Header Ads
Showing 126001 words to 129000 words out of 193443 words

Chapter 43 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

warm water, kana ya dawo ya ɗauke ta bayan ya zame jallabiyar daya sanya mata, wata wahalalliyar ajjiyar zuciya Sarah ta sauke tana zabura yyi saurin danna cikin ruwan, cikin kamilalliyar muryarsa mai tsafta ya buɗe baki da ƙyar yace "So... Sowie" ya faɗa a raunace, wahala tasa ko kuka ta kasa sai hawaye ko hannunta bata iya motsawa,a haka ya sauya mata ruwan tare dayi mata wanka ya naɗe ta cikin towel, kan bed ya kwantar da ita yaja mata duvet ya kunna heater.... Har lokacin bata motsa ba, cikin dauriya ya koma yyi wanka shima yana jin ya akaita babban laifi wlh bai san yaya akai hakan ya faru, he lost his mind a time ɗin, a daddafe yyi sllh daga shi sai Arabian jallabiya ya dawo kan bed ɗin, can kusa da ita ya zauna yana yaye bargo, fuskarta ya kalla ta wani kwaɓe fuska tare da marairaicewa siraran hawaye na fitowa daga cikin idanunta wanda suke rufe, lallaɓawa yyi ya sanya mata jallabiya yana taɓa ta take zabura ta sakin ajjiyar zuciya sai hawaye, yana rungome da ita zuciyarsa fal tunani jikinsa sai rawar zazzaɓi yake, ɗaya Wayarsa ya kunna ya kira Khabeer, babu jimawa Khabeer ya ƙaraso yana mmkin kira da asubar nan, yana zuwa ya samu Abeed zaune a bayan mota riƙe da Sarah, yanayin kallon da Abeed ke jefe masa yasa Khabeer jinjina kai tare da yiwa motar key ya nufi babban hospital... Emergency aka amshi Sarah faɗan duniya ba wanda Abeed bai sha ba, Dr ɗin ta kalli Abeed yace "Ko raped akai mata sai haka, ban taɓa ganin ciwon da akaji a sex irin haka ba, Sometimes maza kuna da son zuciya da yawa, she's too young da irin wannan" Dr Soumayya ta faɗa cikin ɓacin rai, Abeed dai ko zarafin kallo bata samu wajansa ba, hannunsa bibbiyu dafe kansa dake masa bala'in ciwo yana jin komai na juya masa, yanzu ba komai yake ganewa ba balle ya fahimta, Dr Soumayya jin Sarah take tamkar ƴar cikinta cikin ɓacin rai tace "Sai anyi mata ɗinki, wannan report ya kamata nayi ma" a gigice Abeed ya buga tabel ɗin dake kusa dashi idanunsa rufe yace "Will you shut up your mouth or not ehee?" Ya faɗa yana ware Manyan idanunsa da sukai jaaa sosai, cikin ɓacin rai da taurin kai irin nasa yace "Are You looking at me and saying that I raped her? How dare you ehhh? D you know who I am?" Ya faɗa yana ƙara dukan tabel ɗin, kana ganin Abeed kasan something fishy akwai abinda ke damunsa akai, gefe guda kuma kunnansa na jiyo masa ihun da Sarah take sbd ɗinkin da ake mata, fesar da Iska yyi mai zafi not looking at her face yace "Don't tell anyone that I had sex with her, tell her that she started to lose weight due to the violence of data entry ok" yana faɗin hakan ya miƙe tsaye baya yyi zai faɗi yyi saurin dafe bango kansa dake juyawa ya riƙe cikin kiɗima Dr Soumayya ta miƙe tsaye ganin Abeed na buga kansa ta jikin bango, lallai yanzu ta ƙara tabbatarwa yana da taɓin hankali amma kamarsa bai nuna hakan ba, fita tayi not too long Khabeer da wasu likitoci suka kama Abeed zuwa wani room nada ban, ganin yadda yake ƙara ƙoƙarin buga kansa yasa sukai masa allurar bacci, Khabeer ya kalli Dr Soumayya yace "Meke damunsa?" Dr Soumayya ta girgiza kai tana yin waje tace "Kai tsaye baza'a gane meyake damunsa ba .... Sai naje anyi masa neurology tests da diagnosis za'a fahimci abinda ya faru, Dr Zubair ai masa Xtray" tana faɗin hakan tayi waje, Khabeer fita yyi zuciyarsa na ayyana masa abubuwa da dama.... Zain ne zaune yana sipping tea a hannunsa idanunsa akan Du'a dake haɗe rai tun dare yaji gabansa na faɗuwa, gently ya miƙe tsaye Du'a tayi saurin shan gabansa tace "Wlh a yau babu inda za kaje wajan munafukar matar taka, kaci amanata ka cuce ni kayi min kishiya ba tare da sani na ba, sai yanzu nayi kuskure na fara faɗa maka kalmar SO" Zain dai da idanu yake bin Du'a tsoro ma take bashi yadda take abu kamar me aljanu, a hankali yace "Nifa Namiji Du'a mata huɗu Ubangiji ya bani damar aura, ina da lafiya,ilimi, kuɗi dame na rage ki? Ba zaki iya yimin uzuri kiyi min adalci ba? Wlh wlh ban auri Sairah sbd bana Sonki ba, Wlh banyi haka ba" kafin yyi wani tunani ta ɗauki ƙatuwar kwalbar humura ta jefo masa da sauri yyi baya yace "Subuhanallahi" Du'a tace "Kada ka sake kiramin sunan watsastsiyyar ka a nan, wallahi zan iya kasheta, na kashe ka, kuma na kashe kaina indai akan soyayyarka ne" Girgiza kai kawai Zain yyi baya son yi mata abinda zai ɓata ƙyakkyawar mu'amalar dake tsakanin Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas da Sarki Al'khasim Abubakar Wahab, Wayarsa ya ɗauka ya kira number Abeed ta wacce ya basa, Khabeer na tsaye yaga ɗaya wayar Abeed na haske wacce bai fasa ba, screen ɗin wayar ya kalla yaga an saka _Partner_ kamar ba zai ɗauka ba sai kuma yyi answering, Zain ya ɗauke ajjiyar zuciya yace "I slept yesterday full of your thoughts, I felt in my mind that you are not well" Khabeer yace "Ikon Allah, Sir baya nan" da Mmki Zain yace "Who Am I speaking with?" Khabeer yace "My name is Khabeer and I am the driver of Sir Zain Abeed" Shiru Zain yyi kafin yace "Bashi wayar" a tsorace Khabeer yake Mgn domin Muryar da yaji babu bambanci data Ogan nasa, a hankali yace "Sorry, he had a car accident last night, we were in the hospital" wata zabura Zain yyi yace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, What happened to my Biyuni, is he alright?" Khabeer yace "Be patient, is noting serious he'll be fine" kasa samun nutsuwa Zain yyi yace "Zan tura maka number ka kira immediately" yana faɗin hakan ya tura masa number...... Yaya Rooma na tsaye tana duban agogo ganin har gari ya waye babu Sarah, ta kira number Abeed kamar yadda Anuty Zulfa ta faɗa amma a kashe Bata san inda zata samesa ba, kiran Anuty Zulfa ya shigo ta ɗaga da sauri, Anuty Zulfa tace "Ta dawo?" Yaya Rooma tace "A'a Yaya" a tsawace tace "Are You at of your sense Roomana? Matar aure kika bari ta kwana waje sbd Shegen son bikinki, mene haɗin ki da Masarauta ba dangin iya balle na baba? Or sbd Mijinki ya rasu sai kika samu lasisi gantalin da ki kaga dama, ki tura min yara na zuwa New York a satin nan" tana faɗin hakan ta kashe wayar,kafin Yaya Rooma tai motsa wayarta ya ƙara yin ƙara ɗauka tayi bayan ta amsa tace "What? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wanne asibiti ok ok" tana faɗin hakan ta kira Anuty Zulfa ta faɗa mata hatsari suka samu, da sauri suka nufi asibitin ita da Auta da Beeba.... Yaya Rooma ta kalli Dr Soumayya tace "Ya jikin nasu?" Dr Soumayya tace "Macan tana cikin duguwar soma, babu wanda zai ganta har 3days" Girgiza kai Yaya Rooma tayi kafin tace "Shi kuma fa?" Ajjiyar zuciya Dr Soumayya tayi tace "Daman yana da taɓin ƙwaƙwalwa ne? Ya taɓa hauka ne?" Beeba tace "Wait wa ake cewa yana hauka ne?" Dr Soumayya ta kalli Beeba tace "Mine your business young lady" Yaya Rooma tace "I'm still wondering wai Abeed kike maganar yana hauka kuma taɓin ƙwaƙwalwar?" Dr Soumayya tace "Yhh" Yaya Rooma tayi shiru can tace "Bani da masaniya, but 15yrs back yyi abu haka kamar mai Aljanu sai kuma ya daina before aje asibiti" jinjina kai Dr Soumayya tayi mmki ya kamata, kafin tace "Ya samu juyewar tunani da kuma shiga ruɗu a Yayin da yake driving har ya samu accident, bincike, scanning da Xtray ya tabbatar ƙwaƙwalwarsa nada matsala bashi da hankali shi mahaukaci ne.....






For those who need Complete book3 it's 500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank.... Via EVEDANCE 08119237616




Dan Allah wanda na bawa complete book3 ya riƙe amana🥰👍🏼 ZAIN ABEED ♥♥♥♥♥♣♣♣♣♣♣♣ 53#### Yaya Rooma dake kallon Dr Soumayya tace "I don't understand what you are said, doctor" She spoke with her mind awakened,She doesn't understand how crazy Abeed is, how can it be said that he is crazy?. Dr Soumayya tace "Ya samu matsalar Trauma,Tashin hankali, ɗimuwa, damuwa, firgici,Suna iya haukata yaro da babba" Hankali tashe Yaya Rooma tace "Trauma, Trauma?" Ta faɗa was so confused Dr Soumayya ta watsa hannunta tace "Psychological trauma: Some mental illnesses may be triggered by psychological trauma, such as severe emotional, physical or sexual abuse;
an important early loss, such as the loss of a parent;
neglect.
Environmental stress Stressful or traumatic events can trigger a mental illness in a person with a vulnerability to a mental disorder, Then..." Tai shiru for some minutes tace "After that yana shaye-shaye, sbd sinadarin Tetrahydrocannabinol da muka samu yana aiki a brain ɗinsa, Sinadarin kuma a jikin wiwi ake samu suna yinta kamar lollipop ko chocolate, Mutumin dake sha kuma zai samu Wahalar numfashi, rudewar tunani da kuma gane-gane yana ninka aikin ƙwaƙwalwa, zai saka ƙwaƙwalwa ta fara abinda ake kira da “Hallucination”... Dafe kai Yaya Rooma tayi tace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Yanzu mene mafita" Dr Soumayya tace "Is noting serious,idan za'a kiyaye a yanzu tunaninsa ba kamar namu bane, kuma a duk sanda ya buƙaci wannan wiwin da suke yinta kamar chocolate ayi ƙoƙari a bashi abinda yafi chocolate ɗin, a barshi da abinda zai ke gani kusa dashi yana jin daɗin, kada a takura tunaninsa zai iya aikin daba shi kenan ba, sai some Drugs da za'a bashi" Jinjina Kai Yaya Rooma tayi tace "Thank you Dr, zamu iya ganinsa" Dr na Miƙewa tace "Of course YES!" Fita sukai Beeba na jinjina ƙarfin zatin Ubangiji, Mutum har mutum kamar Abeed amma ace ya samu matsala a ƙwaƙwalwarsa, ƙilan taurin zuciya da kuma banza da mutum duk a haukan yake..... Tunda suka shiga ward ɗin Yaya Rooma ke kallonsa cike da tausayawa,yana kwance flat yana bacci an gyara ciwon da yaji a goshi ga bandeji nan, sumar kansa duk ta rufe fuskar sai jajayen laɓɓansa dake a waje, kallon drip ɗin hannunsa tayi sai kawai ta juya bata da wani zaɓi dole ta ɗauki abinda take ganin Shine daidai.... Ta window suka leƙa Sarah Beeba tace "Wonderful shall never end" Auta tace "What" Beeba tace "A'a tunanin zuci ne, kawai dai naga banga alamar accident a jikin Sarah baThere is something going on that we don't know,I will put my eyes on it and find out the truth" Auta tace "Allah ya shiryaki" tace "Amin... Yaya Rooma kallon Sarah take a ranta tana hamdala ba ciwo jikinta juyawa tayi tare da fita daga cikin ward ɗin tana danna waya.... Zain da Amma na zaune a parlo tare da Mai martaba wanda kwana biyu yake fama da ciwon kai, wayar Zain ya fara ringing ɗauka yyi cikin nutsuwa yace "Umma" Yaya Rooma tace "Naila fa?" Shiru Zain yyi kafin yace "Umma lafiya?" A tsawace tace "Are You answering my questions with a question Zunaiddeen Abdul-Jabbar Abbas?" Calmly yace "I am sorry Umma, bari na kai mata" Yaya Rooma tace "Kai mata urgent... Immediately" tana faɗin hakan ta kashe wayar tana amsa gaisuwar Yarima Yashim wanda bai samu zuwan New York ɗin ba... Naila ta kwaɓe baki tace "Yaya haka kamar yaƙin badar zai dawo" ta faɗa tana ɗago kanta, ganin Zain yasa tace "A'a to gsky kaji tsoran Allah, ka nemi yafiyar Ubangiji kuma tun tuni, wannan ɗaukan haƙƙin har ina Mutane duk basa tsoran Allah kowa yana tijarar da yaga dama gaba ɗaya Nijeriya ta lalace, duk yadda akai hukuma bacci take" Zain dai baice komai ya kira number Yaya Rooma yace "Gata" ya faɗa yana bawa Naila, Naila ta runtse idanunta tace "Wacce azababbiyar ce kuma, nifa bada kowa nake son halaƙa ba musamman ma dai talaka yanzu zasu ja maka jarfa, to balle Ni da duniya ta saka a gaba ana ganin ɗana Sarki ne ga jikina kuma Babban mawaƙin da babu kamarsa ni kowa mai zance da Ubangiji? Ai sai gdy iya Ni'ima yyi min na iya haihuwa Billahil lazi, nifa ko naƙudar kirki ba nayi ɗaukan cikin ne kawai mai wahala" duk Mgnar da take Yaya Rooma na jinta a hankali tace "Ina kwana Naila" wata zabura Naila tayi tana runtse idanunta tare da ɗauke wayar data ƙwaƙume tace "Huhuhuhu, wacce tsinancewa haka Ziff? A'a Gsky bana son abinda zai haɗani da matar nan, ba ance duk mazan data aura mutuwa suke ba da ƙyar ta samu ɗaya ya tsira har ya ƙunsa mata ciki, shine yanzu zaka haɗani da masifa a gsky kai ma ka zama ɗan iska ba lallai a samu wadataccen hankali a ƙwanyar kanka ba" Zain ya haɗe rai sosai yace "Kinga ina da abinyi" a hargitse tace "To Ubanka zan maka? Kaji Annamimi duk fa alaye ne, me ka iya banda zaftara ƙarya Wlh kaji tsoran mai duka muna zaune ƙasa zata turbuɗe gantalalle" Gajiya Yaya Rooma tayi tace "Daman Abeed" da sauri Naila tace "Auzubillah, ƙul ƙul Roomana da faɗin sunan nan tsirara a gaskiya ba kisan daraja da kimar mawaƙi ba" haɗe fuska Yaya Rooma tayi tace "Daman Abeed ne babu lafiya, tunda naga iyayensa sunyi banza da al'amarin sa yasa na kiraki muna asibiti ma" wani rushewa da kuka Naila tayi tace "Gaskiya garin zan bari, ina ta zama da ƴan daba ban sani ba, nifa Roomana tunda na ganki siririya ba kifi muciyar tuƙa tuwo ba, nasan imani ne da ke yanzu yanzu zan ɗaga hankalin Masarauta da Kano baki ɗaya, yanzu za kiji ana yekuwar zuwana Katsina jirage na dira" tana faɗin hakan ta kashe wayar Zain ya amsa yana son yaji mene amma bai kulata ba, bayansa tabi zuwa shashen Mai martaba... Amma na kusa da Abba tana bashi tea su kaji an kurma ihu a kansu, da sauri Abba ya buɗe idanunsa da sukai jajir ya kalli Naila wacce ke faɗin "Nifa zaman leges da nayi ba'a banza ba, babu kalar tijarar da barikin da ban kuyo a leges ba, billahil lazi yanzu zan saukewa ko wanne ɗan banza kalar tijarar ƴan leges,amma yanzu ba zan kula ku ba kwaci kanku, maza maza a tashi jirgi ya saukeni a Katsina kuma a tabbatar ba'a bi dani inda za'a sami gosulo ba" A hankali Amma tace "Katsina kuma?" Banza Naila tayi mata Amma ta sake cewa "me ake a can?" Runtse idanu Naila tayi tace "Naji masifa, a gsky Ziff kaiwa Uwarka Mgn babu abinda na haɗa da ita" Mai martaba da duk yanayinsa ya sauya ya kalli Naila sai kuma ya juya ya kalli Zain ba tare da yace komai ba, ganin hakan yasa Zain faɗin "Anyi admitted ɗin Abeed a hospital" gaban Amma ya faɗi amma ko motsawa ba tai ba, Miƙewa Abba yyi ya kama hannun Naila zuwa part ɗinsa, tsaye tayi tana sauraransa kafin ta fashe kuka tace "Kaji wata masifa ko? Wlh da ƙyar suga Annabi wannan ɗaukan haƙƙin har ina, in sha Allah sai na maka Uban kowa a hisba ko nayi hayar ƴan iskar Legas su daddatsa kowa a rage irin masifa" Juyawa Abba yyi yana danna number pilot ɗinsa, fita Zain yyi tare da shiga motarsa ya nufi ɗaya gidansa, zuciyarsa sam babu daɗi ya rasa yadda zai da Du'a, parking yyi ya fito yana tafe a nutse harya shiga cikin parlon a zaune ya sameta hannunta riƙe da Honey da lemon tana sha, walking slowly ya Ƙarasa yana zuwa ya kwace lemon ɗin hannunta da sauri Sairah ta miƙe tana turo baki gaba sai kuma ta juya masa baya hawaye na cika mata Idanu, gently Zain ya Ƙarasa wajanta bayan ya ajjiye lemon ɗin a hankali ya manna ƙirjinsa da bayanta tare da ɗura kansa shoulder ɗinta yana mata kiss a wuya yace "Sorry Beee" ya faɗa yana tura hannunsa cikin riga juyawa tayi ta faɗa jikinsa tana sakin kuka tare da faɗin "Nidai kana tafiya dani, sai nai ta tsoro ni ɗaya fa" rungome ta yyi yace "sorry Beee, ban sake bariki ke ɗaya har abada kinji" ya faɗa yana zareta a jikinsa tare da kama hannunta zuwa kan kujera kallonta ya ke tayi, suna haɗa idanu ya sakar mata Murmushi, sajansa ta shafa tace "kana sani faɗuwar gaba da wannan kallon" Murmushi yyi yace "Kina tsoran rasa nine?" Ta kwaɓe fuska tace "Akan me zan rasaka, bayan kai ɗaya na sani a nan ɗin,burina ɗaya ne a yanzu naga Daddynmu naji da gaske ba shine ya haifemu ba" Zain yace "What about your sister Sarah?" Haɗe rai tayi ba tare da tace komai ba, ya jawota jikinsa yana sakin Murmushi yace "Nikam mene sirrin honey da lemon ne, 2days sune abinci" ya faɗa yana zuge Zip ɗin rigarta, Murmushi tayi tace "Kawai sunfi min daɗin sha ne" yace "I see" yana faɗin hakan ya shiga kissing lips ɗinta tare da cilli da rigarta, ganin zasu har gitse a nan ya ɗauken zuwa bedroom, bayan sunyi wanka Zain ya fesa perfume a hankali ya taka kusa da Sairah tun kafin ya ƙaraso ta kwasa da gudu zuwa bathroom tana sheƙa wani wahalallan Amai duk abinda taci sai data amayar dashi da, ɗago ta yyi tare da wanke mata baki, jikinta duk ya tashi ganin kamar jiri na ɗaukan ta yasa ya ɗauke ta zuwa saman bed, a hankali yake binta da kallo kafin yace "Baki da lafiya shine ba zaki faɗan ba?" Girgiza masa kai tayi tace "Lfy nake, yanzu ne kawai fa I'll be fine" kusa da ita ya matsa tayi saurin ɗauke kai tana rufe hanci idanu ya waro waje kafin yyi mgn ta tashi da gudu zuwa bathroom tana kwara amai, Miƙewa yyi tare dabin bayan ta a tsaye ya sameta tana wanke fuska harɗe hannayensa a ƙirji yyi, juyawa tayi suka haɗa idanu ɗauke idanunta tayi calmly Zain yace "Are u

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads