Header Ads
Showing 252001 words to 255000 words out of 296907 words

Chapter 85 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

aiki yayi,tun abun yana mata wani iri har ya koma bata mamaki,tako ina ya koma wani irin tsauri da yake mata kama da ZARGI don yafi gaban kishi,amma tayi qoqarin dannewa,tare da bashi uzuri.

Tafiya ta kamashi katsina ta kwana biyu,har sunyi sallama dashi kan aminatu zata dawo gidan ta zauna har sai ya dawo,amma bayan awa uku sai gashi da fahad,dan yayansa ne shima

"Zai tayaki zama har na dawo" da to kawai ta amsa masa,don abubuwan nasa sun fada daure mata kai.

A tafiyarsa ta kwanaki biyu ya dage da addu'ar Allah ya sassauta komai,ya kawo qarshensa,cikin sa'a daya dawo din sai taga abun ya ragu,satinsa daya da dawowar suka shirya zuwa weekend yadda suka saba,daga nan zasu maida fahad gida.

*R U B U T A C C I Y A R K' A D D A R A II*


Shigar yammaci suka yiwa bauchin,sanda motarsu take shiga gidan duka yaran suna farfajiyar gidan suna wasa saman kekuna,hafsat na tsaye da wata baquwa da alama sallama takeyi tayo mata rakiya ne.

Dukka yaran suka kwaso a guje sukayo kansu suna murna tare da kiran sunan affan,harda yusra dake rarrafe,duka tyai budu budu da jikinta da qurar dake farfajiyar gidan,widad bata barta ta qaraso ba ta isa gaban yarinyar ta dagata tana mata waqa

"Allah rayan.....rayan 'yar nan" sai kuwa ta bangale mata baki tana dariya,ta sanya yarinyar cikin jikinta itama tana dariya,duk da ajiqe jikinta yake,fitsari ne ko ruwa itama bata sani ba,yarinyar akwai fara'a sosai,shi yasa take sonta.

Ga mamakin widad da hafsat ta dawo daga raka baquwar sai tayo wajensu

"Sannu da zuwa daddy" ya daga kai da murmushi yana kallonta

"Yauwa sannu da gida maman yara" ta saki murmushin jin dadi kadan,sai widad ta taka kadan ta gaidata.

Ba yabo ba fallasa ta amsa mata sannan ta maida kanta ga mijinta suka fara hirarrakinsu,har widad taji tadan qosa da tsaiwar ta dauki qaramae jakarta ta cewa fahad

"Shigomin da sauran kayan don Allah" sai tayi gaba ta barsu a wajen.

Sai bayan kusan awa guda aka shigo mata da affan,a lokacin har tayi nisa wajen gyaran sashenta,ta karbeshi tana tambayar fahad ina duka yaran

"Mamansu ta tafi dasu bagaren abbansu" saita gyada kai kawai tana cirema affan pampers dinsa,don ba kasafai take barinsa dashi ba don ba mai yawan fitsari bane.

Ta kama kanta sosai game da lamarin hafsat dama tun ba yau ba,don sai ta gama zamanta a bauchi su koma bata bari hanya ta hadasu ba,to wannan zuwa hutun ma haka ya kasance,hatta dasu mimi ta janyesu,wannan bai damu widad ba,tunda koba komai itama Allah ya bata nata,affan ya isheta suyi sabgarsu a sassansu,ga kasuwancinta dake dauke mata hankali,wani lokacin saita share awanni tana lissafin kaya dana kudade.

Uwa uba wannan zuwan ma da sukayi sai takejin jikinta duka babu dadi,yawan bacci da kasala gaba daya,ranar da ta karba girki washegari abbas din yana saman dining tana shirya masa breakfast yana riqe da affan yana masa wasa,ta kammala taja kujerar ta zauna ta fara saving dinsa,idanunshi a kanta harta gama ta daga kai suka hada ido

"Lafiya yallabai?" Sai ya dage mata girarsa dukka biyun

"Sonki nakeyi" maganar ta bata dariya har sai data murmusa

"So na nawa kuma ranka ya dade?"

"Na babu adadi,malala gashin tunkiya,ina sonki sosai,ina kuma kishinki widad,da ina da hali ko quda bazan bari ya sauka a kanki ba" ajiyar Zuciya ta sauke mai nauyi tadanyi rolling idanunta tana kallonsa,ta yarda kai idanma akwai abinda yafi yarda ta yishi akan irin soyyyar da abbas keyi mata

"Amma jiya kinsan kinci bashi na,kikayi baccinki kina barni da kewa" murmushi ta sakeyi tana dan rufe bakinta

"Amma yallabai,ina jinka fa ka rage zafi sosai fa" fuska yadan bata

"Hakan bai gamsar dani ba madam.....bana wani ganewa rage zafi,na ji na kasance tare dake kawai shine magana,kwanan nan kin koyi lalaci da dogon barci,ko so kike na qara aure oho" ya fada yana dan shan mur kamar da gaske.

Idanu ta fiddo,saita fara bubbuga masa qafa cike da shagwabar nan tata tana masa kukan qarya

"Haka kace uncle?,haka kace?" Dariya ya saki

"Wasa naki miki wuddu na" ya dora affan saman dining din yana cewa

"Idan na biyewa mamarka bazan fita ba,ina da aiki masu yawa,gobe ma kuma sokoto zan tafi daurin aure,zai yiwu ma mu kwana can sai jibi"

"Allah ya nuna mana"ta amsa tana qarasa tura masa sauran breakfast din.

*W A S H E G A R I*


Tunda wuri ta gama masa komai na tafiyan yana kwance yana bacci,hatta da breakfast da ruwan wanka,sai data kammala ta shiga dakin,suna cikin duvet shi da affan suna baccinsu hankali kwance,ta saki murmushi har qasan ranta tana jin dadi idan ta kallesu,su din sanyin idaniyarta ne,kamarsu kullum qara fitowa takeyi da juna,kana ganinsa basai ka tambaya ba kasan mahaifinsa ne,tadan dora hannunta saman pillow din da yake kai ta soma bubbugawa a tausashe,ya motsa kadan saiya dora hannuwansa saman kunnensa ya rufe.

Murmushi ta saki,ta gane ya farka tashi ne bashi da niyyar yi,saita gyara zama ta zame duvet din gaba daya daga fuskarsa,ta kamoshi ya maida fuskarsa,ta sake zamewa,sai kawai ya cakumota gaba daga ya mirginata ya danneta da dukka qarfinsa,sannan ya kama fuskarta ya riqe a tafin hannunsa saitin tasa,ya fara bude manyan idanunsa da suka qara girma kadan saboda barci cikin nata qwayar idanun,suka kuma dan canza launi kadan.

"Na meye zaki dameni da tashin sassafe,bayan ke kika gajiyar dani jiya?" Ya fada da muryar bacci wadda tayi mata dadi qwarai cikin kunnuwanta,saita saki murmushi tana girgiza kai

"Banda sharri uncle,ka fadi gaskiya" girarsa ya daga mata

"Wacce gaskiya ce da tafi wannan,ni wani irin zaqi naji kina......."

"Wayyo uncle,don Allah kada ka fada" ba shiri murmushi mai kama da dariya ya qwace masa,sai ya hade goshinsu waje daya

"Don Allah ki barni na fadi irin abinda naji,da gaske nake widad,kullum sake dad......" Bata da zabi illa hade bakinsu da tayi waje guda,shi kuma hakan ya zamana kamar ta sake bashi dama ne,sai kuwa ya manne mata da kyau.

Da qyar ta qwaci kwanta tana sakin numfashi,ta nuna masa agogo da yatsantsa

"Lokaci yana tafiya, everything is ready" tayi tsalle ta fice daga bedroom din don kada ha biyota.

Binta yayi da kallo yana murmushi,sai ya waiwaua gefan inda affan yake,sun tula masa pillows basu sani ba,ya gyara masa kwanciya sosai sannan ya fada toilet.

Komai ita ta taimaka masa ya gama shi,yayi kyau cikin Wani lallausan yadi ruwan zama,wanda ya sake fitar da haibarsa da kwarjininsa.

Widad dake tsaye tana qare ma kwalliyar tasa kallo,tana sake jinsa har cikin jininta tayi.magana qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta bayan ya ajjiye tissue din da ya gama goge sauran maiqon abincin da yaci,saiya zube hannayensa a aljihun wandonsa ya fara takowa inda take idanunsa akan fuskarta

"Me kika ce?" Dariya take qoqarin dannewa

"Bance komai bafa" da wani irin zafin nama ya kamota ya sakata sosai cikin jikinsa yana sansanarta

"Kayi kyau da kwarjini,idan ka fita kamar ba kai ba,kamar ba kaine ka gama danne 'yar mutane dazu dazu ba,ko ba haka kikace ba?" saita zaro ido sosai,batayi tsammanin yaji abinda ta fada ba,girgiza kai ta fara yi

"Don't say no.....na riga naji" juyo da ita gabansa yayi

"I love you,ina kishinki sosai" ido ta lumshe tana mamakin yadda yake jaddada maganar kishin nan koda yaushe

"I love you too" ta amsa masa a sanyaye.

Har gaban mota ya rakoshi,tana tsaye suka fice daga gidan bayan ya leqa ya yiwa hafsat sallama,ita din dama can batasan rakoshi ba,saidai idan wani abun zata amsa tayi mantuwa ta biyoshi,ko kuma abinda zata karba din yana cikin motar tasa.

*B A Y A N A W A H U D U*


Misalin qarfe hudu na yammaci,tana kwancw a falo tana chart,affan yana kwance saman cikinta yayi bacci kira ga shigo wayarta,data duba da kyau sai taga abubakar ne,dan uwa ga mahaifiyarta wanda yake kamar mazaunin uba a wajenta,yana da matuqar kirki,ya kuma dauketa kamar diyar cikinsa.

Kwantar da affan tayi,ta zauna sosai tana amsa wayar,suka gaida dashi sannan yace

"Muna garinku,amma bamusan inda zamu iso gidanki ba,don wannan shine shigowarmu ta farko bauchi" sosai dadi ya kamata,iya zuwan da takeyi wajen mummynta kawai ta fahimci yadda sukeson mommyn nata,bama ita kadai ba,har su da suka fito daga cikinta

"Ta wanne guri kuke?"

"FAAZ hotels"

"Bansan gurin ba kawu,amma zan tambaya saina taho daku" ta fada cikin murna,karon farko wasu daga dangin mahaifiyarta zasu kawo mata ziyara gidanta.

Suna gama wayar ta kira abbas din don ta gaya masa zata taho dasu,saidai cikin rashin sa'a dukka layukansa is switched off,ta kira rose tace ta yiwa samuel magana ko tare suke ya cewa ogansa ya kirata,to amma shima ba tare dashi sukayi tafiyar ba,ta kusa minti talatin tana kira bata sameshi ba,sai ta miqe ta gyara yafen mayafinta ta fito farfajiyar gidan.
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 26


Hafsat da lawal ta hango tsaye jikin motar hafsat din suna magana,da alama fita zasuyi ko kuma sun dawo,ba kasafai takeson shiga sabgarsu ba,amma yanzun dole tayi tambaya taji ta inane wurin yake tunda ba garinta bane,saita sauya akalar tafiyarta zuwa wajensu.

Dif sukayi sanda suka ganta a wajen,hafsat ta dauke kai kamar bata ganta ba

"Don Allah lawal ta ina faaz hotels yake?" Tambayar data fusgi hankalin hafsat,saita waiwayo ta zubawa widad din ido

"Faaz hotel kuma?"

"Eh nayi baqi ne zan taho dasu"

"Okay" ya fada sannan ya fara mata kwantance inda yake ya qarashe da cewa

"Kibi ta nan ahmadu bello way"

"Aah,ta sa'adu zungur road kaman yafi" hafsat ta tsoma bakinta,bata kawo komai a ranta ba,cikin tsarkakakkiyar zuciya tace

"Yauwa na gode" kamar tace lawal din ya kaita ganin suna rufe motar sun gama uzurinsu da ita amma saita fasa,ta shige part dinta da sauri ga sauya kayanta zuwa abaya wadatacciya tayi rolling,saita saba affan a kafadarta ta dauki key dinta da kudin napep da zai kaita ta fita,tasan ba zata jima ba,duka duka da zuwa da dawowar ba lallai ta wuce awa daya tunda basu da wani nisa sosai.

Wani irin duumm yaji kansa yayi,ya sake daukan wayar jikinsa yana rawa ya kuma buda hotunan,itace dai..... widad dinsa ce dai babu canji, itace dauke da affan dinsa,yaron dake tsananin kama dashi

"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" ya fada wannan karon har bakinsa yana rawa,kansa ya sara masa yasa hannu bibbiyu ya dafe,wani sashen na zuciyarsa yanata qoqarin kawo uzuri da kariya a gareta,amma wani sashen kuma yana qaryata haka hadi da sukan duk wani hanzari da zuciyarsa ke badawa,sashe mafi qarfi kuma mafi rinjaye kenan.

A hankali sai zuciya ta fara ayyano masa irin abubuwan da suka faru a jiyan,ita tafara tashinsa a bacci,ta kuma shirya masa komai na tafiyar tun lokacin tafiyar baiyi ba,ta dameshi kuma ya tashi ya shirya kada yayi latti,hakan yana nufin dama akwai abinda ta shirya zatayi a ranar shiyasa take Allah Allah ya tafi?.

Bayan nan yayi kiranta da yammar kusan miscal uku,bata biyoshi kiran ba,har sai cikin dare bayan bacci ya daukeshi,sai da safe yaga miscal,bata kuma sake nemansa ba,me hakan yake nufi,duka wadan nan abubuwan da ido yake gani ya zama gaskiya kenan?, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya sake fada kansa yana qara sara masa sosai yayi qas da kansa yana jin yadda zuciyarsa ke masa wani masifaffen zafi.

Yafi awa uku cikin matsanancin halin da baisan dame zai kwatantashi ba,kafin daga bisani wata qaqqarfar zuciya ta yunquro masa,ya miqe ya fara hada kayansa,abinda sam baiyi shirinsa a sannan ba har sai zuwa gobe da safe.

Bashi da kuzari ko qarfin halin da zai iya tuqi daga sokoto zuwa bauchi,dole ya nemi daya daga cikin yaransa da sukayi tafiyar tare ya bashi driving din.

Tunda suka dauki hanya bai iya katabus din komai ba,sunci rabin tafiyar saiga kiran widad din ya shigo,ya kalli wayar sosai kamar widad dince a gabansa,zuciyarsa na wani irin bugawa,wani sashe na zuciyarsa na bashi izinin dagawa,wani sashen kuma yana hanashi tare da tuna masa girman laifinta a gareshi,daga qarshe daya sashen yayi rinjaye,sai yayi rejecting kiran,yama kashe wayar gaba daya,ya maida kansa jikin kujera ya kwantar yana lumshe idanunsa,kanshi yana ci gaba da sara masa

"Widad fa,widad" abinda zuciyarsa keta maimaitawa kenan cike da wani irin zulumi tashin hankali tsoro da kuma fargaba.

Cikin mamaki ta sauke wayar tana kallon fuskar wayar sosai,zuciyarta na gaya mata rejecting kiran nata yayi amma ta kasa gasgatawa,saita katse shakka da mamakinta ta sake yunqurin kiransa a karo na biyu,saidai computer ta gaya mata wayar tasa a kashe take.

Jim ta danyi,to kodai wayar tasa babu charge ne,ya qare sanda take kiran nasa?,bata sani ba,amma daga qarshe saita barwa kanta cewa hakanne,don baka ta miqe ta soma aikace aikacenta lokaci lokaci tana gwada sake kiransa,saidai babu wani abu daya canza,a kashe din dai take.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 27


Yamma lis suka sauka a bauchi saboda gudun da yaron nasa ya tsula bisa umarnin ogan nasa

"FAAZ hotels zaka kaini" ya fada a wani galabaice,kamar yau ya fara doguwar tafiya a mota

"Yes sir" ya fada yana karya kan motar tasu ya dauki titin da zai sadasu da hotel din.

Karon farko gabansa yayi mummunar faduwa sanda suka isa gaban hotel din,abind aya jima baiji ba kenan,duk irin hatsarin aikin da zai shiga kuwa,zuciyarsa ta dinga masa saqe saqen munana abubuwa,tana ayyana masa adadin xuwan widad wajen,kamar wanda allurarsa ta motsa ya zunkuda cikin zafin nama ya buda murfin motar ya fice,bayan ya yiwa yaron umarnin ya zauna cikin motar ya jirashi,yanzu zai dawo su wuce gida.

Cikin rashin nutsuwa yake takawa zuwa makekiyar qofar hotel din,hannunsa cikin aljihun wandonsa yana qarewa qofar kallo,duk da irin qwarewarsa a wajen aiki,duk da qwarewarsa wajen iya bincike amma a yau kamar an bude kwanyarsa an kwashe dukka wannan qwarewar,komai ya kwance masa,a haka ya isa ga security din dake zaune daga bakin qofar.

Sallama yayi masa ya bashi hannu suka gaisa,ya gabatar masa da kansa gami da nuna masa ID card dinsa,ya jinjina kai

"To na shiga ciki ne na sanar da manager zuwanka?" Kai ya girgiza da sauri ransa yana masa suya,yau wai shine zai gwada aikinsa akan widad?,yau shine yazo bincike hotel akan widad?,halittar da duk duniya babu ta biyunta a wajensa?.

"Ba buqatar haka,personal investigation ne,tambaya daya ce kawai zan maka,idan akwai buqatar shiga cikin sai na sanar maka"

"To officer ba damuwa" .

Wayarsa ya ciro daga aljihunsa yana rawa,ya buda hoton widad sannan ya miqa masa yana hadiye wani abu mai tauri a wuyansa,zuciyarsa kamar zata fashe

"Zaka iya shaida wannan fuskar?,ina nufin ka taba ganinta a nan wajen naku?" Cira kai yayi daga kallon fuskar,ya shaidata sosai,matar da yayita jiya mamaki da yaji tana hausa,don bai zaci ta iya hausa ba

"Tabbas jiya ma na ganta"

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ya furta yana saurin dafe qarfen qofar sanadiyyar jiri da yaji yana niyyar kayar da shi, idanunsa suka rufe na wucin gadi,da qyar ya samu ya daidaita kansa jin security din yana tambayarsa lafiyarsa lau?.

"Na gode" ya fada yana karbar wayar daga hannunsa,sannan ya juya da wata irin tafiya yana nufar motar.

Koda ya shiga sai ya saka kansa tsakiyar hannayensa yana jin kamar ana masa laguden tashin hankali,wani saqo can qasan zuciyarsa na gaya masa qarya ne,amma wani abu mai qarfi yana taso masa daga wani guri da baisan ina bane,yana gasgata masa abinda yake son ha zarga din

"Idan hafsat kishiyace,bata qaunar ta,zata iya mata sharri,shi kuma wannan security din fa?,meye hadinsa da ita da zai mata sharri?,ga shaidu da suka tabbatar kuma da haka?"

"Sir.......sai ina?" Muryar yaron ta kutsa tunaninsa

"Kaini gida"ya furta ba tare da ya iya daga kai ya kalleshi ba.

Farfajiyar gidan babu kowa,sai lawal dake zaune daga bakin gate yana yiwa hafsat CID din shigowar abbas din,ko karbar key din motar bai iya tsaiwa yayi ba ya wuce sashensa,yace lawal ya sallami

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads