Showing 63001 words to 66000 words out of 296907 words
Chapter 22 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
yadda tayi namijin qoqarin boyewa,to amma a yadda taji ta masa magana ba wani mummunan lafazi sai yaji hankalinsa ya sake kwanciya,da ya tambayeta mai ya sami wayarta tun jiya yake kira a kashe
"Kamar da gaske an damu dakai" ta fada a qasan ranta bayan tayi tsaki,amma a zahiri sai yace
"Nawwara ce ta jefamin ita bayan freezer,ruwa ma ya tabata,yanzu nakeson bada ita game gyara"
"Ya salam,shikenan,ki jira na dawo zan bayar a duba miki da kaina" tuni zuciyarta ta gama hasko mata abinda zatayi da wayar don haka tace
"A'ah,ai yaronma yana waje jirana ma yakeyi na bashi wayar"
"Is okay,yayi,saimun qaraso"
"Ala tsare" ta fada tana gintse wayar,saita maidata flight mode din,gobe ko jibi idan zata gidan anty ummee zata biya ta saidata ta sake hade kan kudadenta,ya sake kashe wani kudin ya siya mata wata,don ba imani ko daga qafa yanzun tsakaninta dashi.
Zuciyarta nata gaya mata ta shiga kitchen tadan samar masa wani abun da zaici,amma sai tayi fatali da wannan tunanin,taja tsaki ta miqe kan kujera abinta tana cewa
"Bazan iya ba wallahi,wannan pretending dinma da nakeyi duka ya fara isata" ta sake jan wani tsakin tana rufe idanunta tanajin yadda ranta ke mata suya.
Awanni kusan biyu tana zaune a wajen,sai data gaji don kanta,sannan ta miqe ta kom bedroom dinta,yanayin da jikinta yake ciki itama ya fara damunta,don haka ta hada ruwa ta shiga wanka,gaba daya hatta da yaran batason motsinsu ko bari bari da zasuyita sakata,don haka tun da safe ta aika gidansu dasu,wannan ne kadai zai bata damar zama tayi jinyar kanta da kyau.
A nutse ya fita a motar bakinsa dauke da addu'o'i,samuel ya zagayo yayi saluting nashi sannan ya miqa masa key din cikin girmamawa,hannu yasa ya karba yana masa ban gajiya,sannan samuel din ya juya ya fita a gidan,zasu qarasa a ragowar motocinsu dake cikin layin.
Jefa key din yayi a aljihun rigarsa,sannan ya juyo yana nufar gidan bayan ya sauke ajiyar zuciya,zuciyarsa na gaya masa ko me zaya tarar cikin gidan kuma?,sanin gaibu sai Allah,haka yaci gaba da takawa da kuzarinsa da qarfin gabban nan nasa da ya zama kamae signature dinsa.
Da sallama a bakinsa ya yaye labulen falon yana qarewa falon kallon,as usual yana nan kamar kowanne lokaci,kamar yadda ya saba tarar dashi, matuqar sa'a ce zaici yayi wata tafiya ya dawo ya samu falon a kintse,har ya zame masa jiki,bawai ya dawo ya sameshi a hargitse ne abun mamaki ba a gareshi,babban abun mamakin ya sameshi neat,sai ya saki labulen ya kutsa kai zuwa ciki.
Shurun da yaji yayi yawa sai ya dauka ko bacci yaran sukayi bayan ya kalli agogo,bakwai sa rabi na dare harda wasu mintuna,kansa tsaye ya tunkari dakinsu,amma daya tura sai yaga wayam babu kowa,dakin dai shima kamar ko yaushe,saiya maida qofarsa ya rufe ya sauya akalarsa zuwa dakinta.
Tana tsaye bayan ta fito a wankan,daure da zanin jikinta wanda tayi masa daurin gaba(daurin qirji),tana ta qoqarin taje gashinta yana cije mata saboda taurin da yayi,ya turo qofar suka hada idanu,saita amsa masa sallamar ta maida kanta wajen taje kan nata,kamar ma batasan wayeshi ba.
Kofar ya saka yana zare idanunsa daga saman gashinta yana takowa zuwa ciki,yasan kafin ya tafi ya ajjiye mata kudaden gyaran jiki da gyaran kai,yafi tsanar qazantar gashi fiye da qazantar komai,amma ita kwata kwata ba damuwarta bane,to ina takai kudin?,me kuma ya hanata zuwa gyaran kan?,jikinma baiga alamun an gyarashi ba, tun yana sanyata a gaba ya kaita har ya daina bata lokacinsa da kudinsa,tunda ya siya mata mota kudin kawai yake bata,cikin kaso goma kuma kaso biyu kacal take zuwa,kaso takwas din saidai ta adana kudinta,duk da shi baisan me takeyi dasu ba.
Cikin juriya ya isa bayanta,ya kuma rungumota ta baya zuwa cikin jikinsa, hannayenta biyu ta saka da dukka qarfinta tana son janyeshi a jikinta,yasan zata aikata hakan,shi yasa bai mata qaramin riqo ba
"Am sorry" ya fada da muryar da yasan tana matuqar tasiri wajen karya lagonta,turjiya da tijara takeson masa koda zata rage zafin dake danqare a ranta,mugun guguwar baqin kishin da anty ummeen tasa ta danneshi bisa salo na kissa,amma sautin muryarsa data sauka a kunnenta ta karya dukka lagonta,sai ta sakar masa kuka,kuka kuwa sosai wanda ke bayyana ftsananun zafin da zuciya ke fuskanta.
Ya sani,kishi yana da zafi,don haka ya fara lallashinta cikin wani salo da yasan yana saukar da zafinta,a hankali sai ya soma birkice mata,abinda yaja hankalinta kenan ta soma zame masa tana tureshi,cikin ranta tana mita,sai an fara abun arziqi dashi sai kuma ya canza hanya,shi din babu dama a hada jiki dashi sai wani zance na daban.
Sosai yayi mata riqon tsauri,baisan meye damuwarta ba,bata taba iya karbar damuwarsa hannu bibbiyu ta bashi hadin kai ya sauketa ba,kamar bata da wani feeling,kuma qarya ne!, tabbas tana dashi,saidai ta sanyama ranta wani baqin rai da girman kan banza.
Duk yadda taso tayi avoiding nasa amma ta kasa,dole ta bada kai bori ya hau,duk da ba wani hadin kai ya samu ba,ya saba da hakan,har kusan ya zame masa jiki,bayan komai ya kammala kuma ta shiga quncinta kamar yadda ta saba,baibi ta kai ba,hasalima kafin tayi wanka sai daya tabbatar ta wanke kanta da kyau,ya hadata da hand drayer sannan ya fito,ya wuce sassansa don ya shirya.
Ko da ya gama shirinsa ya fito kitchen ya duba saboda yadda cikinsa ya rarake kamar an masa yasa,babu alamun an girka komai,sai kawai ya dauki key ya fita don yi musu takeaway ba tare da ya tsaya jiranta ba,yasan ba abinda zata dafa a wannan lokacin,a hanya yayi kiran hajiyarsa,har kuma ya qarasa wajen sunata wayar,yace mata gobe zai shigo da wuri kafin ya wuce,don a gobe yakeso ya koma kaduna.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 32
Yana daga tsaye yake shanye tea din dake cikin cup din,yana yi yana hadawa da qonannen cake din da hafsat din tayi,dai dai sanda ita kuma ke sanye da kampala dinkin tea bubu,fuskarta a wanke tas babu digon kwalliya kamar kullum,hakanan fuskar tata a dinke take babu walwala sam sam.
A duk lokacin data kalli abbas....ta kuma tuna a yanzun bawai ita daya ce mutum dake amsa sunan matarsa ba,sai taji kamar ta shaqe kanta,kota zauna tayita zunduma ihu har sai dukkan jama'ar dake kewaye da ita sun fuskanci irin zafi radadi gami da qunar dake cikin ranta,tsantsar bacin ran da babu halin nuna shi,baqinciki da tashin hankalin data zabi lullubeshi da kissa da kuma nuna halin ko in kula da lamarin aurensa,wanda ko kusa ko alama ba haka bane cikin ranta.
Cup din ya dire saman fridge din yana furta
"Alhmdlh" da Peace voice dinsa dake dauke da wani calmness da bai cika son hayaniya ba,idanunsa ya zube saman fuskarta yana kallonta,saita janye nata idanun daga kallonsa,batason zuciyarta ta karye ko sonshi ya motsa mata har tayi wani misbehaving,tsaki yana subucewa daga bakin nata,saidai Allah yasa baiji ba
"Zan wuce" ya fada murya can qasa
"Allah ya kiyaye hanya" ta amsa masa a taqaice tana folding hannayenta a qirji,matsawa gabanta kadan ya sakeyi yana rage kusancin dake tsakaninsu
"Me da me kuke buqata?,ko kuma shikenan?,ba wani taro da zakiyi?" Kusan duk abinda takeso ya dire mata,ta wanki aljihunsa yadda ya kamata,to amma duk da haka batasi tace masa shikenan din, tunda zataje wajen anty ummee,batasan me zasu tattauna ba,don haka tace masa
"Idan akwai wani abu zamuyi waya" kansa ya jinjina,ya sauke mata soft kiss a goshinta,sannan yaja da baya ya juya yana barin wajen,dole ta kama masa qaramar jakar tabi bayansa da ita tana qoqarin gyara yanayin fuskarta,don komai ya sake hawa kan saiti,ya kuma ci gaba da tafiya yadda suke tsarawar.
Da murmushin yaqe ta bishi sanda yake waving mata hannunsa,motarsu tana fita ta koma ciki da sauri,ta dauki jakarta mayafi da key din motarta,har takai bakin qofa ta koma ta rage yawan kudin dake cikin jakar ta adana a locker dinta,cikin ranta tana raya
"Kada bacin rana ya gifta ta kansu" duk kuwa da cewa gidansu zataje,acan zasu hadu da anty ummee din.
Tunda ya tafi kusan ayyuka suka cunkushe masa,bashi da wani cikakken lokacin kansa bare na sauran abubuwan,haka ya dinga qoqarin handling komai,ga gida babu mace,idan ya dawo kusan wasi hidimomin da ya cancanci ace matar aurensa ce tayi masa kafin isowarsa gidan shi zai gabatar dasu,wanann ya sanya shi yanke hukuncin ajjiye widad a nan kadunan,ko babu komai gidan bazai zamana shuru babu dan adam a cikinsa ba.
Yana daga nan ya sanya aka sake gyara part guda daga cikin parts din gidansu na bauchi,a nan kadunan ma yayi wasu qananun gyare gyare,mutum ne shi koda yaushe mai tsananin kyautatawa ga duk mutumin da Allah ya dashi zama dashi,hajiya tafi kowa sanin hakan,shi yasa zamansa da hafsa ya tsaya mata a rai qwarai da gaske,tako ta ina abbas din inda rubutawa bawa qaddararsa akeyi ya cancanci samun mace ta gari,wadda zata kula dashi matuqa gaya.
************K'arasa zuba jewel's dinta data debo tayi cikin qaramar jakarta ta zuge,sannan ta dubi alhaji salim mai fata dake zaune kusan awa guda saman kujerar madubi dake dakin widad din
"Alhaji na gama" ta fada tana murmushi
"Da kyau jikata,sai tafiya kenan" kai ta gyada masa tana dariya
"To muje na rakaki da kaina,kada ma mutsaya sauraren kowa su bata mana lokaci" sai ya miqe yana daukar mata jakar,yayin da ta lulluba mayafinta abinta,suka jera ita da kakan nata dake nuna mata zallar qauna hadi da kulawa kamar yadda tsohuwar matarsa ummu ke gwada mata.
Hankali kwance alhaj salim ya bude mata gaban baqa wul don motar qirar range rover,daya daga cikin motoci mallakin ASP abbas muhammad bello
"Shiga abinki ki zauna kafin su fito" sai a sannan ta kalleshi,tadan narke fuska
"Amma alhaji,kace dakai da ummu duka kuna nan tahowa ko?" Kai ya gyada mata yana murmushi,saidai can qasan ransa kewa da kuma tausayinta ne fal zuciyarsa,farincikinsa guda daya zuwa biyu ne......sun aurar da widad din cikin aminci zuwa ga hannun mutumin da basu da haufi a kansa,nagartarta da ingancinsa sunkai,na biyu duk yadda suketa juya yadda za'a fidda widad din daga gidan salin alin bata tara musu taron jama'a ba,sai gashi da qafafunta ta fito zuwa motar da zata daga dasu bauchi,Allah ya bashi hikima da basirar da taketa shauqin tafiyar zuwa gidanta
"Idan bamuzo ba waye zaizo?,kedai sha kuruminki,abinci zaki dafa mana mai dadi nida ita a kitchen dinki" murmushi ne ya sake kubce mata,itakam widad har ta isa macen da zata shiga kitchen tayi girkin baqi kenan,saita kama murfin motar ta kuma shige,alhj salim ya miqa mata jakar,sannan ya tsaya daga bakin motar yana mata hirar dake sake dauke hankalinta.
A gajiye anty deena ta tura qofar dakin ummu tana sauke ajiyar zuciya
"Allah ummu nidai nayi iya dubana banga widad bafa" cikin mamaki ta dubeta
"Har wajen alhajin ku kin duba basa tare?" Kai ta girgiza
"Ban duba ba"
"Yi qoqari ki dubota,kinga kada suyi dare a hanya"
"Gaskiya dai,nima banason muyi tafiyar daren nan saboda sanyi" tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin.
Har zata gota jerin gwanon lafiyayyun motocin da aka shirya su saboda daukar widad din ta hangi alhajin tsaye jikin daya daga cikin motocin,saita dawo da baya,abinda ta gani ya sanyata kusan faduwa saboda dariya,widad ce zaune gaban motar ta qwame abinta,sunata hira da alhajin tana ta qyalqyala dariya,kome yake gaya mata oho,saita tsagaita dariyar tana kallonsu,murmushi na kubce mata,qasan ranta itama tausayin widad din na tsarga mata
"Kuruciya me dadi" ta fada a hankali hawaye nadan tsatstsafo mata,ta tabbatar inda ace babba ce yanzun haka ake shirin tattarata zuwa gidan miji,gidan mijin ma wata duniyar ba duniyarta ba,ba duniyar data rayu a cikinta ba,ba shakka da tuni tana nan hankali tashe,saita juya kawai zuwa cikin gida don ta sanar musu,tafiya ta tabbata tunda amarya har takai kanta cikin mota,murmushi ya sake kubce mata.
Dab da bakin falon sassan ummu sukayi kacibus da inna batulu momma
"Har yanzu ba'a ganta ba?" Ta fada a fuska alhini ne fal,yayin da qasan zuciyarta wani fata ne na daban,ba tare da anty deena ta kawo komai a ranta ba tana danne dariyarta tace
"Wa?,ai widad tuni tayi landing a mota" ido batulu ta zazzaro
"Kamar yaya deena?" Dariyar da take riqewa ta kubce mata
"Wallahi alhaji ya raka amaryarsa,kodan kishin nan ma bayayi,tana can tana jiran 'yan kawo amarya" dogon salati taja tana tafa hannu,sai kuma taja burki ta juya da sauri har tana tuntube ta koma zuwa cikin falon,da kallon mamaki anty deena ta bita,saita take mata baya tabi bayanta itama.
Tana shiga falon batulu na kwazawa 'yan uwan abbas dake zaune a falon suna jiran fitowar widad din don su wuce
"To ai bayin Allah zaman jira da qoqarin bikon da akeyi ya qare,amarya dai takai kanta cikin mota mu take jira" ran anty deena saiya sosu,duk da cewa akwai quruciya ga deena bai kyautu batulu ta kawo saqon a haka ba,fuskarta na nuna zallar alhini kamar ta aikata wani babban sabo a musulunce.
Inna uwa qanwa ga hajiya ta tura wayar hannunta cikin jaka tana sakin dariya
"La la la,lallai yaron namu badai farinjini ba,niko na godewa wannan diya tamu wallahi,ta hutashe shemu,saimu tashi shirin tafiya ta kammala" anty deena ce ta karbe cikin dariya
"Aiko dai batason wahal daku biyan kudin biko,ai shikenan" dariya aka dauka a falon,kowa yana fadin albarkacin bakinsa,kusan yadda batulu taso a juya zancan ya zamarwa widad abun fada abun baizo a haka ba,kusan kowa dariyar quruciyar yakeyi.
Sannu a hankali jerin motocin dake dauke da mafi yawan 'yan uwanta suka fara barin farfajiyar gidan alhj salim mai fata,motar da take ciki itace mota ya qarshe,duk da a tsarin tafiyar zata kasance cikin tsakiyar motar securities din da zasuyi musu rakiya har zuwa garin bauchin.
A hankali tasu motar ta fara motsawa,yayin da taketa dagawa su Aafiya hannu tana fadin
"Sai kunzo,karku damu,alhaji yace kamar wancan lokacin da naje gidan uncle muhsin,wannan lokacin har zuwa zasuyi shida ummu saimu dawo tare,idan zai taho ku taho tare dashi don Allah" ta fada tana kallon afiya,tans jin ba dadi itama,zuciyarta najin wani irin yanayi wanda.bata saba jinsa ba,irin yanayin dako sanda zataje gidan uncle muhsin bata sanshi ba,wannan shi ake kira da yanayi na rabuwa......rabuwa da gida..... rabuwa da muhallin da qaddara ta wanzar maka a haifeka a ciki......rabuwa da bigiren daka rayu kayi kuma gwagwarmaya a ciki.....fadi tashi tsakanin masoya da maqiya,zuwa wani bigiren da RUBUTACCIYAR QADDARARTA ta zana mata......BIGIREN dake qunshe da tarin qaddarorin rayuwarta.....qaddarorin dake da tsananin zafi quna da kuma barwa rayuwa tabo me cin rai.
Tun suna tafiya tana biye da hirar wadanda suke tare cikin motar wato anty deena,anty madeena anty madeeha da inna uwa,wani bangaren na zuciyarta kuma nata hasaso mata kayayyakin da dukka ummu ta nuna mata ta kuma shaida mata nata ne gidanta za'a kai mata,yadda zata sarrafasu ta more kayanta,irin yadda taga su anty deena anty ramziyya basma da sauran yayyunta keyi,zatayi iko irin nasu kenan itama,zata saka wasu wanke wanke idan sunzo gidanta,sai qaramar dariya ta qwace mata ita kadai,tana fasalta yadda zata saka su rafi'ah aiki,kuma dole suyi,saboda jiya jiya taji anty madeena na cewa ita din yanzu dukka ta girmesu,duk kuwa da cewa sun babbata wasu watanni.
*Arewabooks:Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Page 33
Table guda ya kama shi kadai,sanye da fara sol din shirt me gajeran hannu,sai wani lafiyayyen trouser daya dace da boots din qafarsa,coffee kawai yake sha,duk da yana da buqatar abinci,loneliness yake da buqata,yayi hayaniya har baisan iyakar adadinta ba,abinda ba dabi'arsa bace,yana tsoron hakan ya haifar masa da ciwon kai,wannan yasa ya zabi ya kebe shi daya ba tare daya gayawa kowa inda yake ba idan ka dauke suraj.
Tun jiya suke karbar baki,ko kusa ko alama bai dauka wani sabon bikin zasuyi ba,sai da yaje gidan hajiyarsa yaga yadda ta tashi gagarumin biki,ya koma gida bisa ga mamakinsa hafsat ta zauna tayi masa lissafi ta kuma