Showing 288001 words to 291000 words out of 296907 words
Chapter 97 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
wani lafiyayyen murmushi widad din ta sakar mata hankalinta kwance,ta koma ta zauna saman kujerar ta dora qafarta daya kan daya tana kallon hafsat din
"Ki kwantar da hankalinki,kowanne tsuntsu fa kukan gidansu yakeyi,mu namu kukan me dadi kyau da ma'ana ne,haka aka koya mana,yara kuwa sunzo gidan ubansu inda yafi dacewa dasu,inda zasu samu kulawar da suka rasa kaf iya tsahon rayuwarsu,na meye kuma zaki damu?,idan ka shuka alkhairi ai baka tsoron ranar girbi......oh......na manta,kina tsoron kada na maidasu 'yan wanke wanke ba?,ko masu yimin shara ko wanki,ko kina tsoron kada na dinga basu wankin kashin su affan ko su sajjad?" Saita girgiza kai
"Allah ya tsareni,banason ranar girbi na ta zamemin ranar kuka da nadamar baragurbin shukar dana dasa da hannuna,don haka kije kiyi baccinki harda minshari,zasu samu kulawar da ke kanki kika gagara basu,idan iya abinda ya kawoki kenan sai nace ki gaida gida,na gode da kyautar dan mutum sukutum da kikayimin har rai uku ba tare da nayi naqudarsu ba" saita qwalawa aminatu kira tace ta wuce ciki dasu.
A karon farko hafsat tabar gidan jiki a matuqar sanyaye,kalaman widad sun bugeta qwarai,anya batayi gwaari ba data dauka yaranta duka ya danqa mata su?,sai shaidaniyar zuciyarta ta jaddada mata tayi dai dai,dole yaran zasu dameta,kuma shine kawai abinda zatayi ta baqanta musu rai,batasan wannan abun da tayi shine abu na farko data yi wanda ya faranta ran widad ba,don kuwa cikin kwana uku kacal yaran suka fara hawa saiti,farincikinsu ya qaru,dadi kamar suyi me babu ma kamar mimi da taji a duniya an gama mata komai,ta dawo waje antynta.
Wannan kawo sun shi ya bawa abbas damar fara musu shirye shiryen tafiya america din gaba dayansu,ya kashe kudinsa sosai amma baiji komai ba,farincikinsa shine kasancewa da iyalinsa,sai a yanzu yakejinsa cikakken namiji kuma cikakken mutum,widad ta hada masa kan iyalinsa gaba daya,idan ka shigo gidan kai kanka sai ya burgeka,komai a tsare bisa doka da tsari,yaran sun soma samun wata cikakkiyar nutsuwa da kuma tarbiyya.
Ranar da suka bar nigeria ranar hafsat din ta daura auren da ta dinga fatan abbas din yana nan zata daurashi,to baisan ta daura din ba don tuni jirgi ya lula dasu,koda yaji dinma babu abinda zai dameshi,don a duniya bayajin akwai wanda ya fishi farincikin rabuwa da ita,ya yadda KADDARARSA ce zama da ita,a yanzun kuma yana kyautata zaton yaci jarrabawar da Allah ya saukar masa,shi yasa yayi masa tagomashin rabuwa dashi.
Rayuwarsu a america tazo da sabon tagomashi qarin wayewa da kuma budewar ido,don a nan ne widad tayi amfani da result dinta tayi course akan kasuwanci na shekara daya,don sun samu qarin wasu watanni shidan,a nan ta hadu da mutane sosai kala kala data qaru dasu,ta fannin gogewar Rayuwa mu'amala da zamantakewa, nau'in girke girke harma da gyaran kai gyaran jiki da kuma kula da iyali da miji gaba daya,ta samu experience na rayuwa me tarin yawa,bayan sun cika shekara suka tattara suka dawo,dukka yaran sun canza,sunyi dima dima sunyi fresh dasu,sai suka zama wasu ababen kallo,widad business dinta ya kankama,don tayi business sosai tacan,ta kawo kaya a shekarar kamar ba gobe,ta rabawa yan uwanta duka harda dangin miji,kowa ya samu alkhairi yayi murna,don sun qaru da ita,wasu har qaramin jarinsu suka tayar,hannunta me albarka ne sosai da komai ta taba sai ya siyu da tarin alkhairin ubangiji,ne yiwuwa zuciya me kyau da take da ita ne ya zame mata silar hakan.
Kai tsaye suka sauka a tsohon gidansu da suka bari ana yiwa sabon gini,wani irin tsari aka yiwa gidan me matuqar jan hankali kamar a turai,masu sannu da zuwa da zuwa ganin sabon gida aka yita tururuwar zuwa, widad nata jin kunya tana boyen qaramin cikin data dawo dashi,a lokacin duka duka shekarar su sajjad daya da wata shida,ita a ganinta sunyi qanqanta da ayi musu qani,duk da sanda ta haifesu affan ma baikai haka ba.
kuka ta dinga yi tace ita bataso
"Ya kikeso yanzu ayi dashi"
"Nidai a zubar"
"What!!!" Ya fada da mugun qarfi
"Eh lallai na yarda baki da hankali,kuma har yau baki girma ba,bari kiji abun Allah ya kiyaye Allah ya tsare,ko cikin shege nayi miki ai baki isa ki zubarmin da ciki ba" cikin wannan rigimar tasu suka iso nigeria,yana shareta tana shareshi,kowa yana ganin yafi dan uwansa gaskiya.
Yau tunda ta tashi batajin dadin jikinta sosai,don haka koda safe ma tana jinsu suna sabgoginsu daga can babban falon gidan amma bata leqo ba,tasan aminatu zataji da komai,ga adda mimi kamar yadda tasa suke ce mata,yarinyar akwai qoqari,duk wani aikin zaka sameta tana taya aminatu,widad din bata taba hanata ba,saboda tana tuna wahalar data ci sanadiyyar rashin iya komai a aikin gida,duk da gatane na goyon kaka,tafison idan ta tashi aurar da mimi din kamar yadda take fata wanda duk zai auresu ya qare rayuwarsa yana shi mata albarka.
Tana kwance abbas din ya gama shirinsa,yazo kanta ya tsaya,saita dauke kanta gefe,yakai hannunsa ya taba wuyanta,sai ya sauke ajiyar zuciya jin bawai zazzabin da yake takurata ne a jikinta ba,yana mamakin yadda ta iya shareshi da gasken tsahon kwanakin,sai yasa hannu yadan shafi fuskarta kadan yana fadin
"Sai na dawo"
"A dawo lafiya" ta fada ciki ciki,sai kuma tabi bayansa da kallo,bayan ya fitanbta lumshe ido tana fidda numfashi mai sanyi.
Abbas miji ne na musamman,idan tace na musamman tana nufin hakan,duk yadda sukakai ga fada ko sabani da juna saidai iya kan harshe kawai,amma duk wata kulawa basa fasa baiwa junansu.
Agogo ta kalla,qarfe daya saura,ta yunqura zata miqe ihun sajjad ya kawo mata har nan inda take,tasa hannuwanta ta toshe kunnuwanta
"Allah ya yiwa aminatu albarka" ta fada idanunta a runtse,batason hayaniya kwata kwata,banda akwai aminatu da mimi da batasan yadda zatayi ba,dole yanzun ta fita,tasan filin dambe aka bude tsakanin affan sajjad da sajid,wataqila yusra na gefa tana tilliqa dariya,nawwara na qoqarin shigarwa affan mutuminta,saita sauko kawai ta shiga bandaki ta wanke fuskarta da bakinta ta fito ta zura wata sassalkar abaya a jikinta,already da wankanta dama,don bata iya kaiwa haka batayi wanka ba sam,ta zura wasu lausasan slipper kalar abayar ta fito tana daura siririn dankwalin rigar a kanta wanda bai rufe komai a gashin kanta ba.
Falon kuwa ya kacame gaba daya,duk sun ruda aminatu kamar tayi kuka,dama gata gwanar sanyi,saida widad tayi musu tsawa sannan suka dakata da abinda sukeyi,sai kowa ya fara shiga taitayinsa,suka matso kowa yana gaidata
"Maami ya jiki?" Suka dinga cewa,mamaki ya kamata,oh wato abbas yace musu bata da lafiya kenan?,zai hada mata case,yanzun idan suka dinga mata sannu har sai ta gaji,har sai an fuskanci abinda ke maqale a jikinta
"Jiki alhmdlh,na warke ai"
"Allah ya baki lafiya maami" mimi ta fada cikin damuwa da kulawa
"Ameen mimi na" tattarasu duka tasa aminatu tayi waje daya,ta kunna musu cartoon din da sukafi so,sai aka samu salama kowa ya nutsu,sai sajjad da sajid da lokaci bayan lokaci ake fama dasu ana bari bari.
Dining ta wuce ta duba abinda aminatu ta dafa musu,saita zauna daga can saman ta hafa baqin tea tana dan kurba kadan kadan tana kallon yaran,rai shida dukka yaran abbas,ga na bakwai a jikinta,kome zata haifa kuma Alla masani,cikin ranta ta samu kanta da addu'ar Allah ya raya mata su taga girmansu,ya bata ikon ci gaba da tarbiyyantar dasu.
Qarar wayarta dake gefe ya katseta,ta duba wayar saita saki murmushi,ummunta ce,ta gyara zama ta daga wayar cikin shagwabar da har yau bata iya daina yiwa mutum biyu a duniya ita,suma kuma har yau bata girma a wajensu,abbas da ummunta.
Ta sakankance sosai suna hirarsu kusan rabin awa,sai taga aminatu ta buda qofar falon ta fita,sai gata ta dawo,ta hauro inda widad ke zaune
"Maami baquwa kikayi,to mai gadi ya hanata shigowa waisai an gaya miki" mamaki ya cikata,bai tana hana kowa shigowa ba muddin ya yarda dashi sai yau?,da yake qarin matsayin da ya samu yana da me gadi cikin qananun 'yan sanda,hakanan an bashi driver da security
"Koma wace a barta ta shigo" ta fada tana maida wayarta kunne,idanunta akan qofar falon har zuwa sanda labulen ya dage fuskarta data jirkice ta bayyana,saita zame wayar daga kunnenta tana cewa ummu
"Zan kiraki ummu anjima"
"To babu damuwa" ummun ta fada tana a gaida mata kishiyoyinta da masu gidan.
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02
Page 44
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba ko kit dinsu inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd wnn new soap din💣ne,😯 bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida
You can check pic👇for the soap reviews🥰
Soap price:4k
maiso yy mgn Whatsapp
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook: mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki sannan akwai na amare special Wanda inkinyi using baki Kuma bukatar kiyi Wani gyaranjiki domin keda kanki zaki shaida cewa fatar taki ta wanku tarwai😍08062991549
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏
_______________________________
Har yanzu kallon fuskarta takeyi,tanason tantancewa itace ko ba ita bace.
Yadda itama take kallonta haka baquwar,kafin ta janye idanun nata ta maida kan yaranta dake zaune gaban tv sun bata hankalinsu,wasu hawaye masu ciwo suka tsatstsafo mata,dai dai sanda widad ta miqe tana cewa
"Sannu da zuwa" gami da gangarowa daha step na dining din
"Yauwa sannu" ta amsa mata murya a dakushe,widad ta qaraso wajen can gefe daga inda yaran suke tana fadin
"Bismillah zauna"
"Har ina iya zama?"
"Ba damuwa ki zauna......mimi ga mummynku,nawwara yusra?,maza ku taso,aminatu a kawowa baquwa abun tabawa" duk sai hankulansu yayo kanta,duk suka tsaya suna kallonta da kyau,kamar basu ganeta ba.
Itama ido ta tsura musu,hawayen da take riqewa ya silmiyo mata,sai suka miqe dukansu sukayo wajen uwar jiki a matuqar sanyaye,dadi ya kamata,ta bude dukka hannuwanta suna isowa ta rungumesu tana sakin kuka mara sauti.
Sun jima a haka,tausayinsu yana ratsa widad,Allah alhakim,Allah mai iko,Allah me gaggawar hukunci mai sakayya da hisabi tun a nan gidan duniya,wai yanxu hafsat ce haka?,kamar wata almajira?,cikin shekara guda kacal,cikin wata mummunar kama da siffa.
"Naji dadin ganinku haka mimi,duk da dama raina yana rayamin ba za'a samu wata matsala ba,kuna cikin aminci da kulawa,don na tabbatar ban barku a mummunan hannu ba" hafsat ta fada tana sharce hawaye
"Na gode,Allah ya saka da alkhairi,Allah ya biyaki da yadda kika riqemin yarana" ta sake fada tana kallon widad kamar me kunyar su hada ido.
Duk mamaki sai ya kama widad din,hafsat dince ke mata godiya har tana yabonta,lallai kaji tsoron duniya kaji tsoron ubangijinka
"Ba komai,d'a ai na kowa ne,da dukiya da d'a babu wanda yasan me morarsu sai Allah"
"Haka yake" ta fada tana jinjina kai,gami da tuna tata dukiyar data dinga salwanta daya bayan daya,har ta zamana a yanzun bata da komai bata mallaki komai ba.
Ta jima da yaran a falo widad ta basu waje suna hira,sunata gaya mata abubuwan da suka faru da kuma zamansu a america,a ranar taji farinciki da nishadin data jima bataji irinsa ba,damuwarta ta ragu qwarai da gaske,ta sake gasgatawa lallai yaran sune sanyin idaniyarta.
Data tashi tafiya cikin d'ari d'ari tace da widad
"Don Allah zan roqi alfarma guda biyu a wajenki idan zan samu"
"Babu wata damuwa,ki fada ko menene"
"Don Allah ina roqarki ki yafemin duk abubuwan da nayi miki,sannan ki roqarmin babansu shima ya yafemin,duk da nasan saimai qarfin imani ne zai iya yafewar"
"Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe,duk abinda ya faru ya riga da ya faru,shima zan gaya masa,zai kuma yafe din in sha Allah"
"To na gode qwarai qwarai....alfarma ta biyu don Allah ki sake roqarmin shi,ya dinga barin yaran nan suna zuwarmin,koda ba kwana ba,ko basu yini bama don Allah" tausayinta ya sake kama widad,kaida yaranka amma saika roqi a baka su ka gansu
"Xan gaya masa,kada ki damu kinji" godiya sosai ta sake yiwa widad din,sannan ta miqe tana musu sallama
"Gashi ban kawo muku komai ba,kuyi haquri babu dama ne" cikin son kwantar mata da hankali tayi murmushi
"Karki damu fa,suna da komai mummyn mimi" kai ta jinjina
"Shikenan,na gode Allah ya saka da alkhairi" tsaidata widad tayi ta wuce bedroom dinta,cikin matuqar sanyin jiki da kuma tsoron halin duniya ta dauko hand bag dinta data dawo da ita ta buda,ta laluba kudin ciki,duka duka dubu goma ce tayi mata saura kudin nigeria,saita shiryasu ta fita dasu ta miqawa hafsat.
Jikinta na rawa cikin mamakin yawan kyautar da tayi mata tasa hannu biyu ta karba qwalla tana cika idanunta,shekara guda kenan rabonta da riqe kudade irin wadan nan,godiya sosai ta dinga yi mata,sannan ta juya ta fice hawaye wani yana korar wani.
Haqiqa duk wanda baiji tsoron Allah ba yana tare da wahala,duk wansa baibi duniya a sannu ba matsala bata qare masa ba,a yau yaran da take banzatarwa gasu tana ganinsu tana qaunar su rabeta,tana qaunar zama dasu amma sunfi qarfinta,don tasan ko sama da qasa zasu hade a yadda taga sun samu kwanciyar hankali da kulawa abbas bazai taba bata ko daya daga ciki ba.
Gidanta da take ganinsa kamar mallakinta,ta kasa kula dashi,ta banzatar dashi gashi a yau yafi qarfinta,ta fita ta barwa wadda tazo gidan daga baya.
Mijin da take banzatarwa,ta kasa tsayawa ta gyara kurenta,ta kasa tsayawa ta karanci abinda yakeso da wanda bayaso,ta kasa bashi abinda yake muradi cikin rayuwarsa.....gashi qaramar yarinyar da a haife ta haifeta,tazo ta sha gabanta,ta shiga rayuwarsa ta maye masa gurbin komai.
Idanunta sun rufe,amma a yau suna bude kansu da kansu,tsantsar kishin banza da jahilci mara ma'ana yasa tabar gidanta, mijinta da yaranta dukka yanzu sun zama mallakin wata,saboda anyi mata kishiya ta kasa haqurin zama a gidanta,ta fita daga raminta ta fada ramin wata,tabar ramin data gina ta fada ramin wata,watar dake gallaza mata ita da mijin da baisan darajarta ba (babban qalubalen dake damun mata, mijinki da yasan darajarki,gidanki da kikasan ciwonsa,yaranki da basu da kamarki,dukka sanadin miji zai qara aure saiki watsar dasu kice saiya sakeki,bayan bai wulaqantaki ba,yayi hakanne saboda wani qarin auren a qaddararsa yake bai isa ya tsallaketa ba,babban abun mamakin kuma shine,sai ka ganta can ta buge da auren wani me matar,wai shin da ramin daka gina da kanka?,da wanda wani ya gina ka shiga zai zamto daya a wajenka gurin samun 'yanci da komai ma?,mata mu nutsu mu yiwa kanmu karatun ta nutsa,kishi yana da ciwo,yana da matuqar zafi,babu komai ke gane hakan sai masu zaune da kishiyoyin,to amma kuma ita addu'a maganin komai ce,sannan duk wanda ya miqa lamarinsa ga Allah,Allah ya isar masa,Allah yasa mu dace,yasa mufi qarfin zukatanmu amen).
Widad ta dade tana juya abun cikin ranta,ta dade tana tuna fuskar hafsat,Allah abun tsoro duniya abun tsoro,sai jikinta ya sake sanyi,hakanan ta sake lafkewa akan kujera,tana tuna ko akwai inda ta sabi ubangijinta?,iya tunaninta bata tuna ba,amma saita samu kanta da istigfari,zuicyarta kuma ta sake tsarkaka,tare da sake daura aniyar kula da yaran tsakaninta da mahaliccinta,duk da dama ko sau daya zuciyarta bata taba bata wai ta zaluncesu ba.
*H A F S A T*
Sai data tsaya a soron gidan ta gyara zaman kudin sosai a jikinta cikin zaninta sannan ta sanya kai cikin gidan qirjinta yana dukan uku uku.
Da ita kuwa ta fara hada ido,tana tsaye a gaban falonta,gaban hafsat yayi wata mummunar faduwa,tayi saurin janye idanunta,sannan da hanzari ta doshi dakinta kamar zataci da baka,tasa hannu ta tura qofar ta bude kai tsaye don dama bata kulle qofar ba,saboda bata ma da ikon don zata fita ta rufe qofar dakin nata.
Falo ne falle da daki a ciki,kujerunta ne tun na aure,wanda su kadai ne suka tsira mu'awiya bai dauka ya siyar ba,maimakon ta samu guri ta zauna saita maqale jikin window din tana leqen tsakar gidan,tana kallon sahura dake mazaunin kishiyarta tana hararar qofar dakin nata,sai kuma ta daga zaninta ta ciro wayarta tecno keypad.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" hafsat ta fada jikinta yana rawa,tasan yau ta kade daga ita har ganyenta,dama tasan tunda ta fita batayi mata sallama tare da gaya