Showing 81001 words to 84000 words out of 193443 words
Chapter 28 - ZAIN ABEED Book 1 Complete Document by Nimcey luve Sarauta .txt
Idanunta ta buɗe da ƙyar tana Kallonsa kafin ta kwaɓe fuska tace "Uncle..." Ƙuri yyi mata da fararen idanunsa still hannunsa yana kan fuskarta kafin a hankali ya shafi kumatun ta kaɗan yana manna fuskarsa akan nata idanunsa cikin nata yace "Uhm..meke maki ciwo Saaaa?" Hawaye ya kawo Idanunta tace "Uncle cikina.." idanunsa ya lumshe kana ya buɗe kafin gently ya kama hannayenta data riƙe cikinta ya ware su tare da mayar dasu baya, da sauri ta kama hannunsa tace "A'a,kai na ne" baice mata komai ba ya shiga zame rigar jikinta, top ɗin ta manne da jikinta sosai, yana Zamewa ya kalli Idanunta yaga bashi take kallo ba domin ta maida idanun ta rufe alamar dai sosai take jin ciwo, Numfashi Abeed ya sauke lokacin daya gama zame rigar jikinta bai yarda ya kalleta ba idanunsa akan fuskarta a karo na farko daya shiga ƙare mata kallo jacket ɗin ya ɗaga ya sanya mata saman farar t.shirt ɗin ta, kana ya mayar da top ɗin hakan kuma ba ƙaramin daɗin yyi mata ba, gently ya ƙara matsar da fuskarsa saman nata goshinsa akan nata a hankali ya shiga goga mata kwantaccen sajansa kafin ya manna bakinsa ta ƙasan wuyanta ya sakar mata wani hot kisses daya sanya ta saki ajjiyar zuciya, so take ta buɗe idanunta amma ta kasa, ƙara shigar da hancinsa yyi sbd fitinan nan ƙamshi da yake shaƙa bai taɓa jin ƙamshi mai daɗin sa ba, bakinsa ya sanya a kunnanta tare da wura mata iska kaɗan wanda ya sanya Sara saurin fisgar numfashi a hankali tace "Uhm... please" bai ɗago ba sai daya ɗan tura bakinsa ya fesa mata wani numfashi tare da kama skin ɗin wajan ya bata wani ƙyakƙyawan sumbata mai tsayawa a zuciyar mace a hankali a taushashe cikin nutsuwa da kamewar sa wacce take shirin gudu a yanzu ya buɗe Murya with a very low tone yace "Sowwiee.....Saaaaa" ya faɗa Murya kame yana wani irin murza mata fuskarsa a wuyanta, yunƙurin aman data fara ya sanya Abeed saurin buɗe ido wanda suka fara janyewa, ganin yadda take yunƙurin aman amma baya zuba jikinta duk yyi sanyi ya sanya ya ɗago ta tare da mannata a shoulder ɗinsa kamar wata baby ya shiga shafa bayanta ba tare da yace komai iya wahala kam tana wahala, shi kuma yaƙi fita ne sbd mazan da suke wajan, kuka ta fashe masa dashi a hankali ya sakko ta zuwa cinyarsa yana kallon yadda take kuka shi ba wani iya rarrashi yyi ba, hakan yasa kawai ya jawota jikinsa sa sosai tare da rungometa kamar wani zai ƙwace masa ita, gaba ɗaya ta jiƙa masa gaban riga da hawaye sai da yaji kukan yyi yawa ya sanya ya cirota a hankali daga jikinsa yana kallon fuskarta firr kuma taƙi buɗe idanunta, gashi dai so take ta ƙwace kanta amma bata da ƙwari, fuskarta da tayi jajur sbd zafin ciwo da kuma kukan da tayi, fuskarta ya kalla kamar wanda zai ɗauki wani abu haka ya miƙa hannunsa zuwa gaban motar bakinsa ya sauka akan goshinta a hankali ya buɗe bakin kana ya tsuke ya bata wani sauti na sakar mata light kisss da yyi a forehead "Uhm" Sara ta sauke numfashi tare da buɗe Idanunta suna haɗa idanu ya sha kunu kamar bashi ba, zame fuskarsa yyi daga nata zai fito da ita a hannunsa a hankali tace "Sake ni" ta faɗa fuska babu walwala ga zafin ciwo ga baƙin cikin abinda yyi mata, kallon ta yyi bai ce komai ba ya saketa daman kanta a rufe yake, ya fita ita kuma ta sakko ƙafarta a hankali zuwa waje da ƙyar take jan numfashi dauriya kawai take bata son abinda Abeed ɗin ke mata... tana gaba yana binta a baya hannunsa zube cikin Aljihu da tayi tafiya sai ta tsaya, tsaki yaja kawai ya sunkuya tare da ɗaukan ta yyi gaba Mutane suka bisa da kallo, Idanunta ta runtse kawai amma wannan abin kunyar har ina, bai sauke ta sai a baƙin ƙofar shiga cikin room yana sauke ta, ta murguɗa masa baki bai kulata ba ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga, Dr Adyan na tsaye ya gama haɗa komai ganinsu kuma ya sanya yace "Sannu, Sara" da mmki Sara take kallonsa jikinta har rawa yake wajan ƙara sawa inda Dr Adyan yake tace "Dr ka gano inda yake? Please faɗa min dan Allah ka faɗa min ka samu labarin inda yake?" Dr Adyan ya ɗan saci kallon Abeed, kafin yace "Be patient Sara" Sara tace "Wanne irin be patient Dr? Shekara nawa? Ban taɓa tunanin zan sake ganinka ba number daka bawa Daddynmu baya tafiya dan Allah ka tausayi na ka faɗa idan kasan wani abu game dashi" Abeddeen dai na tsaye fuska ɗaure idanunsa akan Wayarsa yana dannawa, girgiza kai Dr Adyan yyi yace "Ba wani information, amma soon zamu samu nasara ina ta bincike" baya tayi ta zauna saman bed Sbd jin ciwonta na dawowa sabo, kasa magana tayi sai kawai ta kifa kanta a cinyoyinta ta shiga rera kuka ƙasa ƙasa, taɓe baki Abeed yyi tare da juyawa ya fita ya jima a waje lokacin daya dawo tana kwance tana bacci drip maƙale a hannunta, zama yyi kan kujerar dake kusa da ita idanunsa akan fuskarta data faɗa, ya daɗe yana kallonta kafin ya kama left hand ɗin ta, hannunsa ya saka cikin Aljihu ya zaro wata box mai masifar kyau, buɗe box ɗin yyi wani silver gold ring ya bayyana mai kyau sai sheƙi yake, ga wata ƴar blue ɗin danja sai kuma rubutu da aka sanya kalmar _Absar_ yatsarta ya kama tare da sanya mata, ring ya wani kama hannun sosai yyi mata kyau sakinta yyi da sauri, shifa babu soyayya a lissafin ƙaddararsa bawai mancewa yyi ba, kawai dai ya siyi Ring ɗin zai bawa Naila sai kuma ya bata shi domin itace kusa dashi a yanzu ba Naila ba.... Sai bayan sallar Asr Sara ta motsa daga baccin daya ɗauke ta, a hankali ta shiga buɗe Idanunta ganin babu kowa room ɗin ya sanya ta mayar da Idanunta ta rufe da kuma sauri ya buɗe tana ƙoƙarin tashi ya turo ƙofar a hankali tare da shigowa sai Dr Adyan ya biyo bayansa da alama gaba ɗaya daga Mosque suke ganin yadda take ƙoƙarin tashi ya sanya Abeed nufar inda take yana zuwa ya zauna tare da sanya hannunsa akan shoulder ɗinta a hankali ya mayar da ita kwanciyar yana kallon yadda ta haɗe fuska yyi mata banza, Dr Adyan yace "Sannu, ya kike jin jikin" tana haɗe rai kamar ba zatai mgn tace "Better" ya jinjina kai yace "Ki daina zama da yunwa ok" kafin ya hankali Abeed da idanunsa ke kan waya yace "Za'ai mata injection sai ku shige" gaban Sara ya faɗi a fili tace "A'a ban so" Dr Adyan yace "Ai aman zai taso maki dole sai anyi maki" ƙoƙarin sauka take daga kan bed tana faɗin "No, thank you am feeling much better" hannunta Abeed ya riƙe yana kallon Dr Adyan yace "Bisimillah" ya faɗi hakan yana riƙe da hannunta Sara tace "Ka sake ni bana so, dole ne? Ni banso Allah" Dr Adyan dai na tsaya yana kallon ikon Allah Abeed ya fisgo hannunta gaba ɗaya tayo baya saboda bata da wani ƙwari zaunar da ita yyi akan cinyarsa, a hankali ya sanya hannunsa tare da juyo da fuskarta zuwa nasa yace "Zaki sha mmki idan baki tsaya ba" ya faɗa yana ƙara riƙe ta kafin ya kama hannunta ya riƙe idanun Sara ya cika da hawaye ta shiga turesa tace "Wlh ban so, daman kai mugu ne mene haɗi na dakai kake tayi min mugunta" ta faɗa tana dukan ƙirjinsa sakar mata nauyin sa yyi baki ɗaya yana ƙara kwantar da kanta bakinsa daidai kunnanta yace "Shiiiittt...." Da idanu yyiwa Dr Adyan mgn akan yyi mata, wani ihu Sara ta saka lokacin da Dr Adyan yyi mata allurar da sauri ya saketa tare da bar musu ɗakin, wani kalar ihu take da kuka ta shiga birgima akan bed ɗin, wani cute smile Abeed ya sauke ganin da gaske bata son allurar shima kuma ba wani so yake ba, sunkuyawa yyi ya sunkuceta tare dayi sama da ita yana sakin Murmushi yace "Shiit, am sorry Sahraah.." ya faɗa yana zama da ita akan bed ɗin bata ko kulasa ba sai kuka take tana ƙoƙarin sauka daga jikinsa, fuskarta ya kama a hankali tare da manna fuskarsa a saman nata, saukar bakinsa da taji a a cikin nata ya sanya cak ta tsayar da kukan nata, Idanunta wanda sukai jaa sosai ta buɗe suka haɗa idanu ya lumshe mata idanu tare da buɗewa alamar _“Begen”_ gaba ɗaya Sara neman kukan tayi ta rasa sbd fargabar jin abinda Abeed ke mata,bata san mene yake damunsa a yanzu ba, gaba ɗaya ya sauya, yatsarsa guda ɗaya ya sanya a daidai wajan allurar ya shiga murzawa kaɗan, still kissing her wani kalar kiss ya kewa lip's ɗinta, ƙoƙarin ƙwace fuskarta take amma ta kasa da sauri ta sanya hannunta tare da riƙe waist ɗinsa tana rufe idanunta tana jin yadda yake shan bakinta tamkar ya samu chocolate ɗin daya saba sha a kullum... Sara bata sare da al'amarin nasa ba sai da taji saukar tongue ɗinsa a saman Idanunta a hankali yake bi yana tsotse all hawayen dake zubu mata, sai daya shanye hawayen tass kana ya zame fuskarsa a hankali tare da ɗago ta ya zaunar da ita sosai magana ya ke son mata amma ya kasa dan haka kawai sai ya ɗauke ta baki ɗaya ya nufi waje da ita, Sara sbd kunya kamar zata zunduma ihu haka ta keji, har mota ya sanya ta kana ya zauna wajan driver yana ƙoƙarin tashin motar wani securitie ya kwankwsa musu glass ɗin motar, a hankali ya zuge glass ganin mutumin a side ɗin Sara ya sanya Abeed ya kafe securities ɗin da idanu yana jiran yaji me zaice, securitie ɗin ya kalli Sara yace "Kece Sara Salman?" Sara ta waro idanu waje sbd jin sunan daya kirata dashi,kai ta ɗaga masa ya miƙo mata wata rose mai kyau red and white sai ƙamshi take sosai, gefe guda na rose ɗin farar paper ce da zanan heart sai hoto nan mutane biyu mace da namiji suna rungome da juna, yana bata yace "Wani yace na baki" har zatai magana sai kuma ta amsa a hankali ta shiga ware paper ƙirjinta ne ya buga ganin abinda yake jikin paper.
_Zan iya bada Rayuwa ta a kanki SARAHH, ba iya kidey ba, dake nake kwana nake tashi i wish my dream to come true_
Fita tayi da sauri daga cikin motar jikinta na rawa tace da securitie "Please waye? A ina yake zaka iya gane sa, shi nake nema tsayin shekaru" securitie ya watsa hannu yace "I have no idea, kawai ya bani ya tafi fuskarsa a rufe" dafe kai tayi hawaye na neman zubu mata, Abeed dake cikin motar yaja tsaki yace "Ke zan tafi" motar ta buɗe ta shiga tana shiga ta kifa kanta a cinyarta ta shiga rera kuka, tana jin zuciyarta babu daɗi abu goma da ashirin yyi mata yawa, har suka isa gida bata daina kuka ba, a hankali Abeed yyi parking tana ƙoƙarin fita yace "Wait..." Banza tayi masa ya daka mata tsawa yace "Am i your mate? Da ina mgn zaki min banza?" Ɓata fuska tayi tace "To me zan maka?" Tsaki yaja yace "Who is he?" Ta waro idanu tace "Wa?" Yace "ban sani ba" tai shiru can kuma tace "I don't even know his name bare ganin fuskarsa" Calmy yace "kuma hadda kuka?" Kallonsa tayi tace "Shi fa ya ceci rayuwata ya bani kyautar kidney ɗinsa" yace "And so what?" Tace "Noting,kawai ina son ganinsa ne, i have looked for him babu labari Daddy na da duk ƴan gidanmu shine yazo naga Dr kuma shine yyi min aikin gashi kuma yanzu ya bani wasiƙa with rose ke nan shima nema na yake" Abeed ya taɓe baki yace "Out..." Fita tayi tana ɗaukan rose ɗin jikinta babu Kwari ga fargabar abinda zata faɗawa Anuty Zulfa, tana fita daga motar Abeed ya kifa kansa a string motar yana dafe ƙirjinsa dake masa zafi kamar zuciyarsa zata fito waje.**36**Fitowa Abeddeen yyi daga cikin motar a hankali yake tafiya cike da nutsuwa da kamewar nan tasa a ko da yaushe,
Yana shiga cikin parlon ya ganta tsaye kanta a ƙasa sai kuma Anuty Zulfa dake zaune kan kujerar hannunta riƙe da ipad, idanunsa ya juya kaɗan sai kuma ya juya a hankali, Anuty Zulfa dake zaune tace "Ina zaka? U have to stay..." Cak ya tsaya daga tafiyar kafin gently ya nemi saman Kujera ya zauna tare da harɗe ƙafarsa, Anuty Zulfa tace "Magana nake kina jina?" Sara tayi rau rau da Idanunta murya can ƙasa tace "Mami hospital aka kaini dg schl" Anuty Zulfa tace "Hospital? Ke dawa?" Sara dai ba tace komai ba can dai Anuty Zulfa taja tsaki tace "Ba kijin magana, matsa a kai na" kamar jira take da ɗan ragowar ƙarfin ta, tayi saurin shigewa bedroom ɗin su, Auta ta gani zaune tana waya tana ganin Sara tace "Yawwa, she's back Yaa Yarima" daga can cikin wayar Yarima Yashim dake zaune cikin gidan da yake sanye da farar jallabiya mai kyau hannunsu riƙe da coffee yace "Bata wayar" Auta ta miƙa wa Sara wayar, a hankali Sara ta nemi waje ta zaune jikinta duk yyi sanyi, jin yadda Yarima Yashim yyi shiru ya sanya a cikin nutsuwa tace "Ina yini?" Shiru yyi mata kwaɓe fuska tayi sosai tace "Ina yini Yaa Yashim?" Shiru yasa keyi da alama yau sarautar na kansa shima kamar zatai kuka tace "Ko baka ji ne?" Wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke Calmy yace "How was your body, Sara!?" A hankali tace "Da sauƙi" a hankali Shima yace "G.w.s sweetheart" shiru ya biyo baya kafin Yace "Kinci abinci?" Ta girgiza masa kanta yace "I see...eat first I'll calling later" bai tsaya jiran mene za tace ba ya kashe wayar, shiru tayi bata san adadin son da Yarima Yashim ke mata ba, itama kuma bata ƙinsa amma what about the secret lover? Idanunta ta rufe kaɗan kafin ta miƙe ta shiga zame kayanta a hankali ta shige bathroom bayan ta haɗa warm water..... Anuty Zulfa takalli Abeed sosai kamar me nazari kafin tace "What's wrong with you?" Fararen idanunsa ya ware sosai ga wani ƙamshin Spraymintt mouth freshener dake fita daga cikin bakinsa, a nutse cike da nutsuwa da kamewa yana wani rufe idanunsa sosai a hankali cikin golden voice ɗinsa yace "Uhm.." Anuty Zulfa tace "Baka ƙarya ko zaka fara yanzu ne? I'm asking you meke damunka" a lokaci na farko Abeed ya marairaice fuska tare da langwaɓar da kai yace "Mami me nayi to?" Harararsa tayi tace "Are You answering my questions with a question Abeed?" Shiru yyi mata tace "Kana shan maganin ka?" Ya girgiza mata kai tace "To why?" Kwaɓe fuska yyi calmly yace "Mami, ba naji sauƙi ba?" Tace "Shiyasa gashi nan kake ramewa sbd samun lafiya, and wannan jan idanun na mene?" Shidai shiru yyi mata can ya miƙe zai fita tace "Anjima jirgi na zai tashi zuwa India, akwai wani abu da zamuyi na likitoci, 2days zanyi Abban Auta baya gida U can come and stay with my children..." Kai ya ɗaga mata kana yabar gidan ta bishi da idanu tace "Ji banza, mutum ya sauya kamar me damuwa a zuciya" Auta dake tsaye tace "Mami kika ce 9ja zaki, why yanzu kika cewa Yaa Abeed India zaki?" Idanun Anuty Zulfa akan ipad ɗinta tana Research na abu tace "zuki matse baki na Auta" Auta tayi dry tace "Kai Mami, dan ki siyo mana Gucci shoe and bags masu kyau da Expensive Glasses and Abaya" Anuty Zulfa tace "To duk kawo kuɗin a Monthly ɗin da Abbanki yake bayarwa" Turo baki Auta tayi tace "Mami iphone 13 pro max zan siya fa" shiru Anuty Zulfa tayi mata domin tasan halin Auta da Shegen surutu....Sara ta shirya cikin Ripped top designers da Cropped trousers mai ɗan faɗi sai wata Harry styles ɗin bandana data saka saman sumar kanta wacce Anuty Zulfa ta kunce mata kalbar kanta, sai ƙamshin Valentino take, ta ɗan ji sauƙin jikin ba kamar ɗazo ba, fitowa tayi ƙafarta cikin Slippers hannunta riƙe da wayar Auta, kallo ɗaya Anuty Zulfa tai mata ta ɗauke kai tace "Je kiyi lunch ki same ni a part ɗin na" Sara da gabanta ke faɗuwa tace "Mami am full..." Anuty Zulfa ta miƙe tsaye tace "Idan kinci ki amayar" tana faɗin hakan tabar parlon, ba dan taso ba ta nufi dinning area Liver sauce ce da supergetti sai haɗin salad, a hankali ta shiga tura abinci kaɗan taci ta ɗauki yankakkon fruits ta fara ci, ita daman tafi shan su yafi mata daɗi sai Madarar mai kyau mara miss, tana cikin shan Madarar Auta tace "Sara gobe ne walimar yau ba'ai ba, sbd wasu basu gama exam ba" jinjina kai Sara tayi Auta tace "And you know what? Someone send you a gift ɗazon nan..." Sara ta ware idanunta sosai da mmki ba tare da tace komai ba, miƙewa tsaye tayi ta nufi part ɗin Anuty Zulfa lokacin Tana zaune tana operating system gaba ɗaya tayi busy, amsa Sallamar Sara tayi Sara ta nemi waje ta zaune kanta a ƙasa Anuty Zulfa ta ɗauki wata ƙaramar bag mai kyau an rufe ta da wani abu mai ƙyalli miƙa mata tayi, ganin Sara bata amshi bag ɗin ba yasa Anuty Zulfa ta kalleta tace "Kike zare min idanu amshi mana" Sara ta amsa tace "Thank you, Mami." Anuty Zulfa tace "A'a babu ruwa na, kiji gulma bayan kin san ko waye ya baki" Sara tai shiru can kuma tace "Mami ban sani ba" tace "jeki duba" tashi tayi a hankali tayi waje kai tsaye kuma bedroom ɗinsu ta shiga, lokacin wayar hannunta tana ta ringing ganin sunan Yaa Yashim ya sanya ta ɗaga kiran a hankali tace "Hello.."