Header Ads
Showing 279001 words to 282000 words out of 296907 words

Chapter 94 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

zai qarasa gidan suraj da yake basu da nisa,idan sun shiga wata sabgar yasan zata iya maida kanta gida,idan kuma ya dawo da wuri sai ya maidata

"Koka maidani dawowa zakayi,kasan dai kwanan waye ai" harara ya balla mata,tayi kamar bata gani ba ta wuce ciki tana qunshe dariya tana riqe da hannun affan da ya fara koyon tafiya,wannan yasa ta dinga takawa a hankali cikin kula da takatsantsan.

Tun daga qofar gidan jama'a ne,ta dinga gaisawa da mutane sunayi mata sannu saboda ganin yadda tayi nauyi sosai da uban ciki a gaba,yan mata matan suka daukar mata affan din suka kutsa cikin gidan dashi ita kuma ta tsaya tana ci gaba da gaisawa da mutane.

Hafsat din na tsakar gida anata rabon tuwon sauka,gaba daya ba cikin sukuninta take ba ganin yadda su mimi suka shiga sabgarsu cikin mutane,ko ta kanta basayi,yaran sunyi fes dasu sunyi haske sunyi qiba

"La la la,da gani babu tambaya wannan yaron sir abbas ne" wata qanwar mijin yaaya bara'atu ta fada bayan an shigo da affan ciki

"Tubarkalla ma sha Allah,yaro ya debo ruwa biyu,miqomin shi na ganshi" ta miqa hannu tana karbar affan dake fidda qamshi cikin navy blue din jeans da shirt dinsa.

Sosai maganar taja hankalin hafsat,gabanta ya fadi ta waiwaya tana kallon yaron dake da yawan fara'a,abinda ya qara masa farinjini kenan,saita dauke kanta wani abu yana tsaya mata a wuya,shi da babansa sukazo lo shi kadai?, indai kuwa shi da babansa ne lallai abun abbas qara ta'azzara yakeyi,har yazo bauchi amma bata da mutuncin da zai gaya mata yazo din?.

Bata gama wanann taraddadin ba widad ta danno kai,kamar kunna fitila cikin duhu haka ta haska gurin,da kyakkyawar shigarta me aji,dama tunda can din ita gwanar iya dressing ce,tunda quruciya ballantana yanzu data mallaki hankalin kanta,wata lafiyayyar atamfa ce a jikinta wadda tafi kama da material.

Suna hada ido gaban hafsat din yayi Wani mummunar faduwa,faduwar da sai data rufe idanunta don tanajin sautin bugun zuciyarta har kunnenta,kamar ciki fa take gani a jikin widad din,ciki fa,cikin ma tsoho?,saita miqe tana laluben hanya,wanda banda Allah ya kare tayi hanzarin dafa bango da tuni ta timu a gurin ta fadi.

Ba wanda ma ya kula da ita suna yiwa widad din maraba,kowa na qoqarin mata godiyar alkhairin da ya samu wannan karon daga wajen abbas din,wanda da yawansu sun tabbatar widad din ce sila,hakan yake kuwa,a wannan karon tayi shirin karbar soyayyarsu ne gaba daya,ribar kasuwancinta ta raba biyu,rabi ta dinga qarawa kowa akan abinda abbas ya saba bayarwar,har sai da suka qare,ita da fahad sukayi,batasan bakinsa bai iya shuru ba sai daya gaya musu,saboda shidai abun mamaki ya bashi,don koda wasa bai taba ganin hafsat din tayi musu haka ba,saidai tayi qoqarin ragewa ma.

Mayafi da takalminta ta dauka ta sulale sai gidansu,tsananin bacin rai yasa da tashin hankali yasa ta manta da batun daukansu mimi da jiran zuwan abbas tayi masa kwance kwance ya bata yaranta.

Tana shiga gidan ta dora hannu aka ta sakama maman nasu kuka,tayo wajenta hankali tashe

"Wani cikinne da ita umma na shiga uku,ta kusa haihuwa fa?"

"Ina fatan bakiyi wannan haukar a gabansu ba ko?" Ta fada cikin taraddadi,ta jinjina kai kawai don ta kasa cewa komai

"Shikenan tashi muje ciki" yunqurin miqewa tayi amma sai jini ya soma bin qafafunta,ta fidda idanu waje ta qwala qara tana fadin

"Wayyo Allah!.....cikina umma" sai kuma tayi baya luuuu ta sume umman tata ta tareta cikin tashin hankali.

Kai tsaye asibiti suka wuce da ita,bayan an basu gado anyi gwaje gwaje aka tabbatar da zubewar cikin jikinta,kamar zatayi dan qaramin hauka koma ace qaramin haukan ta dinga yi a asibitin,har sai da haushi ya kama 'yan uwanta.

Ta ciwa cikin jikinta buri sosai,tasan abbas din da matuqar son yara,ta gama tsara yadda zai zame mata makamin da zata yaqi abbas ta kuma dawo dashi tsundum cikin rayuwarta.

Ba abinda abbas din baiyi ba na hidimar asibitin,hatta da ruwan da yan dubiya zasu sha bai bari kowa ya siya masa ba,ko dama can shi din tsayayye ne,baya dorawa kowa lalurar iyalinsa.

Ranar da aka sallameta ranar suke komawa bauchi,don haka duk wani plan dinta ya gama rushewa,umman nata tace kada ta damu,ta bari ta gama jinin biqin nan,sai su shirya ma komai da kyau.


********Shirin haihuwa sosai abbas yake yiwa widad din,siyayya yakema twince din da basuzo duniya ba kamar ba gobe,abun yazo masa akan gaba,saboda wani irin budi yake samu sosai,harkokin kasuwancinsa da yake gudanarwa a gefe kamar ana musu yayyafin alkhairi,haka ta fannin aikinsa,ya tsare gaskiya da amana,hakanan koda cikin yaransa ya kamaka da laifin karbar cin hanci ko rashawa to ka kade,dukkansu sun sani kuma suna kiyayewa dokokinsa.

Already likita ya gaya mata,tana cika watanni takwas to zata iya haihuwa daga sannan,kasancewar cikin twince,kuma ba haihuwar fari bace,don haka kullum abbas din cikin shiri yake,tayita dariya saboda yadda yakeyi din,kamar lokacin za'a fara yi masa haihuwa.

Ranar da zaije bauchi weekend kamar kada ya tafi,tace sam sai yaje,watansa guda kenan baije ba saboda cunkoson aiki anan katsinan,hakadai ya tattara ya tafin ya barta da aminatu da yasa akaje aka dauko mata ita kafin ya wuce,sai da ya dawo sannan hankalinsa ya kwanta.

********Tun kafin su gama cin abincin dare bayanta da mararta ke ciwo,amma take daurewa tana cijewa,suna gama cin abincin tasa aminatu ta dauki affan suka wuce dakinsu,sai itama tace kwanciya zatayi,don bayan sun gama cin abincin fita ta kama abbas din ta gaggawa,don haka suka rufe ko ina,yana da key din kowacce qofa tasan idan ya dawo zai bude.

Tashinta uku xuwa wani irin fitsari da yake takura mata,a zuwa na hudunne ta durqushe a bakin toilet din tana riqe da mararta da bayanta saboda wani mugun murdawa da tayi

"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" ta dinga maimaitawa,sai ta koma ta zauna sosai a wajen.

Tun a can yaji jikinsa bai bashi ba,don haka ya katse meeting din,yabar mataimakinsa yace su qarasa,kome ake ciki su gaya masa.

Yana buda qofar nishinta ya fara ji,a rude ya qaraso inda take yana tambayarta,amma babu baki,sai kawai ya fara sauko da kayan haihuwar data hadasu jiya jiya ya fidda cikin mota,ya kamata ya kaita mota,ya qwanqwasa dakinsu aminatu ta bude,ya gaya mata su kulle ko ina su kwanta,ya bata dukka keys din na gidan yace zasu asibiti,hankalin aminatun a tashe tayi musu addu'a ya fice.

Kafin su isa ya kira daya daga cikin juniors dinsa,suka sameta a asibitin,bayan an dubata aka wuce labor room da ita.

Addu'ar data dinga yi ba kadan bace,a wannan karon duk yadda ta zata ba haka bane,ana kiraye kirayen sallar asuba lokacin da abbas ya wuce masallaci cikin hukuncin ubangiji ta haife kyawawan twins dinta dukka maza.

Yana kuma idar da sallar kira na shigowa wayarsa,ya daga yana sauraren bayanin da ake masa,tafiyar gaggawa ce ta taso musu shida matimakinsa da wanda abbas din ke bi,shine matsayar tattaunawarsu ta jiya,qarfe shida na safe,don dole ba yadda zaiyi haka ya amsa,don a qa'idar aikinsu ba sabawa umarni,ya baro masallacin yazo ya tarar da alkhairin da Allah ya saukar masa a wannan sassanyar asubar,baki da dukka zuciyarsa sun gaza daina furta godiya ga Allah,yaran kawai ya samu gani suma a gaggauce,haka yabar asibitin cike da kewar yaran da kuma mamarsu.

Tun a hanya ya buga waya ya gayawa dukkan wanda ya dace ace ya sani,daga danginsa zuwa nata,gab da zai shiga gida ya kashe wayar don ya samu ya shirya,bai kunna wayar ba sai da suka dauki hanya.

Yana kunnawa hafsat ya fara kira don ya fita hakkinta,ko basa tare indai zaiyi tafiya ya saba yana sanar da kowaccensu,bayan ya gama gaya mata tafiyar ya dora mata da batun haihuwar.

Uffan kasa cewa tayi,saboda wani qaton abu da ya toshe mata qofofin maganarta,twince?,to maza ko mata?,ko Mace da namiji?,kai koma meye yarinyar ta haifa itakam ta shiga uku.

Shurun da yaji yayi yawa sai ya mata sallama kawai ya katse wayar,ya amsa kiran yaaya bara'atu daya shigo masa.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 40

Jikinta yana rawa ta lalubi layin muneera don jin me widad ta haifa

"innalillahi,na shiga uku" shine abinda hafsat ta samu kanta da fada bayan muneera ta tabbatar mata twins ta haifa kuma dukka maza,ta dinga safa da marwa cikin falonta kamar wata zautacciya,kamar kuma wadda ciwon naquda ya sameta,kuka takeyi wurjanjan,tana tsinewa widad a zuciyarta,yarinyar ta gama cutarta,cuta tahar abada,ta gama da rayuwarta gaba daya,haihuwa?,haihuwa tayi?,haihuwar kuma ta yara maza ma?,sai yaushe zata iya ruguza dukkan wannan ginin da widad tayi?,yaushe haqarta zai cimma ruwa?,rayuwa na qara tafiya,tana saqa widad din tana warware mata tana dawo da komai baya,ta gaji da wannan jiran gawon shanun,sai ta kira habiba ta fashe mata da kuka me cin rai ta fara gaya mata.

Ajiyar zuciya ta sauke

"Abinda nakeso dake kiyi haquri kawai,ko kowa ya kasa yi miki komai boka bagwaare ina mai imanin zai miki komai(wa'iyazubillah),saura wata daya kacal aikinka ya kammala,wallahi kinji na rantse miki,ko hajiya dake kabari inda zata dawo duniya tace masa yayi kaza wallahi wallahi naki zai dauka,kudade kika kashe bana wasa ba kin manta?, fiye da rabin jarinki kika bayar,ta yaya zan bari asara ta hauki?" Bayanan habiba sun sanyaya mata rai qwarai sun bata kuma qwarin gwiwa

"Kedai abinda nakeso dake,kici gaba da lallabawa,ki sake ayi komai dake,yadda kome zaizo zaizo da sauqi"

"Anya zan iya kuwa habiba?, zuciyata bata da wannan qwarin gwiwar"

"Ke matsalata dake kenan, kwata kwata baki iya cinye jarabarki ba,wannan karon kuwa dole kiyi haka ko don amfanin kanki"

"Zan jarraba in sha Allah".

Wunin ranar haka ya yishi babu wata walwala ko jin dadi,ranta a mugun quntace,a zuciyarta tanata fatan taji wani mummunan abu ya samu yaran kowa ya huta,duk bayan mintuna saita tsine musu su da uwarsu,amma cikin ikon Allah lafiya sumul widad ita da jariranta.

Wannan karon ummu ce ta kashe kunya da kanta ta yiwo tattaki katsina,gidan widad din sai ya kasance kullum cikin jama'a yake abokan aikin abbas na nan katsinan,gashi kuma a gida take,garin ummanta,dangi tako ina barkowa suke barka ,haka daga kanon ma,wasu na zuwa barka,wasu kuma sai ranar suna sannan zasu iso,yara dai sunyo goshi sosai kamar affan,kowa yasan yadda twins suke da farinjini daman,widad din taga gata tako ina.

Ko yaushe suna waya da abbas din da yakejin kamar yayi tsuntsuwa ya dawo,an katse masa hanzarinsa sosai,don bai gama kallon yaransa,iya kallo guda dayan da yayi musu qaunarsu sosai yakeji cikin rayuwarsa da ruhinsa.

Komai ya sakar musu dai dai bakin samunsa,don yanzu babu abinda zaice da Allah sai godiya,hatta da hafsat da yara bai barta ba,sai daya gwangwajesu da dinkunan fitar suna na alfarma har kala uku,ta kalli kayan taja mugun tsaki ta nadesu a waje daya,wannan karon kam koda ba'a ce mata ba tabbas zataje suna,zataje kallon sunan widad na qarshe a gidan abbas din,zata je kuma ko don ta sake ganin yadda zata qara sawa bokanta ya qara tsanantawa da aikinsa.

_batasan tuni qaddara tayi mata nata tanadin ba,tanadin da tabbas da tana da masaniya a kansa......da babu abinda zai kaita garin katsina_

_hukuncin Allah,da kaf dube duben bokayen nata basu iso suka gano shi ba,hukuncin Allah TALALA mai kamar sake,lallai qaddarar kowanne nawa A RUBUCE TAKE_

Ana ya gobe suna gidan widad din ya qara cika sosai da jama'a,ba laifi gidan yana da nashi girman,don haka kowa ya samu masauki da wajen zama,duk da dakuna biyu ne,nata dana baqi wanda aminatu ke ciki don na abbas a rufe yake,sai wasu dakunan guda biyu da toilet ta baya.

A ranar widad ta gama komai,gyaran kai kawai ya rage mata,tayi wani mugun kyau na fitar hankali saboda yadda jegon ya fara karbarta tun a sannan,da safiyar ranar sukayi waya da abbas din yace ta bari sai azahar taje gyaran gashin,abun mamaki zuwa azahar din taji wayarsa,yace ta fito qofar gida ya miqata.

Na'eema da marwa ta dauka, kowacce ta dauki baby daya suka fito,tayi kyau cikin maroon din abaya, fuskarta tamkar madubi.

Tunda ta fito ya zuba mata ido yana kallonta ta madubi,ya lunshe ido sannan ya bude,yana tuna muryarta lokacin da take naquda,addu'o'i da salati kadai ke fita a bakinta cikin wani hali,ya sake gasgata lallai haihuwa ba wasa bace,duk dan a baibi uwarsa ba ba shakka ya tabe,hakanan duk namijin da bai girmama matarsa ba kodon darajar yaransu lallai ya cika abun zargi.

Buda motar tayi ta shigo,suka hada ido ta saki murmushi

"Amma fa ka shammaceni,shine baka gayamin zaka dawo yau ba?"

"Bakiji dadi ba da kika ganni kenan?" Shagwabe masa tayi

"Sosai ma uncle, Surprise fa kayimin"

"Good me jego" a ladabce ta gaidashi,sannan suka gaisa dasu marwa da suka zama 'yammata suma,ya tayar da motar yana tambayarta

"To yaya?,meye labari?, Ya akaji da jama'a yan suna?,hope komai dai lafiya ko?".

Qasa qasa suke hirarsu cike da wani irin kulawa da juna,kosu marwa dake baya basajin me suke fada kamar masu rada,abinda yayi matuqat burgesu ya kuma tafi dasu,don basu taba ganin irin wannan soyayyar tsakanin miji da mata ba,sunfi ganinta ga saurayi da budurwa,amma yau anty widad da uncle abbas din sun karya musu record.

A saloon din ya ajjiyeta sannan yace

"Zanje na karbo dinkina gaba da nan,idan na tashi dawowa sai na daukeku mu wuce"

"Tom,godiya nake sosai,Allah ya qara girma" ta fada tana dunqule hannu cikin salon jinjina da kuma rusunawa, murmushi ya balle masa,tana bala'in respect dinsa,ko meye zai hadasu bata kasa ganin wannan girman nasa.

Yana ci gaba da tuqi yana murmushi,halaye da dabi'un widad din yaketa tariyowa,tun daga aurensu kawo yau,tana da sauqin kai da dadin mu'amala over,bata da fushi ko tsaurara abu indai ba bango taje ba.

Ya isa ya samu tailor din ya masa halinsu,don a sannan yake qarashe hade dinkin,yana ganinsa ya rude

"Sir.....ayimin afuwa yallabai,tuba nake" sai ya jawo stool ya bashi

"Yanzun nan za'a kammala sir" bai zauna ba,yadai harde hannayensa a qirji yana dubansa

"Kome zakayi ka dinga qoqarin cika alqawari,shine cikar kamalar mutum,sannan sana'arka,duk yadda ka riqeta haka take zamar maka"

"In sha Allah sir" yaci gaba da qoqarin hada masa kayan

"Ka zauna mana sir" ya sake masa tayin zama

"Karka damu,qarasa aikinka" ya fada a nutse,don shi bayajin tsaiwa duba da yanayin aikinsa.

Wayarsa ce dake aljihun trouser dinsa ta dauki ruri,ya saka hannu a hankali yana qoqarin cirota,yana duba me kiran kiran ya katse,saiya fara qoqarin kira sai gashi an sake kiransa.

Hafsat ce,ya daga wayar a nutse ya kara a kunnensa

"Kana ta wajen ina?,gamu a park kazo ka daukemu" ta fadi kanta tsaye cikin son nunawa wadanda take tare dasu lallai har yanzu itace da gwamnati,fiye da rabinsu jama'ar widad ne ta fahimci haka ta yadda suketa hirarta da fadan alkhairinta tun a mota,hakan ya sake hassala zuciyarta da wani mugun bacin rai.

Cikin mamaki yace

"Me ya biyo dake titi bayan na tura kudin ticket a siya muku keda yara,yanzun haka fahad inajin yana airport yana jiran saukarkuya dauko ku" baki ta tura gaba hadi da tura dankwalinta ma,haka kawai ga mota tana gani sai ta bari ayi asarar kudin a wani siya musu ticket,kudi ba dubu biyar ba ba goma ba

"Kawai haka nafiso,na karba kudin ticket din nayi saving mayi wani abun dashi" yadda take masa magana a tsaitsaye yadan bashi mamaki,don tunda tayi kome ta danyi laushi

"Okay,to yanzu haka ina cikin wani uzuri,ki kira fahad din ki kwatanta masa inda kuke sai ya daukoku" daga haka ya datse wayarsa shima.

Sai yaushe zata bar son kudi?,yaushe zai saka doka ta daina karya masa kanta tsaye?.

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads