Header Ads
Showing 78001 words to 81000 words out of 193443 words

Chapter 27 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

fuska ɗaure yake kallon wani wajan Anuty Zulfa ta kalli Sara tace "jeki ɗauko mayafin ki" Sara ta ɗaga Idanunta tare da kallon Anuty Zulfa ganin yadda Anuty Zulfa ta haɗe rai yasa ta miƙe ta nufi bedroom, Anuty Zulfa ta kalli Abeed da yake danna Wayarsa tace "Wato Abeed ni zakaiwa tijara, ga dai yara kaca kaca a gabana ba, so ban damu ba dan kaƙi ganin kima da daraja ta, kai ne Ruɓaɓɓe wlh, daga yau sai yau kada ka kuskura ka ƙara ɗaukan Sara zuwa wannan gidan, mene haɗin ka da ita?" Sai a lokacin ya juya ya kalli Anuty Zulfa yana Kallonta ya ɗauke kansa baice komai ba, tace "Mene dalilinka na kawo ta gidanka,ehhh Abeed? Ko kuma ita tace ta gaji da zama dani?" Shiru kawai yyiwa Anuty Zulfa idan yace zai mgn to fa iya gskyar abin zai faɗa mata, Murmushi Anuty Zulfa tayi tace "Ko son Sara kake?" Nan ma ya juya ya kalli Anuty Zulfa daidai lokacin kuma Sara ta fito daga cikin ɗakin gaba ɗaya suka zuba masa idanu suna jiran suji mene zai faɗa.


Sorry for the short typing....Ina wajan aiki yau currr, to ba sai dai hqr ba don Allah? Contact to subscribe.... 08119237616.


**34**she never thought of herself, she had never found herself in such a situation, jikinta sai rawa yake ta wani rufe idanunta sbd tsoro da fargaba,a kind of kiss kisses her, further inserting her into his body, da wani irin sauri kuma Abeed ya saki Sara yana juya mata baya tare da nufar wajan sink a hankali ya tari ruwa a hannunsu ya shiga kuskure bakinsa zuwa fuskarsa, Sara dai har lokacin bata dawo daidai ba, tana jin bakinta na mata wani irin zafi da zugi tamkar fatar wajan zata cire sbd zafi. Kallon yadda ta rufe idanu yyi hannunta akan baki sai kuma sharr hawaye ya shiga zubu mata daga cikin Idanunta, walking slowly ya nufi inda take tsaye yana zuwa ya shiga ƙare mata kallo frm head to toe, har ya juya sai kuma ya sake kallon ta fuska kame babu alamar wasa yace "Keee..." Kin buɗe ido tayi a ɗan tsawace "Open your eyes" buɗe Idanunta tayi hawaye har lokacin bai tsaya mata ba, hannunsa ya zuba cikin Aljihu kafin Murya can ciki kamar me raɗa ya ƙara matsawa inda take Numfashinsa na haɗewa waje guda har yana iya jin yadda ƙirjinta ke ɗagawa, gently ya ranƙwafa daidai fuskarta da wata kalar Murya yace "Uhm, na haɗiye ƙwaro,za kici abinci amma sai kin ɓata baki? Bani da hanky shiyasa...." Ya ƙare maganar a hankali yana manna mata kwantaccen beard ɗinsa a matar wuyanta tana ƙoƙarin mgn kuma taji saukar wani fitanan nan kiss a ƙasan ƙunanta wanda ya sanya har danshin softness lip's ɗinsa.... Wani numfashi taja da ƙarfi tana buɗe idanunta babu kowa a kitchen ɗin kamar walkiya haka yabar wajan baki ɗaya, to ! Kodai bashi bane daman? Amma ga ƙamshi turaren sa nan, ta jima a wajan daga ta shafa baki sai ta shafa ƙasan kunnanta Ita dai bata taɓa ganin Tijara irin wannan ba, fuskarta ta wanke ba tare data ɗauki pancakes ɗin ba ta nufi Parlo, nan ma babu kowa da alama tuni yabar gidan ma, bedroom ta nufa tana zuwa ta kwanta kan bed tare da ƙanƙame jikinta tai shiru data rufe idanunta sai kuma ta buɗe tana ganin kamar lokacin ne yake mata dukkan abinda yayi a yau ɗin. Abeddeen na barin kitchen ɗin ya fito Parlo bai tsaya jiran komai ba yyi waje yana haɗa hanya yana jin kansa na sara masa, a hankali kamar mai tsoron takawa haka ya nufi cikin motarsa yana zuwa ya shiga mai gadi ya buɗe masa gate yabar gidan baki ɗaya, yana tafiya kan titi ya gangara zuwa gefen titi tare da kifa kansa a string motar yana fidda numfashi yana jin wani sanyi na shigar masa jiki, idanunsa da sukai masa nauyi ya buɗe sosai kafin ya ɗauki bottle water mai sanyi tare da ɓalle murfin ya shiga tsiyayawa tsakiyar sumar kansa sai dai yaji ya samu sauƙi akan abinda ke masa yawo a jiki kafin ya tayar da motar ya nufi wani haɗaɗɗan pharmacy ya siyi magani 5 pack kana ya nufi gidansa, yana tafe mota na bin bayansa tsaki yaja a hankali kuma ya tsayar da driving da yake yana kallon motar ta cikin madubi..... Sarki Mabus dake cikin motar shi da Ayyana yace "Shige kada ki tsaya.." hakan yasa suna zuwa sukai gaba ba tare da sun tsaya ba, kasancewar Ayyana ba tafiya magana ba ya sanya ta ɗanyi shiru kafin a hankali tace "Ba'a gyara biyar ba, goma zata ɓaci" Sarki Mabus yace "Kamar ya ya fa?" Ta ware idanunta dake cikin glass fuskarta a cikin liƙab tace "Ba'a samu Abeddeen ba, Zahel kuma zata lalace" bai gane me take nufi ba dan haka sai kawai yyi mata shiru ta kuma cewa "Samun nasara akansa abu ne mai wahala..." Sarki Mabus yace "Me muke buƙata ne? Ba kuɗin sa da dukkan abinda ya mallaka a rayuwa ba? Sai fa yaƙi bada haɗin kai sannan ne zamu kaiwa rayuwarsa hari" Calmy Ayyana tace "Uhm, gashi wani Company yake ƙoƙarin buɗewa a yanzu" da mmki Sarki Mabus yace "Wanne Company ina kika sani?" A karo na farko ta saki wani Murmushi tace "Company biyu ne, dana kayan kiɗe kiɗe wanda za'a dinga fitar dasu ƙasashe, sai kuma na haɗin gwiwa mutum zai zuba hannun jari duk shera yana ɗaukan kason sa, wanda Company ya samu riba,amma kaso mafi yawa duk na Abeddeen Abdul-Jabbar Abbas ne..." Shiru Sarki Mabus yyi kafin yace "Idan haka ne muma zamu saka hannun jarin, daga ƙarshe kuma zamu ƙwace Company ya samu mallaki na baki ɗaya, zamu tura mutane biyu wanda zasu je zuwa ga Abeddeen" Ayyana ta jinjina kai alamar hakan yyi kafin su shiga hotel ɗin da suke ta tsaya Sarki Mabus ya sauka daga motar ita kuma ta shige ciki, 30 seconds da shigewarta Sarki Mabus ya shiga.....wani mutum dake tsaye kusa da hotel ɗin ya ɗauki Wayarsa sai da ta kusa tsinkewa aka ɗauka cike da girmamawa mutumin yace "Sir, zargin ka ya tabbata,ina tunanin matarsa ce amma suke pretending sbd kada a gano su" yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da shigewa cikin hotel ɗin. Da ƙyar Abeed yaja motarsa zuwa can gidansa yana zuwa ya shiga toilet tare da sakarwa kansa ruwa ya fito yana ƙamshi shower gel kana ya shirya cikin kayan shan iska kafin gently ya fito daga cikin part ɗin sa, ya ɗauki madara mai kyau da system ɗin ya nufi cikin lambun dake cikin gidansa, yana zaune kusa da ruwa ƙafafuwan sa miƙe a hankali yake operating system ɗin yana shan Madara, ya jima a wajan kafin ya gama ya miƙe tare da komawar ciki, kwanciya yyi saman Kujera ya rufe idanunsa da sauri kuma ya buɗe idanun daga ƙarshe Miƙewa yyi ya nufi gym ɗinsa....... Bayan sallar Issha Sara na zaune sanye da wata maroon ɗin Diva Abaya mai kyau tayi rolling kanta sai Gucci shoe dake ƙafarta, sai ƙamshin take wanda yake ƙara narkar da zuciyar Yarima Yashim dake zaune kujerar dake farcing nata, a hankali yace "Kinji yadda na keji kowa Sara?" Tayi ɗan Murmushi ba tare da tace komai ba yace "Gobe zaki zo ɗin? Ta ware idanunta tace "sai na tambayi Mami" yace "Mami ba zata hana ba, please zanji daɗi idan za'a bani Award ɗin da ƙaramin matsayi na ganki kina min Murmushi" a hankali Sara tace "To zan zo" yace "Good gal" ya faɗa yana jan hancinta kaɗan kafin yace "Zan koma gida daga nan zanwa Mai martaba bayani sai a turo" ta wani kwaɓe fuska tace "To kuma tun yanzu?" Kallonta kawai Yarima Yashim yyi kafin yace "Ehmn, ko baki so na ne?" Ta girgiza masa kai yace "To mene matsalar?" Murya a shagwaɓe tace " Zan ƙarasa sclh" shiru yyi sai kuma yace "Shekara uku Sara?" A hankali duk ta wani narke masa tace "Idan na gama schl sai yafi Yaa Yashim please.." ya jinjina kai yace "A bari kawai kina last semester na level 2 Sara please don't say no...I luv u so much" Turo baki tayi tace "Bana son karatu da Baby fa" wani kalar Murmushi Yarima Yashim yyi yace "To ba zan bari ki samu baby ba har ki gama schl" kamar wata ƙaramar yarinya tace "Da gaske?" Yace "Eh, idan kin amince zaki aure ni ba, ina tsoron rasaki sosai Sara" shiru tayi masa a hankali ya matsa kusa da ita yana ƙoƙarin kama hannunta, ƙamshin Bois elite ya cika gaba ɗaya Parlon ƙasa Sara tayi da Idanunta Yarima Yashim tuni ya fahimci waye, hakan yasa yayi baya fuska ɗaure shima, Sara da taji ba zata iya jurewa ba ta ɗaga fararen idanunta zuwa direction ɗin da yake, abinda bata taɓa gani ba ke nan, yana tsaye cikin wani tattausan farin voyel mai Manyan zane domin har farar singlet ɗin jikinsa ana gani ga wata Black half hula daya sanya sumar kansa tayi baya yyi wani irin kyau baka ganin komai sai fararen idanunsa haɗa idanu sukai dashi tayi saurin ɗauke kanta, a hankali Abeed dake tsaye ya shige zuwa cikin parlon kan kujera ya zauna yana harɗe ƙafarsa kafin ya ɗauki Wayarsa ya shiga dannawa, Yarima Yashim ya kalli Sara yace "Bari naje we'll talk tomorrow in sha Allah" ya faɗa yana Miƙewa tsaye itama Miƙewa tayi a hankali sukai waje Abeed ya bisu da kallo baka gane yanayin da yake ciki, domin idan ransa ya ɓaci ko ƙala baya iya cewa komai, suna fita waje Yarima Yashim yace "Wannan Uncle ɗin naki bai iya mu'amala ba" ta dai yi shiru yace "ko sonki yake?" Ta wani waro idanu tace "Kai tab, ba aure tsakanin mu har abada ai, shi ɗin da yake jin kansa" Calmy Yarima Yashim yace "Uhm, Allah yasa don't betray me please Sara" kanta a ƙasa tace "In sha Allah" mota ya shiga tana tsaye yabar wajan yana ɗaga mata hannu, tsayawa tayi tana tunanin shiga amma tana tsoro da ƙyar dai ta shige ciki yana ɗaure fuskarta. a Parlo ta same su Anuty Zulfa Auta sai kuma Oga da kansa, kanta a ƙasa ta kalli Anuty Zulfa tace "Good night Mami" Mami tace "Tun yanzu?" Tana shigewa tace "Mami kai na ciwo, gobe tun safe muke da exam ga walimar da Za'ai" Anuty Zulfa tace "Ayyah daughter, take your medicine before baccin" Anuty Zulfa ta kalli Abeed tace "Kai kazo sai zarewa Mutane idanu kake, nace abinci kai min banza, nace Coffee kayi shiru ko ruwa kaƙi sha" Miƙewa tsaye yyi ba tare da yace mata komai ba ya ɗauki key car ɗinsa yyi waje abinsa, Anuty Zulfa ta saki baki tace "Ji gantalalle ko fa gaisheni bai ba, ni wlh tsoran yanayinsa nake ko jikin ne? Duk ya wani rame fuska babu ɗigon fara'a" Auta tace "Mami, Amma kin faɗawa Amma da Yaa Zain, Yaa Abeed na nan?" Anuty Zulfa tace "A'a ƴar iya abinda kikace dai yanzu shi zanyi" Auta tayi dry tace "Am sorry Mami.... Abeed da ƙyar ya iya kai kansa zuwa wani haɗaɗɗan hotel tunda yaje kansa yake ƙasa hannunsa riƙe da kwalba idanunsa sunyi jajurr duk irin matan da suke kallonsa suke tattaɓasa amma babu wacce ya kalla bawai kuma dan baya buƙatar kasancewa dasu bane..... Zain na zaune akan bed abin duniya yyi masa zafi, ya rasa ta yarda zai kalli Du'a ya faɗa mata cewa duk yake daidai da rana ɗaya bai taɓa samun gamsuwa da ita ba, wani kalar infection ne da ita wanda baya jin daɗin komai sai a zaba idan ya shiga jikinta, Du'a data fito daga cikin toilet tana gyara sumar kanta tace "Meke damunka ne? Duk dare sai naga ka kasa bacci? What's up?" Murmushi ya saki tare da Miƙewa zuwa inda take yana zuwa ya wani rungome ta sosai yace "Kawai a gonna miss you Sweetheart.." ta ware idanunta tace "Kamarya U gonna miss me?" Yana warware towel ɗin jikinta yace "Kullum missing nki nake ai" ya faɗa yana jin wani irin ciwo a ƙasan cikinsa mace har mace amma bata da daɗin sha'ani" sakinta yyi ya nufi parlo kafin ya tashi ya shiga kicthen ya haɗa black tea with lemon ya shiga sha a hankali, sai da akai kiran sallah kafin ya miƙe yana zuwa ya sameta zaune tana share hawayen idanunta ya ware idanunsa yace "Are You cry Diva? For what reason?" Tana sakin kuka tace "Nasan cewa ba daɗin zama dani kake ba, amma mene amfani kayi min shiru ba zaka iya faɗa min na nemi magani ba? Kullum kaje Parlo ka kwana bayan lemon daɗin da kke sha? Eh What i have done to you? Zaman aure muke fa zama na dindin" jawota yyi jikinsa yace "Am sorry nayi laifi, gobe zamu je hospital stop cry" ƙanƙamesa tayi tana ƙara sakin kuka ƙilan shine yasa ko ɓatan wata bata taɓa yi ba.." washegari bayan sunyi breakfast sun gaida Amma da Mai martaba suka nufi asibiti....Naila na zaune a parlo yana faman cin nama aka buɗe ƙofa da sauri tace "Yau naga haihuwar Asara wacce masifa ce wannan ne,ai razana jama'a hankali tashe....," Shiru tayi lokacin da suka haɗa idanu da Junaid wanda yake sanye cikin wata Nevy blue ɗin Alkyabba washe baki tayi tace "A'a, lale lale da Junaidu mara ba, nafa ɗauka waccar tsumammiyar yarinyar ce wace take ta zuƙewa ba gaira babu dalili, nifa ita kaɗai idan na kalla sai naji tsoran Allah ya kamani" Junaid ya cire hannayensa da suke goye a bayansa idanunsa jajurr ya ƙarasa inda Naila take ganinsa haka kuma ya sanya duk jininta yyi sanyi, kafin tayi magana Junaid ya ɗura kansa a cinyarta yana wani jan numfashi Naila tace "Jama'a na shiga uku, akawo min ɗauki Junaidu, Junaidu, Junaidu....Hoooooo! A'a wlh ba lafiya ba nifa tun dana kallesa naji tsoran Allah ya kamani wannan uwar rama ta mece, kai faɗa min uban me kake so mene ya zuƙar da naman jikinka haka?" Ƙanƙame ƙafar Naila Junaid yyi wasu zafaffun hawaye na fitowa daga cikin idanunsa yace "I love her, ina sonta Naila zan mutu....." fitowarsu ke nan daga cikin exam hall kowa sai farin ciki yake, Sara dubawa tayi taga babu Auta a hankali ta zame ta nufi wani waje da babu mutane kanta na wani irin juya mata ga wani amai dake taso mata ciwon datai kwana biyu bai tasar mata ba shine yake ƙoƙarin kwantar da ita, zama tayi tana jan numfashi Idanunta yyi jaa da ƙyar take buɗewa, zamanta ke nan taji wani amai yazo mata kakarin aman ta fara amma yaƙi fita sai wahala take sha, gashi babu kowa a Wajan da ƙyar ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin tafiya gaba ɗaya tayi baya zata faɗi, kusan a tare Abeddeen da Yarima Yashim suka kai hannunsu domin tare ta Yarima Yashim ta tare hannunta Abeddeen kuma ya riƙe waist ɗinta, haɗa idanu sukai Sara kam bata gane komai idanunta ruf ya rufe saboda wahala, sunkuyawa Abeed yyi tare da ɗaukan ta baki ɗaya ya nufi mota da ita....






Zain Abeed isn't free contact to subscribe 08119237616...... Kuji tsoran Allah😭👏🏻.***35***




Da idanu Yarima yabi Abeed dake ɗauke da Sara da kallo yana jin wani irin abu a zuciyarsa mai kama da kishi, yana so ya gane inda yasan irin fuskar Abeed amma ya mance...A hankali ya nufi motarsa da Sara wacce jikinta tuni ya ɗauki zafin zazzaɓ,i da ta buɗe idanunta sai taji kamar zata faɗi ƙasa, tana ji dai ana tafiya da ita amma bata san waye ba, ina kuma zai kai ta? Motarsa ya buɗe a hankali har lokacin kuma tana riƙe a hannunsa kwantar da kujerar gaban motar yyi kafin ya kwantar da ita kana ya rufe motar shi kuma ya nufi wajan driver, key yyiwa motar a hankali tare da yin reverse cikin nutsuwa da kuma son lallaɓa jikin na Sara ya fara driving a hankali yana cilla idanunsa akan hanya, yana fara tafiya ya juya ya kalleta har lokacin idanunta a rufe yake tana sauke ajjiyar zuciya da ƙyar jikinta yyi very weak haka...Yarima Yashim ji yayi jikinsa yyi sanyi yama kasa tafiya hakan yasa ya nemi waje ya zauna yana dafe kansa dake juya masa, yana tunanin Gwamma a ɗaura auren sa da Sara dadai ya bari wani abun yazo ya kifta ta zama ba tasa ba....A babban wani hospital yyi parking kana ya kashe motar ya fito yana ƙarewa hospital ɗin kallo, Ganin babu likita mace ko guda ɗaya a harabar wajan ya sanya ya ƙara shan kunu fuska ɗaure ya juya zai shiga mota yaji ance "Oh! Da gaske kai ne dai?" Dr Adyan ya faɗa yana sakin Murmushi, a hankali Abeed ya juya yana buɗe idanunsa ganin Dr Adyan ba ƙaramin mmki ya bashi ba yaushe yazo ƙasar to? Dr Adyan yace "Me kake cikin hospital ko jikin naka ne?" Girgiza kai Abeed yyi a hankali ya buɗe murfin gaban motar a lokacin wani zazzaɓi mai zafi ya kama Sara sai rawa jikinta yake, Dr Adyan yace "Oh! God bata lafiya ne, bai kamata ana barinta hk ba sbd gudun abinda zaije ya dawo" ganin yadda take rawar jiki yasa Dr Adyan ya ƙara cewa "Shigo da ita Emergency room 12 yanzu" yana faɗin hakan ya juya, rufe murfin motar Abeed yyi cike da nutsuwa yake tafiya zuwa ɓangaren driver ya shiga tare da jan murfin motar ya rufe, idanunsa ya ware zuwa kanta yana ƙarewa kayan jikinta kallo hakan kuma ya nuna kayan jikin nata bai masa ba, gashi su kaɗai ya isa su sanyata jin sanyi, jacket ɗin jikinsa ya cire wacce take da ɗan girman domin zatai covering jikin Sara yana cire jacket ɗin ya ajjiye gefe guda, a hankali kuma ya ranƙwafa kanta yana jin yadda numfashinta ke dukan fuskarsa fararen hannayensa masu taushi ya sanya tare da tallafo fuskarta, murya can ciki kamar me raɗa daidai kunnanta yace “Saaaa...." Ya faɗa yana ɗago ta baki ɗaya zuwa jikinsa,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads