Showing 159001 words to 162000 words out of 296907 words
Chapter 54 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
masu yawa da yasha tsarawa kansa a tsarin rayuwar gidansa,saidai da daya da daya komai yake rugujewa ya rushe,tsarinsa da ra'ayinsa yayi nisa qwarai dana hafsat,wasu abubuwan ma tana kallonsu as bata lokaci,ko kaiwa maqura,yana jin kamar a yanzun zai gina dukka mafarkansa ya kuma rayasu in reality.
Gaba daya ta saka jikinsa yayi laushi,bayajin zai iya driving dinsu daga kaduna zuwa bauchin,bashi da wannan qarfin kwata kwata,don haka ya ciro wayarsa ya kira samuel yace yazo zasu wuce bauchi yanzu yanzu.
Minti goma kacal samuel ya kirashi kan ya iso,already motar dama a wanke take,hakanan dukka kayansu suna ciki,sai ya miqe yana gyara rigarsa,ya dauki agogo da hularsa duka ya sanya,ya sake fesa turarensa,sannan ya kwashi wasu documents dake cikin wata folder ya fito.
A gaban fridge ya sameta tsaye tana shan ruwa,ya taka a hankali ya tsaya a bayan nata yana dora hannunsa saman nata hannun da ta riqe ruwan dashi tana sha,hannun ya qawatu sosai cikin wasu siraram banguls kusan guda goma ruby color da duka haska farar fatarta datayi wani fresh.
Qwarewa tayi, saboda gaba daya bata ji takunsa ba,ya sanyata a kafadarsa yana dan dukan bayanta harta daina tarin sannan ya janye jikinsa kadan
"Ki dauko komai?,samuel yazo xamu wuce" kai ta jinjina masa alamar eh,sai ya miqa mata document din hannunsa,ya ja mayafin dake kanta ya soma nada mata shi.
Baya ya danja ya kalleta,she looks very gorgeous,sai yaji kishinta yayi bala'in kamashi,har yaji kamar dama bai kira samuel ba.
Hannunta ya kama ya isa da ita gaban wani dan fashion mirror dake maqale cikin falon, murmushi ya subuce mata,ya akayi ya iya rolling haka?,ta cikin idanunta ya karanci tambayar dake cikin zuciyarta,sai ya saki murmushi
"Mimi da nawwara" a taqaice ya amsa mata amma ta gane,saita kauce gefe daya saboda kallon da yake jifanta dashi ta madubin yana mata nauyi da yawa.
Kafin su fita ya kira samuel ya masa aiken dole,wai fita dan kantin dake kusa da gidan ya karbo kasa biro,kafin ya dawo suna cikin motar,yana isowa yace ya aje masa wajensa zai karba,don kada ma.ya juyo har ya ganta,ya amsa masa a ladabce ya kunna motar suka fice daga gidan.
Tun basuyi nisa ba bacci ya soma fusgarta,sai yayi mata majingina da kafadarsa sosai,ya lalubo hannunsa ya sanya a tafin hannunsa ya hadesu waje daya.
Kusan awa biyu ta kwashe tana bacci,sanda ta farka saita janye jikinta daga nasa cikin jin nauyi,ya murmusa kadan yana dubanta
"Kin more min kafada,sai naci tararki" kafada ta noqe tana dariya cikin jin kunya.
Awa biyu da rabin suka shiga garin bauchi,sai tadan dubeshi har yanzu hannunsa yana cikin nata
"Gidan hajiya zaka saukeni" ta fada qasa qasa,don sam sai taji bata qaunar zuwa gidan.
Waiwayowa yayi ya zube mata manyan fararen idanunsa yana kallonta qasa qasa,cikin zuciyarsa yake son qiyasta yadda hakan zata faru,sai kuma ya girgiza kansa a hankali kafin ya dauke idamunsa a kanta
"Ba yau ba" ya fadi kansa tsaye,don baya jin zai iys nesa da ita
"Don Allah uncle" ta fada a mugun shagwabe kamar zata saki kuka
"No,Baby" komawa tayi ta lafe jikinta a sanyaye tayi shuru,tafison gidan hajiyan,tafi qaunar zama a can,saita fara sharar hawaye kafin ta sake masa siririn kukanta.
Idonsa ya lumshe yana jin wani abu mara dadi yana taba zuciyarsa,irin abinda bai tana jin kamarsa ba,duk da dama shi din kusan weak point dinsa kenan
"Is okay" ya fada yana sanya hannunsa cikin nata,sannan ya bawa samuel umarnin canza titi zuwa titin da zai kaisu unguwar gida dubu.
Ajiyar zuciya ta sauke,ta sake lafewa tana dan sakin murmushi
"Na gode" waiwaya yayi a hankali ya kalleta,sai ya sanya hannu yaja hancinta
"Karkiyi saurin godemin,don idan munje ba lallai bane na barki ki kwana ba" baki ta tura gaba,sai ta kwantar da kanta ba tare da tace masa komai ba,ya sake sakin qaramin murmushi yana kallon hanya hadi da matse hannunta sosai kuma a tausashe cikin tafin hannunsa,can qasan zuciyarsa yana jin wani abu mai qarfi a kanta yana sake ginuwa.
Ita ta fara shigewa gidan hajiyan cike da karsashi, zuciyarta fal farinciki,don kusan wata guda kenan bata zo ba,zuwanta na qarshe har suka koma batazo gidan ba.
Su biyu ne falon,ita da gwaggwo fanteka suna taba hira,sun gama cin abinci kenan tayi sallama,sosai farincikin dake fuskar hajiyan ya bayyana,ta amsa sallamar tana cewa
"A'ah,mutan kaduna.....irin wannan ba zata haka?"
"Aiko dai,haka amaryar abas din ta fara canzawa,ah lallai yarinya taji kiwo" gwaggwo fanteka data kama haba cike da jin wani abu a ranta me kama da qyashi qyashi ta fada,maganar da ta yiwa widad din nauyi,karon farko da kunyar hajiya ta kamata,musamman da ta tuna abinda ya wanzu tsakaninta da abbas din,sai take ganin kamar ma kowa yana iya karantar hakan,don haka tun daga dan nesa dasu ta zube tana gaidasu.
Cikin kulawa hajiyan ta amsa, gwaggwo fanteka kuwa ta zuba mata ido tana kallonta,sosai widad din ta canza,ta fara cika ta kuma yi kyau abinta,ta amsa tata gaisuwar tana sauke numfashi hadi da gyara zamanta
"Kundai tafi kunbar uwar gida da jiran gida ko?" Ta jeho widad da batasan ma kan asalin abinda kae faruwa ba tambaya
"Uhmmm,ina ruwan widad,ita da batasan komai ba akai" hajiya tayi saurin karbar zancan
"To ai shikenan,Allah ya kyauta" ta sake fada tana gyara zamanta,dai dai sanda abbas yayi sallama ya shigo parlor din,qaninsa muneer yana biye dashi da babban ledar da muddin da ransa da lafiyarsa baya gaza shigowa da hajiyan tashi ita.
Washe baki gwaggwo fanteka tahau yi tana sake gyara zama,lallai yau din ta shigo a sa'a,tasan cewa shar da ita zata fita,harda ita wajen marabtar abbas din,ya duqa ya gaidasu cikin girmamawa sannan ya koma ya zauna sosai daura da hajiyan tasa.
Miqewa gwaggwo fanteka tayi tana cewa
"Ni bari na wuce gida,naga la'asariya ta kusa"
"Ki tsaya mana ki karbi tsarabar taki?"
"A'ah haba,kya dai aiko muneera ko muniru ya kawomin,yallabai Allah ya huta gajiya" hannu abbas ya sanya a aljihunsa ya fidda sabbin 'yan dubu dubu ya miqa mata,tasa hannu kuwa ta amshe babu tayi tana zuba godiya.
Nan falon hajiyan yayi zamansa suna hirar yaushe gamo,duk danda widad dake kitchen tare da muneera ta gifta sai taji ranta ya mata sanyi,ta kuma sake godewa Allah,kallo daya ta yiwa abbas din harma da widad din ta karanci akwai wani gagarumin sabon canji cikin rayuwarsu,walwalar abbas din ta qaru,idan ma ba idonta bane ke mata gizo har 'yar qiba taga yadan qara,abinda bata taba gani a tare dashi ba,sannan duk sanda widad din zata gifta idanuwansa suna biye da ita,kamar yadda itama duk sanda ta ratso ta falon saita saci kallonsa.
