Header Ads
Showing 48001 words to 51000 words out of 193443 words

Chapter 17 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

daga cikin Rukunnan Musulunci biyar na imani a Islam kuma aikin addini na wajibi akan ko wane musulmi, (Mace & Namiji) Taqwa. Aiki ne na Zahiri, mental, da kuma spiritual act na bauta wanda akayin su sau biyar a rana a wadansu kayyadaddun lokuta prescribed times. Lokacin yinsa dole mutum ya fuskanci kasar Makkah. A aika ce, mai bautan zai tsaya, zaiyi ruku'u, kuma zaiyi sujada, sannan ya kammala yayin da yake zaune a kasa.A yayin ko wacce raka'a, mai bautar zai karanta wasu ayoyi daga cikin Qur'ani, da yabon Allah da kuma addu'o'i. Kalmar Sallah dai ana fassara ta da bauta, amma Kalmar na nufin addu'a ne, shiyasa ma'anar keda rikitarwa. Musulmai na amfani da Kalmar "du'a" "ambato" wurin ma'anar Kalmar addu'a wanda roko ne akeyi ko nema a wajen Allah" shiru kawai Subash yyi kafin ya juya ya fita daga cikin kurkukun har yayi nisa ya dawo yace "A buɗe ta"..... Parking Abeed yyi a harabar gidansa, lokacin ya duba yaga 9:30 idanunsa ya rufe, gaba ɗaya ya gaji Allah yasa ya gama komai yau, waƙar da zai yi ita ta ke ta cinsa a rai duk abinda yake buƙata ya zuba, fitowa yyi daga cikin motar hannunsa riƙe da rigar suit ɗinsa da ɗan sauri yake tafiya sbd dosar ƙanƙarar dake zubo masa a jiki, yana zuwa Main Parlo yaja ya tsaya sbd warin gas da yaji ga kuma ihu da kukan Sara da yake jiyo wa, da sauri ya saki rigar hannunsa yama rasa yadda akai aka samo gas a gidan, idan ya shiga Wannan part ɗin sai ya fito, yana ƙoƙarin shiga wani ya hango wani part ya hango kitchen hayaƙi na fitowa daga cikin kitchen ɗin ga warin gas da ko'ina, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un jikinsa har ɓari yake ya shiga kitchen ɗin yana faɗin "Saaaaa..." Shiru da ɗan ƙarfi yace "Saraaarh.. Where are, I'm here to save you.." Sara da taji maganar Abeed ta fito daga inda ta ɓoya jikinta gaba ɗaya rawa yake sbd tsoro, tana ganinsa ta nufi wajansa da sauri shima wajanta yyi yana zuwa yace "Saaaaaa..." Ya faɗa yana buɗe hannayensa tare da....




Zain Abeed.... Isn't free contact to subscribe....08119237616


Sarautar marubuta
Nimcyluv
[08-15 08:44] +234 703 831 1110: *20 Nimcyluv*
Zamewa yyi zuwa ƙasa yana faɗin "Thank God" ya faɗi hakan yana ƙarewa Sara kallo wacce ta tsaya gabansa jikinta na rawa, ta ƙanƙame idanunta sbd tsananin tsoro, hannunsa ya ɗura a fuskarta ya kalleta kafin ya juyata zuwa baya babu ciwo ko kaɗan a jikinta, wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke yana hamdala a zuciyarsa, he can't take it.. if something happened to his Sara, miƙewa yyi tare da kama hannunta zai fita sai a lokacin ya tuna da warin gas ɗin wanda ya ɗan fara ƙara alamar zai fashe, da sauri ya sake ta yana faɗin "Out...." Ƙin tafiya tayi ya juya yana kallonta yaga hawaye na sakko mata a fuska yace "what again?" Marairaicewa tayi tace "what about you,idan na fita?" Waro idanunsa waje yyi kamar ba zai mgn ba sai kuma yace "U don't hve any problem with me...." Tana sakin kuka tace "To zaka ƙone ai" a fusace ya juya kamar zai daketa ta saki ƙara tare da ƙanƙame jikinta, numfashi ya sauke yace "Saaaaa, Leave..." Fita tayi tana sakin kuka shi kuma ya nufi wajan gas ɗin, yana zuwa yyi saurin kashewa kafin ya buɗe duk windows ɗin kitchen, da sauri ya hayaƙin ke fita ya rufe hancinsa da hannunsa sbd warin gas, ga kuma hayaƙi, idanunsa ne ya sauka akan indomie wacce ta ɗauko da alama dafawa zatai shine tayi wannan haukan, hannunsa ya zame daga hancinsa tare da matsawa kusa da jinin daya gani, ga wuƙa ga albasa ke nan ita ta yanke ko mene? Baki ya buɗe zai Mgna cikin rashin Sa'a ya shaƙi wani mugun hayaƙi da baka da hanci, hakan ya sanya Numfashinsa tsayawa, ya zama kamar wani wanda ake ƙoƙarin zarewa rai, in few minutes idanunsa sukai jajir, suka ɗan fito waje sbd sosai Abeed ya shaƙi hayaƙi, daman kuma yau gaba ɗaya sanyin garin a kansa ya ƙare, Baya yayi kaɗan tare da jingina da sink, a hankali ya kama ƙirjinsa ya riƙe wata kalar azaba ya keji mara misaltuwa, ya jima a haka kafin ya samu damar fisgar Numfashinsa da ƙyar wanda ya sanya idanunsa fitowa waje sbd tsananin azaba, Sunan Allah kawai yake kira a cikin ransa, yasan da Zain na tare dashi da tuni ya bashi inhaler, shi yanzu bai ma san inda take ba, idanunsa har ruwan azaba ke fitarwa, da ƙyar yaja jikinsa zuwa waje yana ƙanƙame ƙirjinsa dake ɗagawa yana wani irin harbawa, amma duk da haka Numfashinsa baya fita bare ya shaƙi wani, yana zuwa parlon ya zubewa ƙasan carpet tare da kifa kansa a ƙasa, har jijiyoyin kansa sai da suka fito, Sara dake maƙale baƙin ƙofa ta tsora masa idanunta wanda suke cike da hawaye, ita dai shi kawai ta sani bata san komai ya taɓa sa, ganin abinda yake kamar zai mutu yasa ta fasa kuka tare da ƙarasa wa wajansa, ta zauna tana leƙa fuskarsa, fuskarsa ta yi jajur abinka da farin mutum, idanuna sun kumbura a tsorace tace "Uhm...Am...Are You alright?" Shiru bai kulata ba, bawai dan baya jin abinda tace ba, sai dan shi kansa bai san makomarsa a yanzu ba, kukanta ya ƙaro tace "Baka da lafiya, are you sick?" Ta faɗa tana taɓa wuyansa ko za taji Fever amma babu, tashi tayi tsaye ita wlh bata san me zatai ba, danma Allah ya nufa a kullum ƙara nutsuwa take, waje ta nufa tana zuwa taga ƙofar gaba ɗaya a rufe, da gudu ta dawo lokacin a kwance ta samesa idanunsa rufe ga wani karkarwa da jikinsa yake ƙirjinsa na sama da ƙasa, zubewa tayi gabansa tana kallon yadda yake kokawa da breathing nasa, jikinta na rawa tace "Twin...open your eyes,nine nake Mgn" ta faɗa tana taɓa ƙirjinsa kamar jira yake ya kamata tafin hannunta ya riƙe cikin nasa gam, wani irin ɗumi Sara taji a hannunsa ga wani gumi dake tsastsafowa, idanunsa da suka kumbura sosai ya buɗe a wahale tare da Kallonta dasu, idan ya buɗe baki zai Mgna sai idanunsa su wani kafe kamar zai suma, gaba ɗaya ƙirjinsa a takure yake (chest tightness) Numfashinsa na wani whistling alamar yana matuƙar shan wahala, wasu Asthma na tashar musu ne ta hanyoyi daban daban kamar, Exercise-induced asthma, Occupational asthma,Allergy-induced asthma. Abeed tsora mata idanunsa yyi kawai, yasan it's difficult ta fahimci ciwonsa bare tasan mene zatai masa, yarinyar ba kai, idanunsa ya mayar ya rufe numfashin na ƙoƙarin ɗauke masa baki ɗaya, gefe guda kuma still ya riƙe hannunta jikinsa sai rawa yake, Sara zama ta gyara gaba ɗaya hawaye ya cika mata fuska, itama nata fuskar yyi jaaa, yana jin sanda ta miƙar da ƙafafuwan ta, hakan ya sanya ya ɗaga kansa kaɗan ya ɗura saman cinyarta, Sara ganin fuskarsa na kallon sama, taji yaja wani numfashi da ƙyar wanda ya fita tare da zubuwar wasu hawaye, ya san ta saki wani irin kuka tare da jijjiga shi tana faɗin "Twin..Twin... bacci zakai to ka buɗe ido mana.... Are you crying ciwo kke sosai ko? Me zan maka ko nai tayi kuka?" Ta faɗa tana ƙoƙarin zame hannunta dake cikin nasa amma ya riƙe gam, sunkuyar da fuskarta tayi zata cire veil ɗin kansa, taji Abeed ya ɗura ɗaya hannunsa a saman wuyanta, tare da kifa fuskarta a saman nashi fuskar, idanunsa rufe har lokacin, jikinsa kuma bai bar rawa ba, gyara fuskarsa yyi, ya saita bakinta a daidai nasa bakin, kafin gently ya buɗe bakinsa hakan yasa ɗan ƙaramin bakinta shigewa cikin nasa ba sosai ba, idanunta ta zaro waje sbd tsoro this is the first time da hakan ya kasance da ita, duk da bata ɗauki hakan a Something serious ba, kawai ai rashin kunya ce kuma babu kyau, sun jima a haka a tunanin Abeed zata iya sakin numfashi ko kaɗan ne a cikin bakinsa ya samu ya shaƙa, ko Numfashinsa zaiyi daidai, amma batai hakan ba, hannunsa daya riƙe nata ya saka ya ɗura a cikinta tare da kama gefen cikinta ya matsa da ƙarfi, hakan yasa Sara sakin ƙara tare da fitar da wani mahaukaciya Numfashi a cikin bakin Abeed, hakan yyi daidai da ɗagawar ƙirjinsa alamar ya shaƙi nata numfashi har yaje inda ake buƙata, nan da nan kuma zufa ta shiga yanko masa, Sara da cikinta yyi mata wani irin murɗawa a tsorace ta fara ƙoƙarin zare bakinta da sauri shima Abeed ya datse bakinsa ya hanata cire nata, a hankali ya ƙara matsa cikinta ta ƙara sakin numfashi, ƙirjinsa ya ƙara ɗagawa, Sara wahalar da taji yasa ta fara sakin numfashi da sauri da sauri, hakan kuma ba ƙaramin taimakawa Abeed yyi ba, idanunsa rufe gam yana jin yadda numfashinta ke shiga cikin bakinsa yana taimakawa wajan bawa hunhunsa iska, sun jima a haka har jikinsa ya daina rawa, slowly ya shiga buɗe idanunsa akan fuskarta da ke kan nasa fuskar, yaga ta rufe idanunta hawayen dake fita daga idanunta yana sauka akan nasa face ɗin, ya daɗe a haka yana Kallonta kafin ya mayar da idanunsa ya rufe a haka baccin wahala ya ɗauke sa, saukar Numfashinsa yasa Sara buɗe idanunta kana ta ɗauke fuskarta, tare da zuba masa idanu tausayinsa ya kamata, tana nan zaune bacci ya ɗauke ta itama.. Kiran sallar farko na Subhi ya sanya Abeed motsawa tare da dafe kansa dake masa ciwo sosai, kafin slowly ya shiga buɗe gajiyayyun idanunsa wanda sukai masa nauyi, bakinsa ɗauke da addu'a ya motsa, sosai yyi mamakin ganinsa a kwance saman carpet abinda bai taɓa yi ba in all his life, hannunsa ya miƙa zuwa ƙirjinsa zai taɓa yaji hannunsa ya sauka akan nata, juyawa yyi kaɗan ya ganta kwance kusa dashi ta kifa kanta a gefen shoulder ɗinsa, hannunta kuma akan ƙirjinsa, rufe idonsa yyi kafin ya buɗe ya ƙara kallonta, without making any sounds ya janye ta kaɗan, kana ya miƙe zaune jikinsa duk ciwo yake, ya ɗan daɗe a haka kafin ya miƙe tsaye, Kallon ta yyi harya juya sai kuma ya dawo ya saka hannunsa yana ya motsa fuska ya ɗaga ta zuwa saman kujure tare da janye mata gashin daya rufe mata fuska, bedroom ya shige yana tafiya a hankali yana zuwa ya zame duk kayan jikinsa ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa, ajjiyar zuciya ya sauke yana daɗi sosai ga Numfashinsa dake fita a nutse, ya daɗe a haka kafin ya koma ya saka warm water, domim yaji ƙarfin jikinsa, brush yyi ya wanke sumar kansa ta tas, kafin ya daka bathrube ya fito, shiryawa yyi cikin jallabiya mai santsi, kafin ya shimfiɗa pra mat ya tayar da raka'atul fajr kana yyi Subhi, azkar yyi ya miƙe, ya ɗauki Wayarsa yana duba abu can ya kashe, tare da ɗaukan remote ya kashe a.c ya kunna heater, jallabiyar ya cire ya zama daga shi sai boxer, kwanciya yyi ya rufe jikinsa da wani duvet dake bata ɗumi yana jin yadda zafin ke ratsa masa jiki, tunanin Zain ya faɗo masa, gobe ɗaurin auren Biyunina amma wai baya wajan? Wacce kalar rayuwa ce wannan, Abba ya faɗo masa a rai da sauri ya ɗauke tunanin a ransa jin kansa na masa ciwo, not too long bacci ya ɗauke sa. Wajan 8 Sara ta farka tana tashi ta shiga dube dube bata gansa ba, tagumi tayi tace "Uhm, yau ma tafiya yyi ya barni" idanunta yyi rau rau zatai kuka, can dai ta miƙe ta nufi nata bedroom ɗin wanka tayi ta shafe jikinta na cream, ta fesa dukkan perfume ɗin data gani, kafin taje wajan kayanta wata tie-front T.shirt ta saka mai kyau wacce dake da net a sama, hannun rigar babba, sai cropped trousers mai belet, wanda yake da faɗi daga ƙasa gaba ɗaya sky blue ne, ta ɗauki bandana white ta saka, she doesn't know how to cook, garin haka ta kusa saka gas yyi bindiga jiya, ta jima a haka yunwa ta keji domin rabonta da abinci tun jiya da yamma, Miƙewa tayi ta nufi Parlo harta shige ta dawo ta leƙa bedroom ɗin sa data gani a buɗe, kwance ta gansa yana bacci sosai ya rungome pillow a jikinsa, he looks so sick and learn... Tana zaune a parlo ta rungome hannunta a ƙirji tai shiru kamari mai tunani taji motsi a samanta, kanta ta ɗaga suka haɗa idanu yana sanye cikin wata Armless da wando dark blue iya gwiwa, hannunsu ɗaya cikin aljihunsa ɗaya kuma Wayarsa ce, sai ƙamshi yake ƙafarsa cikin Scuff faux-shearling slippers, zama yyi kan 3seater ba tare da yace komai ba, suna zaune kanta a ƙasa shi kuma yana Kallonta bai dai ce komai ba, Wayarsa ya fara ringing ganin sunan Danish yasa ya miƙe a hankali yake tafiya cike da kuzari da kuma tarin haiba, ƙofar part ɗin ya nufa ya buɗe ƙofar, wani matashin saurayi ne tsaya, tsaye hannunsa riƙe da leder Restaurant, Danish yace "Evening sir" kai kawai Abeed ya jinjina tare da amsar ledar, kana ya ƙara amsar wata ledar pharmacy, da ƙyar ya buɗe baki yace "Thanks, Danish." Danish yace "It's my pleasure, someone came to see you" Abeed ya ware idanunsa da mmki bai dai ce komai ba ya juy bayan ya rufe ƙofar, parlon ya dawo ya zaun bayan ya ajjiye ledar, wajan deep frizeer yaje ya ɗauki fresh milk da cup ya dawo ya zauna, a cup ɗin ya tsiyaya idanunsa akan t.v yana kallonta news, juyawa yyi suka haɗa ido da Sara, kamar ba zai mgn ba sai kuma yace "eat.." ƙasa ta sakko tare da buɗe takeaway ɗin, wani lafiyayyan gashasshen kifi ne, sai kuma yankakken tomato's da onion, ɗaya takeaway ɗin ta buɗe taga Irish sai kuma meat shawarma da lemo mai sanyi, abincin tabi da kallo a hankali Abeed dake watching TV yace "Fish.." kallonsa tayi jin kamar yyi Mgna, ai kuwa kifin ta fara ci a hankali a fili Abeed yace "I knw.." ƙara kallonsa tayi tace "Me kace" bai kalleta ba bare yyi Mgna, kaɗan bayan taci kifin taji cikinta ya murɗe yana mata zafi, ta ajjiye ya ɗauki lemon gashi mai gas kaɗan tasha ta ajjiye, miƙewa tayi zata ɗauki kayan still not looking at her yace "Me Zaki?" Tace "Ajjiyewa" yace "sauran ni zan ci?" Tace "Eh, kai ma kana jin yunwa ai" juyawa yyi gaba ɗaya ya zuba mata idanunsa kafin yace "Nine nace?" Tai shiru yace "To cinye ta tass kafin na ƙwarfe siraran ƙafar nan" ware idanunta tayi tana Shagwaɓewa tace "Idan naci kina zafi yake, Allah ba kaji ba" yace "A ina zanji?" Ya faɗa yana kallon cikinta da yadda take langwaɓar da kai, idanunsa ya ɗauke ita kuma ta nufi kitchen ya bita da kallo...


Shigowar su ke nan, daga wajan ɗaurin auren, suna zaune a wani haɗaɗɗan parlo mai kyau da tsari, Sarki Al'khasim Abubakar Wahab da Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas, sai matan Sarki Al'khasim, sai kuma Zain a ƙasa kusa da Abba, Du'a can kusa da Kilishi da alamar kamar nasiha ake musu, Kilishi ta buɗe baki zatai mgn daga bakin ƙofa taji ance "To Allah na tuba Zazzau gidan uban kowa kuma, ka kaff Duniya waye bai Sanni ba bare kuma wata Zazzau, shima munafukin ai bai faɗa min nan za su zo ba, da shalale ne sam ba zai ci amanata ba, kaga dai yadda Uban nasa ya mai dani wata ƴar iska, balle kuma Zaif da babu dangi iya balle na baba Allah na tuba, ban da dai lalacewa ta samu Audillahi ai bazai biye musu ba, to shima Ƙasimun ai ba'a san zuciyarsa ba, da yace a bani babban jirgi ya ɗago ni zuwa Zazzau Allah ya sanya ba su kaɗai bane ƴar ƴar...." Yarima Yashim dai na biye da ita riƙe da ƙatuwar jakarta, kallon ta kawai Abba yyi ya ɗauke kansa, Zain kam bai ba ɗago ba, shigowa tayi tana faɗin "A'a ya duk aka zuba min ido haka, nice fa Naila uwar Jafar, wanda ake ta faɗa a gidan rediyo, kakar shelale ba kuga kamar ba ne?" Funali Bilkisu tayi Murmushi tace "A'a mungane ki,sannu da zuwa" ta faɗa tana Miƙewa ta nuna mata waje, zama Naila tayi tace "Ai nace na zama sallamammiya idan banzo bikin ba, ko ƴar alawar ɗaurin auren na samu, kinga ai jama'ar Zazzau basa killace ni ba" Babu dai wanda yace komai idanun Naila ya sauka akan Kilishi ta dafe ƙirji tana faɗin "Muhammadur Rasulullah s.a.w, ashe mutum ce nafa ɗauka irin kayan nanne, ke kowa ya mai ya damu ranki kike zuƙe haka kamar kuɗin gurizi, kuma shi Sarkin yana kallon ki bai ɗauki wani ma taki ba, to Allah ya kyauta ya tsare imanin mu, amma dai ba kyau ki daina sunkuyar da kai sai a ɗauka munafuka ce ke wlh.." Miƙewa Kilishi tayi tana ƙaƙaro Murmushi tace "bari a kawo maki ruwa" Naila ta zaro idanu tace "Wa ɗin? Bayan ba'a gama tantance abinda ke damunki ba, salon ko jawo min masifa ba, a'a wlh na gode Allah ya bada ladan niyya" Naila ta kalli Fulani Bilkisu tace "Naga ke kamar kinfi lafiya, maza kawo min ruwan amma warcan ai sai dai a nema mata kaffara" Miƙewa Fulani Bilkisu tayi tace "Bari a gyara maki wancan parlon" Naila ta bita da ido tace "Ikon Allah, Ubangiji yyi halitta a nan, amma dai kai mai garin Zazzau kana nema mata maganin baki ko? To ai duniya babu gaskiya ne, kana zaune da mutum baka san mene a zuciyarsa ba, sai dai aita hailala da salatin fati wlh" Sarki Al'khasim Abubakar Wahab yyi Murmushi yace "Barka da zuwa, ya hanya?" Naila ta washe baki tace "lafiya, sai jinkirin jirgi ina ga dai gosilo aka samu a saman" duk kallon ta sukai, a nutse Abba ya kalli Zain da Du'a yace "Kuje Allah ya sanya muku albarka, zuwa anjima zamu shige" Zain ya fara Miƙewa sai Du'a duk suka bisu da ido, Abba har ransa yaji inama Abeed na

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads