Showing 30001 words to 33000 words out of 193443 words
Chapter 11 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt
sayin rai" Zain yace "Shall we..?" Junaid ya miƙe yana shafa kansa tare da juya idanunsa zuwa parlon kamar me neman wani abu, a haka suka ƙarasa dinning area, not too long da zaman su Abeddeen ya ƙaraso cikin parlon yana zabga ƙamshi, yana sanye da wando 3gauter sai Gymashark sports t.shirt sai wata farar bandaner a gaban sumar kansa, ƙamshin perfume duk ya cika wajan, bakinsa yana fidda ƙamshin Spraymintt mouth freshener. Zama yyi kan kujerar dake zagaye da dinning idanunsa a ɗan lumshe kafin ya kalli Amma yace "Ammaa.." ya kira sunanta a taushashe kallonsa tayi tace "Ya akai" Girgiza kai yyi ba tare da yace komai ba, yaja idanunsa ya rufe, Abinci Junaid ya fara ci ba tare daya kalli Abeed ba, kamar yadda shima Abeed ɗin bai kalli Junaid ba, kowa girman kai na cinsa. A hankali Sara ke ɗan leƙo kanta tana son fitowa waje amma tsoro ya hanata sbd bata son cin karo da Abeed balle ya ƙara dukanta, Junaid ya ɗan runtse idanunsa sbd zuciyarsa da yaji tana bugawa, spoon ɗin hannunsa ya ajjiye tare da daukan ruwa ya sha, gently ya buɗe idanunsa kai tsaye ganinsa ya sauka akan Sara, buɗe idanunsa yyi sosai, sai kuma ya ɗan janye ya kalli Abeed ganinsa yyi shima Sara yake kallo, idanu suka haɗa da Abeed da Junaid, miƙewa Abeed yyi ya koma Parlo tare da kwanciya kam 4seater ya miƙe ƙafafuwan sa, Zain ne ya kalli Sara data ƙaraso wajan yace "Sai yanzu Mamana?" Kai ta ɗaga tana ɗan washe bakinta yace "Zauna kici abinci" ya faɗa yana ja mata kujera, zama tayi tana ƙarewa abincin kallo, idanunta ya sauka akan farfesun naman rago wanda yaji kayan ƙamshi sai tiriri yake, Hannunta zata saka cikin kwanon Junaid dake kallon ta yace "Why not spoon?" Ya faɗa yana goge bakinsa da tissue, kallon Junaid tayi suka haɗa idanu sai kawai ta ɗauki spoon ɗin ta fara ci, Zain ya miƙe tsaye yace "Bari naje,ina da meeting gobe by 9 zan kwata bacci" Junaid yace "all the best" ya faɗa yana danna Wayarsa, ya ɗan jima a haka Sara kuma na cin Naman ta hankali kwance, slowly Junaid ya kalli Sara bayan ya rufe Wayarsa kamar ba zai mgn ba sai kuma yace "What's your name?" Cikin siririyar muryarta tace "Saraa." Ya jinjina kai yace "Ok, can we be friends Saraa?" Ya faɗa yana miƙa hannunsa, dry tayi tace "Friends?" Ta faɗa tana ware idanunta kamar yadda taga Abeed nayi yace "Yap" shima ya faɗa yana ɗaga mata gira ɗaya tare da miƙa mata hannunsa, tana ƙoƙarin miƙa masa nata hannun Abeed ya ƙaraso wajan tare da zama saman kujera ba tare daya kalleta yace "jeki ɗauko min ruwa" ya faɗa yana jan basket ɗin fruit, tare da ɗaukan Apple bawai dan yana jin daɗin ta ba, ya shiga taunawa a hankali yana ɓata fuska, Junaid yyi Murmushi yace "How was your body, ance baka da lfy, U looks so learn" Abeed yace "Allhamdulillah" Sara ta ɗauki bottle water ta kawowa Abeed tana shirin zama yace "Jeki, idan na bar parlon kya dawo" ya faɗa ba tare daya kalleta ba, Sara tana tura baki gaba kamar zatai kuka tace "To" suka haɗa ido da Junaid shima ya ɗauke kai tare da Miƙewa yyi waje abinsa daman yyiwa Amma night tun ɗazo, ganin fitar Junaid yasa Abeed ya sauke Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya a hankali ya juya kalli Sara dake tafiya yace "Saaa" juyawa tayi suna haɗa ido tayi ƙasa da kanta, yace "Zo nan" inda yake ta ƙarasa tana zuwa ya kama kunnanta yace "Ke how old are you?" Tayi masa shiru tuni hawaye ya far sauka idanunta, yace "Ba nace ki daina barin kai buɗe ba? Allah zan mammareki" ya faɗa yana murɗe kunnan tare da ranƙwashi ta, baki ta buɗe zata saki kuka yayi saurin rufe mata bakin yace "shittt" shiru tayi ta shiga jan ajjiyar zuciya, Abeed Apple ɗinsa yaci gaba daci sai da yaci guda huɗu ya sha ruwa, ya miƙe tsaye ganinta yyi tsaye da mmki ya ware idanunsa yace "Are You still crying?" Tayi shiru ya ɗago fuskarta da hannunsa hawaye ya gani kwance saman idanunta, a hankali ya share mata hawayen yace "Muje" gaba tayi yana binta a baya, time to time sai ta juya suna haɗa ido yake ware mata manyan idanunsa masu kaifi, har bedroom ɗin ta ya shiga ta gyara ba sosai ba, yace "kwanta" ta kwanta zama yyi a gefen bed ɗin domin meeting ne dashi a zoom, link ɗin meeting ɗin yabi na zoom ɗin ya saka code nan da nan jama'ar dake zoom ɗin suka bayyana, bai wani saka Camera ba kawai yabarta iya audio ya fara sauraran abinda ake cewa, sai wajan 1:30 aka gama meeting ɗin ya juya yaga tuni tayi bacci, ta ƙanƙame pillow gashi ya rufe mata fuska, durƙosawa yayi ya ɗauki ruwan addu'ar ya shafa mata a fuska zuwa tafin ƙafarta, kana yyi mata addu'a tare da ja mata duvet, a.c ya ƙaro ya fita daga cikin ɗakin a ransa yana jinjina yanayin da take ciki, he just help her daga matsalar aljanun da suke damunta, da kuma ganin ya jawo hankalinta zuwa ga addinin Musulunci. Da wannan tunanin shima ya shirya ya kwanta.
Washegari tun 8:30 Zain ya shirya cikin Suit ya ɗauki briefcase ya ɗauka, har zai tashi Abeed yace masa goodbye sai kuma kawai ya shige baya son takura masa. 11:00 duk suna kan dinning area dake weekend ne, daman duk weekend a gidan Abba ake breakfast, lunch dinner. Waziri, Ummi, Riya, Junaid da Uncle AY duk suna zaune sai Mai martaba da Amma da kuma Sara wacce take wani iri, ga duk sanda zata ɗaga ido sai sun haɗa ido da Junaid ko Riya, yanayin kallon kowa ya bambanta. Daga bakin kofa sukaji ance "Yaya kamar ana yaƙi sai kace an daina sarrafa shinkafa a duniya, tun fa kafin nazo ake ta shela zan zo ko ba kuji bane? Wlh fa sai da aka Sanarwa" Naila ta faɗa tana ƙarasa shigowa cikin parlon, Junaid yace "Wace ke da za'a sanar?" Naila tace "A'a aikai ba wani imani ne dakai ba, duk wanda zai saka wuƙa babu tsoran Allah ya yanka mutum ai Wlh abin tsoro ne, nan nan naga wani likita ya yanka cikin mutum babu kunya babu tsoran Allah" sai kuma ta fashe da kuka tace "Kai dai Ubanka ya cucemu, ya rasa wanne karatu zaka sai na likitoci? Yanzu fa lalle ace akwai ɗigon tausayi a zuciyarka ba ko Juwal?" Junaid yace "Daman, na ɗauka kin mutu ai?" Da sauri tace "A'a wlh da Uwarka kke gata nan a kusa dakai, daka gani baƙin halinta kwaso" Waziri yace "Junaid zaka bar wajan nan" shiru Junaid yayi, Naila tace "Daman fa ina zaune naji ana sanyawa Mai martaba albarka wai yana da hankali, nace nidai bawai rashin kirki ba, ba wani hankalinsa na gani tunda ƙiriƙiri ya saka baki a auren yaran nan yaƙi, to dai ba ance hannunka baya ruɓewa ka yarba da nace wani, amma dai wlh duk duniya da kuma Nijeriya sun shaida ban taɓa haihuwar banza ba, wankakkun yara nake haifa, shiyasa duniya ake ta shela tun safe ba yar yanzu wai na iya haihuwa" dry taso kama Junaid amma ya dake, wai ta iya haihuwa kamar wata akuya. Riya tace "Amma Abeed fa?" Tace "Yana part ɗin su" Tace "Bari naje" sauri Naila tace "A'a ke kuma awa? Babu dangin iya balle na baba dan Allah? Yarinyar nan kowa lafiya kike? Sai bushewa kike kamar wacce cutar yunwa ta kama? Muhammadur Rasulullah s.a.w nafa ɗauka Jakadiya Abar ce,kuji na faɗa maku to Allah ya tsare mana imaninmu" ta faɗa tana jan kujera. Mai martaba taba ya numfasa a hankali tare da cewa "Ina tinani this week ya dace a ɗaura Abeed da Riya aure, I'll talk to Zain naji wacce yake so, kai ma Junaid kafin ranar ka fito da matar aure" Naila tace "To, to! Yanzu na san na iya haihuwa da wlh na ɗauka ƙarya ƴan gidan rediyon suka shuka, yanzu kuma dan Allah nace mutum ne ke Wannan surutun ko kuma dai matar cikin sailola ce?" Amma tayi Murmushi tace "Mutum ne" Naila tace "To idan yana da hankali Allah ya tsine..." Da yamma Abeed na kwance saman kujera a parlonsu tunda ya samu Maganar aurensa da Riya zuciyarsa ta cunkushe,yaya zaiyi yanzu? Idanunsa ya rufe sosai zuciyarsa na bugawa yama rasa mafita baki ɗaya, a sanyaye ya miƙe tsaye tare da nufar Kofar main Parlo tun daga nesa yaji Mai martaba na cewa "Junaid yace bashi da wacce yake so i think zan haɗasa da wannan yarinyar Sara......
Zain Abeed isn't free, if you read for free🤷🏾♀️🤷🏾♀️🤷🏾♀️🤷🏾♀️🤷🏾♀️ it's 500 masu son double posting mrng and night 1k via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank evidence of payment 08119237616
Sarautar marubuta
[08-15 08:44] +234 703 831 1110: *14 Nimcyluv*
Abeed bai tsaya jin Abinda Mai martaba zai ƙarasa faɗa ba, ya juya a hankali ya nufi part ɗin da Sara ke ciki, kallo guda zakai masa ka fahimci how sad he's. Shi a gobe ma zai bar 9ja sai yaga yadda za'ai ya zauna da wata mace, macan ma wai Riya? Tura ƙofar parlon yyi ya sameta zaune tana kallon hannunta riƙe da ice cream, a nan bakin ƙofar yaja ya tsaya shi bai ma san mene ya kawo sa ba, Sara jin motsi a kanta ya sanya ta ɗan ɗaga kanta haɗa sukai da Abeed, tayi saurin ƙasa da kanta ta kasa ci gaba da shan ice cream ɗin. Can ƙasa yace "Na gaisheki ne?" Ta ɗago kai da sauri sai ba tace komai ba, domin wlh idanunsa tsoro suke mata, tsaki yana yace "Tashi ki ɗauki hijab kizo" ta miƙe da sauri har taje bakin ƙofa tace "Me zan ɗauka?" Ya haɗe fuska yace "Nii" dry ta kyalkyale da ita wanda kuma shine first time daya kalli fararen teeths a waje dasu, jere gwanin sha'awa, tace "Ai ƙato ne kai ban iyawa" fuska ɗaure yace "Ai haba?" Da ɗaga kai tace "Eh" ganin zata sake mgn yasa ya ɗan zare mata firgitattun idanuna yace "go and carry ur Vail" juyawa tayi shi kuma yabi bayanta da kallo, wando da riga ne jikinta light blue wanda suka ɗan kama jikinta, sai blue ɗin ribbon daya haska dugun gashin ta. "Mtwss" ya ƙara jan gajeren tsaki, Sara kai tsaye inda Amma ta ajjiye mata kayan ta nufa, ta buɗe wardrobe ɗin, a hankali take bin kayan da kallo Ita dai ba taga wani abu hijab ba, infact ma bata gane mene hijab ɗin ba. Juyawa tayi jiki a sanyaye ta nufi Parlo samunsa tayi waya manne a kunnansa yana magana a hankali, kallo ɗaya yyi mata ya ɗauke kansa, ya jima na magana wacce gaba ɗaya abinda yake faɗa bai shige "Uhm, ok, yeah" ba shine reply ɗinsa. Kashe wayar yyi ya miƙe a hankali ba tare da yabi ta kanta ba, cikin bedroom ɗin nata ya shiga, har wajan wardrobe ya nufa yana ya taɓe bakinsa, tarin kayan nata ya fara ƙare wa kallo, gaba ɗaya kayanta ƴan kanti ne, riga da wando, riga da skert sai short duguwar riga, ya jima a haka kafin ya ɗauki wani milk ɗin wani baby hijab, bata yyi yana rufe wardrobe ɗin tana kallon Hijab ɗin tace "Twin" shiru yyi mata domin baya son surutu, Kallonsa tayi taga ya juya mata baya ta juya direction ɗin da yake suka haɗa ido tace "Shine Hijab ɗin?" Banza yyi mata ta ɗan kwaɓe fuska tace "To ban iya sawa ba ai" amsa yyi yace "Matso" matsawa tayi ya saka mata hijab ɗin sam bai yarda ya taɓa jikinta ba, domin for now yaga ta fara ɗan dawowa hankalinta, bayan ya gama saka mata ya kalli round face ɗinta hijab ɗin yyi mugun mata kyau, slippers ya nuna mata ta saka yana yin gaba yace "follow me" bayansa tabi tana Murmushi Allah yasa unguwa zashi da ita. Babu kowa Main Parlo a haka suke tafiya har suka isa compound, wata mota ya shiga itama ta shiga gaba bayan ya buɗe mata, a hankali yyi mata key idanunsa ya ɗan lumshe kaɗan kafin yaja motar da wani irin gudu yabar cikin Masarautar.
A wani butik ya tsaya, tare da kashe motar ya fito, Sara ma fitowa tayi tana shaƙar fresh air ta waje, kallonta yyi yaga take Murmushi ita ɗaya alamar fitar yyi mata daɗi, suna haɗa ido ya haɗe rai yace "Muje" gaba tayi yana biye da ita a baya, har suka isa wata mata tayi musu wlcm, wajan abayas ya nufa tare da neman kujera ya zauna, Sara kuma ta tsaya daga gefensa, bai ce mata komai idan ƙafar ta sage ta nemi abun zama. Wata Ma'aikaciya tazo tace "Wlcm Mrs, what the you want?" Idanunsa a ƙasa yana danna waya yace "Some abayas haka" tace "Ok can i help you?" Shiru yyi can yace "sure" tace "Ok number fa?" Sai a lokacin ya ɗaga kansa tare da kallon matar na few seconds ya kalli Saraa wacce hankalinta ke kan wani ƙaton Teddy yace "check her" matar ta kalli Sara kai tsaye ta gane number da zai mata, tace "Ok, after Abaya than what? No shoe's, bags, inners, bar" ware idanunsa yyi jin tace bar, sai kuma ya juya ya kalli Sara daga sama har ƙasa, wani irin danne cute smile yyi yace "Anything na mata, pech, blue, black, and maroon colors" matar ta jinjina tace "Ok sir" juyawa tayi shi kuma yana zaune yana kallon Mutanan da suke wajan, bai ƙara kallon inda Sara take baya, bayan after 45mnts matar tazo da wasu haɗaɗɗun kaya very unique haka, masu azabar kyau da tsada, Abeed ya harɗe ƙafarsa tare da ɗura ta akan ɗaya, ya shiga duban kayan da shanyayyun idanunsa masu kyau, tun daga kan abayas ɗin zuwa bags underwears, harda su necklace, idanunsa ya sauka akan bar masu kyau taɓe bakinsa yyi ya ɗauki wani shoe kamar na makaranta ya bawa ma'aikaciyar yace "Baida wannan" matar tace "bai maka kyau bane? Latest shoe ne na ƴan mata?" Abeed ya kalli matar yace "color zaki sauya" tace "wacce?" Yace "White" Tace "Ok sir" ba jimawa ta dawo ɗauke ta kalmin, aka haɗa komai zuwa Booth ɗin motarsa, ya bada atm aka ciri kuɗi. Miƙewa yyi sai a lokacin ya lura Saraa bata wajan, da mmki ya dinga dubawa amma babu ita with shock yake tafiya a wajan yana dubawa, amma babu Sara hankalinsa ya ɗan fara tashi kamar daga sama ya hango ta kusa da wani ƙaton Teddy ga wani magidancin mutum a kusa da ita ya juya mata baya, hannunsa zube cikin Aljihu da alama yana duba mata wani Teddy ɗin. Juyawa Sara tayi suka haɗa ido da Abeed ta ware idanunta tace "Twin" fuskarsa ba yabo ba fallasa kafin kuma ya ɗaga kansa magidancin mutumin tuni yabar wajan. Abeed ya ƙare mata kallo yace "waye wanda kuke tare?" Ta watsa hannunta alamar bata sani ba, ya kalleta yace "muje" ta marairaice fuska sosai tace "Twin Teddy" yace "bazan siya ba" maƙale kafaɗa tayi tace "Uhm nidai" ganin mutane a wajan gashi kowa daman kallansa yake irin anga celebratie ɗin nan, yasa kawai a ƙufule ya fisgi hannunta ya shiga janta tana turjewa a haka ya ƙarasa mota da ita, bayan ya sakata a mota ya shiga yyiwa motar key yaja da ƙarfi har yana buge mata kai, kuka sosai Sara take harda shassheƙa Allah yana kallo tana mutuwar son Teddy, hakan kuma ya samo a sali tun tana yarinya. Sai da sukai nisa Abeed ya kalleta yace "Shiru a nan" ƙin shiru tayi sai ma ƙara sautin kukanta da tayi, jin kukan yake har tsakiyar kansa ga zuciyarsa dake bugawa time to time baya son ganin mace na kuka, kukan mace shine rauninsa. A haka suka ƙarasa gida har lokacin kuka take, mota ya buɗe ya fita da hannu yyiwa wasu hadimai nuni da sukwaso masa kayansa, Bai ƙara bin takan Sara ba, yyi shigewarsa, Sara da gudu tabi bayansa domin mutanan da suke wajan sun firgitar da ita. Yana shiga Main Parlo ana kiran sallar Magrib a kuma Main Parlo ɗin ya sami Zain da Junaid suna kallo, Sallama kawai yyi Suka amsa Zain yace "frm where?" Shiru yyi kai tsaye yyi shigewarsa cikin part ɗin su, ganin kayan da ake shigowa dasu yasa kawai Zain yin Murmushi yace "ko ajjiye a nan" suka zube tare da juyawa, Junaid dake jin kuka sama sama ya ɗaga kansa a tsaye yaga Sara tana goge hawayen da sukaƙi tsaya mata, da mamki yace "Saraa" taƙi ɗagowa Zain yace "Ƴar rigima ce ƙilan ita da mutumin nata ne" Shiru Junaid yyi bai ce komai ba, Zain ya miƙe yace "bari nayi alwala" Junaid yace "Ok" Zain na barin wajan Junaid ya miƙe gently ya ƙarasa inda Sara take murya a taushashe yace "what's wrong?" Ƙara sautin kukanta tayi hadda buga, Junaid duk ya diriri ce shi wlh mmkin kukan yake, baiyi tunanin zatai shagwaɓa ba, yace "Me akai maki?" Tayi shiru ya ɗan durƙosawa daidai tsayinta tare da kama hannayenta ya riƙe a nasa yace "Abeed ne right?" Kai ta ɗaga masa yace "Ok Stop cry, big girls basa kuka" sai a lokacin tace "To zaka bani Teddy ƙatowa haka" ta faɗa tana ɗaga hannunta sama sama, alamar ita dai babba take so, Junaid ya ɗan ja numfashi yace "Ok akan Teddy kike kuka?" Tace "Eh, kuma da yawa nayi kukan fa" ya ɗan saki Murmushi yana share mata hawayen fuskarta yace "to zan kawo maki ƙatuwa like you sai me?" Tai shiru can kuma sai tace "Twin zani" a zahiri Sara tana nufin wajan Sairah take son zuwa, Junaid kuma bai ɗauka wani abu bane yace "Jeki sallah yanzu zan kawo maki" Tai shiru Zain dake fitowa yace "Bata sallah ai, ta zama dangin su Zahel sai ta sake karɓar musulunci" da mmki Junaid yace "Are You sure..? This is wonderful" Zain yace "Za kaji lokaci zuwa lokaci