Header Ads
Showing 258001 words to 261000 words out of 296907 words

Chapter 87 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

kazo ka karbi affan" saboda yadda taji qafarta da mararta duka sun riqe mata gam.

Yana shiga ya fito ya karbi affan din suka shige ciki suka barta,ta buda murfin motar,saidai har a sannan abbas din baice mata komai ba,sai ta dakata da fitar ta waiwayo

"To sai yaushe kenan?,sannan a nan zaka sauka?" Kai ya girgiza mata alamun a'ah,ya bude bakinsa da yakejin kamar ya manne yace

"Ki zauna kawai,sai lokacin dana gama aikin,zanzo na daukeki" duk da yanayin da yayi mata maganar yana saka mata rashin jin dadi a ranta,saboda ba yanayin daya saba mata mu'amala dashi bane,amma jin zata dan zauna a gidan ya mata dadi,tanason kasancewa sosai da mamarta,don tana jin dadin haka,uwa uba tana qaruwa da abubuwa masu yawa,sajta jinjina kai

"Allah ya bada sa'a,yasa a gama lafiya, zamuyi kewarka nida affan" ta fadi a sanyaye da wani abu dake bugun zuciyarta wanda batasan meye ba

"Ameen" ya fada muryarsa a qasa

"Ba zaka shiga ku gaisa ba?" Tayi masa tayi,abinda bata taba ba kenan sai yau

"Later" ya fada a gajarce,saita jinjina kai kawai,ta saka qafarta ta fice a motar jikinta a mugun sanyaye kamar wadda aka zarewa laka.

*H U G U M A*
Arewabooks:huguma
A RUBUCE TAKE
(k'addarata)
Part 2
Page 29

A nutse ta bude k'ofar toilet din ta fito daure da babban towel fari sol,lallausar farar fatarta mai santsi da sheqi tana ta daukan idanu.

Gaban dressing mirror din dake dakin ta isa,ta ja kujera ta zauna tana kallon fuskarta a ciki,gaba daya jin ranta da jikinta takeyi babu dadi,fuskarsa ke gilma mata cikin idanuwanta,sam jikinta bai bata ba,ta kasa nutsuwa gami da gamsuwa da wannan tafiyar da ya qirqirar mata bagtatan lokaci guda,tana tsaka da hidindimunta,tun daga yanayi fuskarsa da kuma yadda ya dinga tuqi daga bauchi zuwa katsina takejin kamar ba abbas dinta ba,tabbas akwai abinda ke faruwa,akwai wani muhimmin abu dake gudana,tayi tunani har babu iyaka,ta laluba dalilin tas tun daga randa ya sanya qafa ya fita daga gidan zuwa dawowarsa da kuma isowarsu katsina......tayi zagaye cikin tunani da abubuwan da suka wanzu kaf! Ta kasa gano abu guda daya farun.

A iya saninta sun rabu suna masu kewa da kuma shauqin juna kamar ko yaushe,hakanan koda safiyar ranar sun jima ita dashi akan waya suna hira,wata irin hira irin wadda ke fallasa sirrin zuciyar masoyi zuwa ga dan uwansa,yana ta mata qorafin a takure yake acan din tare da mita tana lallabashi tana kuma masa dariya,har suka rabu kyawawan kalamai ne bisa fatar baki da zuciyar kowannensu,to amma me ya canza hakan?

"AKWAI WANI ABU" ta fada murya qasa qasa tana motsa tausasan lips din bakinta tare da zare idanunta daga kallon da take qarewa fuskartata,ta dauki lotion dinta mai taushi da qamshi ta fara shafawa fatarta cikin kasala taraddadi da kuma damuwa.

Duk bayan wasu mintuna saita kalli wayarta dake gefe tana tsammanin kiransa,saboda ta sani haka suka sabarwa juna,duk inda zashi cikin nigeria..... matuqar tafiyar mota zaiyi itace abokiyar hirarsa har ya isa inda zashi,idan kuma hakan bata kasance ba.....zaiyita kiranta har ya isa din,amma wannan karon ko gilmawar miscall dinsa bata gani ba bare kiransa,a qididdigen da tayi a yanzun kuma, tabbas koda baije gida ba yana gab da isa

"Waishin meke faruwa?" Ta sake jefawa kanta tambayar wata irin damuwa tana tabata tun daga qasan zuciyarta.

Cikin dauriya ta shirya kanta cikin doguwar rigar atamfa,ta fidda ainihin kyanta da surarta sosai,duk da yanayin da take ciki sai data tsaya gaban mudubi ta kalli kanta,lokutta da dama takan dubi kanta da kanta tana tuna WACECE ITA A SHEKARUN DA SUKA SHUDE,a yanzun sai taga kamar ba ita ba.....komai yana zuwa yana shudewa da wani irin sauyi mai ban mamaki.

Lausasan slippers ta zurawa qafarta,sannan ta isa bakin qofa ta kama handle din ta bude tabi siririn corridor din da zai sadaka da ainihin falon gidan.

Tun bata qarasa ba ta hangeta zaune cikin falon,halittace mai girman matsayi a wajenta,halitta dake sahun farko cikin halittu mafi soyuwa a wajenta,a duk lokaci irin wannan da zatayi balaguro ta taho takanas saboda kasancewa da ita.....duniyarta kan cika da farinciki,takanji a duniya yanayi irin wannan bashi da tsaara a wajenta.

A jikinta taji tahowarta,saita dauke idanunta daga kan tv din da take kalla ta maida kanta,kusan lokaci daya suka sakarwa juna murmushi,ta kuma rigata magana

"Wannan nauyin wankan naki dai yana nan,affan ya fara kuka har sai da aka fitar dashi" cikin karaya da rauni da takeji cikin gangar jikinta da zuciyarta ta qaraso dab da ita ta zauna,tana shirin amsa mata.....kamar me kiran yana jiran dai dai lokacinne kira ya shigo wayarta,a hanzarce ta daga wayar tana duba me kiran, zuciyarta cike da fata da burin ganin wanda ranta ke darsa mata.

Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba hadi da fitar siririyar ajiyar zuciya ba

"Ina zuwa" tace da mommie,ba zata iya amsa wayarshi a gabanta ba,ita kadai tasan hottest words da suke gayama junansu,kuma muddin aka samu mishkila mommie taji daga ita har shi sun gama tafka abun kunya.

Kai tsaye dakin ta koma,ta samu gaban madubin data tashi dazu ta zauna tana yunqurin daga wayar

"Assalamualaikum" ta fada a shagwabe tana karyar da wuyanta gefe,abu mafi soyuwa kenan da tasan yana so tattare da ita,har yau kallonta yake cikin madubin da yake kallonta shekarun baya da suka shude,bata canza a idanunsa ba

"Wa'alaikumus salam" mummunar faduwa gabanta yayi daka jin sautin muryarsa me taushi da sanyi da yake mata magana da ita koda yaushe ta juye zuwa wata iriyar murya,irin muryar da yake magana da cirminals a yayin da aikinsa ya biyo ta kansu.....irin muryar da yake magana da juniors dinsa a yayin da suke hurumin aiki......irin muryar da yake magana da ita a duk sanda ya shiga qololuwar bacin rai da fushi,muryar da bata taba jin yayi mata magana da ita ba.

Kowacce gaba ta jikinta tayi sanyi,tayi namijin qoqarin tattaro nutsuwarta da juriyarta tace masa

"Ka sauka lafiya?,ya kaje gida"

"Me yasa zaki aikata min haka?" Ya fada muryarsa tana ninka ta da kaushi da ban tsoro,daga cikin wayar tana iya jin hucinsa,da alama a matuqar bacin rai da kuma fusata yake, tambayar tasa kuma ta dilmiyar da ita kogin tunanin ina ya nufa ne?,kafin ta lalubo amsa kunnuwanta sun fara isar mata da saqo mafi muni cikin rayuwarta,daga bakin halitta mafi soyuwa a gareta

"Ashe haka kike?,ina miki kallon saliha ashe mayaudariya ce ke?,maciyar amana ce?,macuciya ce ke?,na baki dukkan yarda,na damqi miki rayuwata ashe zaki wasa da rai na da lafiyata?" Wani irin tashin hankali ne ya sauko mata,me abbas ke fada ne

"Me nayi maka?,abban affan me ya faru?,kasan me kake fada kuwa?"

"Na sani!,nace miki na sani, tsahon yaushe tsahon kuma wanne lokaci kika dauka kina cin amanata kina kuma ha'intata WIDAD?" Kasa zama tayi,ilahirin jikinta ya dauki tsuma,sai ta miqe tsaye qafafuwanta suna rawa

"Kana cikin hankalinka kuwa abban affan?,a ins kake yanzu?" Ta tambayeshi don ta tabbatar da cewa he's safe,ba gusar masa da hankali akayi ba yake gaya mata hakan

"Har kinyi wayon fara bin maza?,ki kwana a hotel?,hakan bai isheki ba har sai kin dauko gardi kin kawomin gidana?,kin kuma kaishi har gadona na sunna widad?,wane laifi na aikata miki haka dana cancanci irin wannan hukuncin?" Yayi maganar ta qarshe muryarsa a wani mugun karye,saidai zafi da kaushin nan suna nan taf a muryarsa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada a bayyane,qafafuwanta suka hau rawa,gabanta yayi wani irin bugawa da zuciyarta ta hasko mata abinda yake magana a kai.

"Hotel kuma?" Ta tambayeshi muryarta na wata mugun rawa,irin rawar dake bayyanar da zallar daburce wa a sanda aka ritsaka bisa wani abu na rashin gaskiya

"Bakije bane?,ko zaki shiryamin irin qaryar da kika saba?"

"Naje,tabbas naje....amm......"

"Ya isa!!!!" Abinda ya fada kenan a tsawace

"Abinda nakeson ji kenan kuma naji,kije ke da Allah,bazan taba yafe miki ba,amanata da kikaci ubangiji ne kawai zaiyimin sakayya,Allah ya isa ban yafe miki ba!!!" Kit! Wayar ta katse

"Abban affan,daddy!!!" Ta fada a gigice,saidai tuni ya katse layin

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta sake maimaitawa jikinta na wani irin kyarma tana yunqurin binsa,saidai a take kamfanin sadarwa suka gaya mata is switched off,saita saki wayar ta sulale a wajen tana sakin wani azababben kuka,wani abu mai tauri da zafi yana tokare mata qirji.

"Waye ya ganta?,waye ya gaya masa?,waye???" Ta soma nacin gano daga inda maganar ta fita

"Hafsah" taji an bata amsa daga can tsakiyar zuciyarta,kukanta ya tsaya cak na wasu sakanni,sai ta sake rushewa da kukan tana jin kanta yana sara mata,tana son miqewa amma ta kasa,idan tayi kamar zata tashi sai jiri ya maidata ya kayar,a haka aka turo qofar dakin,ta daga idanunta da taji kamar basa dauko.mata hoton komai da kyau ta tsurawa qofar idanu tanason tantance mai shigowar.

*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
Part 02

Page 30


Mummy ce dauke affan da yake faman tsala kuka,kukan nasa daya dinga shiga kunnuwan widad kamar a duniyar mafarki

"Karbeshi ki bashi yasha,kamar bacci yakeyi" mummyn ta fada tana miqa mata shi,saidai ko motsawa batayi ba bare tayi azamar karbarsa,abinda yaja hankalin mummyn kenan

"Ke widad.... widad lafiya?" A hankali ta ajjiye affan ta zauna tana jan widad din cikin jikinta gami da ambaton

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil" ganin kamar tana neman fita a hayyacinta,addu'o'i ta soma karantawa tana shafa mata a fuska,a hankali sai nutsuwarta ta fara dai daita,ganinta ya fara dawowa dai dai,ta zubawa mummyn idanu wasu hawaye masu zafin gaske suka fara zarya akan fuskarta.

"Meyake faruwa?,me ya sameki?"

"Mummy cikina ne yakemin wani irin ciwo"

"Ya subhanallah" ta fada wani sashen na zuciyarta yana mata wasi wasi,yanayin da taga ta shiga baiyi kama da yanayin ciwo ba,yafi kama da wanda yaga wani mummunan tashin hankalin

"Bari na kira saleem sai mu muje kiga likita,ai bai kamata a zauna ba" kama hannun mummyn tayi

"Aah mummy,addu'a zakici gaba da yimin,ko yanzun da kika yimin na samu sassauci" kai ta jinjina badon ta yarda da widad da abinda yake damunta ba,a haka ta sakata ta shayar da affan saita sake karbarsa ta fita,saidai fiye da rabin hankalinta yana kan widad din,duk bayan wani lokaci saita leqata tare da tambayarta ya jikin?,akwai abinda take buqata?,saidai tace babu.

A ranar yadda taga baqar rana haka taga baqin dare,baqin daren daya zame mata baqiqqirin,yayi mata kuma tsaho tamkar daren mutuwa,tayi dukka Wani qoqari na fahimtar da abbas abinda yake zato ba haka bane amma yaqi saurararta,ta kira har sau ba adadi,ta tura masa tex na bayanai har batasan yawansu ba amma ba abinda ya canza,kafin gari ya waye ta fige ta fita hayyacinta da tashin hankali,kamar yadda shima a nasa bangaren wani irin firgici tashin hankali da razani yaso da'ai d'aitashi,duk sanda ya tuna har lawal ya shaida fitar tata ya kuma bashi tabbacin zuwa take hotel din tana kuma kawo maza sai yaji kamar zuciyarsa ta fashe ya mutu.

Sanda mummy ta shigo da safen ja da baya tayi tana salati ganin yadda fuskar widad din tayi jajur da ita ta tasa

"Ke tashi,tashi ki gayamin gaskiyar abinda yake damunki" mummyn ta fada tan ajjiye kayan tea data shigo mata dasu,ta nemi gefanta ta zauna ta a nutse tana rutsata da ido.

Batasan ba zata iya daukan wannan tashin hankalin ba,batasan zuciyarta ba zata iya jure wannan al'amarin ba sai data dora kanta a kafadar mummyn,a sannan ta sake gasgata uwa rahamace da babu kamarta a doron duniya,tayi kuka tayi kuka,har sai data zagwanye dukkan wasu damuwoyi data jima tana dakonsu a ranta,sannan a hankali cikin wani irin ciwo da zuciyarta ke mata ta furta ma mummyn abinda ke faruwa

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta maimaita sau uku cikin mugun gigicewa tana daga widad daga kafadarta

"Da wannan abun kike boyewa?,wacce iri ce ke widad?,to ni kaina wannan abun yafi qarfina,yafi kuma qarfin jina da kunnuwana,bazan iya jin wannan abun ni kadai ba,maza tashi"ta fada tana dauko ruwan tea din data shigo dashi

"Tashi kisha wannan yanzun nan fita ta kamani,banga ta zama ba" haka ta dinga bata tea din,tana kurba tana jin kamar mutuwa takesha,mararta kamar zata fashe saboda tsananin ciwo,amma wannan ciwon bashi ke damunta ba,salama ne akan ciwon dake danqare cikin zuciyarta.

Mummy na bata tea din tana sake maimaita innalillahin saboda yadda batun ya daki zuciyarta,ta sani ta kare kanta da mutuncinta tsahon rayuwarta,dai dai da rana daya kuma bata taba hutawa da yiwa yaranta da jikokinta addu'a kan samun kariya daga zina ba,tayi imanin addu'arta ba zata tashi a banza ba.

Da cup din ta fice bayan ta sakata kwanciya sanda taga gumi yana yanko mata ko ina

"Ki cire damuwa a ranki,Allah yana tare dame gaskiya muddin kinsan kedin me gaskiya ce,komai daren dadewa Allah bazai bar gaskiya ta tozarta ba" da wannan kalamin na mummy widad ta samu nutsuwa kadan,saidai duk da haka hawaye baibar fita daga idanunta ba,yadda abbas ya rufe idanu kamar yau ya fara saninta,yaqi ji yaqi gani,yaqi tsaiwa ya saurari gaskiyar ta.

Shiryawa mummyn tayi tsaf suka fice zuwa gidan yayanta,tabarsu a gidan ita da affan da su saleem,tace su kula da ita su dinga yawan leqata,zasuje su dawo ita da usama.

Shi kansa uncle bashir ya kadu da jin batun da mommyn tazo dashi,yayi Shuru yana jinjina maganar cikin ransa

"Abinda nake gani,mu basu iska shida ita,shi din na tabbatar tunda jami'in tsaro ne bazai gaza bincike ba,zuwa sannan ya huce ba kamar yanzun da yake kan doron zargi ba,kuma wala'alla ya kammala bincikensa sai mu tuntubeshi muji daga gareshi,zan shigo naga widad din in sha Allah,kici gaba da tausarta komai zai dai daita in sha Allah" mummyn ta gamsu da shawararsa,da wannan kuma ta dawo gida ta shiga kula da widad din,dukkan qoqarinta ta sanaya akanta,bata barinta ta kebe kwata kwata saidai idan ya zama dole gudun kada ta shiga damuwa,saidai abar zuciya da abinda takeso,wata muguwar damuwa keta cin ranta ta can qasa,duk da tana ta qoqarin sakewa saboda yadda take ganin mummyn nata tana wahala da ita.

Komai nata mutanen gidan sun bashi muhimmanci,kowa qoqarin ganin ya nuna mata damuwa da kulawarsa yake,amma har yau al'amarin abbas yaqi sakinta,mamakinsa ke cikata a duk sanda ta tunashi,a kowacce rana tana duba wayarta sau babu adadi waiko zataga kira ko saqonsa,kozai bayyana mata ya gano qarya ne sharri ne,ya gano kuskuren fahimtarta yayi,a kullum dakonsa takeyo ko zataga saqon ban haquri,amma shuruuuuu kakeji,babu shi babu dalilinsa.

Idan tace zata kwatanta yanayin da rayuwarta ta fada a wannan tsukin ma bata baki ne,wata irin damuwa me cin gangar jiki da ruhi,duk yadda take wuni cikin jama'a idan dare yayi tazo bacci saita kasa,kuka kuwa ta yishi kamar hawayen idanunta zasu qare,wai yau ita uncle dinta ke tuhuma da laifin zina,zina fa?,saita rushe da kuka tana jin kamar ranta zai bar gangar jikinta ta huta.

*H A F S A T*

Duniya ta zame mata sabuwa,sai takejin kamar bata da sauran wata matsala kuma yanzun,duk sanda ta dubi sassan widad ta ganshi a garqame,ta tafi kuma ba'asan ranar dawowarta ba,tayi rawa tayi juyi duk ita kadai,ta kuma kira habiba tayi mata godiya mai yawa,tare da fadin zasu koma wajen malaminta nan kusa,amma abu daya dake damunta,irin yadda abbas din gaba daya ya canza,bashi da kuzari bare walwala, fara'a kam babu ita,tuni tayi nata waje,duk da qoqarin da takeyi taga ta gyaggara yadda widad keyi amma babu abinda ya canza,sai abubuwa suka fara mata wuya,ga qoqarin ganin ta dauki pattern din widad wanda dukka jiki da zuciyarta suka gaza saboda bata saba ba,ga sauyin yanayin abbas din.

Shikam kome baisan yana yi ba,duk yadda yaso ya manta komai ya cisge widad daga rayuwarsa amma ya gaza,abun ya masa tsaye a rai,ya tsaya masa fiye da duk yadda ya zata,ko mutuwar mahiafiyarsa ya dangana amma ya kasa dangana da widad din,ya tsaya a gaban mudubi ya kalli kansa da kansa ya yiwa kansa fada amma ko gezau,yasha rasa bacci cikin dare idan abun ya taso masa amma abu guda zuciyarsa keta nacin bashi shawara

"Ki saketa kawai ka huta,ka saketa zaka manta da ita" saidai sam hannuwansa sun gaza rubutu takardar sakin.

Irin wannan maganar hafsat din tayi masa,bayan sallar isha'i yana zaune a falonsa yana kallon labaran duniya a tv,ga mai zuzzurfan hankali duba daya zaiyi masa ya gane tunani yakeyi bawai kallo ba,ta turo qofar ta shigo idanunta a kansa,ta dauke kai tana jan tsaki qasan ranta

"Haka zakayita yi kazo kuma ka haqura,kun rabu kenan har abada billahillazi" kafin ta qaraso ta sauya fuskarta zuwa yanayi na tausayi

"Daddyn mimi,nifa banajin dadin ganinka a haka gaskiya,wannan abun tunda ya riga daya faru,kawai ka sawwaqe mata,saika samu nutsuwar zuciya idan aka rabu gaba daya,badai affan ne zai hada

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads