Header Ads
Showing 270001 words to 273000 words out of 296907 words

Chapter 91 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan,dukkaninsu zuciyoyinsu babu dadi.

Idanunsa qyar akan allon computer din sanda likita yake mata scanning,yara biyu ne gasunan kwance a mahaifarta har zuciyoyinsu sun fara bugawa.

Da sauri ta dauke kanta gefe hawaye yana sauko mata,ta yaya zata iya rainon cikin 'yan biyu?,bayan ko yaye affan batayi ba,a wannan yanayin da take ciki bata jin tana da qwarin gwiwar da zata iya rainon cikin ma gaba daya

"Satin cikin sha biyu gashinan,congratulations" Dr anwar likitan mai matuqar kirki da barkwanci ya fada.

Abbas dake jinsa kamar a duniyar mafarki ya miqa masa nasa hannun,Allah me yadda yaso a lokacin da yaso,cikin yanayin da yake na daukewar dukkan wani farinciki daga rayuwarsa sai ga hasken farinciki ya ratso daga ubangiji,ya maida dubansa ga widad hankalinsa ya tashi da ganin hawayen da take zubarwa,ya matsa saman kanta yana jera mata tambayoyin akwai abinda ke mata ciwo ne?,saita gyada kai

"Bari ina zuwa" Dr anwar ya fada yana fita a office din,hakan ya bawa abbas damar dagata,ta zauna sosai yana riqe da hannunta,saidai ya kasa zama,yana tsaye ne tsakiyar qafafunta yana kallonta

"Bani da qwarin gwiwar rainonsu da haifarsu" ta fada tana zubda sabbin qwalla,sai ya dora yatsantsa saman labbansa

"Zan baki duk wani qwarin gwiwa da kika rasa,zan baki dukan hope,zamu rainesu tare na kuma tayaki naqudarsu,don Allah ki kwantar da hankalinki na roqeki,ina da buqatarsu,burin kuma hajiya kenan kullum taga tarin jikoki daga wajenki" furta sunan hajiya da yayi ya sake sanya damuwa da karyewar zuciya a zukatansu su duka biyun,sai ya matso ya sanyata cikin qirjinsa yanason saukar mata da nutsuwa.

Tun daga wanna lokaci gaba daya ya maido hankalinsa akan widad din,ya bata dukkan lokacinsa ya rage ranakun fita aikinsa,ya hanata yin komai,komai shi yake mata,yayi nata yayi nasa yayi na affan,sai daya gama karantar komai da takeso naci sha da sauransu,wani lokacin har tausayi yake bata,duk da har yanzu ta kasa warewa yadda suke a baya,abinda yake qara masa damuwa cikin qirjinsa kenan,yake ganin kamar komai bai wuce a wajenta ba.

Tun randa yaci wannan abincin qirjinsa yake yawan riqe masa da ciwo,amma sam bai nuna mata ba,don so yake ya dawo da dukkan farinciki da walwalarta.





*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 35

Wannan shine babban damuwarsa kafin ya tunkari abinda yake gabansa.

*******Qarfe daya na tsakiyar dare ya farka da wani irin mugun gumi da yake karyo masa,saboda riqewa da qirjinsa yayi da wani irin mugun ciwo,da qyar yake iya jan numfashi,ya laluba hannunsa ya kunna fitilar gefan gado,haske ua gauraye dakin nasa,shi daya yake kwana,bai taba takurata ko sau daya akan su hada makwanci ba,hasalima ta lafiyarta yake,ya sauko daga gadon ya fita waje don ya samu ruwa mai sanyi yasha ko qirjin nasa zai sake,ya tabbatar ciwon da yaketa dannewa ne yau yaci qarfinsa.

Haki ya dinga yi sosai bayan yasha ruwan,ya samu hannun kujera ya zauna yana riqe da qirjinsa,a hankali ya fara kiran sunan Allah ganin ciwon yana neman yafi qarfinsa.

Tana yawan fama da qishirwar dare,tsakiyar baccinta ta tasheta,ta farka a hankali tana mutsitsike idanu sannan ta zauna sosai tana kallon sashen da abbas din ya zauna dazun,wayam babu shi,ya zauna ne yana karanto mata wasu laifuka cikin system dinsa da wasu suka aikata ya kamasu ya kaisu kotu da hukuncin da kotu ta yiwa kowannensu,batasan sanda bacci ma ya dauketa ba.

Ba ruwa a dakin,dole ta gyara farar hular data dora kan sassalkar sumarta ta zura bedroom slippers dinta ta fito.

Da farko tsorata tayi jin alamun mutum cikin parlor din,amma kuma sai sautin muryarsa dake tashi can qasa ta gaya mata waye,cikin tashin hankali sosai ta iso gareshi.

Gaba daya ta rude da yadda taga ya fita a hayyacinsa,tana ta son ta kira wani cikin mutanensu na nan amma ya riqe hannunta gam ya hanata motsawa,batasan sanda hawaye ya fara zaryar saman fuskarta ba,yanayin yadda yake riqe da qirjinsa ta tabbatar ulcer dinsa data jima bata tashi bace a yau ta tashi,kuma ko bai gaya mata ba ta tabbatar abincin data bashi ne yaci.

Sosai hankalinta ya tashi,gani take kamar mutuwa zaiyi a daren,kamar bazai kwana ba,indai hakan ta kasance kenan itace ajalinsa?,abinda ya sake daga mata hankali ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai.

Duk da cikin ciwo yake amma hakan bai hanashi jawota cikin jikinsa ba yana dan bubbuga bayanta

"Kayi haquri daddy,ni na jawo maka"

"Shshshsshsh" kawai yace da ita,sai tayi lamo cikin jikinsa,cikin ikon Allah zufar jikinsa ta fara raguwa,kasa sakinsa tayi,har zuwa sanda taji numfashinsa yana sauka a hankali da alama bacci ya fisgeshi.

Har zuwa lokacin bata bar share hawaye ba,ta sake qanqameshi cikin jikinta tausayinsa ya kamata a karo na farko,hajiya ce ta fado mata,tayi imani inda tana raye ko meye zai faru bazaikai tsananin wannan ba,ta tuna maganarta ta qarshe akan abbas da affan

"Allah ya baki ikon riqesu gaba daya" har maganar ta bawa widad din mamaki,ashe kusan wasiyya hajiyan ke bata.

Dukkansu kukan affan ne ya tayar dasu,da tafiyarsa daya fara koya ya qaraso wajen,sai abbas din ya miqa hannu yana daga kwancen ya daukoshi cak ya azashi saman ruwan cikinsa yana kallon yaron fuskarsa dauke da murmushi

"Am sorry son.....na hanaku bacci kai da mamanka ko?" Ya fada a karye,saita miqe ta zauna sosai tana masa sannu kafin ta kalli agogo,an riga an idar da sallar asuba,dole sai hakanan suka yita a makare.

Yau din musayar aiki akayi,ta hanashi yin komai tayi dukkan wani aiki kamar yadda ta saba a baya,yana kwance yana binta da kallo,duk inda ta gifta sai wani abu ya motsa ransa,zuciyarsa bata masa dadi da yadda ya zargeta ya dasa bacin rai a ranta,ashe yaransa har biyu suna kwance a mahaifarta.

Wuni sukayi ranar a tare,har bayan la'asar tana ta hidimar hada musu abincin dare,affan yana kwance saman cikinsa,tayi tayi ya dagashi saboda qirjinsa amma yace

"Ki qyaleshi,yayi missing dina shima" tasan akwai magana a bakinsa amma ta shareshi.

Cewa yayi tazo ta dauke affan din,tana isowa yasa hannu ya janyota jikinsa,sannan ya sauke affan a gefe,sosai ya sakata cikin jikinsa yana kallon fuskarta

"Da gaske widad....bagarar dani kiketa yi,yau kwanaki nawa da dawowarki,da gaske bakiyi missing dina ba?,hala kin daina sona?" Ya fada murya a karye,hannu tasa tana ture fuskarsa daga tata,saboda wani nauyi yake sakar mata da manyan idanun nan nasa

"Daddy bamu da lafiya dukkanmu,ka barmu mu warke cikin salaama" ido yadan lumshe sannan ya budesu ya zubesu fes kan fuskarta,saita janye idanunta tayi kamar bata ganshi ba

"Alright.....jibi nakeso na wuce bauchi" ta daga kai a hankali ta kalleshi,ranta yadan quntata kadan da zuciyarta ta tuna mata da hafsat,wajenta zaije kenan?,kamar yasan me take rayawa sai yace

"Wani aiki ne mai muhimmanci ya tasomin"

"Amma daddy,su office din basusan har yanzu baka gama warkewa ba?"

"Saun dauka na gama warkewa sumul,tunda sunsan ina da jarumar mata dake bani kulawar dake warkar da zuciya da gangar jiki,basusan wannan karon ta zama raguwa ba" kanta ta kawar kawai,tasan jan magana yakeso,ya saki boyayyen murmushi,wannan boyayyen fushin nata ya barta ne kawai,yana jiran lokaci,zai sauke mata shi tassss,a yanzun taci albarkacin abinda yake jikinta ne,amma itama ta sani,yasan lagonta fiye da yadda take tsammani,ya kauda shurun da ya wanzu a tsakaninsu

"Aikin yana da muhimmancin da bazai iya jikirtuwa ba,saidai kiyimin fatan nasara kawai" ya fada yana lumshe idanu,yana tuna wayar da sukayi dazu da umar dinsa,wadda a qalla ta kwashesu kusan awa guda.

"Allah ya bada sa'a ya kuma bada nasara"

"Ameeen ya hayyu ya qayyumu".

Bayan ya kwantar da affan sai ya bita kitchen suka kama aikin tare,ba wata doguwar hira a tsakaninsu,amma lokaci lokaci tana kamashi yana satar kallonta,kallon da batasan na meye ba,daga bisani ya gaza jurewa,ya zagayo ta bayanta ya riqe qugunta sosai ya jawota cikin jikinsa, ya dora habarsa saman kafadarta

"Wannan cikin yayi miki kyau fiye dana affan,ina fatan zaki bani baby girls masu kama dake this time around" murmushi ta saki tana jin saukar numfashinsa har cikin kunnenta,hakan kuma ya fara tayar mata da tsigar jikinta,saita zame a hankali

"Eheeennnn.....gwara ma ka fadi gaskiyar ka,koda baby girls dinne masu kama dakai kakeso,ka dauka ba'a gayamin ba,sanda na haifi affan yadda ya deboka ya dinga maka dadi har baka iya jure fada" siririyar dariya ya saki,ya koma ya jingina da kitchen cabinet yana kallon kyakkyawar fuskarta

"Bakisan kin fini kyau ba?,affan namiji ne,duk munina idan yayoni ba matsala,kinga kenan dama baby girls din ne yafi kamata su dauko ki ko?" Yadda ya kira kansa da mummuna ya sanyata dole ta daga kai tana sake dubansa da kyau,suka hada ido yayi wani kalar tausayi kamar ita zata zana masa yaran,sai dariya ta qwace mata.

A sirrance ya sauka a bauchi,ba wanda yasan ya iso bauchi sai umar,ya kuma gana da manager din hotel din a ranar bayan ya kama daki a wani hotel na daban.

Duk wani dauka na cctv camera dake hotel din saida yasa aka sauke masa,tun daga kwanan watan da kwanyarsa zata iya riqe masa na sanda suka fara zuwa weekend shi da widad,ya wuce dasu dakin hotel dinsa dasu.

Sai da ya gama komai ya nutsu sannan ya fara bibiya,komai tiryan tiryan,bayan ya bawa umar wasu yace ya tayashi,amma ya tabbatar sai yana kebantaccen waje kamar haka.

Aikin ba wani sabon aiki bane a wajensa ba,yana da kafiya da jajircewa akan aikinsa,idan yasa qahon zuqa akan abu sai ya ganoshi,saidai idan baiyi niyya bako bai sa kansa ba,wannan na daya daga cikin sirrin samun qarin girmansa akai akai,dom haka kuma zama bibiyat dukka motsin hotel din na watanni bai wani jigatashi ba,daren gaba daya ya sadaukar yayi wannan aikin,sai coffe kawai da yake makawa cikinsa.

Ya tsaya ya jajirce yayi aikinne bawai don har a sannan akwai sauran zargin widad a ransa ba,a'ah,yayi hakanne saboda ya zamana shima yana da hujja kamar yadda tsarin aikinsu yake.

Bai gama ba sai kusan azahar,zuwa sannan idanunsa sun kada saboda tsabar rashin baccin da kallon abu daya,amma duka wannan bai dameshi ba,sai wata nutsuwa data dinga saukar masa

"Subhanallahi wabi hamdih,subhanallahil azeem" ya dinga maimaitawa yana lanqwasa yatsunsa,cikin tsakiyar kansa yana sake samun kansa da tuhumar kansa da kansa,tuhumar da tunda ya dawo hayyacinsa yakewa kansa,har yau kuma ya rasa dalilin da yasa ya fita hayyacinsa a wancan lokacin da har yau iya aminta da wannan mummunan zargin wa widad,wanda baisan me zaiyi da zai wankeshi ba,amma ya dora hakan bisa mizanin qaddara da jarrabawar rayuwa da rayuwar kowanne bawa bata rabuwa da ita.

Ko kwana daya bai qara a hotel din ba ya hada kayansa gaba daya ya kira umar yace yazo ya kaishi gida,yawan baccin dake kansa bazai samu sakewa yayishi cikin dakin hotel din ba.

Yana cikin mota ya kira Ezekiel,daya daga cikin yaransa dake bauchi,ya kuma bada umarnin ya hada yara suje su kamo masa lawal duk inda yake,amma bayason sunansa ya fito a ciki gaba daya,ko don saboda yaaya sa'id(mahaifinsa),ya masa bayanin kalar tuhumar da yakeso ayi masa,ya kuma aika masa da number wayar lawal din,yace kada su karbe wayarsa,muddin ya buqaci kiran wata me suna hafsat su bashi dama ya kirata,sannan ya kashe wayar,ya maida bayansa sosai jikin makarin kujerar yana karkata akalar tunaninsa kan next target.



*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 36

Har sun dauki hanyar gida ya cewa umar ya kaishi gidan hajiya,ya sakashi ya shiga da motar ciki ya karbi key din gidan ya bude ya shiga.

Komai na gidan yana nan tsaf tamkar tana raye,ba qazanta ba komai,su umar suna kula da gidan yadda ya kamata,har ya bude parlor dinta zai shiga sai ya kasa daurewa,ya fito ya bude dakinsu umar din.

Wanka yayi ya sanya boxer da farar riga armless,ya rage hasken dake shigowa dakin ya kwanta,a maimakon bacci sai tunani suka cika kwanyarsa fal,ya dinga bitar halaye da dabi'un hafsat din,yana kuma irgen shekarun da suka dauka a haka ba tare da wani sauyi daga gareta ba,har cikin zuciyarsa yana jin ya fara qosawa,haqurinsa kuma yana dab da qarewa,abu daya yake tunawa yake kuma tausayawa,mimi nawwara da yusra,bayason su girma su kalleshi a matsayin wanda ya gaza wajen samar musu da nagartacciyar uwa.

Haka yayita saqe saqe,kansa kamar tsage saboda rashin bacci da tunani,dole ya jawo wayarsa yana dubawa,ya cika da mamaki fal na rashin ganin kiran widad ko sau daya daga jiya zuwa yau,wani abune da bai taba faruwa ba a tsakaninsu saida wannan ibtila'in ya fadowa rayuwarsu,ya gama lalubensa sai ya kirata kai tsaye.

Tana zaune riqe da wani qaramin littafin addu'o'i da anty madeena ta hadota dashi tana dubawa tare da qoqarin haddace wadanda suke na ko yaushe suke fi kuma muhimmanci,tun jiyan yana ranta,amma kuma batason bada kanta ta kirashi,tanason ta auna yadda take da matsayinta a yanzu a zuciyarsa,akwai abinda ya sauya ne ko har yanzun tana nan dai a yadda take a wajensa bata motsa ba.

Qarar wayar yaja hankalinta,koda ta duba taga sunan data saka masa akan wayar sai ajiyar zuciya ta qwace mata,ta kife littafin ta dauki wayar ta kara a kunnenta.

Sassanyar muryarta ta sauka a kunnensa, abinda ya sakashi sakin ajiyar zuciya da sautinta ya shiga kunnuwan widad

"Kina azabtar dani da yawa maman affan,na dahu haka na dahu,wallahi nayi laushi over,don Allah kiyi haquri ki sassautawa dan marayan da baida uwa baida uba......sai Allah saike......"

"Sai kuma uwar gidansa,sarautar mata" ta tari numfashinsa tana qarasa maganar da ba ita ta daukota ba.

Dif sukayi gaba dayansu shida ita,ita tana sauraren amsar da zai bata,shi kuma yana fama da wasu abubuwa data saukarwa zuciyarsa,sai yaji harshensa yayi nauyi,duk wani abu da yayi shirin fada ya kama gabansa,bashi da sauran zabi illa zame wayar daga kunnensa ya kuma kasheta gaba daya ya koma yayi rub da ciki yana sauke numfashi da qarfi.

Taji lokacin da wayar ta tsinke,don haka ta cireta daga kunnenta tana kallon wayar,tausayinsa ya darsu a ranta,amma ya zatayi,ta kasa daina jin zafin wai hafsta ce zata hadasu?,har ta isa ta zama silar girgizar yadda tsaftatacciyar qauna shaquwa da soyayyar da suka ginata ita dashi?,wata zuciyar na raya mata ta kirashi,wata tana hanata tare da gaya mata ki barshi ya sake dandanar irin abinda kika dandana,duk da ranta ba dadi hakanan ta shareshi,ta dauki littafin addu'o'inta taci gaba da dubawa.

Da qyar ya samu bacci ya daukeshi,saboda maganar data gaya masa tayi masa nauyi da yawa a qirji,ya samu baccin nasa yayi nisan zango,don har missing salloli biyu yayi,ya tashi da hanzari ya daura alwala ya bada su, kafin ya kammala wayarsa ta fara tsuwwa alamun shigowar kira.

Miscall uku ne na ezekiel,kafin ya gama dubawa tex ya shigo masa akan idan ya samu miscall dinsa ya kirashi.

Sai da ya gama 'yan addu'o'insa sannan ya zauna sosai gefan katifa ya kira Ezekiel din,bugu daya ya daga,ya gaidashi cikin girmamawa,sannan ya fara bashi feedback akan aikin da ya basu.

Tunda ezekiel ya fara bayanin idanunsa a kulle suke yana saurarensa,babu abinda zuciyarsa keyi illa bugawa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai yake maimaitawa a hankali bakinsa yana motsawa,sai da ya gama bayanin tas abbas yayi saluting nasa,ya kuma tattara komai kama daga recording na muryarsa da video ya turawa abbas din ta email dinsa sannan sukayi sallama bayan ya gaya masa kwana biyu yakeso lawan yayi a cell,zaizo da kansa ya fiddashi.

Duk da jikinsa yayita bashi hakan,duba da sanya idanun da yasa umar yayi masa kan yanayin mu'amalar dake tsakanin hafsat da lawan din,amma kuma ya girgiza matuqa,yadda har lawan ya iya aminta suka hada baki suka shiryawa widad din wannan tuggun,wanda kai tsaye zai iya cewa shi suka cutar bawai widad

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads