Header Ads
Showing 156001 words to 159000 words out of 296907 words

Chapter 53 - A RUBUCE TAKE BOOK COMPLETE DOCUMENT

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

dadi yayi awon gaba da ita,ya sauke ajiyar zuciya yana gyara mata kwanciya sosai yana kallon fuskarta, murmushi ya sake subuce masa,yakai.hannu zai shafi lips dinta sai kuma ya janye hannu da sauri gudun kada ya tasheta.

Wuni guda ranar suna tare cikin gidan,kwata kwata ma ya manta da wani batun aiki,sai da aka nemeshi a gurin aikin sannan ya bada excuse din yana da patient.

A daren duk yadda taso bijirewa kwana dakin haka ya mata dole ta kwana a dakin kuma cikin jikinsa,dukkansu shi da itan wani irin ni'imtaccen bacci ne yayi awon gaba dasu.

Ko cikin duniyar baccinsa ya tabbatar da cewa wani gagarumin ci gaba da sauyi ne ya tunkaro rayuwarsa,sauka da shigar numfashinsa cikin wata irin nutsuwa.

Washegari bayan sun idar da sallar asuba,dukkansu shi da ita suna saman abun sallah,kowanne jinsa yake kamar a wata sabuwar duniyar,musamman abbas da yakejin jiki da qirjinsa wasai,babu komai a ciki sai wata irin mahaukaciyar soyayyar widad din.

"Ina kwana?" Ta fada qasa qasa kanta a qasa tana murza tafin hannunta.

Gaba dayansa ya waiwayo,sai ya saki murmushi,ya cira hannunsa a nutse ya miqa mata yana cewa

"Zo nan mu gaisa da kyau" manyan idanunta da suka dan fada kadan ta daga ta kalleshi,sai ta noqe kafada,don gaba daya tsoronsa takeji

"Please mana baby doll" ya fada da wata irin kwantacciyar murya,qas ta sakeyi da kanta tana tuna kalaman mommynta,sai ta miqe a hankali ta fara takowa zuwa gabansa.

Da idanu ya bita,yana jinta tana tsarga masa har cikin jinin jikinsa,yabi takunta da kallo,akan tsari take ajiye qafafun nata kamar wadda ake qirga ma adadin takunta.

A gabansa ta tsugunna tana watsa masa qamshin jikinta,lumshe idonsa yayi zuciyarsa na bugawa,duk yadda taso daurewa ya kauda kai ya gaza,sai yasa hannunsa ya fusgota a tausashe yayi masauki a jikinsa.

A tausashe ya maida hannuwansa ya rungumeta

"Kin tashi lpy my baby?,ya jikin?" Ya rada mata a hankali cikin kunnuwanta,har sai da duk wata tsiga ta jikinta ta tashi,ta lumshe idonta gabanta yana bugawa da sauri da sauri

"Da sauqi"

"Ma sha Allah......haka nakeson ji,Allah yayi miki albarka" har cikin zuciyarta taji sanyin addu'ar,ya motsa bakinsa zaiyi magana,kafin yace komai wayarsa dake gefe ta dauki ringing.

A nutse ya sauke idanunsa yana duba mai kiran,hafsat ce,sai ya tsaya yana kallon wayar kamar mai son karanto dalilin kiran nata ta cikin wayar.

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Page 79

Kaman wanda aka yiwa hani da daga wayar har ta katse sannan ya miqa hannu ya dauki wayar,yana shirin binta kiran ya sake shigowa,sai ya gyarawa widad zama a jikinsa sosai,yana sake riqeta a jikinsa cikin wani taushi da salo

"Ina ka shiga ne inata kira" abinda kunnuwansa suka fara jiye masa kenan,sai ya lumshe idanunsa ya kuma bude lokaci guda

"Assalamualaikum" ya furta a nutse,a tunaninsa zata ankara da kuskurenta ta kuma gyara

"Wa'alaikumus salam......inata kiran wayarku baku daga ba duka ku biyun" ta sake maimaitawa tare da amsa sallamar duka guri guda.

Danne zuciyarsa yayi kadan,idan da sabo yaci ace ya saba da duk wata dabi'a ta hafsat din,to amma kullum baqin halayenta sake qaruwa sukeyi

"jiya gaba daya ko ka nemeni,sannan itama inata kiranta bata daga ba" ta kuma fadi cikin azalzala da ci da zuci

"Tana ina ka bani ita" ta kuma fadi dai still,sai ya buda idanunsa gaba daya kamar tana gabansa

"Wai me yasa koda yaushe ki bakisan abinda ya kamata ba?,da sassafen nan kin kirani kina jeramin tambayoyi kamar wani yaronki?,me yake damunki ne?,baki ji ya na kwana ya na tashi ba?" Fuska sosai ta bata,ita ba wannan bane ya dameta,hidimar bikin qanwarsu da suka fada kwana biyu bata kirata ta jaddada mata jan kunnen data saba mata ba shine damuwarta,uwa uba yadda ra'ayoyin mutane da kuma hirarrakin da aka sha akan kishiya gidan bikin ya dugunzuma mata lissafi gaba daya

"Jiya kadai ban kiraki ba kinji babu dadi....kinyi tunanin yadda nakeji?,ke da sam idan ban kiraki ba saidai a zauna a haka idan ba buqatar kanki bane ya taso?"

"Nidai don Allah,kai me yasa ba'a yi maka abun arziqi?,yanzu gashi dana kiraka ka hauni da qorafe qorafe?, widad nace ka bawa tunda naji muryarka ai nasan lafiya lau kake"

"Bacci takeyi" ya amsa mata kai tsaye,zuciyar hafsat ta buga,bacci a dai dai wannan lokacin?,ya akayi ma yasan tana bacci idan dai ba tare suke kwana ba?

"Bacci kuma kamar tare kuke kwana?" tayi subutar bakin fada,sai tambayar tayi masa banbarakwai,kulata sam bashi da amfani,don haka ya sauke wayar kawai ya kashe.

Sosai hankalinta ya daga,ta saka lalubo number dinsa da tayi saving da abban mimi ta soma.kira ba qaqqautawa,har abun ya sake daure masa kai,daga baya sai ya kashe wayar ma gaba daya,ya sauke ajiyar zuciya yana sake gyarama widad kwanciya cikin jikinsa.

Sau tari idan hafsat din tayi wani abun....sai ka rantse da Allah bata da maraba da masu tabin hankali idan ta aikata wani abun,kuma a wajenta wannan dai dai ne?.

Kasa zama tayi,ta dinga kai kawo a dakinta,tana ganin kamar ta fara sakewa fa da yawa,kamar abbas din yana son canza hali da dabi'a,indai hakanne bai kamata taci gaba da sakewa yarinyar ba,bai kamata taci gaba da ganin haqorinta a waje ba,lallai dole tasa tsananin rashin wasa da rashin sakin fuska a tsakaninsu,amma ta ina zata fara?,duk shi ya cuceta da haramta mata zuwa kaduna,tasan halinsa kuma,yana da wahala kaga fushinsa,amma a duk sanda ya taurare lallai babu mai sakashi ya sauko,sai wata zuciyar ta bata shawarar ta kaiwa hajia ko kawu hassan qorafinta,to amma kuma hakan bamai yiwu bane,tasan babu abinda hakan zai haifar sai tashin tashina,abun qarshe yazo ya juye a kanta,amma kam tabbas ba zata dauki wannan dokar nashi taci gaba da tafiya a haka ba.

Qarfe goma na safe ta motsa,ta bude idanuwanta a hankali ta zubesu kan fuskarsa,ta lumshe su tana sake budesu,wata bala'e'iyar kunyarsa tana saukar mata,sanda ya motsa yana ajjiye magazine din hannunsa ta maida idanunta ta kulle ganin yana niyyar fahimtar ta farka,batasan ya akayi ya gane ba,tadai ji fitar murmushinsa sannan ya sukunya yayi mata rumfa,ya sakar mata lallausan kiss saman tausasan labbanta dake matuqar jan hankalinsa

"Good morning baby doll" cusa kanta tayi cikin cinyarsa cikin wani yanayi najin kunya,yaja numfashi mau nauyi saboda yadda ta sanya kan nata tana sauke masa numfashi mai dumi yana ratsa fatar cinyoyinsa ya tabashi sosai, hannuwansa ya saka ya dagata gaba daya ya sauketa cikin jikinsa,ya mamayeta da hannuwansa duka ta shige jikinsa sosai cikin wani lallausan riqo.

Kasa kasa yake mata magana cikin kunne,kamar wani na a wajen zai iya jinsu

"Yanzun ke babba ce babyn uncle,don Allah ki daina kunyar nan,tun jiya uncle dinki baiji muryarki ba,mommy tace banda musu...... mommmy tace ni mijinki ne......mommy tace ki kula dani kin manta?" Kai ta gyada a hankali,karon farko qaramin murmushi ya qwacewa fuskarta daya tuna mata da mommyn nata

"That's good mommy's girl,say something please,i wanna hear your sweet sweet sweet voice"

"Ina kwana uncle?" Ta fada a mugun shagwabe,zaka dauka tana sane tayi hakan,saidai ko kusa,kawai sound din ya fita a haka ne.

Hannunta guda ya riqe cikin nasa tana murzawa a hankali

"Lafiya lau baby.....ya jikin?,hope kin warware?" Kafada ta maqale masa a narke tana mele baki kamar yadda qaramin yaro keyi duk lokacin da yake shirin sakin kuka,hakan ya bashi damar ganin baby face dinta da kyau,ta sake wani fresh sossaaii,ko wannan shi ake kira da qyallin amarcin da ake fada?,ya raya hakan a ransa

"Har yanzu gurin da ciwo"

"Sosai?"

"Ba sosai ba" ta amsa mishi tana kallon qwayar idanunsa,abinda ya haifar masa da wani sabon feeling mai qarfi a kanta

"Kinsan me za'a yi?" Ya sake fada yana gyara mata zama sosai a jikinsa

"A sake guda daya zaki warke" wani shagwababben kuka daya tasheshi a aiki ta saka,ta fara tuttureshi tana shura qafafuwa,irin yadda takewa ummunta duk sanda rigimarta ta tashi

"Iyeeee,eh lallai babyn uncle ta warke,let's try again" shigewa jikinsa tayi ta qanqameshi tana sake sakar masa kuka,irin wannan shagwabar yakeso ya gani.....irinta yake da buri.....a matsayinsa na police.....He knows hardship,he knows hardness,duk wani nau'i na tsawa bada umarni da seniority shi ya sani yake gani, at least a gidansa yana buqatar soft and cool attitudes which can make him peaceful and calm.

Shuru yayi ba tare da ya lallasheta ba,ya lumshe ido yana jin yadda muryarta ke fita da da wani irin taushi sakalci da kuma quruciya,har sai da yaga bata da niyyar tsagaitawa da gaske ta tsorata,sai ya saki murmushi,ya sunkuya a hankali,ya cusa fuskarsa ta gefan fuskarta ya lalubi kunnenta,cikin rada yake gaya mata wasu.maganganu da suka sanyata jin kunya

"Uncle..... uncle" abinda ta fara fada kenan tana riqe gaban rigarsa da kyau wai zata boye fuskarta a ciki,sai ya saki siririyar dariya ya dagata gaba daya yana cewa

"it's bath time".

Sai da sukayi wanka gaba dayansu ya hada musu breakfast a gurguje sannan ya bata magungunanta tasha.

Komai ya hanata yi,tana daga kwance tana kallo,saidai duk giftarawar da zaiyi saiya bar mata abinda zai sanyata dariya,inda zaka ganshi a lokacin,zaka rantse ba ASP abbas bane,miskilin da ganin haqorinsa ko murmushinsa ke zama wani babban aiki,zaka zaci wani mutum ne can na daban mai kama da abbas din.

Cikin kwanaki biyun gaba da babu inda yaje,suna tare cikin gidan,komai na gidan ya dauke mata,yayi wani irin mugun sakewa da ita matuqa gaya,ya kuma jata jikinsa sosai,a yanzun babban burinsa ya gina rayuwa mai.inganci ya gina rayuwar da zata zame masa madubin gobensa,duk wani abu da yasan tana so,ya kuma fuskanci yana sakata nishadi da walwala shi yakeyi,wani irin tattali da kula yake nuna mata,wani abunma baisan yanayi ba,don yana tasowa ne daga qasan zuciyarsa komai yake tasowa,wani irin yanayi dashi kansa baisan a ina zai ajjiyeshi ba.

Kudi yake zuba mata sosai a waya,tana daga zaune tayita kiran 'yan gida tana shan hira,musamman ummunta da mommynta,kusan ko da yaushe maganar mommyn tabi mijinta,banda musu ko taurin kai,sabawa umarninsa da sauran dukka abubuwan da bayaso,koda yaushe tana gaya masa

"Ki kula dashi,kiyi masa dukkan abinda yakeso,banason na sake jin kowa yaji wani abu da yake gudana a tsakaninku,ko meye zaiyi miki ko ke zakiyi masa,mai dadi ko mara dadi,sirri ne tsakaninku,ki zauna kiyi tunani ki koyi warwarewa da kanki,idan kin gaza ki nemeni" kusan rabi da rabin hirarsu da ita kenan cikin hikima.

Hutun satin ya dauka ganin ba wasu tarin ayyuka sosai a office,saidai lokaci lokaci ya leqa office din yayi awa daya ko biyu ya dawo gida a daddafe,don baya iya haura hakan,sai yaji gaba daya nutsuwarsa da hankalinsa sunyo gidan.

Ita dinma komawa take kamar wata mara lafiya muddin xai fita ya barta a gidan,saidai idan ta fita makaranta,wanda zuwa yanzun da kansa yake jigilar kaita da daukota,bai sake yarda wani ya kaita koya dauko masa ita ba,bayajin zuciyarsa zata iya dauka wannan.

Cikin sati guda ta warware,ta warware da wani irin soyayya da shaquwa dashi sabuwa data ginu a ranta,ya bar mata wani babban tambari da ya kame ilahirin zuciyarta gaba daya ba tare data ankara kota fuskanci meye ba,tasan dai a wannan lokacin tana matuqar son kasancewa tare dashi,tana jin wani farinciki duk lokacin daya zamana yana kusa da ita,suna hira aikin gida ko kuma assignments,tana jinta sukuku cikin rashin sakewa da walwala a duk lokacin da ya zamana ya nesanta da ita.

_cikin wannan yanayin sati biyu da suka biyo baya ya shirya ma zuwa gida weekend,yace ta shirya su wuce tare,don baya jin zai iya barinta har tsahon kwanaki uku ba tare da tana kusa kusa da rayuwarsa ba_

*_muje zuwa dai masu karatu,yanzu takun zai fara daukan zafi_*

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Page 80


Tsaye yake gaban mirror yana taje kansa,shirye yake cikin mulberry silk da ya kwanta sosai a jikinsa,ya kuma fidda kyan fatarsa data wadata da tsafta da kuma hutu,jikinsa na fidda sassanyan qamshin turarensa.

A nutse take takowa zuwa qofar dakin nasa,tura qofar a hankali saita tsaya tana kallonsa ta cikin madubin ba tare data saki hannun qofar ba,hakanan bata koma ba bata kuma shigo dakin ba.

Idanu ta zuba masa sosai tana kallonsa,yayi bala'in yi mata wani sassanyan kyau,a yau din quruciya kyansa da haduwarsa sun sake fito mata muraran fiye da ko yaushe, shigar ta karbeshi,duk da dama zaiyi wuya ya saka kaya a jikinsa basu karbeshin ba,ta'ammali da uniform saboda yanayin aikinsa ya sanya yafi mu'amala da manyan kaya akan qanana,saita saki qofar a hankali ta goye hannunta a qirji taci gaba da kallonsa.

A nutse ya sauke idanunsa a kanta,shi dinma shigarta ta yau ta fusgi hankalinsa sosai,abaya ce a jikinta ruby color,saita dora dan qaramin Vail a kayanta dusty rose,dan siririn pink lips dinta na fidda qyallin lipstick data shafa musu, fuskar ta ta kwanta da color din powder din data shafa

"Ma sha Allah" ya fada ta hanyar motsa labbansa,ya ajjiye comb din hannunsa a hankali,yana so yau ne ya kamata real tana satar kallonsa,abinda ya lura fa koya kenan cikin satin nan,idan kuma ya fada saita waske harda qananun hawayen ita ba kallonsa take ba.

Batayi zato ba taga ya waiwayo gaba dayansa,idanunsu suka sarqe cikin na juna,kunya ta kamata,tayi taku biyu baya zata koma ya dakatar da ita

"Don't move baby" yayi maganar muryarsa nadan sarqewa,ganin da yayi mata a yanzu da idanu sai yake ganin kamar madubin ashe ya rage kyan da tayi,turarenta da ko yaushe yake tsaye masa a rai ya iska na kadoshi kadan kadan yana cakuda da nasa yana bayar da wani kalar qamshi na musamman,sai ya cira qafarsa ya soma takawa a hankali zuwa inda take, qafafunsa na nutsewa cikin lallausan carfet din daya malale dakin dashi,bazai iya kauda kai ba a yanzun,yana qishirwa wadan nan labban nata,yanason yaji duminta sosai.......wanda rabonsa da hakan tun randa ya maidata tasa halak malak,duk kuwa da cewa gado daya suke kwana,amma bai sake neman komai daga gareta ba, saboda yana son fidda duk wani sauran tsoro nasa dake ranta.

Qugunta ya kamo da dukka hannayensa biyu ya matso da ita jikinsa sosai har jikin nasa yana gogar nata,gabanta ya fadi sosai ta lumshe ido tana son hadiye tsoronta

"Bude idon na gani..... please my baby" ji tayi ba zata iya tsallake umarninsa ba,sautin muryarsa gaba daya ta kashe mata jiki,ta bude manyan idanuntan fes a kansa,sai yaja numfashi da kyau,yasa yatsunsa biyu ya kama kumatunta yadan ja kadan

"Inason wadan nan idanun,inajin kamar na hadiyesu" ido ta fidda fuskarta na washewa

"Ana cinye idon mutum uncle?" Ta fada a sakarce,sai ya saki murmushi kawai yana tunanin yaushe widad din tashi zata gama girma ne,ya girgiza kansa a hankali,yana jin komai na jikinsa yana amsawa

"Ba'a cinye ido,amma ana iya lasheshi,ana lashe kunne,ana lashe baki ana lashe harsh........"

"Stop uncle,wallahi kunya nakeji" ta fada a narke kamar zata sanya kuka,yadda fuskarta tayi ta sake tafiya da imaninsa,mitsitsin bakinta data turo gaba ya kalla,zuwa yanzun gaba daya burinsa ya tattara a kai,a tausashe yace

"Bari na nuna miki ki gani" bai qara ko second biyu ba ya hade bakinsu waje daya,cikin wani irin lallausan salo da kuma qwarewa yake aike ma qwaqwalwarta saqo ta hanyar bata zazzafan french kiss daya birkita tunaninta gaba daya,ya kuma zare mata kowanne kuzari da qarfin hali da take jin tana dashi.

Ba inda bai aika da harshensa cikin bakinta ba,ya lasheshi tsaf ciki da waje sannan ya saketa yana jan numfashi.

Taga taga tayi zata fadi saboda yadda jikinta yayi laushi gaba daya,yayi hanzari da sauran nasa kuzarin ya tarota yana kallon qwayar idanunta,sai ya jinginata da jikinsa,hakan kuwa ya mata,don boye fuskarta tayi a qirjinsa,wata kunya tana dawainiya da ita.

Qaramar dariya mai hade da ajiyar zuciya ya sake

"Good baby.....da alama kin fara daukan haske ko?" Ya fada yana leqa fuskarta,saita kebe masa baki ta soma 'yar sheshsheqar kuka,har cikin jininsa ta aike masa da wani saqo daya huda zuciyarsa,sai ya dinga jij sheshsheqar tata kamar da manufa,yadan janye jikinsa kadan don bayason abun yaci gaba da tafiya,amma saita riqe hannunsa tana sake neman wajen buya a jikinsa,don gaba daya ya gama aza mata nauyinsa,amma ta lura shi ko a jikinsa,abinda yayi mata a yanzun tana jin kamar ba zata iya sake kallonsa ba har abada

"Ohhh.....kina buqatar qari kenan?" Kai ta girgiza da sauri,saita sakeshi taja da baya tan lalubar qofa ta fice da sauri.

Da kallo ya bita kamar wani sakarai harta fita din,ya koma da baya ya zube gefan gado,wannan din wani dadadden mafarkinsa ne da a yau ya cika,he loves kisses sosai,yana bala'in so body contact da iyalinsa qwarai,amma hakan bata samuwa sam sam a gareshi,saidai yayita fama da hakan a tarin mafarkansa,yayi loosing abubuwa

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads