Showing 147001 words to 150000 words out of 296907 words
Chapter 50 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT
yarda mijina ya dinga kallon wannan surar ba wallahi tallahi....."
"Yanzu me kikeso kice?" Hafsat ta katseta daga yadda take kuranta kyan widad,saboda a yanzun a duniya babu abinda ta tsana irin taji an fada ko an yabi kyanta,ko tunawa ta fita kyau bataso tayi tsakanin ita da zuciyarta bare har a furta mata
"Yauwa,idan kana da kyau ka qara da wanka,kudi zaki saka ki shiga malamai su sake kauda idonsa da zuciyarsa daga kanta,sannan a sake kama miki ita sai abinda kika ce" shuru hafsat tayi tana nazari,nan fa daya,an kuma zo wajen,ita indai zancan ta fidda kudi ne to babu ita a wajen,sannan ma kuma me take da buqata wai,komai da anty ummee ke tsara mata yana tafiya yadda ya kamata,ko canzawar da widad din ta fara yi hakan baya rasa nasaba da raga matan da takeyi kwana biyu qila shi yasa ta fara sakewa,kuma ko yadda anty umnee ke gudanar da gidanta ya isheta ishara,babu boka ba malam,amma ko meye ta fada ya zauna,kowa juyashi take a cikin gidan ta ruwan sanyi.
"Gaskiya banajin a yanzu ina da buqatar wani malamin tsubbu hajiya,saidai ban sani ba ko nan gaba bana ma fata" jinjina kai kawai hahiya habiba tayi,tana ganin ta gaya mata iya abinda zata gaya mata,sauran dabara ta rage game shiga rijiya
"Yanzun nawa ne balance dina a hannunki?" Hafsat din ta dawo dasu kan maganar kudi,abinda tafi qauna kenan.
Gaba daya ta dinga jin sassan kamar a kanta yake,sai taji batason qara koda minti biyar a cikinsa,akwai tambayoyin da take da buqatar amsoshinsu,saboda haka sauri sauri ta gama mata duk abinda zatayin ta fito,sai mimi ta maqale zata bita,dama neman kai hafsat din take dasu tace su bita,amma sai nawwara taqi bin nata
"Sai kiyita zama ai"ta fadi tana jifan yarinyar da harara,so take tadan samu ta dafa ma abbas wani abun,kafin yazo yahau kanta da qorafi.
Ruwa me zafi ta hada tayi wanka,ta yiwa mimi ma,take walwalar yarinyar ta qaru,don har gashin kanta ta wanke mata.
Cikin abaya ta shirya kamar yadda take zabinta,zataso shiga kitchen ta dafama yarinyar wani abu,to amma a gajiye take jinta,sai ta fidda snacks din da tayi ta zubo a jaka,ta zuba mata ta hada mata da lemo,sai gashi tana ci hannu baka hannu qwarya,don yafi mata indomie din da ta zame musu 'yar kullum safe rana dare,sai randa Allah ya cishesu suka fita unguwa ko taso ta dafa wani abun.
Snacks kuwa irin haka ba samunsa sukeyi ba,muddin ba daddyn nasu bane yazo bauchin ya fita dasu wasu gureren ba.
Tana saman kujera a zaune tana sauraren hirar da mimi ke mata,gaba daya kuzarin jikinta babushi,sunayen da hajiya habiba ta kirata dasu su suketa mata yawo akai
"Kishiya/'yar aiki",so take yamma ta qarayi ta kira anty deena ko anty madeena ko hajjaa tayi musu tambaya.
Tare da sallama ya tura qofar falon nata ya shigo,ya canza shiga zuwa wasu qananun kaya da sukayi masifar karbarsa,suka kuma fidda zatinsa sosai.
Idanunsa a kanta sanda mimi ta kamo hannunsa tana cewa
"Daddy zo muci,anty ce ta bani,yayi dadi sosai daddy,kace mommy ta dinga yi mana irinsa" biyewa yarinyar yayi,yaje ya tsugunna gaban plate din ya dauka ya gutsura yana yaba dadinsa,wasa wasa sai gashi yana ta ci,ya daga kai ya kalli widad dake zaune gefe tana kallonsu
"Ya akayi?,yau babu sakalcinne?" Ya tambayeta da sigar tsokana, murmushi ya kubce mata,itadai batasan me yasa yake mata kallon quruciya sosai da sosai ba,itakam tana gani zuwa yanzun ma ai ta isa mace
"Ga wayarki da kika manta" ya.miqa mata wayar yana kallonta,hannu biyu tasa ta karba,tama manta da ita
"Adan qara mana snacks din mana baby doll" sunan da ya fara kiranta dashi kenan,tun last week da akayi wani taro na matan police,rose ta kawo me kwalliya har gida tayi mata,ya dinga tsokanarta wai ta zama kamar 'yar tsana,da wayo da wayo ma ya hanata zuwa taron,yace tayi kyau da yawa,bazai barta taje ba,data saka masa kukan shagwabarta sai yace
"Wa yace kiyi kyau haka?,bazan iya barinki ba kije,but i promised you zan fita dake anjima kiga gari" da wannan ya fanshi kansa.
Koda ta zuba musu snack din ta dawo zama tayi shuru,baice mata komai ba amma yaci gaba da karantar ta cikin qwarewa ta gefan idanu,ya fahimci kamar damuwa ce da ita,sannan tana yawan taba yatsarta
"Me ya samu hannun?" Ya tambayeta a tausashe bayan ya miqe yana kallonta,kai ta girgiza da sauri
"Ba komai" ta amsa masa tana dunqule hannun nata,baice komai,ya taka a hankali ya isa gabanta,ya kama yatsan yana dubawa,yanka ne,ga wajen yayi ja abinka da farar fata,sai ya daga kai ya kalleta
"A ina kikaji wannan?" Shuru ta danyi sannan a hankali tace
"Kitchen"
"Me ya kaiki kitchen daga dawowarki?" Rasa amsar da zata bashi tayi,saita zabi tayi shuru
"But na shigo sau biyu ban sameki ba kina wajen maman mimi"
"Eh na dan shiga ne" shuru yayi yana tattara maganganunta guri guda,ya fahimci tana yawan zama a wajen hafsat din,to amma a idanunsa na zahiri baiga wani hali ko wani abu da take mata da zai sanya ya hana ko ya tuhumi zuwanta ba,sannan yafi ta'allaqa zuwan nata can akan su mimi,yasan halinta sarai nason yara,saidai sauyawar yanayin nata a yau yasa yaji bai gamsu da yadda ya ganta ba
"Zanje na dawo indai da qarfe kika yanke sai an miki anti tetanus" narai narai tayi da.idanunta jin batun allura,yayi murmushin gefan baki,idan ya biyewa wannan sakalcin nata tabbas yasan ba za'a yi ba.
Har yakai qofa ya waiwayo yana kallonta,idanunsa qasa qasa,kasa jurewa kallonsa tayi tadan kauda kallonta gefe
"Ko zaki rakani,gidan suraj zanje na dubashi" kai.ta girgiza alamun a'ah,yau din tana jin gajiya sosai a jikinta,bugu da qari ma kuma tana son yin waya.
Kai ya mirgina hagu da dama sannan yace
"Alright,take care" yayi maganar yana aza mata nauyin kallon nan nasa,saita jinjina masa kai,ya juya ya fita.
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 75
Kamar yadda ya saba ko yaushe bayan sallar asuba yana shigowa ya tabbatar da lafiyarta yauma haka
"Gidan hajiya nakeso naje yau" ta fadi masa bayan sun gama gaisawa
"Ba damuwa,jiya ban samu zuwa ba,ki shirya na fita dake idan zan fita anjima kadan" saita gyada kai,tana maida idanuwanta ta lumshesu,kwata kwata daga jiya zuwa yau batason zaman gidan.
Karfe goma na safe ta gama komai a bangarenta,ta gyarashi ta hada breakfast dan dai dai cikinta,ta kuma shirya cikin atamfa dinkin doguwar riga,tana zaune a falonta tana buga game a wayarta tana jiran fitowar abbas,hatta mayafinta yana gefe.
A nutse ya tura qofar falon,yana sanye da shadda butter color da aka tsarama wani lafiyayyen dinki me aji,a kanta idanunsa suka fara sauka,sai yayi tsaye riqe da handle din qofar yana kallonta idanuwansa suna lumshewa,tayi masa kyau har baisan iya yadda zai musalta ba,atamfar ta karbeta ainun,har ya gaza gane doguwar riga da kuma atamfa wanne ne yafi mata kyau,ya dan rufe idonsa yana shafar qirjinsa da hannunsa,yana jin tana sake saka kai sosai cikin zuciyarsa tana samun kyakkyawan mazauni,illa take masa a kowacce rana,kullum yaqi yake da zuciyarsa,yana ganin kamar ya fiya zaqewa da yawa,yanason canzata,yana son sake kawo kusancin da yafi wannan a tsakaninsu,baisan ta yadda komai zai zo ya kuma kasance ba.
Batasan da tsaiwarsa ba,saboda hankalinta yayi gaba a game din da takeyi,sai da qamshinsa ya fara kawowa hancinta ziyara,ta daga manyan idanuwanta a hankali,idanuwansu suka sarqe waje guda,siririn murmushi ya subuce mata,ta shagwabe fuska
"Ka tsoratani uncle" ta fada tana tura baki gaba,yabi dan qaramin bakinta da kallo,wanda yau yasha jambaki pink,hakan ya qarawa lips dinta color akan ainihin color dinsa.
Hannu ya saka ya yafitota yana jin jikinsa na mutuwa,ta miqe a hankali tana dubansa tare da takowa inda yake
"Uncleee.......na gama fa na dauko.mayafina?" Kasa amsa mata yayi har ta iso gabansa,yasa hannu a tausashe ya kamo qugunta janyota gabansa,suka zama very close sosai a tsakaninsu.
A tare suka lumshe idanu sannan suka bude,suka zubawa juna idanu kamar shiri,kowa da abinda jiki da zuciyarsa ke gaya masa,ya motsa labbansa da salon miskilancin nan nasa
"Kinyi kyau baby doll" murmushi ya kubce mata tana kallon manyan idanunsa da suka qara masa kyau a idanunta,kafin tace komai sautin muryar hafsat ta tunkarosu,da alama sassan take nufowa,tana ta hayagaga da mimi da nawwara,sai ka dauka wasu manyan 'yammata ne.
Hannunta ta sanya da sauri ta zare hannayensa daga qugunta taja da baya,idamunsa a lumshe yana jinta,sai data matsa ta tsaya daga can baya sannan ya bude idon nasa fes a kanta yana kallonta
"Meye hakan?"
"Mommy" ta fada a tana yin narai narai da ido, kafin ya bata amsa hafsat din ta iso cikin saurinta kamar me shirin tashi sama,amma ganinsa a tsaye daga bakin qofa goye da hannayensa yana kallon ciki ya sauke mata duk wani fada da cin mutunci da tazo yiwa widad din nayin rana batazo tayi shara ba balle wanke wanke.
Ta gefansa ta raba ta shiga ciki,da widad din ta fara cin karo,wanda ke tsaye rataye da qaramar jaka a kafadarta tana qoqarin yane kanta da kyakkyawan mayafin daya dace da kayan jikinta.
Zuciyarta ce ta tsinke da irin kyan da yarinyar tayi,zuciyartata ta fara rawa,ta kuma fara ayyana mata tsaiwar da yayi widad din yake kallo,saita tsaya cak,ta fara raba kallonta tsakanin fuskokinsu su biyun,gabanta yana luguden faduwa.
Fes yake kallon widad din kansa tsaye ba tare daya nuna kara ko alkunyar wanzuwarta a wajen ba,abinda ya sake dimautata kenan,bakinta har rawa yakeyi sanda jefa musu tambaya kamar wasu 'ya'yan cikinta
"Ina kuma zaku da safen nan.....naga har kun shirya" maganar ta ta tuna masa inda zasu,ya sauke hannayensa dake goye a qirjinsa yana daukar mimi da tafi kusa dashi ya juya zuwa waje yana cewa
"Ki sameni a mota,rana tana yi" da kallo hafsat din ta bishi har ya fice,saita dawo da dubanta ga widad,kamae zatayi kuka saboda wani malolon kishi daya riqe mata wuya
"Izinin wa kika nema da zaki shirya fita unguwa?kin fara rainani fa widad,ki shiga hankalinki" karon farko da taji maganar banbarakwai,tunda dai ita ce mata akayi ta tambayi abbas ne a duk sanda zata fita bawai hafsat ba,to amma tana jin shakkarta ba zata iya tsaiwa mata bayani ba,don batason fada ita sam a rayuwarta.
Hon din motarsa ya hana kowa a cikinsu magana,da wannan yake maka sign idan yana jiranka,duk da haka sai hafsat din ta kalli widad a gaggauce
"Ina zakuje?"
"Gidan hajiya"
"Shine kika saka wadan nan kayan?,bana gaya miki ki dinga killace kanki ba karki bari ya dinga ganin tsiraicinki?" Ta fafa gajiya da soki burutsun hafsat,ita kawai so take taga ta fita a gidan
"Aiba haram bane,tunda miji da mata ne ni dashi" ta amsa mata ba tare da kawo komai a zuciyarta ba,tunda dai tasan da wannan salon anty madeena tayi mata bayani.
Mummunar faduwar gaba ta saukar mata,yaushe yarinyar ta fara fahimtar kalmar MIJI da MATA?,lallai akwai qura,liqi yana shirin balle mata kenan,kasa ce mata komai tayi,saita juya kawai ya fita,widad din ta bita da kallo,akwai abubuwa da yawa.na mommy hafsat din dake bata mamaki,takowa tayi ta kulle sassan nata ta wuce zuwa motar tasa.
Ranar wuni tayi ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga qarshe ta dauka waya ta kira anty ummee don ta labarta mata,kiran duniya wayar taqi tafiya,sai taji tana ds buqatar fita taje gidanta zaifi mata sauqi,wannan ya sanya ta yita kiran abbas ta gaya masa zata fita amma bai dauka ba,ashe yabar wayar cikin mota.
Ta kuwa cika tayi fam,zuciya ta dinga raya mata suna can suna holewarsa da yarinyar,lallai biri yayi kama da mutum,ba banza ba yarinyar ke iya kallon qwayar idanuwanta ba ta maida mata magana haka gatsal.
Ji tayi kamar ta rataya mayafi ta fice abinta,to amma tana shakkarsa,tasan ko zai dauki komai banda wannan,bazai lamunta ba,haka tana ji tana gani ta haqura da fitar,taci gaba da kiransa amma saita daina shiga ma daga qarshe.
Basu dawo ba sai dare,suna isowa kuma fa shige sassanta ta kulle abinta,abbas din ya bita da kallo, quruciya har yanzu taba dawainiya da ita ba ruwanta da zancan yau kwananta nw,baya mantawa akwai ranar da a gaban hafsat din ya zolayeta akan a sassansa zata kwana,kamar zata hadiyi zuciya haka hafsat taji amma ta dake tana tuna wasu daga cikin karatuttukan anty ummee,ta dake tana tayashi tsokanartata akan anan zata kwana, qarshe sulalewa tayi ya gudu abinta.
°°°°°°°Tun daga wannan ranar ya zamana fiye da rabin weekend dinta agidan hajiya takeyi,wani lokacin tun a hanya taje cewa ya wuce da ita,sai ya wuce gida bayan ya ajjiyeta,baya musu, saboda hakan shi kansa yana faranta masa rai,saboda yadda take nunawa hajiyan qauna da kulawa,ita kanta hajiyan hakan yana mata dadi,don duk sanda widad din tazo saita gaji da kala kalar girki,saiya zamana shi kansa zaiyiwu wuya baka sameshi a gidan ba,a nan zaici abincin rana har na dare,kai wani binma da safe yake fitowa da jallabiya yazo yaci breakfast ya koma hafsat din na bacci,idan taga bai nema abinci ba saita share taci gaba da sabgarta tana ganin sauqi ta samu.
Abu daya ke qonawa hafsan rai,yadda widad din ke guduwa tana barinta da tulin ayyukanta,tuni ungulu ta koma gidanta na gargajiya,qazanta sai wadda ta qaru,saboda gyaran weekend din data qwallafa rai akansa yanzu ba samuwa yake ba,idan widad ta shigo gidan sai daren da ana ya gobe zasu koma kaduna.
*_MAFARI RAYUWA DA SOYAYYA_*
Tun daga daren jiya daya daukota daga katsina gidan mahaifiyarta,har kawo yanzun da yake shigowa gidan jikinsa gaba daya baya jin dadinsa.
Ya jima a parking space bayan dawowarsa daga aiki,yana zaune cikin mota,shi bai shiga ba shi bai fita a motar ba,daga nan inda yake yana iya jiyo daddadan qamshin turaren wutarta daya zama tambarinta,qamshin da duk sanda zasu bar kaduna zuwa bauchi yake kewarsa,haqurinsa ya fara gazawa,yana dab da hanata weekend gidan hajiyan,tunda ko ba komai idan tana gida,iya qamshinta kawai na saukar masa da nutsuwa.
Cikin tattara qwarin gwiwar sa ya buda murfin motar ya fito,dai dai sanda ake qwala kiran sallar magariba a garin kadunan,sanye yake da uniform dinsa masu matuqar daraja da kuma qara masa kwarjini,yana iya hangen mai gadin gidan amma ya ratse yayi kaman bai ganshi ba,saboda yana jin kamae qafafuwansa ba zasu daukeshi ba.
Da sallam ya shiga parlor din,dai dai sanda take fitowa daga kitchen dauke da wani tray data jera lemon zobo da abarba data koya ta gwada,ya kuma bata ma'ana sosai har fiye da yadda ta zata.
Murmushi ne shimfide saman fuskartata,batasan dalilin da ya sanya kwata kwata batajin dadin gidan ba har sai sanda ya dawo,yayin da abbas din ya zube mata.manyan idanunsa yana kallonta,qafafunsa.na sakeyin laushi kamar bazasu iya daukarsa ba.
Sanye take da wata baqa wul din gown wadda kwata kwata tsahonta iyakarsa qasan gwiwarta,hannunta gajere ne don kana iya hangen hammatarta da kuma tundun qirjinta da cikar da suka fara yasa suke bayyana kansu.
Kanta babu komai sai lallausar sumarta baqa sidik mai laushi data yiwa kalba guda daya tak a kan nata,jelar ta sauka gadon bayanta taba reto,zata tsammaci relaxer ta sakawa kan nata.
Tray din ta ajjiye,saita fara takowa gabansa tana juyawa gaba da baya
"Uncle kalla ka gani,nayi kyau?,don Allah kwalliyata ba tayi kyau ba?" Ta fada bilhaqqi har cikin ranta tanason yace tayi kyau din,saboda ire iren kaya ne da mamarta mahaifiya ta hada mata su masu yawa da kyan gaske bayan ziyartarta da tayi,tsaraba tayi mata mara iyaka,don bata samu halartar bikinta ba,hasalima sai ana gobe daurin auren widad din ta sani,wannan yasa tayi fushi kwata kwata ta koma gefe,saidai zuwantan yasa tayi mata kyakkyawar tarba,ta kuma hada mata nau'in dukka wani kaya da tasan uwa zata yiwa diyarta,ta hada da nasiha mai kama da hannunka mai sanda
"Kar na sake jin sirrinku ya fito keda mijinki,idan ba haka ba zamu bata dake,kome ya umarceki kiyi kiyishi indai kinaso muci gaba da shiri" a duniya idan akwai abinda ta tsana wani yace sun b'ata,waninma mahaifiyarta da take mata wata irin qauna take jinta har ranta.
Bai ankara ba har ta iso gabansa,juyi daya tak tayi ta fada jikinsa,sai ta riqeshi tana dariya dariya
"Uncle.....ba kace wannan rigar ba zata yimin kyau ba?,shi yasa itama na gwada maka ka gani.....bakace komai ba" ta furta tana tsareshi da ido.
Tuni maqoshinsa ya bushe,ya tattaro yawu ya hadiye yana dan ja da baya
"You look so good baby doll" dan tsalle ta saki a jikinsa tana cewa
"Thank you uncle"