Header Ads
Showing 120001 words to 123000 words out of 296907 words

Chapter 41 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

dinga saqa tana warwarewa,wa zata tambaya wanda zaiyi mata bayanin da zata gane da kyau,ta kuma fita daga shakka?,ita kanta anty deena maganganun da taga tayin sai suka weedad ke tunani a kanta,tasan dai anty deena ba 'yar iska bace,to amma.......

Katsewa tunanina yayi sanda wayarta ta soma wani qaramun ringing mai dadi,ta kalli wayar,kamar ta gane number din,ta jawo wayar ta daga ta sakata a kunnenta.

A nutse muryarsa a qasa yayi mata sallama,ajiyar zuciya ta kubce mata ba tare data shirya ba,ajiyar zuciyar data sauka a kunnensa,ta kuma sanya tsigar jikinsa zubawa

"Bakiyi bacci ba?"kai ta gyada sannan ta amsa masa

"Eh"

"Me yasa?" Rasa amsar bashi tayi,saboda dai ba zata iya ce masa ga abinda take karantawa ba

"Me tayin kwanan ta shigo?"

"Eh" ta bashi amsa,don sai da sukayi sallama da ita sannan ta shigo dakinta,saboda ita a falo take kwana,taqi yarda ta kwana dakin widad din

"Yayi,yanzu gaya min dame dame kikayi yau?" Ya tambayeta yana hangen hafsa daga inda yake zaune cikn falonsa,tana nannade wandon kashin da nawwara tayi tana cusashi qasan kujera,ya dauke kallonsa daga kanta ya maida wani gefin,don bayason ransa ya baci.

Sosai ta narke cikin pillow din,zuciyarta tana narkewa,kewa tana sake cikata

"Bayan kaine....kaine kayi tafiyarka ka barni" ta fada a wanu kugun shagwabe,abinda yayi masifar tabashi,tsigar jikinsa ta zuba sosai,ita kuwa ko a jikinta,saboda tana ganin tayi maganarta ne sak

"Am sorry......bazan sake ba" ya samu kansa da fadin hakan ba tare daya shirya ba,dai dai sanda hafsat din ta qaraso wajen,sai taji kamar kunnuwanta basu jiye mata dai dai ba,waye yake baiwa haquri wai?,ta tambayi kanta,ta tsaya cak tana dubansa,yayi kamar bai ganta ba,yaja cup din coffe daya hada kafin ya zauna ya kurba kadan

"Yanzu kiyi addu'a ki kwanta,akwai school gobe"

"Tom.....sai da safe?" Ta tambayeshi a sanyaye,saboda har ga Allah hirar ta mata dadi,bataso yace ta kwanta ba.

Murmushi ya sake kubce masa,a hankali ya furta

"Goodnight" sai ya zame wayar daga kunnensa yana kasheta,dai dai sanda hafsat din ta kasa tsaiwa,ta zame ta zauna a kujerar dame kusa dashi

"Wai da waye kuje waya haka?" Sai daya kashe wayar ya ajjiye sannan ya dago yana dubanta,yadan zuba mata ido na wasu sakanni sannan ya saki murmushi

"Qanwarki ce"

"Qanwata ko kishiyata"shine abinda bakibta taji ya kamata ta furta,to amma tana tsoron kada ta barar da tafiyarta,don haka ta hadiye maganarta,sai gefw da tayi da kanta ta tabe baki

"Dole yarinyar ta dinga tsoronka,ya zaka dinga gaya mata maganganun da sukafi qarfi kanta,a haife fa ka kusa haifarta,tunda ka ninka shekarunta harda doriya" ta qarasa maganar tana dawo da dubanta kansa.

Fuskarsa a sake,saima murmushi daya saki,ya shafa kanshi zuwa kyakkyawan hanarsa dake dauke da gashi baqi sidik daya sha gyara

"Kinason ki gayamin na tsufa kenan fa"

"Kusan haka ne" ta fada tana tabe baki,a nufinta na zare masa karsashinsa da sha'awar komai,murmushi ya sake saki,abu daya ya sani,komai zatayi ba zataji komai daga bakinsa ba,ta manta wayeshi din wajen riqe sirri

"Ki zaro wancan andon kashin ki fita dashi ki wanke,and please.....kada na ganshi a dustbin" ya maida zancan zuwa wani topic din na daban.

Kunya da haushi suka cikata,ba wannan batyn takeso suyi ba,ita batasan ma ya ganta ba,maganar gaskiya babu agender din wanke kashi yanzu a gabanta,amma dole ta miqe rana cewa

"Kadai dinga mata a hankali tunda yarinya ce,bawai wani abu zata fahimta daga gareka ba" da kallo ya bita yana son tantance da wanne irin sound tayi masa maganar,sai ya maida nayansa jikin kujera,ya lumshe ido yana maimaita maganarta,abubuwa da yawa sunzo kansa a sannan wadanda suka sanya dole murmushi ya qwace masa.

Dukka abinda ta karanta a daren washegari ta dunga bitarsu a makaranta,kwatsam ranar sunyi missing periods har biyu,sai ajin ya zamana na surutu da hira,abinda ya sake sanyata daukar wayarta taci gaba da dubawa,saidai tana tsaka da dubawar hirar da 'yan bench din bayansu keyi yaja hankalinta,bata suaje wayarta ba amma ta bada kunnuwanta tana saurarensu,hirace ta aure da yawanci ba'a rasa matasan 'yammata da suke ganun sun fara zama seniors da yinta,fiye da rabin hirar ta zame mata kamar wani mabudi kuma amsa na dukka tambayoyinta,ta dinga saurarnsu tana ciro abubuwa masu yawa tana hadawa cikin maganganun data ji a groups daban daban.

Koda aka tashi daya daga cikin qawayenta ta bata ajiyar hausa novels

"Ki ajjiyemin don allah widad,yayana yazo gutu,doke sai ya koma zan karba,hanani karatun yakeyi,kada yaje garin bincike bincike ya ganosu na shiga uku" a karba din ta tafi dasu gida,da daddare ta buda jakarta bayan ta gama wani assignment zata maida jakar don kada ta manta idanunta suka gano mata litattafan,saita jawosu ta buda tana kallo tare da mamakin meye a ciki da za'a hanata karabtawa,don ita kallon normal kowanne littafi take masa,taji sha'awar duba meye a ciki,ta dauki daya part one ta buda ta fara karantawa.

Ko page daya bata dauka da niyyar karantawa ba,sannu sannu sai gashi har tajai page na wajen biyar,ta saki murmushi saboda labarin yaja hankalinta,saita kife littafin,ta wuce kitchen ta zuba abinci ta dawo taci gaba da dubawa.

Sannu a hankali sai gashi ta raba dare tana karatun,sam batasan dare yayi haka ba,don hatta da wayarta ta manta da ita,taje ta samu miscall na abbas kuwa harda sms guda daya,dare yayi don haka bata kirashi ba,sai tayi addu'a ta kwanta,amma kuma bacci ya qauracewa idanunta,tanata bitar abinda ta karanta din cikin kwanyarta,da gaske akwai soyayya irin haka?,soyayyar jaruman littafin ya tafi da ita,ta dinga kwantanta kanta dasu,kunya ta kamata ita akdai cikin dakin,saita kifa kai tana murmushi.

Washegari babu makaranta good friday ce,wuni tayi tana karatun,wanda a ranar ta gama da part 02 ta shiga 03,sai data qare littafin a ranar ma sannan ta kwanta,nan dinma dai dukka labarin ta dinga tunawa,yadda jarumar ke gudanar da rayuwarta

"Kamar ni da uncle kenan?" Ta ayyana a ranta,da sauri ta girgiza kai,kai anya?,ita kanta wasu abunuwan cikin labarin kunya suka dinga bata,first night dinsu ya dawo mata a rai,sai tsoro ya shigeta,itama wataran haka uncle din nata zaiyi mata?,amma wannan ai iskanci ne,to amma dama akwai ranar da wannan abun zai tashi daga sunan iskanci?,ta tuna haihuwar da jarumar tayi,suna nufin kowacce mace ta haka take haihuwa?.

A daren qwaqwalwa da tunanin yarinya kala kala ta dinga yi,abubuwa da yawa ta watsar dasu tana ganin bazai yiwu ba,ta rungumi abubuwa da yawa da syka dinga burgeta,har ta dinga kwantata gwadawa.

Da safe kuwa ta gwada abunuwa da yawa da ta karanta din,duk da tana wasu qarawa tayi,ta gama komai ta hada breakfast dai dai cikinta,din me tayata kwana gari na wayewa take komawa cikun gida tayi ayyukanta,bata dawowa sai wani daren,ko idan bata da abinda zatayi ta leqota su gaisa sannan ta koma,mayar mai gadin gidan ce,tana da matuqar kirki sosai.

Tana cikin yin breakfast taji sha'awar kiransa kamar yadda taji jarumar littafin tana yi,gabanta ya dinga faduwa sabida rashin sabo,ta dinga jin tsoro tana ganin kamar ba wani abun burgewa bane,saidai duk da haka bata fasa kira ba.

Lokacin ya shiga wanka,hafsat na zaune daga gefan gadon nasa tana dakon fitowarsa,da sauri kamar wadda aka kirayi wayarta ta dauki wayar tana duba mai kiran

"Weedad" ta maimaita sunan data gani a rubucen cike da mamaki,kanta ya daure da kyau,ita dince ke kiran ko kuma dai idanunta ne,ko wata ce mai irin sunan,saita daga kawai kai tsaye.

Shagwababbiyar muryarta data zame mata jiki,ta kuma saba magana da ita,da ita tayi sallama

"Ke tsaya" hafsat ta fada da sauri dai dai sanda take ficewa a bedroom din don kada ma ya jiyota.

Wani mugun faduwa gaban widad yayi jin muryar mommy hafsa

"Ina kwana mommy"

"Da ban kwana na zaki jini?,wa ya sakaki kiransa ko shi din sa'anki ne?" Mamaki ya bayyana a fuskar widad din,ta dauka ba komai,ta dauka momy din zata ce ta kyauta,saita kasa gane yadda abun yake

"Kiransa nayi mu gaisa mommy,jiya ya kirani ban dauka ba" tashin hankali!!, Ta fada a ranta tana jin yadda fuskarta ta dauki wani irin zafi,zazzafan kishinta da taketa qoqarin dannewa ya taso mata

"Yanzu ke har kisan ki kira d'a namiji kusan sa'an babban wanki koma babanki,ashe baki da kunya kwata kwata,to ba sa'anki bane,idan kika sake kiransa ko kuma ya sake kiranki kika daga saina miki mugun duka,ke bakya tsoron abinda zai sameki?,na gaya miki ba'a sakar musu fuska ko jiki,so kike yayi miki ciki ki mutu ko?" Karon farko taji maganar mommy hafsa din banbarakwai,sai taji kanta ya kulle

"Karna sake ji kuma kada na sake gani,kina jina?" Ta tambayeta a tsawace

"Tom" ta amsa mata jiki a sanyaye,sai hafsat din ta katae wayar tana jan tsaki,taso yarinyar na gabanta,amma bari ya fita,zata sake kiranta ta sake jadda da mata.

Jiki a sanyaye ta ajjiye wayar, kwanyarta ta shiga rububin lissafin maganganun hafsat din,zuciyarta taqi amincewa da hakan jikinta yaqi karba kuma ranta yaqi gamsuwa,saboda aduk abubuwan data karanta bataga ta inda aka nuna abune mara kyau ba da har mommy hafsat din zata dinga mata fada haka ba,kusan minti goma ta kasa samun nutsuwa,sai tunani yazo mata,sai kawai ta kira anty deena tace bari ta tambayeta.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijerπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63


*Thanks for choosing us*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:huguma*

Page 61

Kiran farko aka gaya mata user busy,tadan dakata na wasu mintuna sannan ta qara kiranta,cikin sa'a kuwa ta shiga

"Aah,kaga amaren kaduna" anty deena ta fada cikin tsokana,da yake idan taso tsokanarta haka take ce mata,dariya ta danyi ta gaidata tambayarta yaranta,ta amsa mata da suna lafiya,suka dan taba hirar data shafi gda sannan daga bisani shuru ya biyo baya,sai anty deena dince tace

"Kina bibiyar kuwa karatun da ake a groups din nan,kinsan kudi na biya kada ki sakani nayi asarar kudina" dariya ta danyi

"Inabi Allah anty,a ciki ma naga wani abu,nayi kuma to mommy hafsa tanata fada,nace anty ko banyi dai dai bane?" Ta qarasa fada a shagwabe

"Me kikayi kuma?" Antu deena ta tambayeta,bata boye mata ba ta gaya mata komai,anty deena tayi shuru tana nazarin maganar cikin ranta,zuciyarta na hasaso mata wani abu,amma kuma nataso ta dora nata tunajun ko tunanun yarinyar akan hakan,tunda dukka dan adam ajizine,zai yiwu ajizanci ne da kuma yanayi ma kishi da zai iya motsawa kowacce mace a kowanne lokaci

"Bakiyi abu mara kyau ba widadun ummu..."

"Ba wani widad din ummu yanzun fa anty deena ta daina sona,su Aafiya tafiso,kullun mukayi waya sai tace zatazo amma taqi zuwa" murmushi ya kubce mata

"Zatazo weedad,kullum ummu cikin zancanki take,amma kafin sannan.....inaso kome kika gani ance ayi kiyi qoqarin yinsa,zaki yi?" Ta tambayeta,saita gyada kai

"Eh anty deena"
"Yauwa widad dinmu,sannan ko meye kika gani baki gane ba ko ya faru ki kirani,koni ko anty madeena ki tambayemu,ba komai ne idan mommy hafsa tace kiyiwa uncle din naki zaki dinga yi ba kinji ko?"

"Tom anty deena" sun dan jima suna waya tana sake wayar mata da kai a fakaice sannan sukayi sallama,koda suka gama wayar litattafan ta debo ta sake zabo wasu a ciki ta dora da karatunta,itama tama manta d batun mommy hafsa da duk matsalolinta.

Rai bace hafsat din ta goge kiran da widad din tayi masa,sannan ta koma dakin ta maida wayar ta ajjiye ta kamar yadda ta ganta taci gaba da zaman jiransa,amma kuna qasan ranta a quntace yake da abinda ya farun,tana zargi da kuma tuhumar kanta,kwana biyu ta watsar da kiran yarinyar bare taci gaba da saita mata hanya,amma fa tana tsoro,kada ya zamana ta hadu da gogaggu kima wayayyun da zasuyi mata karatun da yafi nata shiga,tunda kaduna badai hadakar gamayyar mutane daga gari da qabila kala daban daban ba,amma zata kira ta binciki hajiya amina taji dawa dawa take hulda.

Koda ya fito daga wankan baisan anyi kiranshi ba,saboda qarar shower ta hanashi jin ringtone din,yana goge ruwan jikinsa tana binsa da kallo,jikinsa luwai luwai, fatarsa mai santsi da taushi sai daukar idanu takeyi, muscles din a hade alamun ya samu kyakkyawan training,ta hadiye wani abu da qyar saboda kishinsa daya tsarga mata.

Waiwayawa yayi suka hada idanu da ita,saiya dauke kansa yana cewa

"Ya akayi?,me yake faruwa?" Qaqalo murmushi tayi sannan tace

"Har yanzu banji kace na fara hada kayana ba"

"Zuwa ina?" Yayi mata tambayar bayan ya isa gaban madubi yaja lotion dinsa zai fara shafawa,wani abu ya tsarga mata amma ta dake

"Umara mana" sai daya kalleta ya kuma ci gaba da shafa mansa sannan yace

"Ban shirya wannan zuwan dake ba,babu kudi a hannuna,ina cewa ma ko wata shida bamuyi da zuwa ba ko?"

"Eh amma ai musulmi baya gajiya da zuwa" kai ya gyada

"Haka ne,amma yanxun bani da kudin da xamu iya tafiya mu duka,ke ni da hajiya" ranta ya baci sosai, zuciyarta tayita qissimata mata abubuwa da yawa da zata gaya masa,a fakaice dai hajiyan kusan duk shekara saiya kaita kenan,tunda itama ai baara iwar haka taje

"Aure ya cinye maka kudin kenan?" Ta tambayeshi tana tsareshi da ido,ya sake waiwayowa ya kalleta,ya kuma karanci yanayinta cikin sakanni,sai ya kuma dauke kansa ya maida ga abinda yakeyi,bayason doguwar magana,hakanan baya qaunar mita da qorafi

"Idanma hakanne ba mamaki bane" tofa,baki yasan me zai fada amma baisan me za'a mayar masa ba,saita miqe a mugun fusace

"Allah yayi mana arziqin da zamuyi ta zuwa babu mai hanamu" sai tayi waje fuuuu kamar zata tada iska.

Ransa ya sosu,amma ko iskar data kwasota bai kalla ba,yaci gaba da shirinsa,kafin ya sanya kayansa ya tsaya ya tsaftace sassansa,ya kuma dafa coffee yasha sannan ya qarasa shiryawa ya fice abinsa,yasan bazai rasa abinci gidan hajiya ba.

Tun daga wannan maganar ta dauke masa wuta gaba daya,shima kuma ya tattarata ya watsar ya baiwa banza ajiyarsa,yana ganin guga koda baiyi tsiran komai ba yayi na igiya,ta yaya zatayi kishi da mahaifiyarsa ko nawa kuwa zai kashe mata?,ita din ai ba tsararta bace.

Duka kwanakin da yayi kowa sabgarsa yake,amma hafsa din ta fishi damuwa,saboda tana da buqatar kudi a wajensa,baya ga haka tanason ya dawo da widad din har su dawo daga tafiyar,a wata dayan da zasuyi tasan zata moreta sosai,zata kuma dora mata karatun da zai zauna daram a kwanyarta,amma girman kai da jin tafi qarfin tayi qasa yasa taji gwara tayi shuru duk abinda ma ya yanke shikenan.

Ta bangaren widad kuwa cikin kwanaki qalilan karatun hausa novels ya shigeta sosai,idan tana karantawa tana jinta ne kamar a wata duniyar ta daban,yana debe mata kewa,tana kuma ganin abubuwan da suke bata mamaki,duk kuwa girki ko drinks din data gani saita gwada,a lokacin kitchen dinta yaga rayuwa,saidai duk abinda ta gwada din idan taga yayi farinciki cikata yakeyi,mai aikin maama(hajiya amina) ke tayata wani bin,tana ganinta kamar latifa saboda kirkinta.

Ranar da zai baro kadunan zai biya ta gidan hajiya ya daukota su wuce,har ya kammala shirinsa tsaf a sassansa tana nata sashen tana baccinta,don tun daga waccan ranar basu qara hada makwanci ba,tana sashenta yana nasa,yaci alwashin ko meye zatayi badai shi da qafafunsa ya bita yayi begging nata ba,yasan abinda takeso kenan.

Tare dasu mimi suka fito,a wajensa yaran suka kwana,tsaf dasu don su kansu sai daya shiryasu ya kuma gyara sasssan,suna riqe da hannunsa ya tura ya shiga,falon a hargitse kamar wanda aka tashi taron biki,harsa pampers din nawwara da yayi imanin idan bana shekaran jiya bane na jiya ne

"Ku zauna nayi sallama da mamanku" ya fada yana kallonsu,sai suka amsa suna hayewa saman kujerar,ya ajjiye luggage dinsa ya nufi qofar bedroom dinta,don ko takalminsa bai fidda ba saboda tsaftar tiles din ma bata gamsheshi ba,duka yayi rod'i rod'i kamar an watsar da ruwan tea ya fara bushewa samansa.

Sau uku yana knocking sannan yaji ana tambayar waye da cunkusashiyar muryar bacci,gyaran murya kawai yayi,ta taso tana turbune fuskarta daya kacame saboda bacci ta buda qofar.

Ido hudu sukayi, doguwar rigar wata kodaddiyar atamfa ce a jikinta da aka yiwa adon net,net din har ya soma bubbulewa alamun dake nuna ya fara gajiya da aikinsa,kanta gashinta ne him daya hautsine kamar ciyawar da aka tara za'a ciyar da dabbobi,abinka da baqar fata idan bai shafa mai ba....duk jikinta yayi fari fari,dakin yana fidda irin abinda jikinta ke fiddawa,da alama ya kama ko ina.

Kansa ya dauke,don takaicinta bazai kasheshi ba,ya fara gajiya da al'amuranta da kullum babu gyara sai gaba da abun yakeyi,ya sanya kai cikin dakin,dole ta

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads