Showing 207001 words to 210000 words out of 296907 words
Chapter 70 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
matan ya qona mata rai sosai,ta tabbatar akwai gagarumin dauki ba dadi da zai biyo baya kafin ta samu bauqatarta ta biya,sai ta dauki wayarta kawai tayi kiran ummanta ta gaya mata yadda sukayi
"Ai gaba da gabanta,baba ma da babanshi,ki kira babarsa ki gaya mata,itace dole zata turasashi kuma yabi" fuska hafsat din ta yatsine
"Nifa matar nan ban yarda da ita ba,sonshi take fiye da kowa cikin yaranta,munafuka ce kawai,umma....na gaji da kaishi qara,don Allah don annabi ayi a kammala aikin nan,nafison idan nace eh ta zauna kawai" ajiyar zuciya ta sauke
"Hafsatu.....da mijinki da kishiyarki aikinsu dole sai an dinga binsa a hankali,idan kuma ba haka ba yace za'a yi hasara masu yawa"
"Ko hasarar mecece can ta matse musu ayita indai buqatata zata biya"
"Aah.....ke bari kiji,daga bangarenmu ne hasarar,shi yasa nace abi a sannun,inda daga gurinsu ne ina ruwan wani?,da tuni aikin gama ya gama ai" sun jima akan wayar suna tattaunawa,duka saqa ca a mugun zare da yadda zasu ida mugun nufinsu.
Har ta ajjiye wayar ta tuna da yaya baraka,dabarar kiranta takai mata qara a wannan karon ta fado mata,kai tsaye tayi kiran nata,bugu uku ta daga.
Suna gama gaisawa ta fashe mata da kuka,sannan ta rattabo mata abinda yake faruwa,bayan ta qawata zancan da qarya da gaskiya,yaaya barakan ba komai ta sani akan lamarin gidan abbas din ba,tunda itace babba a dakinsu itama ba shiga zancan takeyi ba,a yadda hafsat din ta gaya mata maganar sai taji ranta ya baci sosai,saboda rashin adalci zalla data hango,sannan hafsat din tayi sara akan gaba,don bata jima da jin tsegumin da ake na tafiyarsu widad din hajji akabar hafsat a gida ba
"Zan sameshi nayi magana dashi,basaima hajiya taji ba,ki kwantar da hankalinki,wannan ma ai rashin adalci ne,ita widad din da gwal aka yita da zaiyita yawo da ita gari gari ke ya barki tsugunne da 'ya'ya?,ya ajjiyeta a tafi dake wannan karon,ko kuma ya hada kanku duka ya tafi daku,shi yaga zai iya" maganar tayi mata dadi,don haka sai tahau shirinta abinta,duk da shirin ya hadu da cikas,kusan kowanne kaya nata suna da naqasu,da qyar take tsintar wanda zata iya dauka a ciki.
°°°°°°°°°Yana daga zaune saman carfet tana kai kawon dire masa abincinsa,duk inda ta gifta sai ya bita da ido,yana jin wani abu yana tsarga masa dangane da ita,a yanzun data sallama masa kanta yadda yakeso,sai.yakejin kamar shi kadai yayi sa'ar mace a duniya,komai na matsalolin hafsat a yanzun baya musu kallon da yake musu ada.
Boom Short ne a jikinta da wata armless turtle neck shirt wadda ta kama jikinta,dukka kayan black ne,wannan ya qara fitar da haskenta sosai,ga wani kyau me jan hankali,ya kasa dauke idonsa daga kanta,ba wanda zai kalleta yace akwai juna biyu a jikinta,yabi tsaho da kuma qibarta ya boyeshi tsaf.
Zuwanta na qarshe ta ajjiye masa strawberry juice data hada masa,zata miqe ya kamo hannunta da kyau ya kuma jawota jikinsa a tausashe yayi mata mazauni saman cinyarsa yana cewa
"Na gaji da wannan qwalelen da aketa min tun daxu,ko yaya dai ai kyazo naji duminki ko?,kinsan kuma nayi missing dinki fa" ya fada yana saka hannunsa ya ware gashin kanta,ya cusa fuskarsa cikin wuyanta yana shaqar azababben qamshinta daya sauya daga aihinin wanda ya sani
"Ya sub....hanallah.......babyn uncle so kike ki kasheni.....wannan qamshin......" Sai ya kasa qarasawa ya sake cusa kansa sosai a jikinta,sumarta tana yiwa kansa da fuskarsa rumfa, yayin da ita kuma ta saki siririyar dariya tana riqe kansa da kyau saboda saukar hucin numfashinsa.
Basu ce komai.ba sukaji an tura qofar falon da mugun qarfi,a firgice weedad ta maida dubanta ga qofar,shi kuma ya zaro kansa daga inda ya boye fuskarsa yana kallon bakin qofar da idanunsa da suka sauya launi.
Hafsat ce,baya tayi.kamar zata fadi,tunda take bata taba mummunan gani irin wannan ba, widad ce saman cinyar abbas din?,ko ita ba zata iya tuna when last da tahau cinyarsa kamar haka ba,wani abu me zafi ya taso ya riqe mata qirji,ta fada zuqar numfashi da qyar.
Motsawa widad din tayi da nufin zamewa daga kan cinyarsa,sai ya janyota ya gyara mata zama sosai akam cinyar tasa yana zagaye qugunta da hannayensa,yayin da idanuwansa ke kan fuskar hafsat yana kallonta cikin bacin rai,ita kuma widad din take kallo,tana jira taga ta sauka,amma sai taga ko motsi batayi ba,saima shirin jingina da take da jikinsa,saboda yadda ya hanata sauka daga cinyar tasa,kunyar yadda ta gansun kuma tana tabata,duk da haushi da taji na yadda ta shigo musu babu ko sallama
"Wajenka nazo" ta fada murya a tsaye,tana fatan widad ta sanya baki a maganar ko zata samu hanyar da zata dake ta fa huce takaicinta
"Fita waje ki jirani"
"Yaaya baraka ce tace na kawo maka waya tanata kiranka baka dauka ba" ta fada a kausashe tana jin yadda hawaye keson kunno kai cikin idanunta tana hanasu zuba,wannan cin fuska da rainin da yarinyar tayi mata har ina,tana zaune sosai saman cinyar mijinta kuma tana kallon qwayar idanunta?.
"Ki fita nace ki jirani" ido ta zuba masa kamar zuciyarta zata fado,ita yake kora a gaban qaramar yarinya?,saita jinjina kai ta fice fuuu kamar zata tashi sama.
Da sauri ya sanya hannu ya sake tarota sosai cikin jikinsa,ya maida gashinta gefen kafada yana sake zura kansa gefen wuyanta
"Un..... uncle" ta kirashi murya a rarrabe, fuskarsa kawai ya dago dab da tata yana kallon fararen qwayar idanunta
"Kace mummyn mimi ta jiraka a waje fa"
"Ba zata jirani ba,tafiya zatayi"
"Amm....."
"Shshshs......" Ya fada yana dora yatsarsa akan labbansa yana duban qwayar idanunta
"Kada kicemin komai,sannan daga yau,duk sanda ta sake shigo miki waje irin haka muna tare kikace zaki matsa ko zaki tashi,zan hukuntaki ne,ai bata nema izininki ba kafin ta shigo miki waje.........ko ban fada miki ba nasan dole ki sani,a nan ne kadai wajen da nake samun nutsuwa da kwanciyar hankali,kawai sai na bari lissafina ya dagulemin?,nayi wasa da damata kamar yadda tayi wasa da tata?,come-on.....forget her, let's continue to enjoy" ya fada yana sake shige mata.
Sai daya gama rage zafinsa sannan yace ta dauko masa wayar,ta dauko ta miqa masa cikin girmamawa,ya saki murmushi yana cewa
"Thanks" sannan ya buda wayar yana duba me kiran.
Yaya baraka dince,sai kawu hassan,kowanne miscall bibbiyu yayi masa,baibi takan yaya baraka ba,tunda har sunanta ya fita a bakin hafsat yasan akwai wata a qasa,bare yana sane da maganarsu ta daxu,sai ya fara da kiran kawu hassan.
Cikin girmama juna suka gaisa,sannan ya shigar masa da zancan baraka ta sameshi da batun iyalinsa kan komawa kaduna,ya yiwa kawu hassan din bayanin komai,yayi shuru yana nazari
"Duk dadai mun gama magana da hajiyarku,kusan abu daya muke gani,kayi.haquri ta biku kada duniya ta zageka,kuma ita kanta kada ta sake daukar cewa kana hakanne don rashin adalci,don rashin kyautawa bata kyautata ba,amma ko yanzun ma baka da tabbas din zata zauna idan taje din,tunda mai hali baya fasa halinsa,don haka ka zuba mata ido,taje din".
Koda suka gama waya da kawun hajiya ya kira,itama kusan abinda tace dashi kenan,dole ya sauko daga dokin naqin da yahau,saidai baice mata zataje ko bazataje din ba,ya barta tana ta raba ido da taraddadin zai yarda ko zaiyi halin nasa na kafiya,saida asubahin ranar da zasu tafi tunda girkinta ne yace ta shirya da wuri zasu wuce.
Jikinta na rawa take kintsa abinda zata iya,qarfe goma na safe sale ya gama fidda kayansu duka an zuba a booth din motarsa,dole ya canza motar komawa saboda wadda suka saba zuwa da ita kamar zasu matsu da yawaga yara biyu ga hafsat din ga widad gashi.
Ta riga kowa fitowa ita da yaran,ta buda gidan gaba ta shige ta watsa yaran a baya
"Kya zauna a cikinsu,dama nan ne yafi dacewa dake" ta fada a ranta,don dama ko sama da qasa zasu hadu batajin zata yarda ta barwa widad din gidan gaban.
Batasan ma me yake faruwa ba,ta fito abinta a shirye tsaf cikin wata atamfa dinkin A shape budadde sosai,duk da yadda hafsat din take ganin ta qurewa ado sai data raina kanta,sai dataji ta muzanta,ta zuba mata ido.tana fatan Allah ya kawo wani mummunan sanadin da zai dakushe wannan kyan da kullum kwanan duniya yake mata barazana cikin idanunta.
Tun bata qaraso ba taja hankalin abbas dake tsaye jikin motar yana amsa waya ba tare da yakai ga shiga ba,ya bita da kallo tun daga can harta kawo bakin motar,yaran duka suka fito suna mata oyoyo tasa hannu ta rungumesu cikin jikinta,mimi tace
"Anty qamshi,qamshi kike,ki sakamin turaren nima"
"Yanzu kuwa.babbar qawa" ta fada tana zuge hand bag din dake maqale a hannunta,ta fidda qaramar kwalbae turare mai kyan gaske ta fara fesawa yarinyar
"Ranki ya dade.....mu baza'a san mana qamshin ba?" Abbas data gama kashe masa jiki da adonta ya fada yana turo hularsa gaban goshinsa.
Zata iya cewa hatta kalar murmushi hajiya fanna sun koya mata,daya daga ciki ta aro ta aike masa dashi tana juya fararen idanunta,saqonta kuwa ya isa,don kasa takawa yayi ya koma a dole ya manne bayansa da motar yana jin qafafunsa sun saki
"Idan ba'a fesa maka ba wa za'a fesawa" sai ta tako a hankali ta matsa gabansa ta fara fesa masa turaren daga wuyansa zuwa qirjinsa,sanyinsa da qamshinsa ya ratsa fatarsa,ya saki ajiyar zuciya,sai ya kama hannunta ya riqe cikin nasa yana cewa
"Kada fa ki jawo hannun agogo ya koma baya,zan iya kasa tuqin nan f........" Bai qarasa ba uban horn din motar ya karade gidan,a tare suka juya zuwa ga motar,yayin dasu mimi suka tsorata saboda yadda ta danne horn din har baka iya jin abinda wani ke fada.
Hafsat ce da komai ya faru a gaban idanunta,abinda suke fada ne kawai kunnuwanta basa iya jiyowa,sabida Glass din side din a rufe yake,ta cika tayi fam kamar zata fashe,ita zasu rainawa hankali su shanya a cikin mota?,zame hannunsa yayi ya tako a nutse ya buda murfin motar yana kallonta
"Idan tafiya tafiya,idan zama zama,ya zaku tsaya gaban yara kuna abu iskanci iskanci?" Ta fada tana huci,tana jin kamar ta fita ta kamo widad ta shaqeta.
Kamar ransa zai baci sai kuma murmushi ya kubce masa,ashefa ita duk irin wadan nan abubuwan a rayuwar ma'aurata iskanci ne a wajenta,kuma shi har ga Allah ya manta da ita
"Yi haquri mommy" yana fadin haka ya maida.murfin ya rufe,bai dai fasa ba,sai daya koma ta fesa.masa turaren sannan suka dawo cikin motar,xuwa sannan tayi nisa wajen juya kalmar.mommy daya jefeta da ita,aiba haka yake gaya mata ba,yanzun kuma daya fada me yake nufi kenan?,babu me amsa mata,haka suka cika motar da karadinsu widad na biye musu tana kume jefo abbas a ciki shima yana shiga sabgartasu,har ta dinga jin kamar sunyi watsi da ita ne kawai,kamar babu ita ne a cikin motar gaba daya, abun da ya isheta saita dakawa mimi tsawa
"Banason shegen surutu,ki kama min bakinki a wajen" yarinyar tayi tsuru tsuru,sai ta bawa widad din tausayi,ta lura tana yine saboda ita,taja yarinyar jikinta ta fara mata hira qasa qasa,sai gashi ta ware,abbas da yaji shuru yace
"Wai me aka gayawa mamana ne tayi shuru haka?"
"Daddy labari ake bani me dadi" mudubin gefansa ya saita yadda zai hangesu da kyau,suka hada ido ya kashe mata ido daya
"Retired za'a yimin?,ba haka mukeyi dake bafa" baki tadan murguda masa,abinda ya fusgi hankalinsa kenan,don bai taba gani tayi ba sai yau,har sai da murmushi ya subuce masa ba tare daya shirya ba,yayi mata sign na tuba yakeyi saita dauke kai tadan qara volume kadan na muryarta,motar ta dauki shuru suna biye da ita.
Tarihi take basu na daya daga cikin sahabbai,kusan ya zauna sosai a kanta saboda alhaji na yawan yi.mata shi,sosai tarihin yake shigar abbas din yana mamakin yadda ta riqe komai exactly,hafsat da takejin muryar widad din kamar tana watsa mata ruwan zafi taja tsaki karo na kusan goma
"Nifa gsky an shiga hakkina"
"Da akayi me?" Ya jefa mata tambayar ta sigar ko in kula
"Lallai ne kowa sai yaji abinda take fada?"
"Ba lallai" ya fada yana zura hannunsa aljihun motar,ya ciro wata mini laptop da earpiece ya xube mata ba tare da yace da ita komai ba,sai tabi kayan da kallo kafin ta maida kansa,saidai tuni yaci gaba da abinda yakeyi kamar ma baiyi komai ba.
*H U G U M A*
*Arewabooks: Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 05
Kafin sukai kaduna zuciyarta kamar xata fashe,bata samu sauqi ba saida bacci ya daukesu mimi,widad kuma ta sanya earpiece abinta ta kunna data tahau watsapp.
Saidai duk da hakan hankalinsa yana kanta,bini bini ya juya ya gani,ta rasa da wacce siga zata masa magana juyawan da yakeyi tana jinta kamar a qahon zuciyarta yake soka mata abu mai tsini,amma yadda taga ya tsare gida tasan bata isa ma tace komai ba,haka ta dinga cinyewa kamar ta zuqo kaduna ta rage nisan tafiyar suyi su isa,saidai wannan abun ba zata barshi ba,dole taci uban yarinyar da kyau.
Qarfe biyu da mintuna suna cikin gidan,kowa na gidan na maraba da dawowar abbas din,kasancewarsa mutum me kirki da kyauta,ma'aikatan gidan suka kwashe kayansu zuwa falon gidan.
Shi ya buda musu parlor din ya koma don gyara parking,hafsat ce a gaba,tana tafe tan qarewa parlor din kallo,komai na parlor din ba wanda ta sani bane,an canza abubuwa da yawa da wani irin tsari me kyau,komai qal kamar basuyi tafiya sun bar gidan ba,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,tana tuna lokacin data sanya qafa tabar gidan,tana jin duk duniya babu yadda abbas zaiyi da ita.
Awancan lokacin tana jin babu matakin da zai iya dauka,babu wata mace da zata iya shiga rayuwarsa,ashe babbar matsala ce zata biyo baya,yanzun gata ita kusan sa'ar diyarta ta fari inda auren wuri tayi zasu goga kishi.
Gaba widad tayi abinta,ta buda dakinta ta shige,tunda komai nata yana ciki,lokuttan baya kafin kusanci ya samu tsakaninta da abbas din ta koma dakinsa a nan take kwana,da kallo hafsat din ta bita tana jin kamar ta jawota,ganin yadda ta barta tsaye a falon,wato ta samu dakin zama kenan,taja wani mugun tsaki tana kallon dakin nasa dake kulle,sai ya shigo kenan zai bude mata dakin,ta koma ta zauna saman kujerar tana sauke shukra dake bacci,yaran nata guje guje da murnar zuwa gurin da suka jima basu zo ba.
Duka duka part din bedroom biyu ne,a dole abbas din ya budewa hafsat nasa bedroom din suka saka kayansu.
Tana daga gefan gado tana bawa yusra yusra mama tana qarewa dakin kallo shima,komai neat,qamshin shegiyar yarinyar ya kama dakin da kyau,da qyar take iya hadiye yawu saboda wani abu daya tokare mata wuya,ta cirr yusra data koma bacci ta kwantar da ita gefe,sai hannunta ya fada saman wani.abu mai taushi,ta janye hannun tana dubawa da sauri.
Baby pink rigar baccin widad ce wadda ta barta saman gadon garin sauri ranar da zasu bar kadunan,ta daga rigar tana qare mata kallo,bata da maraba da tsirara,saboda duk inda muhallin tsiraici yake neat ne a wajen da wani silk yard duka jikin rigar,nannade rigar tayi tayi wurgi da ita cikin tsananin bacin rai,ita za'a yiwa iskanci?,sai ta miqe ta fara bincike dakin,tun daga drawer dinsa zuwa toilet.
Da qarfi ta buda murfin wardrobe dinsa,idanuwanta ba zasu juri ganin kayansu a cakude waje daya ba,brassiere dinta da qananun kayanshi,kai tsaye ta miqe ta fita a dakin da nufin zuwa ta gaya mata tazo ta kwashe kayan nata.
A falo sukayi kacibus dashi yana shigowa riqe da hannun nawwara,ya bita da kallo
"Ina zuwa?" Kallonsa tayi qirjinta kamar zai fado saboda radadin da zuciyarta keyi mata
"Zuwa zanyi na gaya mata tazo ta kwashe kayanta a dakin" wani nutsatsen kallo ya bita dashi sannan ya gyara tsaiwarsa
"Ki barni da kaina zan gaya mata,sannan ma dole ki samu kayanta cikin dakin tunda batasan da dawowarmu tare ba" galala ta bishi da kallo kanta yana daurewa,ita abbas ke cewa ba'asan da zuwanta ba?,to banda ma iskanci da fidda sabon salo,tana cewa ita din sanda tana nan dankwalinta baya bari a dakin,kome ta bari sai ya sanya ta tattarasu ta fiddasu a dakin kafin ya rufe ya wuce aiki,shine yanzu zata samu kayan yarinyar cike a dakinsa,kayan ma na rashin arziqi da rashin kunya?.
Bai wani nuna ya lura da yanayin data shiga ba ya miqa mata nawwara
"Ki dafa musu wani abun suci kafin ku gama kintsa gidan,yunwa sukeji" bai tsaya jiran amsarta ba ya wuce ciki yana janye da luggage dinsa.
(Widad)
Tun shigowarsu gidan tare duka taji gidan ya canza mata,batasan me takeji game da biyosu da mummyn mimi tayi ba,amma dai tasan har ranta hakan bai mata wani dadi ba,saidai