Header Ads
Showing 294001 words to 296907 words out of 296907 words

Chapter 99 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

sannan yace

"Wait......wai zuwarmin gida ma takeyi ba tare da na sani ba?"

"Relax uncle manaaaaa" ta fadi tana juyowa da sauri cikin wata narkakkiyar shagwaba hadi da zube masa fararen manyan idanunta,sai ya dan lumshe ido ya sauke ajiyar zuciya

"Uhmmmm.....u have all my ears"

"Bata taba zuwa ba sai yau,kaima ka sani,tunda duka duka yaushe muka dawo qasar uhummm?"

"Naji,ni banaso tana shigomin gida,kada ta cutarmin dake wataran,i will send her the kids duk sanda naga ya dace,ama bance zasu kwana ko daya ba,kada ta qara zuwanmin gida please" ido ta lumshe gami da gyada kai,ita komai ma mamaki yake bata,ta yaya zata samu miji irin abbas indai ba mummunar qaddara ba tayi saken da zai kufce mata?,the best husband ever.

Sajjad da sajid ne suka fiddasu don dole,suka zauna dukkansu suda yaran a table mat suna cin abincin cikin wani irin yanayi da zai nun maka kyakkyawar rayuwa da mu'amala ta gari da kuma cikakkiyar tarbiyya da suke samu,kai kanka idan kana wajen sai familyn yayi mugu mugun burgeka.


***********Katafaren gidan da ya zama na daban cikin layin shaqe yake da jama'a,gida ne da ya zama mallakin IG(inspector general of police) ABBAS TURAKI,tako ina kana hangen yadda tun daga layin har zuwa bakin titin dazai shigo dakai ainihin kayin ke shaqe da al'umma da kuma ababen hawa na alfarma,ko ina shaqe yake da jama'a,yadda manyan riguna da kuma fararen kaya keta nuna kansu,na wannan yana wane wancan,da kuma yadda busar algaita ke tashi kadai zai gaya maka cewa wani katafaren daurin aure akeyi.

Ta cikin microphone din dake fitowa daga masallacin,kana iya jiyo muryar wani qaqqarfan mutum na cewa

"An bawa muhammad yasir matawalle auren Dr raheema(mimi) IG abbas turaki akan sadaki naira dubu dari lakadan ba ajalan ba......eh diya ga shugaban duk wani dan sanda dake nigeria" ya sake bayani cikin kambamawa irin na maroqa.

Dai dai lokacin da IG abbas ke zaune daga can wani sashe na masallacin cikin shigar alfarma ta farar shadda da babbar riga me asalin tsadar,fuskarsa cike da wani irin haiba kwarjini da kuma cikar kamala,sanarwar data haifar da wanzuwar murmushi saman nutsatsiyar fuskarsa,ya sauke boyayyr ajiyar zuciya yana godewa Allah da ya fara nuna masa auren diyar cikinsa ta farko.


*C I K I N G I D A*

Wani kebantaccen falo ne dake da matuqar kimar da ba kowa take bawa damar saka qafarsa a ciki ba,falo ne na musamman da aka tanadeshi saboda hutawar IG,yake kuma samun kulawa qarqashin uwar gida sarautar mata wato hajiya widad,kamar yadda komai na IG din yake qarqashin jagoranci da kulawarta,duk kuwa da ma'aikatan dake gidan.

Duk girman falon su biyu ne a ciki,ita da amarya mimi dake lullube cikin wata lafiyyayar alkyabba,hannunta dake dauke da Wani irin lalle yana sanye cikin tafin hannun hajiya widad da yasha lafiyayyen jan lalle da bata rabo dashi,wadda tana zaune ne a gabanta suna fuskantar juna,tana karanto mata wasu addu'o'i tana maimaitawa.

Ta dauketa ne daga cikin taron hayaniyar jama'ar saboda yadda tunda satin bikin ya kama take fama da koke koke,ita batason tafiya tabar maami,ita ba zata je ba,hankalinta na sake tashi idan ta tuna a yau zatabar qasarta ta haihuwa,zata tafi wata uwa duniyar zaman aure ita da mijin da Allah ya bata wato muhammad yasir.

Sai data gama karanta addu'o'in kaf yadda maamin tata ta karanta mata,sai suka hada ido,widad tayi qoqarin danne raunin zuciyarta don kada ta karya ma mimi qwarin gwiwar data samu

"Basai nace miki komai ba mimi,bani da haufi a kanki,kowanne d'a namiji zaki iya zaman aure dashi,ki kuma mallaki zuciya da hankalinsa babu boka ba malam" kai mimi ta jinjina,ita shaidace yadda maamin nasu ke tafiyar da mahaifinsu,koke 'ya mace akewa haka sai an samu kanki fiye da zato,wata irin macace da batasan ya zata fasaltata ba,a taqaice ta zame mata wata role model dinta,tana kuma alfahari da ita,hakanan tana kiranta da uwa a duk inda ta shiga a duniya,maamin ta zamewa rayuwarsa alkhairi,dukkan mutumin da ya shigo rayuwarsu daga baya yana mata kallon mahaifiyarsu ce data tsugunna ta haifesu,ta basu abinda dukka uwa ke bawa yaranta,harma abinda wasu uwayen suka kasa bawa yaran nasu,koda wasa bakinta bai taba kiran widad a matsayin uwar riqo ba bare wani suna na kishiyar uwa,kullum kallon mahaifiya suke mata,duk da sunsan asalin wadda ta haifesun,amma ko ita kullum gaya musu takeyi widad dince babarsu,itakam kawao naqudarsu tayi ta kawosu duniya,amma idan suna neman uwa itace.

Zamewa tayi ta tsugunna gabanta

"Maami ki yafemin don Allah tsahon zamanmu idan na taba bata miki...." Da sauri ta kama kafadunta ta dagota ta zaunar da ita sosai

"Bakiyimin komai ba mimi iya zamana daku,kun riqeni kamar mahaifiyarku,saidai nan gaba zakiyimin laifin" da sauri ta daga kai ta dubeta,saita sakar mata murmushi tana jinjina kai

"Eh,muddin baki zauna lafiya gidan mijinki ba,muddin bakiyi haquri dashi ba,muddin ya kawo qararki gida ya zamana kece da laifi"

"Bazan miki laifi ba kuwa har abada maami,saidai in har ajizanci irin na dan adam" ta fada kuka na qwace mata,idan batayi zaman aure bama ai bata yiwa maaminta adalci ba,ta basu dukkan misalai na rayuwa da zamantakewa a baki da kuma a aikace,su shaida ne sun gani.

Juriya da jarumtar nan tata ce kawai ta hanata kuka,tayi qoqari ta saukar da mimi daga kukan da takesonyi tana tsokanarta,dai dai sanda khadijatou (diya mace qwaya daya da widad din ta haifa qanwa ga mimi) taturo qofar a hankali tana baza ido

"Na shigo maami?" Ta fada a dan shagwabe tana leqo da kanta

"Meye haka kamar munafuka?,shigo ki rufen qofa banason wancan me zuciyar matan(affan) yasan muna ciki yazo su hadu suyita ma mutane kuka kamar cewa akayi idan ta tafi ba zata dawo ba" murmushin yaqe khadijatou kawai tayi,don itama daurewa kawai takeyi,anty mimin she's the part of their lives,ta iya tafiya da qannenta cikin kulawa da qauna,bata fada amma ta iya hukunci,ta iya wasa da dariya amma idan gyara yazo babu wannan wasan,dukkansu sun dauketa kaman abokiyar wasansu,amma kuma suna girmamata sosai,itama ta iya zama da kowa a cikinsu da halinsa,sun taso da shaquwa da qaunar junansu qwarai,ba zaka taba cewa ga wadanda suke uwa daya uba daya ba,yanzun haka khadijatou tafi nawwara jin tafiyar mimin,har gwara yusra ma,itama duk da haka affan ya fita rauni,saboda anty mimin abokiyar sirrinsa ce,kuma abokiyar gulmarsa,sai mimin taji abunsa maami widad bataji ba.

"Wai dangin angon sun sakeyin tuni,sha biyu zasu wuce airport din,jirgi qarfe uku zasu bi" ta fada qasa qasa tana satar kallon anty mimin nasu,kai widad ta jinjina

"Yayi gamu nan" a sanyaye khadijatou din ta juya ta fice tana matse qwallarta.

Hannun mimi maami widad ta riqe cikin nata, suka ratsa falon suka fita ta qofar baya suka wuce kai tsaye suka sashen da aka sauki mummy hafsatu da danginta.

Da sallama ta shiga matsakaicin falon sashen,mummy hafsatu na zaune saman kujerun falon,sanye da wani lace wanda widad dince ta dinka mata shi da kudinta,tace koda bataci arziqin abbas na kai tsaye ba tunda tana da igiyar auren wani a kanta ba,amma zataci arziqi sa darajar yaranta su mimi.

Da sallama ta shiga,hafsat da dangin hafsat din da suke tare da ita suka fara yiwa widad din sannu,don ko maqiyinta ya yaba mata,yaga yadda ta kasa tsaye ta kasa zaune kamar diyar data tsugunna ta haifa take aurarwa.

*_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_*

*LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete*

*GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA*

_kama daga kan_


Furnitures
Decoration
Kitchen items &
Boutiques

_our tittle_

Quality is our watch word at lifestyle

shop kano/kaduna

Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot


Instagram@ Lifestyle_Nig
Facebook@ Lifestyleng
Tik tok@ Lifestyle_Nig
Delivery nation wide

_ku tuntubemu ta wannan number_

08036414048

*Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah*

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 47 END


*_TURK'ASHI!,BABBAN GORO SAI MAGOGIN K'ARFE,KU MARMATSO KUJI,GIDAN KOMAI DA RUWANKA_*

*LIFE STYLE NIGERIA for everything that makes your life style complete*

*GIDAN KOMAI DA KOMAI RUWANKA*

_kama daga kan_


Furnitures
Decoration
Kitchen items &
Boutiques

_our tittle_

Quality is our watch word at lifestyle

shop kano/kaduna

Shop no 58 kabuga housing estate janblo kano on the road in between first gate and second gate near kashe magana suya spot


Instagram@ Lifestyle_Nig
Facebook@ Lifestyleng
Tik tok@ Lifestyle_Nig
Delivery nation wide

_ku tuntubemu ta wannan number_

08036414048

*Muna tura kaya ko ina cikin aminci da yardar Allah*
_________________________________


Gaban hafsat taje ta tsugunnar da mimin sannan ta zauna daga gefe

"Mummyn mimi,ga mimi tazo neman albarka,yau dai Allah yayi zata tafi nata gidan,sai ayi mata sauran nasiha a kuma saka mata albarka" hawaye hafsat din ta fara sharewa,farinciki ne fal zuciyarta na samun uwar riqo ta gari da sukayi,ta tabbatar inda a hannunta suke babu lallai mimi din ma ta samu miji irin muhammad yasir,wanda ba abinda ya fara burgeshi da mimi din sai tarbiyyarta da kuma nutsuwarta,shine babban abinda ya fara jan hankalinsa

"Aikin gama gaya mata komai,nikam babu abinda yayi saura da zan gaya mata wanda baki gaya nata ba, abinda zata samu daga bakinki yafi wanda zataji daga gareni,abu daya zan gaya mata shine,tayi koyi dake,tayi koyi dake,tayi koyi dake,don kin zamewa rayuwata alkhairi,kin maida yarana abun kwantace abun sha'awa,kin gyatta tawa rayuwar nima a yanzu na dace da mijin da yasan darajata,kin rabani da mu'awiya,Allah ya hadani da mudassir kin kuma tsayawa rayuwata da jari da sana'a,wanda yayi maka wannan me zakace dashi?"

"Babu...babu" shine amsar da yan uwanta da a yanzun suke zumunci ta kuma.kamasu da amana irinsu anty uwani amsar da suka bayar kenan,a yanzun suta riqe ta watsar da irinsu anty ummee duk da suma jikin ta qaura yayi la'asar, rayuwa ta gama karanta musu nata karatun.

"Allah ya albarkaci rayuwarki,ya baki ikon yin koyi da babarki widad" shine maganar hafsat na qarshe,akayi addu'a sosai sannan suka miqe don sadata da dangin banbanta su gwaggwo mero sukayi sallama.

Sanda akaxo sanyata a mota don su wuce kasa tsaiwa gurin widad tayi,don dukka dauriyarta ta qare,yaran duka affan sajjad sajid khadijatou nawwara yusra al'ameen harda auta fadil kuka sukeyi,sun riqeta kyam sai da IG yazo ya tsawatar musu yana hararar affan

"Kai dai kam anyi yaayan banza,ita kanta yanzun mimi din ba kaine yayanta ba?" Akasa dariya gaba daya,sai affan din ya fara ciccijewa kuma yana qoqarin maida qwallar data cika masa ido,ya waiwaya gasu sajjad, identical twins masu kama daya

"Ku kuma mage da bera.......kun gama cakar da ita sai yau kukasan yaaya mimin taku ce?, nawwara harda ke?,ranar fa ina jinki kina cewa gwara ta tafi ta barki ki shaqata,ba wanda zanwa jaje ma sai hadizatu" yusra ta yunquro


"Daddy nifa..."kafin ya bata amsa al'ameen ma yace

"Nima daddy" duk sai suka bawa kowa dariya,kowa so yake ya nuna mimin tashi ce,shi kansa IG a sannan qarfin hali da dauriya kawai yakeyi.

Kusan duka motocin gidan aka dauka yiwa mimi rakiya airport,duk titin da suka ratsa sai ansan 'yar IG ce zata wuce,don qarqashin security suke har suka isa.

Sai da suka isa din IG abbas ya juya ya juya baiga widad ba,ya saki murmushi qasan ransa,yasan tana can tana kukan data ci masa alwashin ba zatayi ba,basu bar airport din ba sai da jirginsu mimi ya tashi sannan kuma sukayo gida.

Sanda ya dawo ya dinga bulayin nemanta cikin gidan amma bai ganta ba,daga qarshe acan part dinsa cikin qawataccen bedroom dinsa ya cimmata,ta gama kukan nata ta wanke fuskarta,tana tsaye gaban madubinsa tana laluben powder da takan ajjiye zata shafa.

Sunan hada ido tayi saurin janye idanun nata,ta wani hade rai tasha mur,ita lallai kada yace ta karaya sai da tayi kukan,dariya ta qwace masa ba tare da ya shirya ba,dariyar tasa ta qara raunata zuciyarta,yazo bayanta ta tsaya yana duban qwayar idanunta,sai kawai ta sakar masa kukan shagwaba tana fadawa jikinsa,shagwabar nan da har yau ba abinda ta rage masa a cikinta,bata ganin girmanta idan tana tare dashi,kamar yadda bata ganin girma da shekarun abbas din,har yau tana ganin kamar jiya jiya suka hadu,kamar jiya jiya aka daura musu aure,shi dinma kullum kallonta yake a mitsitsiyar widad din nan,shagwababbiyar ummu,mai yawan tsoro wauta da sakalci.

Ya zare babbar rigarsa ya ajjiye gefan gado yana murmushi,ya sanya hannuwansa duka ya ya lullubeta cikin jikinsa,ya sani daman,ba zata iya jura ba,kuma duk duniya a yanzu shi yafi kowa iya lallashinta,yadan hura mata iska a fuska kadan yana cewa

"Ai dama na sani,you can't take it......ke kuma da son yara,ai dama na shirya aikin lallashi" sai da yaga kamar kukan bazai tsaya ba sanann suka zauna,ya kama dukka hannayenta yana bata baki,daga qarshe ta buge da murmushi cikin jin kunya tana boye fuskarta saboda wata kalma da ya gaya mata,ya miqe shima yana dariya

"Nifa madam aiki yayi kira,ina tunanin nima yau da dare zanbi jirgi na koma abuja,ki taimakeni ki sallami baqinki kiyi qoqari ki biyoni,bana jin dadin gidan sam idan baki kusa" ta riga data saba,duk inda abbas din zashi sai ya ganta a gefansa hankalinsa yake kwanciya,duk inda zashi a nan nigeria ko a waje sai ya tafi da ita,tun tana zolayarsa harta gane haka tsarinsa yake,a jininsa qaunarta take,hafsat ta kasa fuskantar sa tun farko akan irin wannan tsarin nasa abinda ya fara kawo musu matsaloli kenan tun yana qaramin dan sandansa ana yawan masa musayar garuruwan aiki,shi mutum ne dakeson ko yaushe yaga yana tare da iyalinsa,bawai kasancewa ta auratayya ba, a'ah, at least ya dawo daga duk inda yake ya shigo gida ko masauki ya tarar dake,ita data fuskanci hakan sai ta bashi dukka rayuwa da lokacinta,shi kuma ya sakar mata ragamarsa.

Bashi da tsanani ko takura sam,mutum ne mai wani irin sauqin hali kawaici da kuma yawan bada uzuri,shi yasa idan kaga yadda sukeyi da 'ya'yansa da yadda yake mu'amala cikin gidansa abun zai daure maka kai sosai,ba zakace shine wannan namijin zakin IG din ba

"Zaki biyonin please?" Ya tambayeta cikin karya murya, dariya taso kamata

"Habba uncle.......ka girma fa,yau din nan ka aurar da diya ko ka manta?" Mur yadan sha

"Hakane fa,zaki biyonin?" Ya fada yana murtike fuska da murya,dariya ta qwace musu a tare saboda yadda yanayinma sam bai masa kyau ba

"Zan biyoka uncle,kusan zuwa anjima dama kowa zai wuce gida,na nesan ma gobe zasu tafi,amma ayimin alfarma zuwa jibi saina taho,zan sauka na duba jikin ummu daga can saimu siya wani ticket din,banason ma mu wuce jibin saboda yara duka zasu koma school suma,banason faashin makaranta" fuskarta ya kama yayi kissing goshinta

"Na gode,Allah yayi miki albarka,yadda kika kula dani da yarana da sauran dukka dangina,ina roqa miki aljanna madaukakiya tun daga duniya har zuwa lahira" murmushi mai sanyi ya qwace mata,ta kama button din rigarsa tana dan wasa dashi

"Kaine sirrin komai uncle,ka cancani fiye da haka,don ka zamewa rayuwata wani alkhairi,tun bansan meye rayuwa ba har na santa,Allah ya dawwamar da farinciki a rayuwarka yaci gaba da yi maka jagora,ya doraka saman maqiyanka,ya tabbatar da nasara a dukka rayuwarka"

"Ameen summa ameen wuddu na" ya fada yana jifanta da wani sassanyan kallo daya sanyata jin kunyarsa,saita fice tana cewa bari ya hado masa abinci,ta tabbatar jama'a basu barshi yaci ba,daga nan kuma ta duba komai ta samu yana tafiya yadda ya kamata,su amina su nujood Aafiya na'eema da muneera na kula da komai,don haka ta wuce kitchen ta dauki zababbun warmers din IG ta soma shirya masa abincin da kanta.

*Komai yayi farko yana da qarshe!!*


_Alhamdulillah,Alhamdulillah,Alhamdulillah,dukkan godiya ta tabbata ga Alla madaukakin sarki me kowa me komai daya aramin rai da lafiya har na kawo qarshen labarin A RUBUCE TAKE_

_thank you arewabooks followers for being with me all this while from beginning to end_🥰🥰👏🏽

_Godiya ga tarin masoya mabiya daga kowanne lungu da saqo na media,musamman wadanda basa gajiya da kasancewa tare damu da siyan rubututtukan zafafa biyar ta manhajar watsapp,Allah ya qara danqon zumunci da qauna mara yankewa,ubangiji ya kula da lamarinku_

*Abinda muka rubuta dai dai Allah ya bamu lada,wanda muka kuskure kuma ajizanci ne irin na dan adam,muna fatan Allah zai gafarta mana,ya yafe mana kusakurenmu mu daku gaba daya,sai Allah ya sake sadamu a rubutu na gaba da wasu ZAFAFAN LABARAN idan ubangiji ya bamu aron rai da lafiya*

*Na gode na gode na gode*

@team zafafabiyar

_subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'atubu ilaika_👏🏽👏🏽

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads