guri irin wannan sannan kayi zaton samun kwanciyar hankali,muddin kanason zaman lafiya saidai ka raba musu muhalli,wannan shine kawai hanya daya da zaka samu dai daito akan irin wannan matsalolin,daya bataga 'yaruwarta ba bare wani abu ya biyo baya" kai abbas yake jinjinawa yayi, masa godiya sosai,lallai shawarar abban tayi masa qwarai,ya kuma bashi mafitar da shi a kansa ma bai kawo hakan ba
"Amma.....ita hafsatu meye ya dawo da ita kaduna idan ba zallar neman fitina bama?" Abban ya fada cikin mamaki, saboda fes yasan halinta ya kuma san abinda ya wakana wancan karon,abbas din yayi qasa da kansa,yama rasa wacce irin amsa zai bawa abban,Allah shine masanin gaibu,kuma shi daya yasan yadda yakeji a qirjinsa game da dabi'a da halayyar hafsat din,shi kadai yasan irin haqurin da yakeyi da ita
"Kada ka damu,kaci gaba da addu'a,sannan kaci gaba da jajircewa,Allah ya kawo mafita ya shige gaba"
Ranar bai fita aiki ba,gaba daya sai yaji bashi da kuzarin fita aikin, widad din ta gama kashe masa jiki da xuciya da soyayyarta,a irin abinda take masan,yaso ace gidan nasu kamar daa ne sanda suke daga shi sai ita.
Rashin fitarsa aiki ya sake harzuqa hafsat din qwarai,ta sake birkicewa sanda ya fiddo kaf kayansa dake dakin widad da wanda yake dakinta,ya kuma raba komai yace kowacce ta dauka,ranar kamar zata ara hauka
"Wallahi na yarda.......yarinyar nan mallaka da asiri takeyi mai matuqar qarfin da yafi nawa" hankalinta ya tashi sosai,tana ganin abubuwan kamar suna fin na baya lalacewa da jagwalewa,ta rasa inda zata tsoma ranta ranar taji dadi,tanason tayi waya kuma tana shakkar kada ya shigo ko wani ya jita,dole ta dinga hadiyar bacin ranta ita kadai zuciyarta kamar zata fashe.
To tun daga ranar abbas din ya fara neman wani gidan ba tare da sanin kowa a cikinsu ba,satin gaba kuma da zasuje bauchi hutu,zuwansu na farko bayan tahowarsu dukka gaba daya kaduna.
Daren da suka isa da qyar widad takai safiya cikin gidan,saboda wani birkicewa da tayi,an dasa ma zuciyarta wani mummunan tsoron gidan,kwanan zaune tayi tana rusa kuka,tana jin kamar ta fita da gudu tanar cikin gidan,wani irin qunci ne ya cika mata qirji,tana jinta kamar wadda aka jefa cikin dokar daji ita daya.
Sosai hankalin abbas ya tashi lokacin da ya biyo da asuba dubata ya sameta firgai firgai,tana ganinsa ta fada jikinsa ta saki kuka,tambayar duniya me yake faruwa ta gaza yi masa bayani,abu daya dai take fada
"Banason gidan nan uncle don Allah,ka kaini wajen hajiya ko gidansu nujood" ko fita a part din ta hanashi,bata wani damu da jarabar hafsat da zata iya biyo baya ba saboda zamansa a part din nata ranar kwananta,haka shima abbas din,ba wannan bane damuwarsa,abinda ya sauya widad din yasa ta firgice haka ke bashi mamaki,bayan yasan lafiya qalau suka baro kaduna.
Ko part din bai bari ba ya sanyata ta shiga toilet tayi wanka,wankan ma da da tace tayi idan sunje gidansu nujood yace aah,kafin ta fito ya shirya mata jakarta da kansa,ta fito ta shirya agurguje kamar wadda ake jira suka fito ya kulle mata sashen da kansa,yanata binta da kallo cike da mamakin abinda yake damunta.
Sai data shiga motar sannan yace mata yana zuwa,ya juya zuwa sashen hafsat.
Da sauri ta bar bakin window din,ta koma saman dining tana ci gaba da gyara kwanukan data zuba akai,duk da ba wani abun kirki ta dafa ba,a cewarta ta gaji,ba zata iya wani dogon aikin abincin safe ba.
Amsa sallamarsa tayi kamar bataga komai ba,ta daga kai tana dubansa,shima ita yake kallo, already ya saba ba kasafai yake gaidashi da safe ba,wani lokacin yayi mata gyara wani lokacin ya watsar da ita
"Zan kai widad gidan muhsin kada ki jini shuru"
"A dawo lafiya" ta amsa masa ba tare data dubeshi ba hankali kuma kwance,tana jin wani dadi yana ratsata,sai ya shafa kan yusra dake kwance cikin kujera sannan ya juya ya fice.
Yana fita taja wani mugun tsaki sannan ta saki dariya
"Habaaaaa yarinya,ki hanani sakewa a can a nan ma ki hanani?,Allah ya raka taki gona,da ikon Allah ma kin fita kenan ba zaki sake dawowa ba" ta sake rufe zancan nata da tsaki,tabar aikin da takeyi din ta koma saman kujerar tana karkada qafa,a duniya ita daya tasan yadda yarinyar tayi mata karen tsaye a rayuwa,duk yadda takai ga zuba iskancinta bata taba fuskantar matsala irin wannan daga wajen abbas ba sai yanzu,ta sake jan wani tsakin
"In sha Allahu sai nayi maganinki,bazan gaji ba wallahi" ta fadi a fili kamar ita da wani suke magana.
Kamar cirar qaya haka taji bayan fitarsu daga gidan,sai taji komai yana raguwa cikin kanta, nutsuwarta tana dawo mata a hankali a hankali.
Sanda suka isa gidan ta shiga ciki mamaki ne ya kama hajjaa,koda ta tambayeta lafiya?,ce mata tayi ba komai,kawai ta gaji da zaman gidanne.
Cikin mintuna qalilan ta sake sosai kamar ba ita ba,zuwanta ya yiwa yaran gidan duka