Ana idar da sallar la'asar yayi shirin wucewa gida,yace ta fito su wuce,amma saita sakar masa darunta tana maqale wuya,idan zata shekara tana masa wannan shagwabar yanason gani,ba kuma zai gaji ba,tilas ya haqura ya barta bayan hajiya ta sanya baki,ya wuce gidan shi kadai,amma cikin jikinta da zuciyarsa duka sai yakejin wani iri babu dadi,kamar ya baro wani b'ari ne na zuciyarsa a wani waje.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 81
Kamar ko yaushe a harabar gidan ya cimma yaran,sunata wasan qasa sunyi futu futu dasu,qasa har saman kansu,amma hakan bai hanasu murnar ganin juna ba,ya tsugunna ya kwashe abinsa sunata masa surutu yana kerbewa.
Dab da zai shiga sashen nata ta fito,sanye da atamfa dinkin doguwar riga,tayi daurin ture kaga tsiya,duka gashinta da ba kasafai ta fiya son kitso ba ya fito abinsa ta qasan daurin,hannun brassiere dinta daya fito ta kafadarta ya sake muzanta shigar tata,atamfar anko ce da sukayi biki tun shekaran jiya,kuma tun shekaran jiyan take jikinta bata cire ba,sam batayi tsammanin zuwansa a yau din ba,shi yasa ta saki jiki ya sheqi baccinta,bata jima da tashi ba ta biyo sahun su mimi jin shuru ba motsinsu tun dazun.
Tare hanya tayi tana masa sannu da zuwa hadi da karbar jakar hannunsa,bata son ya shiga sashen nata,saboda ita kadai tasan irin badaqalar daya kwasa ba,don hatta da uniform din mimi yana zube a falon da school bag harma da tsadajjen lunch box dinta daya siya mata
"Mu qarasa sashen naka,dama fitowar da nayi gyarawa zanje nayi" ta fada tana sake kankane hanyar.
Bai musa mata ba,don a yadda takeyin din yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,bataso ya shiga yaga ba dai dai ba ya gyara mata ko yayi mata fada,ko shi din yasan idan ya shiga babu lallai ya samu sashen a yanayin da zai iya zama,so no need ya matsa sai ya shiga din,don haka ya juya da yaran suka wuce sashen nasa.
Tun daga qofa yaga abinda aka saba,a yau dinma sashen nasa babu gyara,yadda ya barshi kusan wata guda haka yake a yanzun,sai ya basar,ya ajjiye yaran ya zauna shima saman kujerun falon,ta yiwa jakarsa mazauni sannan ta juya tana kallonsa
"Bari na fara dora maka wani abun sai nazo na gyara nan din" manyan fararen idanunsa ya daga ya kalleta
"No,a bani abinda kuka dafa kawai da rana".
Da sauri tadan kalleshi,sannan cikin yanayi na rashin gaskiya tace
"Ba zaka iya ci ba,infact ma inajin sun cinye....."
"Eh daddy,indomie ce mommy ta dafa mana,kuma saida nawwara ma tace tana jin yunwa s......" Yarinyar bata qarasa ba saiji kake fafff ta doke mata baki,take kuwa bakinta ya fashe
"Shegiyar maganar tsiya,muna magana uban waye ya sako bakinki a ciki?" cikin bacin rai abbas ya kama leban yarinyar yana dubawa,sai da ya gama ganin iya wajen da ya fashe din,ya goge mata wajen ya dorata kan cinyarsa yana lallashi sannan ya dubeta cikin bacin rai
"A gabana zaki fasawa yarinyata baki?,kece me abun duka ba ita ba,amma waye ga dakeki?,na rantse da Allah kinyi na farko kinyi na qarshe,bance kada ki hukuntasu ba,amma ba ta irin wannan hanyar ba".
Ranta ya baci sosai,ta dinga jefawa yarinyar harara,tanason bata mata budget gaba daya,amma tasan maganinsu,tattarasu zatayi kaf kwanakin wajen widad.
Saboda tana da plan sai bata tanka masa ba,illa bata fuska sosai data yi,ta juya tana ficewa daga sassan ranta a bace.
Kai tsaye ta nufi sassan widad,gwara ta fito da ita tun yanzun ta kama mata ayyukan,saboda yau aikin nata suna da yawa,ko gyaran sassansa zuwa abuncinsa aiki ne babba a wajenta,ga nata sashen da tasan zaici tsintsiya ruwa da klien,saidai tun kafin ta qarasa taga kaman babu mutum a sassan,kasa gasgata idanunta tayi,ta dinga ganin kamar gizo,har dai data taba qofar,takuma yi knocking taji shuru.
Sak tayi,ta tsaya yana jinjina kanta,baizo da ita bane?,ko kuma ta wuce gidan hajiyarsa yadda ta tsiri wannan iskancin wani lokacin?,bata da amsa,don haka sai ta wuce sassanta,ta dauki wayarta ta kira muneera.
Tambayar farko tace mata gatacan ita da hajiya a falo suna hira,ta zuqi iska ta fesar,lallai kan yarinyar ya fara wayewa,ita za'a mayar 'yar iska?,aqalla wata guda da wani abu kenan bata saka yarinyar a idonta ba,ko zuwanta na qarshe kwana guda kwata kwata tayi a gidan suka koma.
Sake fitar da iska me zafi tayi daga bakinta,maganganun anty ummee suka dawo mata,ai kuwa ba zata bari hakan ta faru ba,tare ta karantawa yarinyar karatun manya,dole tabi da ita,dole tabi hanyarta,dole ne kuma ta fara gane banbancinta da ita,sai ta fara dora abinci sannan ta kwashi kayan shara ta wuce sashen nasa tana sake saqa abubuwa da yawa da take da shirin aiwatarwa.
*_W A S H E G A R I_*
Karfe goma na safiya ya fito tsaf dashi,cikin lallausan yadin filtex na maza mai asalin kyau da tsada,komai yana yinsa ne a wani kasalance da rashin kuzari,duk kuwa da cewa a jiyan ya samu yadda yakeso daga hafsat din,to amma sai yakejin wani irin mugun banbanci mai tazarar yawa,banbancin da zai iya kiransa kwatankwacin nisan dake tsakanin sama da qasa,gaba daya ma zai iya cewa wani irin bacci yayi mara dadi cije da kewar widad din,duk juyin da zaiyi sai ya dinga ganin kamar itace a gefansa,amma dole ya tattara dukka wadan nan ya danne can qasan zuciyarsa da qarfin gaske gudun shiga hakkin me hakki.
Yana daura links a hannunsa tayi sallama ta shigo dakin,hannunta dauke da plate din data soya plantain wadda ta qone tayi baqi abinta,yadan bita da kallo kadan,tana nan gayanta,bayan wankan ibada da tayi kafin sallar asuba babu wani abu data qara,koda da turare kuwa,wanda zuwa yanzu zamansa da widad hancinsa ya saba da shaqarsa.
Yana yiwa turare wani mugu mugun so,amma ita nata ra'ayin sunyi hannun riga da ta'ammali dashi,sai randa ranta yaso,ko kuma aka taki sa'a ranar tana da ra'ayinsa.
"Fita zakayi kenan" ta fada tana zama gefan gadon da har yanzu ta kasa gyarashi,don tuni dama yayi sallama da kwana a sashenta
"Eh,akwai wani abu?" Ya fada yana takawa gaban mudubi,ya dauki cup din coffe din da yace ta hado masa dashi yakai bakinsa.
"Aah,inason zuwa gidan hajiya ne" dire mug din coffe din yayi saman madubin bayan daci ya ziyarci bakinsa,sannan ya zarce da dubanta yana nazarinta.
A ka'idarta zaiyi wahala taje gidan hajiyan haka siddan,shi yasa maganar ta bashi mamaki ko a yanzun ma,amma taqi yarda ta kalleshi bare ya karanto gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta,har ya gama kallonta,ya jawo qonanniyar plaitain din ya fara kokawa da ita
"Saikin dawo" ya amsa mata daga baya,yana tsame hannnunsa daga plate din,yaja tissue yana goge maiqon daya bata masa hannu.
Sarai taga yadda ya cakali abincin,abu na farko da ya kamata tayi taji dalilin da yasa bai maida kai yaci ba,tunda fita zaiyi,amma inaaaa,ba wannan bane a gabanta,sai kawai ta kwashe kwanukan bayan fitarsa,ta hada da kudin cefanen daya ajiye mata,duk da babu abinda zasu siya,ta soke a lalitarta,sannan ta shiga bandaki tahau shiryawa a gurguje,don tana da tabbacin zaiyi wuya idan ba gidan hajiyan ya nufa ba,tanason kuma ta cimmasa a can ayita ta qare.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 82
Qwafa taja sanda ta gama parking motarta kusa da tashi,ranta ya quntata sosai,duk sauri da taga yana yi dama nan ya nufa,tafison hakan dama,gwara ayi komai a gabansa,ta kashe motar, saidai kafin ma ta zare key din daga jiki tuni mimi ta bude murfin motar ta fice abunta.
Da harara tabi bayan yarinyar,ta tsani yadda take rawar qafa akan wannan tsohuwar,amma tana qara wayo zataci ubanta ne,ba zata dauka wannan ba.
Da gudunta yarinyar ta fada falon tana kiran sunan anty widad da hajiya,abbas ya bita da kallo yana hade ransa
"Koma kiyi sallama" da sauri ta koma tayo sallamar ta sake shigowa,saidai hakan bai rage mata karsashinta ba,tana shigowar ta fada saman cinyar hajiyan,kafin su sake cewa komai hafsat tayi sallama ta shigo
"Ikon Allah,ashe tare kuke" hajiya ta fada tana ma hafsat din sannu da zuwa.
Idanunta akan kwanukan daya gama cin abinci, qamshin abincin yana nan daram a falon,kana shigowa kuma zai buwayi hancinka,haushi da kishi suka cikata,abind aya sassauta ma abinda takeji a ranta rashin ganin gilmawar widad din kwata kwata.
Saman kujerar dake daura da hajiyan ta zauna,a maimakon zama a qasa kamar yadda ta samu abbas din
"Hajiya ina kwana?" Ta gaidata tana sake qarewa falon da kwanukan abincin kallo,a mutunce ta amsa mata cikin nuna kulawa gami da tambayarta yara da kuma gida,duka ta amsa mata da lafiya lau,sai kuma shuru ya biyo baya,dai dai lokacin da baba usaina tayi sallama ta sako kai
"A'ah yau kece a gidan?" Baba usaina ta fada tana zama itama,fuska hafsat din tadan saki,saboda saboda alaqar dake tsakaninsu ta amsa mata tana gaidata,suna tsaka da gaisawan mimi ta dami hajiya da batun anty widad
"Tana daki,leqa kice idan ta gama tazo su gaisa da umminki,a kwashe kayana abincin nan ma a wajen" ta kuwa falla da gudu tayi dakin,abbas yabi yarinyar da kallo,yana jin shima kamar yabi bayanta.
Sauke idanunsa yayi yana miqewa tsaye hadi da daukar wayarsa dake aje gefe
"Kada ka fita fa,inason zamuyi magana ne ai" aninda ya dauke wutar magana cak a falon,kowa yayi shuru sai sautinta daya fita dake yawo,da mamaki ya kalleta,wacce magana ce da basuyita ba kafin ya fito sai a nan?
"Hajiya wajenki nazo akan abbansu mimi"
"Tooo.... ikon Allah,koma to ka zauna" hannuwansa ya sauke,ya koma hannun kujerar daya tashi a kai ya zauna,can qasan zuciyarsa nason darsuwa da bacin rai amma yana kaudarwa,tunda har yanzu baisan dalilin zuwan nata ba,saidai kwanyarsa nata son hakaito masa abinda ya faru da zai sanya tayi tattaki qafa da qafa har gaban mahaifiyarsa ta kawo qararsa,duk da bawai yau aka fara ba.
Kafin takai ga cewa komai widad ta fito,riqe da hannun mimi sunata dariya abinsu,cikin wani lace sky blue da ratsin farin zare da aka yiwa dinkin tea bubu,bata daura dankwali