Header Ads
Showing 42001 words to 45000 words out of 193443 words

Chapter 15 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

yace "Oh! Sweetheart ba dai rigima ba, ke da zaki zama tawa" Murmushi tayi masa tace "Ok I love you my man..." Yace "Love u too cute" tsaki Riya tayi domin sai taga Zain tamkar Abeed. Amma ce ta shigo jikinta duk a sanyaye tace "Yauma haka zaka fita baka ƙarya ba?" Zain yace "Amma bana jin daɗin komai, idan zan abu dana tuna cewa tare muke da Abeed yake fita a raina" Amma tace "Shi Abeed ai ba yaro bane, kuma zai dawo me, am sure ko bai nemi kowa ba definitely zai neme ka" Zain yace "Haka ne, Bye ina da meeting a watan nan zamu garin Zahel" tace "Ok then..Allah ya tsare. Riya na zuwa cikin gidan su ga saki ihu tace "Ummi shawararki tayi yanzu idan muka samu labarin inda Abeed yake fa?" Ummi tace "aiki zan saka ai masa, a sanya shi neman mata da shaye-shaye, da zarar kuma kinje yake zaiyi expecting naki, kinga idan muka samu kika haihu dashi dole zai amince da aurenki domin ba zai so sunansa ya ɓaci ba" Riya tace "Kai Ummi, you're the best mother in the world wlh" Ummi tace "Abeed millionaire ne, idan muka rasa shi munyi asara" Naila dake shigowa parlo tace "Asara tawa nawa kuma Sadiya? A'a Wlh mu a zamanin mu ba'a zaka, Wannan ai ɓakar rashin kunya ce ka zauna da ɗanka kana Shira, a lalace dai zamani ya lalace sai dai kowa yayi harkar gabansa, to daman Meye haɗina dake Sadiya? Zumunci ne fa kawai, Bawai nono na kika sha ba" Ummi dai ba tace komai ba, Can dai Naila tace "To gidan talauci kuke nan? Da banji ƙashin komai ba? A'a wlh wannan dai bayi bane rowa kuma sam bata da wani amfani ba sai kici Kanki ba? Allah ya bamu alkairi daman nazo naji ya Audillahi ya kwana da jiki kada ya kullaceni" tana faɗin hakan tayi waje abinta.. wata baƙar mota ce ta shigo cikin airport ɗin da masifar gudu, lokacin jirgi yana dab da tashi, Gaza ne ya fito fuska rufe, sai kuma driver, bayan motar su kaje tare da buɗe murfin motar, Gaza yace "Keeee" Sara dake zaune ta kifa fuskarta a tsakanin cinyoyinta, rabonta da abinci tun jiya, yunwa ta keji sosai, haka kurum kuma yau tashi kanta a sake, tana ganin yanayin garin kamar ta san shi, lokaci zuwa lokaci take tuna jejin Zahel da kuma ƴar uwarta Sairah, kanta ta ɗago a hankali tare da ware manyan idanunta tayiwa Gaza kallo guda ta ɗauke kai, tana ya taɓe baki, Gaza yace "fito Malama, banda Oga ya nace ba tun a Nijeriya zai aiwatar da abinda muke buƙata ba, ido ne kawai ga za'a ƙwaƙwole" ɗayan yace "A'a Gwamma muje su ganta, su kalli idanunta ko irinsa ake buƙata" Gaza yace "Wlh shine ma, ba gasu nan farare ta tas ba, kuma manya wlh kuɗi za'a samu da yawa" dam! Gaban Sara ya faɗi, ke nan idanunta suke buƙata, tsoro ne ya kamata sai bata nuna ma, a zuciyarta kuma duk yadda tayi ƙoƙarin faɗin sunan Allah kasawa tayi, sai dai tace "Abin bauta kabas ka taimake ni" fitowa tayi ko kayan jikinta bata sauya ba, idanunta yyi jajur sbd kukan data kwana ta nayi. Tana tsaye suka gama komai, kafin Gaza yace "Muje jirgi" binsu tayi kamar wacce aka ja, kasancewar basa buƙatar ta faɗawa wani ya sanya suka kama mata vip, su kuma suka zauna a nrml waje, ƙirjin Sara na bugawa sosai, ta buɗe ƙofar vip ɗin ta shiga tunda ta shiga taji kanta ya tsara, ƙara sawa tayi wajan kujera ta zauna this is the first time data shiga jirgi, zama tayi ta ƙankame jikinta tare da kifa kanta a tsakiyar cibiyoyin ta, wajan 20 minutes da zamanta, aka buɗe ƙofar vip ɗin a hankali aka shigo, hannunsa riƙe da wayarsa ɗaya hannun kuma yana cikin aljihu, ƙana nan kaya ne a jikinsa wanda sukai masa kyau sosai, dugun Mutum mai faɗin ƙirji, sam bai kula da Sara ba, domin already shi kaɗai ya buƙaci zama cikin vip, kujerar kusa da Sara yaje na nema ya zauna, idanunsa ya lumshe ya jima a haka kafin a sanar kowa ya saka belet, Sara na jin Announcement ɗin ta ɗago kai, tsoro ya kamata juyawa tayi ta kalli mutumin dake kusa da ita ganin ko fuskarsa bata ta iya gani, yasa ta ɗauke kanta ta ɗaura belet ɗin kamar yadda taga yayi, a hankali jirgin ya fara tafiya a ƙasa alamar dai ya shirya tashi, Sara ta ƙanƙame jikinta tana ƙoƙarin cire belet ɗin sbd jirin dake kwasar ta, ga aman dake shirin zobu mata, Shi dai yana jinta duk abinda take, ko ɗaga kansa bai ɗago ba, balle yasan wace kusa dashi, Sara gani take tamkar kayan jikinta zai zube hakan yasa ta zare belet ɗin da sauri ta miƙe tsaye, tana Miƙewa jirgi na ɗagawa zuwa sama gaba ɗaya tayi baya tare da faɗawa kansa, jinta jikin mutum yasa gaba ɗaya ta ƙanƙamesa tare da sakin kuka, sai a lokacin ya ware idanunsa dake rufe kallon yadda ta ƙanƙamesa yyi, bai ce komai ba har jirgi ya samu daidaito a saman gajimare, idan ransa yyi dubu ya ɓaci domin baya ƙaunar mace mara aji, jirgi na fara gudu ya sanya hannunsa tare da ture ta, a gigice Sara ta saki ihu tana riƙe kanta tare da kallon mutumin wani irin zare ido tayi tace "Twin...




Masu karanta littafi na as free.... Kada ku damu ba zan Allah ya isa ba, amma nasan akwai haƙƙi na akan ku...... It's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank...08119237616[08-15 08:44] +234 703 831 1110: *18 Nimcyluv*
Idanunsa dake rufe ya buɗe da ɗan sauri, jin kamar ya san mallakin mai Muryar, kallonsa ne ya sauka akan ta lokacin kuma tuni Sara ta sunkuyar da kanta sbd ciwon data keji, bai iya kallon fuskarta ba sai kanta dake sunkuye ya jima yana kallonta a haka, kafin gently ya ɗauke idanunsa yana ɗan taɓe bakinsa, Numfashi Abeed ya sauke yana tunanin yadda Muryar tayi masa kala data “Saaa...” Miƙewa Sara tayi tsaye tana riƙe da kanta matsawa tayi kusa dashi kaɗan kamar zatai kuka tace "Uhm..Amm..." A wannan lokaci bugawa zuciyar Abeed tayi da ƙarfi domin ya gaba tabbatar wa Muryar Sara ce, idan itace mene ya kawo ta nan? Tayaya tabar masarautar Bilhira tazo nan? Ko har an ɗaura aurenta da Junaid ne ya taho tare da ita? Kasa ɗago kansa yyi sai ci gaba da sauke ajjiyar zuciya da yyi, Sara dake tsaye cikinta na juyawa ta fashe da kuka tana ƙanƙame jikinta, ganin ko inda take Abeed bai kalla ba, amai take son yi amma bata san inda zatai aman ba, gently ya buɗe idanunsa ya kalleta suka haɗa ido, suna kallon juna ta ƙara sakin kuka, was shock Abeed ya bita da kallo frm head to toe, gaba ɗaya tayi datti ga yunwar dake damunta wacce duk a lokaci ɗaya ya fahimci hakan, kasa magana yyi sbd mamki juyawa yyi ya fara kallon vip ɗin bbu kowa sai su ɗaya, Sara ta buɗe baki da ƙyar tace "Aman zanyi" Abeed ya ware idanunsa sosai a kanta da ƙyar ya buɗe baki yace "Yi akai na" ba musu ta matso kusa dashi tana riƙe ciki, haɗe fuska yyi sosai kafin yace "Ashe ba hankali?" Turo baki tayi tace "cikina ciwo fa" yana daga zaune ya nuna mata wani waje, da sauri ta tafi wajan ya bita da ido, not too long ta fito fuskarta duk jiƙe da ruwa, kallo ɗaya yyi mata ya ɗauke kansa tsaye tayi kansa tamkar shine ya kawota jirgin, tsaki yaja yace "Matsa kai na" matsawa tayi zuwa kujerar data tashi tana maida numfashi, shiru wajan yyi babu wanda ya sake mgn, sai da Sara ta gaji tace "I'm hungry" bai kalleta ba yace "Cinye Ni" kwaɓe fuska tayi tace "Olser na zai tashi, idan ya tashi ji nake kamar zan mutu kuma ance yaci ƙarfi na fa, ya kusa taɓa hanjin cikina" gabansa ne ya faɗi sai bai nuna ba, kawai ya tura mata abincin da aka kawo masa, kamar wacce ta shekara da yunwa haka ta fara cin abincin sai da ta cinye tass, ta sha ruwa ta kallesa tace "Na cinye" yace "Owk" ta marairaice tace "I'm sorry.." shiru yyi sai kuma yace "For..?" Duk abinda yake idanuna a rufe yake tace "Na cinye maka Abinci, kuma kai baka ci ba" banza yyi mata, lokacin da take cin abinci bata tuna baici ba sai yanzu data cinye komai, sunkuyar da kai tayi hawaye na sakko mata, yanzu shi ke nan idanunta za'a cire? Kuma ta san ba lallai Twin yyi komai ba, tunda ko kallon ta baya son yi, kuka ta saki tana faɗin "Wayyo Idanuna" sai a lokacin ya buɗe idanunsa ya kalleta ganin yadda take kuka da dukkan ƙarfin ta ya sanya yace "Keee" ƙin ɗagowa tayi taci gaba da kuka abinta, tsaki ya saki yace "Tashi kibar nan wajan, Mtwss ban son ihuu hk nan for no reason ok" sai a lokacin ta ɗaga kanta suna haɗa idanu tayi ƙasa da nata kan tace "Ba wasu ne suka ce zasu cire min idanu ba" hannunsu ya sanya ya harɗe ƙirjinsa yana kallon ta, kafin Calmy yace "Su waye?" Tace "A can gida ne, ina fitowa suka ɗauke ni a mota suka kaini wani gida a can ma na kwana" ya ware idanunsa domin bai ɗauka da gske take fa yace "kika kwana tare dasu?" Ta girgiza kai tace "A'a" yace "to yane?" Tace "A bedroom na kwana" Abeed na haɗe fuska yace "na ɗauka kitchen ne" ta kallesa taga ita ɗin yake kallo, shiru tayi ganin ba zatai mgn ba yasa yace "Uhm inaji gantali kike a can gida ke nan?" Ta girgiza kai hawaye na zubo mata tace "A'a, shine gari na wayewa fa suka kawo ni wajan jirgi naji suna waya da wani wai idanuna zaiyi tsada gashi nan manya" Yace "To suna ina?" Tace "A nan waje suka zauna" shiru kawai yyi kafin can yace "To kowa ai idanun naki za su yi kuɗi" ta zare ido tace "Idon nawa" yace "A'a nawa, ai gwamma su siyar kowa ya huta ko?" Tana sakin kuka tace "To dame zanna gani?" Banza yyi mata baice komai ba, yana jinta tayi ta kuka sai can bacci ya ɗauke ta, Abeed kam mmki ne ya kamasa dama har yanzu a duniya akwai masu satar mutane su cire masa wani abu?. Ma'aikaciyar jirgin ta shigo ta tambayi Abeed me za'a kawo masa hannunsa riƙe da jarida yace "fruits.." tace "And what..." Ya ɗan sha kuno yace "Just" tace "Ok Sir" har ta juya ya tuna da sarkin ci yace "Wait..." Tsayawa tayi yace "Ki haɗa da wani mara nauyi haka" tace "Ok Sir" fita tayi ba jimawa ta dawo ɗauke da try, lokacin Sara ta farka daga baccin har wani zazzaɓi taji yana kamata, Abincin tabi da kallo kafin ta kallesa taga ko inda take baya kallo yama sauya kujera, shiru tayi tai masa ƙuri da idanunta, har ya kama shan oranges ya fara shan watermelon bai kalleta ba, sai da yasha duk fruits ɗin Banana kawai ya bari, juyawa yyi yana goge bakinsa da tissue suna haɗa ido ta ɗauke kanta yace "Zo nan" Miƙewa tayi tana zuwa tayi baya zata faɗi yyi saurin riƙe hannunta, yace "Ke kina hauka?" Girgiza kai kawai tayi, ya saki hannunta yana faɗin "take this.." ya nuna mata plate ɗin chips da egg, ɗauka tayi ta koma inda take, bata wani ci da yawa ba ta ajjiye ta sha ruwa, juyawa Abeed ya ɗauke kansa da sauri yana taɓe fuska, Miƙewa tsaye yyi ya nufi toilet, wajan 5mnts ya fito yana goge hannu lokacin ana sanarwar a saka belet jirgi zai sauka, wajansa ya dawo ya zauna ya ɗaura belet, Sara kuma tayi raurau da idanu kamar zatai kuka tace "I'm scared,zanyi amai" fuska ɗaure yace "Tsoro kike?" Ta ɗaga masa kai yace "To Allah ya ƙara" kuka ta saki tace "Please na riƙe ka" ya ware idanunsa waje yace "Sai kin riƙe ni zaki daina jin tsoran?" Ta ɗaga masa kai, kallonta yyi can yace "To bisimillah" ya faɗa da wasa Sara da sauri ta sanya hannunta cikin tafin hannunsu tare da maƙale fuskarta a shoulder ɗin tana wani sakin numfashi na tsoro. Kallonta yyi sai kuma ya ɗauke kai yana faɗin "Saura kimin hauka, duk abinda ki kaji nace kawai Kice eh, understand?" Tana maƙale dashi Zuciyarta na bugawa kamar yadda tasa take ta ɗaga masa kai, shiru yyi mata yana jin yadda take fidda numfashin tsoro.



Jirgin su ne ya sauka a Newark Liberty International Airport. Dake New York, rufe idanuna yyi yana jin yadda jirgin ke sauka a hankali ya ɗan jijjiga, kafin ya fara tafiya a ƙasan titin da aka samar domin shi, Ƙara ƙanƙame hannunsa Sara tayi tana sakin kuka ji tayi gaba ɗaya abincin da taci yana neman dawowa, baice mata komai ba har jirgin ya gama samun daidaito a ƙasa, kafin a hankali ya sauke ajjiyar zuciya yace "Mun kawo sake ni" girgiza masa kai tayi tace "Wlh tsoro na keji" haɗe fuska yyi yana tallafo fuskarta da tafin hannunsa ɗaya, ya nuna mata ƙofar windown jirgin yace "Look! Middle class" kallon sauran jiragen da suke wajan tayi kafin tace "Soma suna tashi?" Yace "A'a kwanciya suke" zame jikinta tayi daga kusa dashi, ya miƙe tsaye yana gyara zaman p.cap ɗinsa ya sanya mars ya rufe fuskarsa, ganin yana shirin fita domin tuni an fara fita, ta miƙe da sauri ta biyo bayansa, a ƙofar vip su kaci karo da Gaza yana faɗin "Come out young lady" haɗa idanun da sukai da Abeed ya sanya Gaza yin baya yana faɗin "Ohh! Sorry" juyawa Abeed yyi ya kalli Sara kana ya kama hannunta ya fara tafiya, Gaza yace "Hello ina zaka da ita Malam?" Abeed ya ware idanunsa kamar ba zai Mgna ba sai kuma yace "Kai ka Kawo ta ne?" Gaza yace "Of course Yes! Tare muke ai" Abeed yace "Ohh really" Ya faɗa yana kallon Sara yace "Saaaa, d u knw him?" Sara tace "I don't even know him" da mmki yake kallonta Ke nan hankalinta ya fara dawowa gashi na masa English, Gaza da mmki ya cika masa zuciya yace "Ke ba tare muka shigo jirgin nan dake ba? Waye wannan ɗin?" Securities ɗin jirgin da suke ƙoƙarin fita suka tsaya suna faɗin "What's going on here?" Abeed ya ɗaga kafaɗa, Gaza yace "I don't understand, tare muka shigo jirgi da ita, sbd bana son a takura ta na kaita vip, yanzu kuma ta fito tare da wani" wani mai suna Sunday yace "Is she your sister?" Gasa yyi shiru bai Mgn ba, Abeed da surutun ya ishesa yasan kuma dan basu ga fuskarsa bane yace "She's my wife, right wify?" Ya faɗa yana kallon Saraa, Sara dai tasan wife na nufin mata, kuma yace duk abinda yace tace haka ne, Ta buɗe baki cikin golden voice nata tace "he's my husband too" hancinta Abeed yaja, Sunday yace "what a perfect couple...." Abeed yace "arrest him, ya faɗi inda ya san matata" Wanda suke tare da Gaza yyi saurin barin wajan, Abeed kuma ya zaro card ɗinsa ya bawa Sunday, kana ya kama hannun Sara zuwa fita daga cikin jirgin yana riƙe da hannunta ɗaya hannun yana jan trolly bag ɗinsa, suna fita yyi saurin sakin hannunta tare da yin gaba zuwa wajan wata haɗaɗɗiyar mota datai parking gabansa, drivern mai suna Khabeer yace "Wlcm sir, ban samu ticket na zuwa Albany County ba, har a Online sbd hazon da ake da zubar snow, Typically, it starts to snow in New York in December and the snow season stops in early March. January and February are the two most likely months to have snow in New York. Amma haka nan yanayin ya fara sauyawa, jinjina kai kawai Abeed yyi ya shiga motar Sara ta shiga Khabeer yaja motar da sauri zuwa Albany County.
Amma ce zaune akan kujera tun ɗazo ake kiranta ta kasa picking call ɗin sbd tsoro, wani kiran ne ya sake shigowa a hankali tayi picking tace "Assalamu alaikum.... Anuty Zulfa" cikin faɗa tare da masifa Anuty Zulfa tace "Ba shakka Saratu, dole kiƙi picking call nawa, how dare you ehhh? Har ina kiranki kina sharewa" A sanyaye Amma tace "I'm sorry Anuty Zulfa, ina bacci ne" Anuty Zulfa tace "you're lying, bakya bacci a wannan time ɗin" Amma tace "Bana jin daɗi ne" Anuty Zulfa tace "And so what? Look Saratu ke baki da iko ne da gidanki? Har akan wata banza ki zubawa Mai martaba idanu ya kore ɗan da kika haifa? Kin san illar koran yaro daga gidan iyayensa kowa? Kin san me hakan ke nufi ehhh? Ciwo da baƙin ciki da kuma rashin kulawar iyaye zai iya sawa Abeed ya faɗa wani irin mugun hali, idan ɗan shaye-shaye Abeddeen ya zama kune, idan macinaci ya zama kune, idan ɗan fashi ya zama or kidnapper kone, billahi kada kiyi kuka da kowa Saratu, kiyi kuka da kanki mu dai ƴan uwanki mune komai naki banda Zain ya faɗa min da ko mutuwa Abeed yyi ba zaki faɗa ba, kin baida miji uwarki Ubanki banda faccala data saki gaba, akan banzar ƴarta, mu ba muna da yara mata ba muce ya aura mana? Amma auren yanzu ba'a haka musamman namiji ba'a masa auren dole, ni nasan har abada Abeed ba zai zo New York ba, domin yasan a can nake da zama" Kuka Amma ta sakawa Zulfa tace "What should I do Anuty Zulfa? Ƙirjina zafi yake nima ina buƙatar ɗana, da sanya hannu kin san ba zan taɓa cewa a kori Abeed ba, yana da naci, zuciya da lafiya haɗi da taurin kai abu ɗaya na sani ba zai taɓa ƙarya ba, no matter how worries he's, ban san ina zan samesa ba" Anuty Zulfa dake amsa gaisuwar Autar ta BIYA tace "Uhm, kuka yanzu kika fara sai kinga wani

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads