Header Ads
Showing 141001 words to 144000 words out of 296907 words

Chapter 48 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

yiwa kanta kenan,sai kuma ta qaryata kanta da kanta,ta yaya abbas din zai fara son diyar cikinsa?,banda kyau babu wani abu data ga yarinyar tana dashi,samun kanta tayi da duqufa addu'ar kada Allah ya bata ikon dawowa.

**********Dukkaninsu suna falon ummu,mahaifinta da ya kasance babba da kuma qannensa gaba daya,ummu da widad na gefe,yayin da widad din tayi kamar ta shige cikin ummun

"Tunda taqi cewa komai yaaya,me zai hana a sake kiran abbas din aji" girgiza kai alhaji mahmud mahaifin widad yayi cikin takaici

"Ya riga yace min babu komai,kuma tunda yace din babu,ita dai tana kwaso wadan nan siraran qafafuwan nata tazo,ita zata bude baki tayi mana bayani ko na tashi na babballata a wajen nan na zubar" ya fada cikin tsananin fushin da tun dazu idanun ummu yasa yake cinyewa.

Duka kallo sai ya koma kanta,cikin hargagi kamar zai kai mata duka yace

"Zaki bude baki kiyi magana ko saikin daku?" Kamar an rufto mata duniya haka taji,ga wani mugun tsoron yadda abban nata ya juye da yake ratsata,tayi qas da kanta tana hawaye, abinda ya tunzura alhj mahmud,ba wanda ya ankara sai gani sukayi ya isa kanta da wayar tv daya ciro ya fara sauke mata ita.

Kuka ta saki sosai,don zata iya cewa wannan shine karon farko da aka taba mata irin wannan dukan kaf rayuwarta,kafin a samu a qwaceta kuwa ta daku yadda ya kamata,latifa ta karbota tana boyeta cikin hijabinta ta fice da ita daga sassan ummun cikin jimami da alhini.

Kai tsaye sassan anty madina tayi da ita,tana kwance a falo ta miqe tana salati

"Dukanta dama yaaya yakeyi dana jiyo muryarta daga nan?" Anty madina ta fada kamar zatayi kuka

"Wallahi,taqi ta fadi komai ne,shi kuma ransa ya baci" rungumeta anty madina tayi tana lallashinta

"Inda kin fada widad ai magani za'a yi miki na koma meye da yake damunki" a nan hannunta latifa ta barta

"Kada kice musu tana wajena please" anty madina tace da latifa ta juya ta fice,ita kuma ta jata zuwa bedroom dinta.

Shuru ne ya ratsa falon bayan fita da widad din,zuciyar ummu duka ba dadi,dukan da mahmud yayi mata saita dinga jin kamar ita aka daka,amma kuma babu wani sauran abinda za'a yiwa widad din

"Inajin ruqiyya zan sanya azo gida ayi mata" ummu ta fada cikin karyewar murya,kai kawu maisara ya gyada

"Eh to,ya kamata a bincika ta wannan fannin ma,saboda suna iya sakata yin hakan,kuma ba kasafai hankali yake kaiwa can din ba,sai abu ya ta'azzara sannan ba fata ake ba"

Miqewa abban yayi

"Ai magana ta qare,gobe in sha Allah zanzo na dauketa da kaina muje,idanma sune sayi bayani"

"Da kanka yaaya,ka bari wasu cikinmu su kaita"

"Gwara ayi komai a gabana sa'idu don qaniyarta" har dariya taso subucewa ummu,mahmud din badai zafi ba,duk cikin yaranta ya fisu zafi,musamman al'amarin aure,baya wasa dashi.

A hankali anty madeena ta turo qofar dakin

"Kinyi bacci ne widad?" Widad dake zaune qasan carfet tana duba wasu litattafai data gani a dakin anty madinan ta amsa

"Ban kwanta ba maman walidi"

"Au na dauka mai gidan ya koya miki baccin wuri" ta fada tana duban fuskarta

"Uhmmm" kawai ta fada tana maida kallonta ga littafin,maganar da anty madinan tayi saita tuna da abbas din,yana da kirki matuqa,yana da tausayi,tanajin dadin hira dashi amma duka ya bata wannan ta sanadin abinda yayi mata.

Kaya ta zuba cikin cupboard sannan ta dawo gefen widad din ta zauna tana kallonta

"Ki shirya gobe inji yaaya abba(haka matan gidan suke kiran babanta),gobe da safe zaku gidan mai ruqiyyar cire aljanu" a tsorace ta kalli anty madina idanunta a waje

"Aljanu kuma?" Kai ta gyada cikin nuna halin ko in kula

"Eh,haka abbansu walid ya gaya min" tuni hawaye suka cika idanun widad,ta narke sosai tana kallon antyn

"Don Allah anty kice kada su kaini wallahi ni ba aljanu bane dani"

"To menene widad?,tundi kinqi gayawa kowa aka sani ko sune?,ai gwara aje can din,qila su zasuyi magana" yadda taga ta rude tana roqonta taji a ranta zasu samu bakin,sai ta gyara zamanta tana dubanta

"Kinga daga ni sai ke,ki gayamin me yasa kika taho kinji"

"Ni bana sonshi anty madina" baki anty madinan ta riqe tana kallonta cikin mamaki,lallai wani halin sai widad din,amma a yadda ta fadi maganar ta fuskanci akwai wani abu,don haka ta hadiye mamakinta tace da ita

"Bakya sonshi?,to me yasa bakya sonshi?"

"Dan iska ne" ta amsa mata kai tsaye hawaye na sauka a idonta.

Dariya ce taso qwacewa anty madeena,to amma tanaso su qarqare qarshen zancan

"Dan iska kamar yaya weedad?,me yayi miki na iskancin?" Kallon anty madeena tayi,idanunta kamar zasu fado,kunya da nauyinta takeji,amma.indai bataso a kaita wajen mai aljannu dole tayi bayani

"Tattabani yakeyi" ta qarasa fada muryarta tana rawa.

Zuwa wannan gabar dole dariya ta kufcewa anty madina,yayin da sautin dariyar ya sanya widad cikin rudu,ta dauka zataga ta saki salati tana tafa hannaye,kota rufeta da fada ko da duka ma akan ta bari ana tabata din,sai kawai taga tana dariya.

Kusan minti biyu sannan anty madeena tayi shuru tana nazari,ba shakka kuskure nasu ne,duk yadda akayi ummu bata zaunar da widad ta gaya mata meye gundarin aure ba,suma kuma bata jin wata a cikinsu tayi hakan,duk da kusan abun ma qurarren lokaci yazo,amma duk da haka alhmdlh da aka gano bakin matsalar.

A ranar dukka wata kunya anty madeena ta cire ta dinga gayawa widad komai gatso gatso,jikin widad har rawa ya dinga yi saboda mamaki,ta dinga kallon anty madeena tana mamakin haka take?

"Eh kalleni da kyau,wannan abun da kika gudowa,kowa yana yi indai mata da miji ne an daura musu aure,harni kaina da kike gani" kunya ta sanyata cusa kanta a cinyoyinta ganin anty madeena din ta danganta abun da kanta,ta kasa daga kanta,sai kuma kwanyarta ta shiga mata research,me yasa mommy hafsa ta dinga jaddada mata kada ta yarda ya taba ko yatsarta yadda ummu take gaya mata sanda tana gida,meye dalili?,tambayar data rasa gano amsarta,sai kawai ta daga kai ta fuskanci anty madeena taga gwara ta tambayeta.......
*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Page 72


"Umman walidi.....amma abinda mommy hafsat take fadamin ba gaskiya bane kenan?,naga itama babba ce kamar ku,amma bata taba gayan abinda kika gayamin yanzu ba"

"Me take ce miki?" Anty madeena ta tambayi widad din tana kallonta,cikun fargabar kada ta koya mata dabi'ar banza

"Ta gayamin abinda ummu ta jima tana gayamin har nabar gidan nan,tace idan ya kama hannuna Allah zai qona ni,idan na yarda ko kusa dani ya zauna sabon Allah ne,kuma Allah zai iya qonani,kuma koda wasa ya tabanin tana ganewa,har waya take tana tambayata"

"Ke kuma idan ta tambayekin sai kike gaya mata?" Anty madina tayi hanzarim tambayar widad tana datsar numfashinta,kai widad din ta gyada,haushi da takaici ya saka anty madina sakin salati,sai yau ta yarda kaf gidan babu wanda yakai widad din rashin wayo,da gaske ne,ada da ake fada tana ganin ba haka bane,kawao miskilanci ne yayi mata yawa,ashe harda rashin wayon

"Yaushe duka ta gaya miki hakan akan uncle din"

"Kullum saita kirani,ta tambayeni dame dame nayi,dame dame yayimin" wanu malolo ya tsayawa anty madina,sai yanzu ta gane.....hafsat din tayi amfani da rashin wayon widad,da kuma tarbiyya me kyau data samu na girmama na gaba da kai da bin umarninsa ta kitsa mata wannaj baragurbin tunanin,tayi kuma sara akan gaba,suma sun manta basu fayyace mata irin rayuwar da ake nufi da rayuwar aure ba.

Zama na dirshan anty madeena tayi ta fara dora mata bayani akan matsayin hafsat din a wajenta,ta fayyace mata wace kishiya fes,sannan ta rufe da cewa

"Ba cewa akayi ki rainata ko kiqi yi mata biyayya ba,amma babu ruwanta da ko mene tsakaninki da uncle dinki,matsayinku daya a wajensa ke dashi,ki rufe sirrinki,karki yarda ki sake gaya mata komai dake tsakaninku".

Sai kusan sha biyu na dare sannan anty madeena tabar dakin ta wuce dakin mijinta,tabar widad a zaune tanata saqa da warwara,komai ya yiwa kanta girma,tana ta jujjuya maganganun da sukayi da anty madina,tun daga farko har zuwa qarshe, yanzun itama data tafi dakin kawu abinda sukeyi kenan?,abinda ya fado.mata a rai kenan,kunya ta kamata ita kadao cikin dakin,saita cusa kanta a cikin filo tana sake hasashen abubuwan da suka dinga faruwa tsakaninta da abbas din.

Bayan sallar asuba anty madeena ta zayyanewa daddynsu walidi yadda sukayi da widad din,tana dariya dariya tace masa

"Kaga babu sauran batun zuw wajen ruqiyya,a gayawa yaaya abba yayi haquri" kai ya jinjina yana murmushi

"Na yarda widad din muguwar sakaliya ce,ku daman baku fada mata komai ba?"

"Wallahi sam ban kawo haka a kaina ba,saboda naga yawanci yaran yanzun ma kafin a gaya musu sunsan komai,amma ita din shekarun nata sunyi qanana da yawa a sanda akayi auren,kuma dai dama widad din gaskiya ko cikin yaran gidan nan tana cikin 'yan ba ruwa na,gatan da qaunar dake tsakaninta da ummu ne kadai yasa ake ganin ta sangarce da yawa,amma tana da dadin zama ainun"

"Shikenan,bari gari ya qara haske,zan shiga na yiwa ummu bayani,sai a shaidawa yaayan kafin yakai.ga fitowa,don nasan da abun ya kwana,da wuri zaki ganshi ya shigo" anty madeena dai tana dariya ta fice daga dakin.

Tare suka shiga kitchen da anty madeena din,saidai yadda taga widad din tana hada breakfast din cikin qwarewa yasa ta tsaya tana kallonta,sosai abun ya daure mata kai ya kuma bata mamaki,widad dince da iya sarrafa abinci haka?

"Me ya faru anty naga kina kallona" murmushi tayi tana sakin habarta

"Hmmmm,ba dole ba,irin wannan delicious haka da ake hada mana yau,lallai aure me gyara mutum,su Aafiya suzo suyi kallo,yau widad din da ummu ke hanawa dosar kitchen yau itace da hada breakfast tsaf mai rai da motsi" dariya tayi kawai,ita kanta a yanzun shiga kitchen na daya daga cikin hobbies dinta.

Kamar yadda daddynsu walid ya fada kuwa da wuri abban nata ya shigo da shirinsa,yana parlor yana breakfast ummu na ciki tana gyara dakin alhaji da ya tafi umra daddyn walid din ya gayawa abban komai.

Kofin hannunsa ya ajjiye yana girgiza kai

"Ashsha.....ashsha" sai yaja tsaki

"Zataci qaniyarta,wanne irin shirmen banza ne wannan?,dama wannan shirmen da shashancin tazo yi mana?"

"Har yanzu quruciya ke damunta yaaya,sai anyi a hankali" abban bai tanka masa ba,illa wayarsa daya ciro yayi kiran uncle muhsin.

Widad kuwa batasan me akeyi ba,tana can tare da anty madeena tanta karanta mata abubuwa,da azahar saiga anty deena,kamar tayi kuka haka ta dinga yiwa widad fada

"Me yasa kika taho,bance komai ya shige miki duhu ki gayamin ba?" Haduwa sukayi suka dinga wayar mata da kai,anty deena bata bar gidan ba sai bayan sallar magariba.

Washegari dai taga an hau mata shirye shirye,sai da azahar anty madeena ke gaya mata gobe zasu maidata kaduna,hawaye fal a idanunta take qorafi

"Tunda na tafi fa anty banzo ba ba'a jemin ba,kuma yanzu kwana hudu kawai sai ace na koma?ko alhaji ban gani ba"

"Eh ai wannan zuwan da kikayi mu ba irinsa mukeso ba,ki bari kizo cikin dadin rai da yardar mijinki,babu me cewa ki koma sai idan ranki yaso" dole tana ji tana gani taja bakinta tayi shuru,sai cika kawai da take tana batsewa.

Washegari samuel ya iso,tana ta kukanta kamar ranar za'a fitar da ita zuwa gidan miji,ita umma batulu,anty halima da anty madeena,anty deena ma taso zuwa,amma kuma a ranar mai gidanta zai dawo daga tafiya.


*_BAYAN WATANNI HUDU_*

*********A nutse motar ta cusa kai cikin gidan,bata saurara ba har sai data dangane da muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci,ya dai daita tsaiwarta sosai sannan ya kasheta,ya zare key din daga jiki yana fadin
"Alhamdulillah".

Waiwayawa yayi gefansa,tana kwance,ta lafe sosai cikin kujerar tana baccinta hankali kwance, murmushi ya subuce masa,bai dauka da tace baccin zatayi da gaske shi din zatayi ba,a hankali ya sanya hannu ya zare littafin dake kife saman cikinta wanda ya fadi bayan bacci ya dauketa,yadan duba page din da take ya saka mata alama sannan ya rufe ya dorashi a gaban motar.

Idonsa ya sake mayarwa kanta,ya zubawa baby face dinta ido,baccin da alama yayi mata dadi,ya saki murmushi,koda yaushe idan ya kalleta saiya tunata da wata wauta da quruciya data tafka,kome tayi ganinta take dai dai ne,har suyita rikici idan yace ba haka bane.

Hannu ya saka yadan bubbuga seat din,a hankali ta bude idanunta,ta zubesu fes cikin nasa,ta kafeshi dasu tana dubansa,he look gorgeous,kaftan din da ya saka sun bala'in amsarsa,ta gani tun daga gida kafin su fito,harma ta yaba,a yanzun kuma sai ta sake gani ya mata fresh sosai

"Yadai...." Ya fada yana dage mata girarsa cikin salon tsokana,murmushi ya subuce mata, kunyarsa ta kamata wanda a 'yan kwanakin nan haka take ji a kansa

"Ba komai......"sai ta saka hannu ta bude murfin motar ta fito zuwa harabar gidan.

Iska ta shaqa tana duban harabar gidan,daga tafiyarsu last two weeks harabar gidan har ta canza,akwai datti da qura sosai,ita ke sawa a gyara duk sanda sukazo din,bayan ta karba hidimar sassan hafsat data tabbatar ko a yanzun akwai aiki jingim yana jiranta,a yanzun zuwa bauchin ya fara fita mata a ka saboda wannan dan uban aikin bautar da hafsat ke hadata dashi.

Waiwayawa tayi zuwa inda yake tsaye,ya fitar musu da kayansu daga booth

"Shikenan?,i have done?" Ya fada yana dubanta,narke fuska tayi sannan ta marairaice masa

"Uncle taimako please,ka qarasa min da luggage din mana" yadda tayi maganar a mugun shagwabe yayi masifar taba ransa,tun daga wancan ranar data dawo daga gudun hijirar da tayi,ba abinda ya sake bari ya hadasu,ko riqe hannunta,wannan yasa ta sake abinta sukaci gaba da mu'amalarsu,amma ya zuwa yanzun yadda kullum taketa canzawa da koyar abubuwa masu yawa ya sanya yaji ta fara taba zuciyarsa.

Kansa ya gyada,ya kama hannun jakar zuwa sassanta tana biye dashi tana masa hira.

Sai daya bude mata ya saka.mata jakar yana duban sashen nata da.har abada badai kaga datti ba saidai qura

"Can you help me?"

"Dame uncle?"

"Idan kin gama gyara sassanki please" murmushi ta saki,ko bai qarasa ba tasan me.yake nufi,kuma tana da wannan nufin a wannan karon,saboda magana da hajjaaa tayi mata tun wancan zuwa sun tsaka da waya

"Za'a yi in sha Allah uncle"

"Thank you" murmushi ya subuce mata,komai.qanqantar abu idan kayi masa sai ya gode maka,tana kallonsa ya juya a hankali ya fice,yabar mata sauran qamshin turarensa data zuqa da kyau ta fesar tana sake sakin murmushi,sannan ta taka zuwa cikin falon nata tana kallon ko ina,tare da tsara yadda zata fara aikin.

Sassan hafsat din ya wuce kai tsaye,yana son saur nauyin alqawarin sweet daya daukarma su mimi.

Yana dosar sashen yana jin dan tashin hayaniya,sai abun ya daure masa kai,saboda iya saninsa ita din bamai sakewa mutane bace,bata da fuskar da za'a zo gidanta a zauna ana hira haka,suma mutanen kowa ya gane don haka zaiyi wuya kaga tayi baqo.

Yana sake dosar sashen yana fahimtar tashin sautin maganganun ba na arziqi bane,yanayinsa yadan canza kadan da fargabar abinda yake faruwa,a haka ya isa qofar falon,ya tura ya shiga da sallama,dai dai lokacin da matar dake tsaye take cewa

"Yanzu dai ki fito da shinkafa kawai,tunda ke waye yazo gidanki ma bare ya dauka" ta buda baki zata bata amsa maganar tata ta maqale a maqoshi,tana tsaye tsakar falon,fuskarta har maiqo takeyi,kayan jikinta wari da wari ne na rigar wani lace nata da har ya fara tashi tashi saboda dadewa,sai zanin atamfa,ta yane jikinta da wani tsohon mayafinta milk color

"Sannu da zuwa" ta fada muryarta tana dan rawa,itama matar dake tsaye dauke da wata babbar roba blue ta miqa masa tata sannu da zuwan,duka ya hada ya amsa musu,sai ya wuce zuwa dakin hafsat din kai tsaye.

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Page 73

A dan tsorace ta kalli matar,ganin kuma ita take kalla saita dake,don ita bata yarda ta fadi ba ako menene

"Bazan bayar bafa,ladan wahalar aikin da mukayi mata,nima idan tawa haihuwar tazo duka biyun haka takeyimin" dubanta matar ta sakeyi sosai,cikin bacin rai da daga harshe tace

"Haka ake taya aiki a kwashe maka abincin suna?,cooler guda saboda dan ke kafadai akayi girkin?,ku haka kukeyi?,don kun taya aiki sai kowa yace anan zaici abincin rana?"

"Sai kuma kiyita yi,don Allah ki fita kiban waje,mijina ya dawo"

"Au haka kika ce?,to wallahi saikin fito da abincin nan kuwa" nan sa'insa ta barke a tsakaninsu,tun sunayi iyasu har hayaniyarsu ta kaiwa abbas dake tsaye yana nazartar dakin hafsat din,yadda likkafara qazantarta taci gaba,ko ina pampers din nawwara da aka cire an kasa kirashi dust bin,ga zanin gadon dake saman gadonta a iya saninsa sanda ya siyoshi milk color ne mai kyau,amma yanzun ya tasamma zama ash color,naira dub ashirin da biyar ya siyeshi,kyansa da taushinsa ne ma ya burgeshi ya siya din,amma bazai iya tuna wani amfanarsa da yayi ba.

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads